Littafi Na Biyu
Jinya sosai Tanimu ya kwanta yayi kwana da kwanaki yana yi Babana yayi ta dawainiya da shi, amma tun bai gama warkewa ba sai naji Babah Lantana tana cewa Babana wai yana gani ana nema a kashe mata da a kan matsiyaciyar ‘yarshi, amma ya kame baki yayi gum kamar na mai cin najasa, gum din din dai ya sake yi mata bai ce mata komai ba har tayi ta gaji tayi shiru.
Duk da kudin da nake da su a hannuna rashin Mubarak yasa nayi matukar. takura komai zan yi sai na saya ban saba wannan rayuwar ba, abinda nafi sabawa dashi a kawo min ne don haka kudin da ke hannuna bai hana ni jin yunwa ba, musamman ma da yake wani lokaci ana sayo min in kasa ci, don bai gamsar da ni ba tunda in yana nan ba irin wannan din nake ci ba.
Babah Lantana tayi girki ta raba ta baiwa kowa nashi ‘ya’yanta guda biyu da Babana yayinda ita kuma take zaune a kicin tana cin nata, na mike naje na same ta na ce Babah a bani nawa abincin.
Ta kalle ni a lalace ta ce in ba haka ba fa a kore ni ko a yi ya ya? Shiru nayi na tsaya.ina kallonta, yayin da ita kuma take bayani a nemi kashe min da a kan ki sannan in yi girki in ba ki.ai ba zai yiwu ba.
Daga bayana Babana ya ce min to zo ki dauki wannan nawan kici, na juyo da sauri ta biyo ni tazo ta fige kwanukan a hannuna in gadaranka kai ka kawo ai ni na girka, ni baiwarta ce? Bata danye itama ta girkawa kanta ai mace ce babu kuma abinda bata sani ba wani abin ma ta fini sanin shi.
Wannan magana da Babah ILantana tayi ta in girkawa kaina shi ne dalilin da yasa da gari ya waye nabi bayan Babana zuwa wurin saida tumatirinshi nace ya bani kayan miya, ya zuba a leda ya miko min.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce, to abin da zan dafa fa? Akwai a gida, na ce ba za ta ba ni ba, bai ce komai ba ya ciro kudi ya bani na wuce na shiga shago na sayi taliya guda daya na juyo na kama hanyar zuwa gida.
Ran ‘yanmata ya dade, na jiyo muryar tashi daga bayana na kuma shaidata ta Mansur ce, bàn waiwaya ba na dai ja na tsaya ina jiran isowarshi.
Ai rannan na hango ki kina dawowa daga Makaranta nayi ta daga miki hannu ina haba in babu busa babu daga hannu ne? Sai na lura ma ba ki ganni ba. Nayi murmushi tare da fadin eh, ka kyauta min kwarai da kai da kanka ka gane ganinka ne ban yi ba.
A’a haba ai nasan ba ki da irin wannan wulakancin ke dai kawai ganinki ne yana wuya da yake kin riga kin zama budurwa. Na ce, kai Mansur ke nan, barkwancinka yana da yawa, can cikin zuciyata kuwa mamakin dabi’arshi kanbama ‘yanmatancina nake yi.
Kullum muka gamu sai ya jaddada min ni din budurwa ce ni din mai kyau ce, ni din daban ce da saura, abinda kuma bai taba damun Mubarak ba ke nan. Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin ko Mubarak ya taba gaya min irin wadannan kalmomin? Kai bani tuna ba.
Kar dai a ce rashin lafiya ki ka yi bai sani ba? Na ce eh amma ba mai tsanani ba ne, ya zuba min ido yana kallona, kina nufin abinda yayi sanadin wannan ramar ba ma tsanani ba ne? Nayi murmushi na cé eh, ya ce to kuwa sai muyi ta addu’a kar mai tsananin yazo, na ce to amin.
