Littafi Na Biyu
Washegari da safe gaba daya mutanen gidan kowa a cikin natsuwarshi yake, in ban da Babah Lantana da ke ta faman zirga-zirga tana fadin maganganu kamar yanda dama al’ adarta take in har wani abu ya bata mata rai.
Haka kawai a cizan mun yarinya sannan wani kato ya shigo har cikin gida ya Dakar min yaro, to wane irin rashin yanci ne wannan? Ai kayi hukuncin da za ka yikawai in gani. Lalle ne kuma kayi hukunci me tsanani don in ba haka ba kam…
Sai tayi kwafa tare da fadin “Hanya ratatata nuna alamar abinda zai farun ba karamin al’amari ba ne.
Koda Babah Lantana bata furta irin wadannan kalaman ba zan kasance ne a cikin natsuwata sosai don na saba jinta tana bada umarnin a rama cizo ko da kuwa bayan shekara guda ne, to balle ni da nayi cizo jiya, cizon kuma ya haifar da sakamako mai tsanani don daga Asabe har Sallau babu wanda bai samu kanshi cikin wani hali ba matsananci.
Asabe dai tana kwance tana fama da matsanancin zazzabi, Sallau kuwa bai iya rufa bakinshi ya daina kurma ihun da yake kurmawa ba, sai da aka kira Mallam Bahago yazo ya gyara mishi targaden da aka yi mishi a kafada.
Don haka sanin a nayi Babana yana cikin gidan nan dai shi ne abinda ya zaunar dani a cikinshi da kuma ganin Asabe a kwance tana fama da kanta nasan a haka ba za ta ce zata rarume ni don ta rama cizon da nayi matan ba, amma duk da haka ina ganin Babana ya dauki kwandon tumatirinshi da nufin fita.
Nima zan yunkura in bar musu gidan don ba zai yiwu in 2auna tare da su ba tunda nasan zama da su din ba zai haifar min da da mai ido ba.
Ina cikin wannai tunanin ne na bango Babana tsaye a tsakar gida rike da kwandon tumatirinshi a hannu alamar zai fita kenan nayi maza na jawo gyalena kusa da ni, don yana fita in bi bayanshi sai kawai naji ya ce ing Yaacuwuna take?
Nayi maza na ce Gani nan Baba, na fadi daidai lokacin da na tsuguna a gebanshi, karki sake ki fita daga gidan nan. Gabana yayi mummunan faduwa, “Kin ji na gaya miki ko ba kiji ba?” cikin sanyin jiki na ce mishi naji Baba.
Na mike tsaye jikina a sanyaye na koma dakin na zauna na jawo littafina na karatu ina dubawa sai dai gabadaya hankalina ba a kan shi ya ke ba.
“Kai Sallau!” Sallau ya yunkura ya fito gani Baba, shirya ka bar min gida ka koma inda dama kake, tunda ka zo kana yi min fada a gida shima wancan din na aika a gayawa Babanshi ya gaya mishi kar ya sake shigo min cikin gidana.” Yanagama fadin hakan yasa kai ya wuce zai tafi.
Babah Lantana ta bishi da kallo irin na takaici tare da fadin “A hau, ahau wannan shi ne hukuncin naka? Taja wani mummunan tsaki ta juya taga Sallau da ke tafiya da kyar yana rike da ledar kayanshi a hannu zai bar gidan don cika umarnin da maigidan ya ba shi.
Sai kawai naji ta daka mishi tsawa “Ina za ka da wannan jikin naka? Maza maida ledar nan kayi kwanciyarka ka huta, ai ko za ka bar gidan nan sai bayan kun rama abinda a ka yi muku tukuna.
Cikina ya badasautin kulululuu! Don nasan me maganar tata ta ke nufi Sallau ya koma daki yayi kwanciyarshi yayin da ita ma ta koma kan hidimominta da maganganun da take ta yi.
