Skip to content
Part 12 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ranar Juma’ar ina tasowa daga Makaranta ko gidan Umma ban biya na ci abinci ba na dawo gida da nufin in yi wanka in yi kwalliya tukuna don ta ganni fes.

Na gama wanka na shafa maina wanda shima Yaya Dijan ce ta bani shi, na shafa hodata na jawo akwati da nufin zaban wanda zan saka sai kawai kaya suka ce dauke ni a inda ki ka ajiye ni.

Kuka sosai na kama yi kafin naje na kai maganar gun Babana, Babah Lantana tana ji ta ce wannan shi ne sharri da ki ka kawo wa ki ka nunawa? Kin nuna min? Na girgiza kai, kin nunawa Babanki?

Na sake girgiza kai, to ai ma ba haka a ke sharrin ba, in ma ita ta koya miki in kin zo ki kala mana sata to bata koya miki daidai ba.

Ta wuce ta taf ta bar ni ina kuka, Babana kuma yana yi min fadan yadda aka yi aka bani kaya nazo na ajiye su ba tare da su sun taya ni murna ba, bakin ciki ne ya ishe ni na fita na tafi gidan Umma naje na gaya mata.

Ita kam bata musa ba, hakuri tayi ta bani ta kuma bani abincin da ta ajiye min na ci na koshi, sannan ta kawo wata atamfa ta ba ni ta ce in yi kwalliyar Juma’ar da ita.

Sannu a hankali sai gidan Umma ya zame min gida na saki jiki sosai da ita ta zame min tamfar uwa babu abinda bata nuna min na hidimar rayuwa.

Hatta wankan al’ada ita ta koya min shi sosai na iya, ita ce kuma ta fahimtar da ni na gane ita al’ada ba laifi ba ne ba kuma abin kunya ba ce.

Sai dai mutunta kai ne ka tsare ta in kana yinta kayi ka gama ba tare da wanda ka ke tare da shi ya gane ba, ita Umman ce ta fahintar da ni cewar dabi’a ce ta cikar halittar mace.

Tun daga nan ne na gane na ma daina yin kuka, in na ganta tazo min. ina zaune da Umma masa nake ci cikin sauri saboda tsoron da nake ji na kar in yi lattin makaranta.

Sai ga Alhaji Mahammadu ya shigo har wajen kicin din yazo ya tsaya, yana kallonta ni ina ki ka samu yarinya ne? Yayi mata tambayar bayan ya anmsa gaisuwar da nayi mishi. Yarinyar nan ne yar gidan Mallam Habu mai Tumatir, nan da nan fuskarshi ta kara daurewa, dama kuma ba mai yawan fara’ar ba ne.

Ba ku rabu da ita ba ke nan kamar yadda ubanta ya ce ayi? Cikin natsuwa ta ce, ubanta ai ba a ta tashi Alhaji, da sauri ya tambayeta, sai tawa? Tayi shiru bata bashi amsa ba.

Mutum da ‘yarshi ki ce ba a ta tashi, sai ta wa? Wane zancen banza ne wannan? Marainiya ce Alhaji, Umma tayi mishi magana cikin murya mai taushi da nuna girmamawa, yayinda nake bake can gefe cikin rawar jiki saboda yanayin fuskarshi da kwarjininshi.

Duk abinda aka yin sharrin matar gidanne, ba ka ga yadda  yarinyar nan ta koma ba, bayan rabata da Ahmad Mubarak da aka yi shi yasa na dawo da ita.

Macce ce rauni ne da ita ga shi kuma ta fara girma, in wahala tayi mata yawa abin ba zai yi kyau ba, yunwa ai musiba ce kuma bayan mu muke dubawa tare da rokon Ubangiji ya tsare mana su.

A hankali ya ce, To amin. Alamar dai ya sauko har ma ya gamsu da kalaman matar tashi.

Wuce ki tafi makaranta Maryamu in kin dawo ki biyo ta nan kar fa ki ki zuwa na ce mata to, har na wuce zan tati ‘sai naji ya ce mata in da canji nan wurinki bata sule biyu ta ce mishi eh akwai, ta miko sule biyu nasa hannu biyu na karba tare da yin godiya, na kama hanyar fita ina jinta tana yi mishị karin bayani a kaina, har da Innata.

Da yamma ban ki biyowa ta gidan ba ina dawowa ta bani abinci na zauna ina ci, ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min kin ga ma Babanku dazusai yace min kullum in ki ka zo tafiya makaranta in kin karya in ba ki sule biyu ki rinka cin abinci a makaranta, na ce mata to na gode.

A wancan lokacin da nake magana akai sule biyu kudi ne masu daraja saboda sule goma ne a Naira guda daya, yayin da ita Nairar take daidai da dalar Amurka.

Don haka sule biyu kudi ne tunda kuma ina cin abinci in koshi a wurinta in zan tafi in na dawo ma kuma za a samu in ci in koshin, sai ya zamo ko ta bani sule biyun ba na karba sai in ce bar su kawai Umma, wata ran kuma in karbi sisi, wato rabin sule daya ko kuma in ce kwabo biyar, ban sani ba ko ganin hakan da nake yi ne ya sanya ita Umma fara yi min banki a wurinta.