To mu ba yaran nan ledar cefanen mana don kar mu bata muşu lokaci na ce a’a babu komai cefanena ne, kina nufin ke ce za ki yi girkin da kanki? Na ce, eh, ya ce a’a to shiga ciki kawai ina zuwa, bari in je in kawo cefane nayi maza na ce a’a ka bari.
Ya daure fuska ya ce, to ai ba ke ki ka roke ni ba, na wuce shi da nufin tafiya gida, ya sake biyo ni ran yanmata ya dade, na dan rage takun da nake yi don nasan wata magana yake son gaya min, kina da bukatar wani abu ne? Nayi maza na ce mishi a’a na tafi.
Ina cikin tafiya sai ga Isiyaku da saurinshi, Anti ai nazo ki ka ce babu aika, na ce eh Isiyaku wurin Babana naje na karbo yasa hannu ya karbi ledar da ke hannuna muna tafiya yana bani labarin wahalar ruwan da ake yin da yanda suma matar Babansu ta sanya dokar sai mutum ya ajiye bokitin ruwa goma kafin ta ba shi abincinshi.
Ba ki ga fa inda muke tafiya diban ruwan ba, na ce eb to wata rana ai zai wuce Isiyaku, ya ce haka a ke fada, nayi tunanin shima yana da irin lamarina kenan, da zuciyata ke yi min a duk lokacin da a ka gaya min haka shi ne na in tambayi kaina to yaushe ne wata ranar zata zo?
Cikin gida na shiga shima ya biyo ni duk da yasan Babah Lamtana ta tsani shigar da yake yi cikin gidan kullum ta ganshi a ciki sai ta tambaye shi kai baka san nan gidan, gidan matan aure ba ne ba? Sai ya ce ya sani ya wuce ta yayi abinda zai yi ya fita.
Na shiga cikin kicin, Ta yi maza ta biyo ni, karki shigar min kicin kar ki taba min komai a wurin nan, don ba zai yiwu ni da ke a ciki ba, in kuma ke ma matar gida ce sai ku zo ke da uban na ki gaya min.”
Ban tanka ba nasa hannu na dauko risho tare da tukunya mai murfi, ba na ce kar ki taba min komai ba, na kalle ta na ce, kin gani? Wannan ai na Inna ne, kadan ya rage ta kifa min mari saboda ambaton Inna da nayi a gabanta, ban san yanda a ka yi ba sai kuma naga ta fasa.
To juye min kananzir din ciki ko shi ma nata ne? Naje na juye mata, ina fitowa Isiyaku da ke biye dani yasa hannu biyu ya karba ya bar ni ina neman wani tsohon galan da na san yana nan a cikin kicin din.
Na fito ina kwance bakin zanina da na daure kudina don na daina ajiye su a ko’ina sai a bakin zanin da ke jikina, na zaro abinda zan ba shi ya tafi yaje ya sayo mana kananzir din, na rasa inda zan sa risho din saboda iskar da ke kadawa.
Na wuce naje na kai shi dakina da nufin yin girkin, à can nan ma ta biyo ni dakin ai ba naki ba ne ke kadai, don haka ba za ki yi girki a ciki ba, balle kije ki rine mata kayanta da hayakin risho.
Don haka ha koma cikin zaure na sa-shi a lungu tunda ni dai nasan kawai zan yi girki ina bukatar cin abincin, ga Isiyaku ma yana bukata, don tunda Mubarak ya hada ni da shi wurina yake zuwa ya karya ya kuma ci na rana, abinda Mubarak din ya gaya mishi ke nan nima ko ban yi niyyar saye ba in yazo sai in ba shi.
Shiga wurin Babah Sumaye ka ce wai ta bani wuka da ludayin miya da kuma kwanukan cin abinci, ya ce to.
Kai yau ga wani abin dadi, girkin ma a zaure a ke yin shi? Alamar dai ke nan da girkin ba na tsayawa yaci. Na waiwaya cikin murmushi na na kalle shi, to mai wucewa a hanya ma zai iya kallon shi, manya-manyan ledoji ne guda biyu a hannunshi a cike da cefane.
