Skip to content
Part 17 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Tun daga ranar da Babah Lantana tayi haka da Mansur nima bata sake shiga harkata da yawa ba balle Mansur din iyaka dai kullum zan ji ta tana cewa Babana wannan yarinyar fa ba a rabu da bukar ba wancan ya tafi ne wani kuma ya mayye gurbinshi.

Ta kwashe bayani na karya da gaskiya tayi mishi, rannan har tana yi mishi rantsuwar wai ta ganshi ya matse ni a lungu in banda ta shiga zauren da bata san abinda zai wakana ba.

Yana jin ta tayi shiru bai ce mata komai ba, takaici ya kamata ta ce koda yake dai kai dama irin wadannan ba su dame ka ba, ba ka tsoron shege ta kalle shi ta tabe baki tare da mikewa ta nufi dakinta tana tafiyar tana magana a hankali sai dai hakan bai hana a ji ta ba, don rage muryar na iya shege ne. Wa yasan abinda kayi ne ma Mallam kafin ka baro gida nake damun kaina a kan ‘yarka?

A zuciyata na tabbatarwa kaina raini ya kai duk inda yakai tsakanin Babah Lantana da Babana, tunda har zata iya furta mishi irin wannan maganar a kan idonshi, bai iya ce mata komai ba, na gaji da irin wadannan kalaman na tozartawa da take yi mishi, koda a bayan idonshi ne balle kuma abin ya kawo kan idonshi.

Raina ya kai matuka wajen 6aci jikina har yana rawa na gaji da irin wulakancin da a ke yi wa Mahaifina a kan idonshi, a kan idona saboda raini da tozartawa. Ban san yanda aka yi ba sai kawai ji na nayi na bude baki ina cewa Babah Lantana, Babana ko ya baro garinshi da danginshi ai kuma bai yi kama da wanda ya aikata abin kunya ba.

Don kuwa bai da wata alama ta rashin mutunci a tare da shi.

Tana jin haka ta zabura ta mike da ke nake ko kuwa rashin kunyar taki ta kai ma za ki zage ni nc? Ko ba da ni ki ke ba ai cin mutuncin mahaifina ki ke yi a gabana da kuma ‘ya’yan da ke da su ya rufa muku asiri.

Ta shiga zage-zage tana dura min ashar, ni kuma ina daki ina fadin a’a haka kawai kullum sai kin wulakanta shi yana kallonki don kawai kin ga baya yi miki magana? Ana cin arzikinshi ana kushe shi? Babana in mutumin banza ne zai rike miki ‘ya’yanki ne?

Asabe tasa kafa ta taka min shimfidata kamar yanda ta saba yi kullum, maimakon .in karkadeta kamar yanda na saba sai na kalleta na ce mata gaskiya wannan wulakancin ya ishe ni haka ke ki taka min shimfida sannan a zagar min ubana ina ji, ya isa haka.

Da sauri ta mike ta zauna a tsakiyar gadon, ke yarinya ina ganin fa wani abu yana yi miki yawo a kai, ni sai in sauke miki shi bari kiji in gaya miki, na harareta na ce kai haba yarinya ai tana bayan uwarta.

Ta zuba min ido, to ba zan daina ba yi abinda za ki yi ta sake tattakawa, na fita naje na tsaya a kofar dakin Babah Lantana don rabon da in shiga dakin har na mance da lissafin tun dai ranar da ta mare ni a kan na taka mata sabuwar ledarta.

Naja na tsaya daga waje na ce Baba ya amsa na gaishe shi kafin nayi mishi bayanin abinda ke faruwa na taka min shimfida da Asabe ke yi kullum.

Kan ya ce komai sai kawai naji Babah Lantana, ta karbe maganar, ai nan karar Asabe ki ka vi wurin ubanki ke nan ga mai uba ko? Aiya sannu mai uba yiwa wacce bata da uba wulakanci. Dadin abin shi kadai gare ki na juya zan koma dakin saboda jin shi Baban nawa bai ce komai ba.

Sai naji tana cewa kai ku kam da kuna da wani asali ba a san irin iya shegen da ki ka yi wa mutane ba. Na ce uba ai shi ne asali Babah, ai ni da asalina a ka ganni tunda a gidan ubana aka ganni wanda ya rasa uba ai shi ya rasa asalirishi.

Gari na wayewa nayi duk abinda na saba yi na yau da kullum dina, ina jira Babana ya fita sai kawai na leka na kira Isiyaku tare da yan Almajiran nan dama na gaya musu kar suyi nisa.

Gaba daya kayan dakina na fitar da nawa da wanda ba nawan ba na share dakin tas na cire cinyayyar ledar da ke ciki na wurgar da ita ina aikin Babah Lantana tana jaddada min in dai hankali da kayan Asabe don ita duk kayanta masu tsada ne.

Ban tanka mata ba na dauke yar shimfidata daga kasa na baje ta karkashin katifar da ke kan gadona sannan na maida katifar akai na jawo wani tsohon zanina na shimfida na gyara komai na maida kayan na ajiye kofar dakin ma na Sanya mishi sabon labulen da Yaya Dijah ta bani sanda ta gayamin abinda zan yi ban iya ba, sai yau na kunna turaren tsinke.