Ana cikin haka ne naji wata irin murya tayi sallama a bakin kofar shigowa tsakar gidanmu.
Muryar ta mata amma abin mamakın shi ne da sunan maza naji Babah Lantana ta kira bakuwar.
“Nalami ne kuma har cikin gida ba za ka tsaya daga waje ka ce ayi maka iso ba? Yayi ‘yar Shewa tare da ‘yar dariya kafin ya ce “In ba kiyi min haka ba ai ba ai ba ki cika ‘yar halak ba, ai ba zan ce kin amsa sunanki na Butulu’ ba ko ba sunan da dama yan gidanku suke kiranki ke nan ba? Butulu ai dama kazo ne har gidan mijina ka ci mutuncina?
Yayi maza ya ce “A’a ko kadan ai darajar aure ya shige haka komai iya shegenka in har ka samu ka shiga karkashin inuwarshi to ka zama mai mutunci sai a mutuntaka saboda darajar shi, don haka ba zan ci mutuncinki a gidan mijinki ba.
To tunda ka fadi haka da bakinka muje daga waje, ya ce a’a nan kuma daya a nan din nan zaan zauna bau ce zan shiga dakinki ba balle kiyi tunanin zan hau kan gadonki in kina tsoron kar mijinki ya shigo ya ganin ne babu komai yana shigowa sai in gyara zama in maida kaina kanin Babanki in kuma ki ka ce za kiyi min iya shege to kema kin san ni Babanki ne a nan ma.
Ina iya zuwa har wurin zaman nasu in yi komai, ai ta can na biyo an nuna min shi,don haka dauko tabarma kawai ki shimfida min.”
Ta kawo tabarmar tana shimiidawa yayinda ni kuma zuciyata ke ta faman kai-kawo a tambayata wane irin mutum ne wannan? Na yunkura na matsa na kebe ta matsin kyauren dakin namu mutum har mutum yasha babbar riga har da hula zanna sai dai kalamanshi.
“Ashe har mazaunai ne da ke haka? Ya yi tambayar daidai ya kaiwa mazaunan nata duka gabana ya sake faduwa, tayi maza ta kara daure fuska kafin Nalami ba ka da mutunci ya gyara zama kan tabarmar ya ce, Eh komai ma kina iya gaya min ni na zo. Ta ce to ka tafi mana ko ni na kira ka?
Ya kalleta a’a ba ke ba ce ai kin samu wurin zama sai cin mutuncin Jama’a ki ke yi ja’ ira kawai mara tuna baya, kai bebi baki da tuna alheri.
“Dakata ka ji Nalami, na daina amsa wannan sunan duk wani abu makaman cin wannan da ka sani na daina shi, mijina mai mutunci ne. “
Yayi maza ya ce “Gaskiya kam gaskiya kam ai na ganshi ruwan Malamai ne da shi inda tambayar take dai na yanda aka yi ya iya zama da ke ne.”
Ta zuba mishi ido cikin takaici ai ba za ka bari muyi magana ta gaskiya ba ke nan? Ya tsura mata nashi idanuwan da suka fi kama da gauta saboda kaduwarsu kafin ya ce ai ba ki da ita ne, gaskiyar balle ayi maganarta da ke. Ta gyada kai tare da fadin to shi ke nan naji me ya kawo ka?
A haka zan fara magana ina zuba tun ban ci komai ba? Ai sai ki kawo min danashar kajin da a ka bani labarin kullum a ka zo’ gidanki sai an ci.
Yana cin naman da ta kawo mishi yana Magana zuwa nayi in dangwali arzikinki tunda kin shigo cikin inuwarshi don kuwa nima babu irin taimakon da ban yi miki ba, sanda su sarka suke wulakantaki, ko sanda ki ka haifiyaran nan…”
Tayi maza ta katse shi “Ba fa tarihi ka zo karanta min ba, arziki ka ce ka zo ci.” Yayi maza ya ce, “Eh haka na ce, to kai duk abinda ka ke da shi bai ishe ka ba sai ka zo wurina ni da nake zaune a dakina ko sana’ a bana yi?