To Hausawa suka ce wai yau da gobe bata bar komai ba, ana tafe a haka sai ga shi har mun gama aji uku mun kammala jarrabawa muna cikin hutun da zamu shiga (SS1), ko kuma aji hudu na Secondary a takaice dai na shiga Senior Section.

Haka nan da ki, da so, da wahalar da komai da lokacin girmana yazo sai na girma saboda Hausawa sun ce wai in rana ta fito to tafin hannu kuma bai kare ta.

A wannan lokacin na zama ba Asabe ba, hatta Babah Lantanar na kere ta a tsayi, haka nan duk da a hakan ma ban wuce a dake ni ba, amma dai nayi matukar rage jin tsoronsu da nake yi tun ma ba na Asabe ba wacce kuma dama ita ce tafi kowa takura min ko dan maina Umma ta saya min a cikin kudina sai ta dauke min ko ta kawo wata kwalbar ta juye shi.

Ana cikin haka Mubarak ya dawo daga hidimar kasar da ya tafi Ibadan, ni da shi ba ma kula juna, ganin da nayi ya ganni bai nuna wata alama ta zai kula ni ba, yasa nima nayi kamar ban ganshi ba.

Sai dai hakan bai sa na daína shiga gidansu in yi hidimomina da Umma ba, saboda na riga na kudurawa raina babu abinda zai sa in sake dauke kafa daga zuwa wurin Umma, matukar ina raye a cikin hayyacina.

Don haka shiga gidan nake yi yana kallona ina kallon babu mai cewa wani ci kanka ita kuma Umman bata taba nuna ta gane abin da ke faruwan ba, balle ta tàmbayi dalilin hakan zuba mana ido kawai tayi.

A wannan lokacin zama tsakanina da Asabe ya matukar baci, saboda muna iya wuni mu kwana tare a daki daya babu wanda ya ce wa wani ci kanka.

Muna cikin hakan ne kawai na dawo daga wurin Yakumbo Halima na samu Asabe ta tsala  kwalliya cikin sabuwar atamfata da Umma ta dinka min su kala hudu.

Cikin natsuwa na kalleta na ce Asabe wannan ai tana cikin sababbin atamfofina da na karbo daga wurin dinki.” Wacce? Na ce wannan ta jikinki tunda gama botin rigar nan da na sayo da hannuna.

Eh ai na san taki ce aro na dauka ta zancen nata, na ce To gaskiya ban yarda ba cire min ita kawai tazuba min ido tana yi min wani irin kallo baki yarda ba fa ki ka ce? Na ce eh ban yarda ba ina ce tawa ce? Ba sai ki cire min ba kawai ni da kayana?

Ai, ke nan babu damar a ari kayanki ke ba kya aron na mutane? Babah Lantana tasa ba ki cikin maganar ban ji nauyinta ba na ce in na ari na wani ya kwace kar ya bar min shi ni dai a cire min nawa kawai.

To ba zan cire ba tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina ba mutane amsa.

Na ce gaskiya sai kin cire ban yarda da aron ba tunda ai ma ba ki tambayen ba in ban da na ganta a jikinki kuma da ba za ki dawo min da ita ba.

Me ki ke nufi da wadannan maganganun naki? Abin da nake nufi ke nan ana diban kayana ba da sanina ba ana salwantar min da nayi in na yi tambaya a ce na kalawa wani sata.

Ko rannan ai nayi miki cigiyar doguwar rigata ta shadda ki ka ce’ rainin hankali ne ya na tambaye ki ita shekaran jiya kuma sai muka yi kacibis ni da kawarki Nuriya da rigar a jikinta da na tambayeta in da ta same ta ta ce min canji ku ka yi ke da ita ki ka bata wannan.

A fusace kwarai Asabe ta tambayen ke me kike so ki ce min na yi miki sata ko kuwa me? Na ce Oho ko ma a me ki ka fassara shi daidai ne, tunda kin daukar min kayana na tambaye ki kin ce ba ke ce ba ce nazo na gani a jikin kawarki da ta ce ke ki ka bata yanzu kuma ga wata na gani a jikinki kin dauka bada izinina ba kuma da kina so kiyi musun ba tawan ba ce.

To ba ki da abin da zan .satar miki bari in gaya miki, to sau nawa? Ta tambaye ta cikin yanayin da ya kara fusatata.

Taja wani mummunan tsaki ta wuce wai zata fita tayi tafiyarta, nayi maza na kama gefen zanin da ke daure a jikin nata na rike ai babu in da za ki da kayana a jikinki.

Riketan da nayi ne ya zama dalilin da ta juyo cikin hanzari ta rufe ni da duka, nima nayi maza na maida martani don haka dambe ya kaure a tsakaninmu.