Na rike baki na ce kai Mansur wacce irin hidima ce kwannan? Ya yi maza ya daure fuska alamar bai son maganar tawa, in wanke hannu dai kawai kenan in yi shirin yankan attarugu da albasa tunda nasan zafinsu ai kin ga ba zai yiwu in bar ki ki taba su ba.
Nayi murmushi na ce ai an riga an yanka su, sayayya sosai Mansur yayi na kayan tea daya ledar kuma kayan ciki ne wanda hanta yafi komai yawa a ciki, ga kuma agada nono gora mai kyau da ita.
Isiyaku yana ganin ledar kayan cikin ya sure shi ya shiga gidan Babah Sumaye yaje ya wanke shi tas ya kawo ya nuna min. ina, dubawa yana yi min magana naga gaushin da Babah Sumaye ta sauke girkinta ko can zan kai wannan? Na ce to kai Isiyaku in babu abinda zata dora a kai. Ko akwai ma ai naga wani kurfon buhun gawayi ne kuma da ita zan hura wata wutar, na ce mishi to.
A zaure na soya agada na hada mana tea muka sha ni da Isiyaku bayan tafiyar da Mansur yayi a kan zai je gida ya dawo.
Sai da muka koshi sannan muka zaune yin girkin dafa dukan taliya mai hade-haden kayan lambu a ciki nayi mana na zubawa Mansur a karamin food flask na zuba mana namu ni da Isiyaku saura na juyewa almajirai da suka zo wucewa su biyu.
Farfesun kayan ciki yayi Isiyaku ya shiga ya fito da tukunyar na zuba mana namu ni da shi, na zubawa Mansur da Babah Sumaye na hada, na baiwa Isiyaku duk yakai musu ya dawo. Muka hadu muka gyara wurin ya kuma yayi mana wanke-wanke ya kife ya dawo.
Wai dan girkin nan da nayi naci sai ya haifar min da wata irin natsuwa da na dade ban samu irinta ba, damuwa tayi min sauki naji dadi cikin raina, don haka da na shiga gida ina ajiye kayan tea na’ da sauran abubuwan da na shigo da su, sai kawai na wuce na shiga wanka don in kara jin dadi.
Na fito daga wanka ina shafa mai na lura naga kamar an taba kayan da na ajiye, na mika hannu don jin ko da gaske ne an taba sai kawai naji an juye babu komai a ciki sai gwangwanayen aka bari. Cikin zuciyata na ce iko sai Ubangiji, na ci gaba da harkokina.
Washegari da safe ina kwance kan shimfidata ban motsa na tashi ba saboda nasan ko na tashin bani da wani abinda zan ci na kuma daina aikin Babah Lantana tunda ko nayi bani da rabo cikin abincinta. Jiran shigowar Isiyaku nake yi don in ba shi ya sayo mana abinda zamu karya dashi.
Jimawa can sai gashi ya shigo rike da kwano mai shake da waina da wani kwanon kuma, miya ce da kashi da man shanu, cikin fara’a ya ajiye kwanon yana murmushi.
“Yaya Mansur ne ya bani wai in kawo in na gama kuma in je in same shi na ce mishi to.”
Wajen karfe goma sha daya da rabi na safe sai ga Isiyaku ya dawo dauke da cefane niki-niki har da kaji da kuma busasshen manya-manya. A.zaure rannan ma muka yi komai muka ci na zuba na Babah Sumaye da na Mansur na aiki Isiyaku ya kai musu na zuba mishi na Almajirai yaje suma ya kai musu.
Sauran kayan kuwa gabadaya na sa shi ya diba yaje ya kai wa Babah Sumaye ya ce ta ajiye cefane ya zamo mishi wata ka’ida da ya dora wa kanshi kullum sai yayi ko da kuwa na jiyan bai kare ba.