To ai ku ne masu rufin asirin amma na wajen nan menene ne a cikin abin? Kin san fa shari’ar nan da a ke ta kafawa ta karya darajar al’amuran namu kana gaba daya ke dai ayi shiru kawai tunda kana Musulmi ba zai yiwu ka buda baki ka ce ba ka ji dadin abin ba.
Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta mika mishi to ungo rike wannan ko sigari ka sha, lokacin ne na tuna farkon zuwan Babah Lantana na gidanmu har sigari sha take ji amma yanzu kam ta daina don na ma manta in ban da yanzu da naji ta ambata da bakinta.
Maimakon ya karba yayi godiya kamar yadda al’adar wanda a ka yi wa kyauta take sai kawai naga ya harari abinda ta ba shin ya ce kyautar matsiyata za ki yi min? Ko da na ce miki ba ni da harka ai kin san nafi Rarfin irin wannan kyautar don kin san ko ni waye?
To in tsaya daga waje mana in yi bara ki bai wa yara su kawo min sadaka, ai a sauwake abinda za ki bani in bar gidannan bakina alaikum jaka guda ne.
Da sauri ta ce mishi a’a buhu guda ba jaka guda ba gaka guda lafiya ce da za ka ce in baka ita ina na ganta? Kai barawo ne? A’a to sai in gyara zama ai sai kin samu, to sai in gyara zama ai sai kin samu to ma me za ki kira ni kuma oho ni dai kin san ba Delu ba ce da ta taimake ki ta rinka yi mii zirga-zirgar gidajen Malamai da ‘yantsubbu bayan irin wahalar da tai tayi miki da ‘ya’yanki.
Sai da ki ka samu kan miji ki ka mallake shi taf ya zama bai da katabus sai naki sannan ki ka yi mata irin tukuicin da ki ka saba yi wa wadanda suka saba taimakonki wanda yayi dalilin da suka rada miki sunanki na ainihi ‘Butulu’ ki ka koreta ki ka ce kar ta sake zuwa miki gidą don ba ki yarda da, ita ba.”
“Ita taje ta turo ka ke nan? ” kan ya bata amsa sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai Maryam ana kiranta a waje.”
Da sauri Nalami ya kalli Babah Lantana cikin yanayin rage murya dama ba mu biyu ba ne a gidan shi ne ba ki gaya min mun yi maganar a hankali ba? Ba ki kyaufa ba La, ai wata kusar tafi wata.
Ai in da ná sani ba zan yi îrin wadannan kalaman wani ya ji ba, na fito zan wuce in je’kiran da a ke yi min ban sani ba ko zaman Nalamin ne ya hanata tuna min da dokar da Babana ya kafa mini ko kuma don taga ita ma bata bi dokar ba ne oho, tunda nasan tafi kowa jin an ce ana kirana a waje.
Ina fitowa muka hada ido da Nalami barin komai yayi ya shiga bina da kallo, wani irin kallo da yafi kama da na kidima, uh’ uh uhhh, wacece wannan Lantana?
Tambayar da naji shi yana yi mata kenan yayin da ni kuma na shige cikin zaure na bar su a nan ban jiwo amsar da ta ba shi ba’ lna daga cikin zaure na hango Mubarak a tsaye daga waje yayi kwalliya sosai.
Karo na farko da ya taka yazo kofar gidanmu tunda ya dawo daga Ibadan, sai ko jiya wannan kuwa naji an ce wai Babah Sumaye ce da taji ihun da nake yi ta aiki almajirinta da gudu yaje ya gaya mishi abinda ke faruwa.
Daga cikin zauren naja na tsaya ban ce mishi komai ba, shi ya matso bakin kofar zauren ya tsaya kina da wata matsala ne? Yayi tambayar yana kallona, na girgiza kai a hankali nuna alamar babu.