Kamar kullum yau ma Asabe ce mai galaba a kaina a damben. Sanin da nayi babu mai raba mu daga Sallau da ke zaune a gefe yana Kallon abinda ke faruwa har Babah Lantana da taci gaba da harkokin aikinta tare da fadin, a to ai dama ke ki ka barta ta raina ki, yasa da na ji zata azabtar dani azabar da ta wuce ka’ida na same ta na gantsara mata cizo da iyakacin karfina.

A gigice kwarai ta kurma ihu mai tsananin firgitarwa nan take kuma ta sake ni.

Da gudu nayi nufin fita in bar gidan, caraf Sallau yasa hannu ya rike ni, saboda umamin da Babah Lantana ta ba shi na kar ya bar ni in fita.

Ina ganin yayi nasarar kama ni na soma kurma ihu mai tsanani tare da kiran sunan Babah Sumaye, ina rokon ta kawo min agaji, duk da nasan ba zai yiwu ta shigo ba saboda wani rikici da ya faru tsakaninta da Babah Lantana a kan dukan da Asabe tayi min.

Maganar har takai Babana ya shaiga ciki ya kuma nuna 6acin ranshi kan keta haddin gidanshi da a ka yi a ka shigo har cikin gida a ka yi fada da iyalinshi.

Yana fadin haka Baba Baidu ya ba shi hakuri ya kuma yi mishi alkawarin Sumaye ba za ta sake shiga gidanshi tayi wata magana ba.

Sumaye! A’a Tasallah, Babah Lantana ce mai wannan maganar kafin ta koma fadin “Tafdijan! A nonuwa ki ka cijeta? Ki rasa inda za ki cijeta sai a nono don sharri da mugunta?

To ai kuwa sai ta rama. Rike min ita tamau, Asabe ta rama wannan sharri da tayi mata, ta sake yi wa Sallau bayanin.

Tashi ke kuma shashasha ji yanda ki ke bari sai ka ce wacce a ka gutsurewa nonon gabadaya, zo ki daidaici inda tayi miki ke ma kiyi mata.

Asabe ta iso gaskiya ne har lokacin jikinta yana rawa, alamar ba karamar wahala tasha ba.

Tun kafin ta dora bakinta a kan nonon nawa don rama cizon da nayi matan na saki. fitsari a tsaye, saboda tsananin tsoratar da nayi da abin da ke shirin samun nawa.

Wayyo! Wayyo!! Abinda kawai nake iya fadi kenan, yayin da zuciyata ke ta neman taimako wurin Ubangiji.

Rike ta da kya inin rikon da ba za ta kubuce mata ba, shi kuma yayi maza ya sake damke ni a hannunshi irin rikon da a ke yi wa kazar kuku.

Sai kuma ta juyo tana kallona ai daga yau ba za ki sake cizon wani ba a rayuwar…ba ta kai karshen maganar tata ba sai ga Mubarak ya shigo gidan a guje.

Kan ka ce meye wannan har ya kirbe Sallau da wani irin gigitaccen naushin da ya kifar da shi a kasa, nima na fada can gefe saboda hantsalawar da nayi.

Shigowar da Mubarak yayi cikin gidanmu da gudu yayi dalilin da mutane da yawa suma suka shigo saboda sun dade suna jiwo ihun da a ke yi daga cikin gidan.

Tankam gidan namu ya cika da Jama’a, sai dai kuma cikar da aka yin bai hana Sallau shan dukan tsiya a hannun Mubarak ba, saboda babu wanda ya koma takan yin rabo.

Da gudu Babah Lantana ta suri tabarya tayi kan Mubarak zata rafka mishi ita, samari suka yi wuf suka café ta suna fadin.

“Haba Babah, haba Babah, da girmanki ki bugawa mutum wannan a ka? Wannan ai ya zama kisan kai ko kuma ta’addanci, ai rabo ne yafi dacewa da ke.

Babah Lantana sai ihu take yi tana fadin an shigo mata har gida ana so za a kashe mata da, ana cikin haka sai ga Babana ya shigo ban san wanda yaje ya gaya mishi ba.

Bakin ciki mai yawa ya bayyana a fuskarshi saboda tsananin baccin da ke tare da shi duk ku fita ku ba ni wuri. Yayi maganar cikin natsuwa nan da nan kuma a ka yi ta fita.

Babah Lantana tana ganin haka ta soma rusa kuka mai tsanani tana fadin “An keta mata haddin cikin gidanta an keta mata haddin aurenta, an shigo har cikin gida an ci mutuncin iyalanta sakacin Babana yasa duk unguwar nan babu mai jin shakkar shigowa cikin gidan shi yaci mutuncin matarshi.

Duk wadannan kalaman da Babah Lantana ke furtawa Babana yana jin ta bai ce mata kala ba, bai kuma cewa kowa ci kanka ba, illa iyaka dai da gari ya waye sai ya zartar da hukuncin da ya ke ganin shi ne daidai a wurinshi.

Mu bi Maryam Abubakar cikin littati na biyu, mu sake shan wani labarin, kafin nan ina yi

muku fatan alheri.

<< Halin Rayuwa 11Halin Rayuwa 13 >>

1 thought on “Halin Rayuwa 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×