Kullum muka yi kuma zan zuba a kai mishi sannu a hankali kuma sai Mansur ya maida zauren gidanmu wurin hirarshi.
Rannan iną tare da Mansur a zauren tare da Isiyaku, muna hirar ne ina yi mana girki sai ga Babah Lantana tana ganin Mansur ta soma zagi da fadin lalatattun maganganu irin wadanda ta saba yiwa Mubarak.
Nan da nan Mansur ya maida wukar da ke hannunshi wacce yake yanka min albasa, da ita ya daga ido ya kalli Babah Lantana cikin natsuwa ya ce mata ai ki na ambaton sunan iyayena a cikan maganganun naki za ki gane kin jawa kanki matsala don ba zan bari ki zagan mun su ki kwashe kalau ba, zan gwammace in biyo ki har cikin gidan in sa dorinata in yi miki dukan tsiya.
In yaso duk abinda zai faru bayan hakan ya faru zai fiye min sauki a kan kiyi wa iyayena zagin wulakanci irin wanda ki ka saba yi wa mutane suna kyale ki, kin taba ganin na shiga lamarinki?
Kin taba ganin na buda bakina na gaya miki wata kalma ko da kuwa ta gaisuwa ce tunda ki ka zo layin nan? Kin taba ganin,na shiga harkokin da ki ke yi? Kin taba ganin na shiga harkar ‘ya’yanki?
Amma shi ne ki ka zo kina zagina har kina ambaton sunan ubana? To sake fadin kalma guda daya ki ka ga ni? In ma nayi mata ciki sai me? Ina ruwanki ai ba zan barta tayi ta yawo da shi kamar yanda a ka barki kina yawo da naki ba.
Ban san yanda a ka yi ba sum-sum naga Babah Lantana ta juya ta shige gida ta bar shi yana fadin haka kawai mata kin zo unguwa kin samu mutane kin tasa su a gaba suna kallonshi sun kyale ki? Ai karyar iya shege ki ke yi.
Na shiga gida don taba ruwa sai kawai naji Sallau yana cewa Babah Lantana na rantse miki Mama in ki ka sake jawo wata fitina ta same ni sai kin gaya min inda Babana yake. Tunda na ce zan shiga duniya kin ce namiji don ya shiga duniya ba komai ba ne, ga maigidan nan ma ai shiga duniyar yayi ya bar danginshi da bai samu yanda ya ke so ba.
Kuma ya hakura ya yafe su to na fasa shige duniyar tunda don na shiga bai dame ki ba, zama zan yi a inda ki ke iyaka in tara miki Jama’a su rokar min ke ki nuna min in da ubana ya ke, a to.
Ya fadi a to din tare da gyada kai nuna alamar da gaske yake yi zai iya aikata abinda ya ce din.
Rannan dai jikin Babah Lantana a sanyaye ya wuni saboda rasbhin mutuncin da Mansur yayi mata ga kuma kalaman danta wanda ko gama warkewa bai yi ba, yanda ta wuni jiki a sanyaye haka Sallau ma ya wuni yana mita ba fa gama warkewa nayi ba har yanzu din nan ji nake kamar kasusuwan jikina Agogo ce suke kuma wai kina sake shiga sabgar wani saboda ba ke suke yi wa ba.
Ina jin su babu ruwana takura ta dai tayi matukar raguwa, gashi abin da nake so shi nake ci na rabu da yunwar da ke yawan damuna a yanzu kuma ina da yan hira ga Isiyaku ga ‘yan Almajiraina guda biyu wadanda in ba wani muhimman abu za su yi ba basa barin gidan, sannan ga Mansur abokin hira mai dadi mai fadin kalamai masu dadi mai barkwanci, mai Sanya zuciya taji tanfar a kan gajimare take yawo, saboda dadadan kalamanshi, gashi kuma da yawan alheri.