Ya miko min ledar da ke hannunshi cikin zauren na mika nawa hannun na karba ya juya ya tafi ba tare da na ce mishi komai ba.
Na koma baya ta cikin lungun zauren saboda jin ledar da nauyi ga kuma sai da na nemi wuri mai dan kyau sannan na zauna na fito da abinda ke ciki, gasasshiyar kaza ce katuwa tayi matukar gasuwa gashin injin ga yaji a wata takardar ga kuma Ruwan lemo na kwali mai sanyi.
Lokacin ne na kara tuna har a wannan lokacin da agogo ya kai kan sha biyu da rabi ban sa komai a bakina ba, da bai zo ya kawo min wannan kazar ba kuma to da ban san lokacin da zan samu abinda zan ci ba, ko a haka kuma Babana yake ganin zan iya tsare dokar da ya kafa min ta kar in tafi ko’ina? Oho!
Ci nayi sai da naga na koshi sannan na dora ruwan lemon nan a kai sannan na mike na dauki saura na nade na adana shi a cikin gyalena, na shiga cikin gida har lokacin Babah Lantana magana take yi da bakon nata, sai dai a yanzu maganar tasu ta dan sauya da alamar sun dan samu daidaituwa.
Yana ganina ya saki wani lallausan murmushi har hakoran Makkanshi suka fito guda biyu, kuma jajaye yana ganin mun hada ido da shi yayi maża ya sakar min signal da idanuwanshi. Nima nayi maza na galla mishi wata irin matsiyaciyar harara na wuce na shiga dakina.
Wasu sabbin kwanukan abincin na gani wurin Asabe da alamun fitan da nayi ya kara bada damar da aka sake kawo mata wani abin.
“Yanzu dai kin gani Hajiýa bani kawai abinda kika ga za ki ba ni tunda ga bayanin da ki ka yi min na halin da kike ciki in an kwana biyu ai zan dawo.”
Da sauri ta ce, “A’a-a’a ni kar ka dawo min gida in ba so ka ke ka kara min wata matsalar ba.”
“A aha, ai ke halinki ke nan ki ka sani ko zuwan nawa na alheri ne? To ta ina zuwanka zai zame min alheri ni kuwa?” ya yi murmushi “Uhum, Babah Lantana kenan, ai na daina kiran sunan naki gatsau sai na sakaya miki shi da Baba ko kuma Hajiya. Ai kin san shi sunan Hajiya ma mai niyya yake nufi.”
“Kai dai karbi amma ni kar ka dawo min gida.”
Ya karba yana kirgawa, ai tunda na ce zan dawo zan dawo din ne kiyi fatan kawai dawowan nawa ya zame miki alheri.” Ya tashi ya tafi.
Ina zaune a gida Babana dokarshi a kaina ni kadai take aiki, Babah Lantana da ‘ya’yanta babu abinda ya shafe su da ya dawo yazo ya samu Sallau a gidan ma bai ce mishi kala ba, sannan da zai kafa min dokar daina fita daga gidan sai ya manta bai sanya ta bani abinda zan ci dole ba.
Duk da haka na bi umarnin da ya banin na in daina fita saboda magnar da Yaya Dijah take yawan gaya min in bi duk wani abinda zai sanya ni komai wuyarshi, kar in ki yi mishi yayya a kai kar kuma in lura da cewar wasa ba su yi mishi ba ni ce ya zama wajibi a kaina in bishi ba su ba.
Ina zaune a haka cikin wani irin matsanancin hali in ba Mubarak ne ya kawo min abinda zan ci ba babu mai bani a hakan kuma ga barazana gami da wulakanci da neman tsokana
Kowane lokaci a cikin maganar ake haka kawai sai ka ci Babah Lantana ta ce ah cizo? Ai sai kin rama a natse za ki rama kara warkewa dai kawai karfinki ya kara dawowa jikinki.”