Nayi wanka nayi kwalliya suma su Isiyaku su je suyi wanka su dawo na ba su kudi na ce su sayi sosa da sabulu na mika masu kwalbar Vaseline din da, dama yake boye cikin kayana bana amfani da shi.

Da daddare ina idar da sallar Isha’i na dare kan gadon nayi kwanciyata gabana sai harbawa yake yi, Asabe ta shigo ta ganni kan uba’ abinda ta fara fadi ke nan kafin taci gaba da cewa, ai kema kin san ba zai taba yiwuwa ba ki ce za ki dawo da kwana a gado. Za ma ki fito da shimfidarki duk inda ki ka kaita ko kuma ki san nayi saboda ba za ki hau gadona ki matse ni ba.

A lalace na kalleta na ce mata kuna da gado ne a gidan nan? Ai duk wani gado da yake cikin gidannan in ba ki sani.ba in gaya miki na Innata ne, na sake kallonta na ce ina ce wannan ne ki ke cewa naki? Kan ta bani amsa na ce mata ba ki da kyau ba, don kuwa wannan gadona ne da na gada a wurin mahaifiyata, kin kuma san kayanta ba zai zamo na baitilmal ba, tunda tana da magada.

Kace-nacen da muka fara yasa Babah Lantana fitowa tana tambayar Asabe menene? Ta tsaya tana yi mata bayani, nima ina daga kwance ina mita tare da kunkunin da ake iya jiwowa.

Haka kawai ni da gidan ubana an zo an Takura min, in gaskiya ne abinda ake fadan kowa yaje gidan ubanshi ya zauna mana, wannan gadona ne da uwata ta mutu ta bar min a ka zalunce ni aka kwace min shi a ka maida ni kwanciyar kasa ba kuma zan sake yarda da hakan ba, sai dai duk abinda za ayi ayi amma ba zan sauka a kai ba.”

To ai sai ki gyara ku kwanta tare ko? Na ce a’a ba mai sake hawa min kai ai bata da gadonta balle ta ce ana ta kason take hawa, hankalin Babah Lantana yayi matukar tashi, bata saba ganin ina yi mata rashin mutunci irin wannan ba, wata kila kuma bata taba zaton irin wannan ranar zai zo ba.

Ni ki ke gayawa wadannan maganganun? Na ce oho, ni dai na gode ina da uba kowa ya san shi dangin uban ne kawai bani da su, yana kuma sona tunda ko unguwa bai barina in je balle yaje ga bada rikona wurin wadan su in je ina zama agola, sai dai a kai mishi karata ya yi min duka amma ba ya tura ni gidan wasu da sunan riko ba.

Da sauri Babah Lantana ta juya wurin Babana da ta bari a daki tana yi mishi magana irin wacce ta saba, wato kana jin rashin kunyar da ‘yar iskar yar nan taka take yi wa mutane amma kaja bakinka kayi shiru, kayi wani shememe a kwance kamar gawar sababi ko? To tashi ka bani wuri don a kan ka abin’zai kare tunda kai ne ka rasa abinda zaka haifa a duniya sai yar iska.

Tashi ka gani in sauke katifar inibáiwa Asabe ita kai ka san nayi, don ba zai yiwu,ita tana gado Asabe tana kasa’ba.

Ina jin haka nayi maza na yiwo waje don nasan abu ne mai sauki Babana ya sauka a gadon, Babah Lantana ta dauki katifar ta baiwa Asabe ita.

Dakin na shiga na kara kallon katifar da Baban nawa ke kwance a kai sai da na fito tsakar gida sai na ce mata, Babah in dai wannan katifar ce to ba taki ba ce ta Innata ce, don haka ko kin fito da ita zan karbeta.

Shiru tayi bata tanka min ba, ina shiga dakina na gane hikimar da Babah Lantana tayi min saboda ganin Asabe da nayi kan gadon a kwance ta babbake ko’ina.

Ki bani gadona na fadi hakan tare da kokarin janye katifar da ke kan gadon ban san yanda a ka yi ba sai ganina kawai nayi muna wani irin dambe ni da Asabe, danbe mai tsanani irin nà kwatar kai.

“Dake ta Asabe, bugi ja’ira kar kiyi mata da wasa. Abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan.

Sallau ya dogara sandarshi da yake dindingisawa ya fito daga dakinshi kwanaki tara da yin abin har lokacin bai gama warkewa ba.

Babah kenan, za ki kara ba Mama? Iyaye suna yiwa ya’ya tattalin abin arziki suna gudarwa ya’yansu fitina amma ke kullum cikinta ki ke jefa su.

Babah Lantana tayi maza ta juya gare shi ta kafa mishi wani gigitaccen mari kau! Tanfar ba shi ta gaurawa irin wannan marin ba, bai motsa ba daga yanayin da yake, ni kam ko sau nawa za ki maren ai zan gaya miki gaskiya tunda dai an ce min uwa ta kwarai tana yarda da shawarar ya’yanta matukar su din sun kai munzali na mallakar hankali.

Ke Asabe in kin yarda ki bar fadan nan, fada ne fa na rashin gaskiya yarinya tana zaune a gidan ubanta mun zo mun kankane komai ai da gaske ne kowa a nuna mishi gidan ubanshi mu tafi mana.

Sallau ne yasa sandarshi ya raba tsakanina da Asabe muka rabu da yake daga ni har ita babu wanda yaji alama na dukanmu muna son rabon da a ka yin sai dai hakan bai sa na yarda da mu kwana mu biyu a kan gadona ba, bałe aje ana fito da katifar Babana a bata shi a bar shi a kan wayar gado.

Duk abinda ke faruwa Babana yana daki yana jin komai amma bai ce uffan ba, har a’ ka yi aka gama ina jin ko shine abinda yafi batawa Babah Lantana rai ta shiga-daki ta figo gýalenta ta fito tana fadin zo Asabe. fito nan yau, kam in kai ki gidan uban nan naki da kullum a ke yi min gorinshi.

Ta tasa ta a gaba suka fita suka bar gidan, naje na kulle kofar gida nazo na ihau gadon.na/kwanta, tausayin Babana yayi matukar kama ni, babu abinda yafi komai tsayawa a raina irin kifin nan da Babah Lantana ta jefawa laya abaki ta daure da zaren ilo tasa a ka je aka jefa a rafi, wai yanuwanshi su cinye shi a haka.

Zuciyata ta raya min acewar wata kila yi tayi don ta daure bakin Babana komai tayi kar ya ce mata komai, tunda gashi a yanzu kome za’ayi a gabanshi ba zai bude bakinshi ya ce don me ba?

To amma yayi ta zama a haka ke nana? Wannan shi ne abinda yafi komai damuna.

A haka har gari yawaye na tashi nayi sallah naje na gaida Babana, na kama hidimomin gida na. Bayana gidan tsaf lungu-lungu duk inda ya dade ba a gyara ba ma na gyara shi komai yayi tsaf Babana ya fito daga daki yasa hannu ya dauki kwandonshi, kasuwa yake nufin tafiya, nayi maza na’ ‘ce mishi “Lah, Baba har za ka tafi kasuwar ba ka karya ba?”

Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce min da wani abu ne a gidan? Na ce mishi eh Baba, ya ce min to ya nemi wuri ya zauna a kan shimfidar tabarmar shi na kawo mishi lafiyayyan abin karyawa ya karya abinda ya dade bai samu hakan ba don tuni

Babah Lantana ta daina ba shi abin karyawa yaron nan ba yana nana a ciki ba?

Na ce eh Baba, ya ce to ba shi mana ko babu ne in rage mishi a nan? Na ce akwai na diba naje na kaiwa Sallau na dawo na zauna a gefenshi, gabana ya fadi, ganin yadda wuyan rigarshi tayi dikin-dikin.

Baba wannan rigar taka ai tayi datti ka canza wata mana, ya sunkuyar da kanshi ga rigar alamar yana kara dubata, ai duk rigunan nawa masu datti ne, na ce to bani in wake maka su. Ya ce To kafin ya sake cewa ko ki bari sai gobe saboda sabulu.

Na ce bani kawai Baba akwai sabulu, ya ce to. Isiyaku ne ya wanke min kayan ya goge su ina kallon yanda suka tsufa suka zama ‘yan fake-fake saboda jin jiki yayinda zuciyata ke tuna min da dadewan da nayi ban ga Babana da sabon dinki ba ko da kuwa da sallah ne.

Komai nashi a hanmun Babah Lantana yake, ita kuma bata da adalcin cewa shima ya yi wa kanshi don a ga mijinta fes ta kanta da ‘ya’yanta kawai take yi ko ni ma da zaninshi nake jira in daura to da yanzu ta kai ma ba ni da na daurawa don tun sallar farko da Babah Lantana tayi a gidanmu bata sake sawa an yi min sabon dinki ba.

Rannan a kicin nayi girkina ban je zaure ba, muka zauna tsakar gida muka yi hidimominmu na zuba a kwano na baiwa Ísiyaku ya kai wa Mansur, ni kuma na dauka da sauri naje na kaiwa Babana, na zauna na tsare mishi tumatirinshi ina yi mishi cinikin, yayinda shi kama ya koma dan lungu yaci abincinshi saboda Babana mutum ne mai kunya.

A hanya ina rike da kwanon abincin da na kai mishin ina tunanin daga yau in dai zan yi girki to kuwa zan zuba in kai mishi sannan ba zan sake barin Babah Lantana da wankin shi ba, balle yaje yana yawo dikin-dikin.

Yana dawowa da yamma naje na wanke bayangida na kai mishi ruwan wanka yayi ya fito na kawo mishi wankakkun kayan shi ya saka yana tayi min addu’a, naji dadi cikin raina har ina tunanin ashe dai in ban da Babah Lantana da Babana bai canza min ba.

<< Halin Rayuwa 16Halin Rayuwa 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×