Skip to content
Part 19 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ina kwance a kan gadona zuciyata ta ca takai kawo cikin sake-saken al’amura, naji wani mai sayen kwalla yana tambayar akwai kwalla ko tangaran ko tasoshi? Da sauri naji Babah Lantana tana cewa babu sai gado mai rumfa in kuna saye, yayi maza ya ce muna saye mana, ai mu duk wani abinda zamu samu amfani a kanshi saye muke yi.

Nayi maza na mike a tsakiyar gadon don ganin gado mai rumfar da Babah Lantana ke Shirin gado mai runfar da Babah Lantana ke Shirin sayarwa tunda naji ta ce ya shigo.

Ina daga zaunen najiwo ta tana kakkarya gadon Innata, Asabe tana tayata, ‘wannan gadon ma ai tuni ya kamata in rabu da shi in canza na bari har wannan shegiyar ta zo tana yiwa mutane gorin shi.

Ba ma a yayinshi fa Babah, ta ce ch ai in suka saya kauye suke kaiwa ko kuma su yankę shi su maida shi na familin mai Rarfe.

Sai da suka fitar da shi zaure suka soma cinikinshi sannan nabi baya na kalli mai sayen nace mishi, kai Mallam gadon ba na sayarwa ba ne, mai gado ya kalle ni ya kalli Babah Lantana ya dan yi turus alamar rudewa.

To ko dai tayin da aka yin ne bai yi miki ba? Babah Lantana ta ce, yau naga fitina, kai Mallam ba ni kudina ka ji na sallama maka. Na ce in ka saya ma banza ka saya gadona ne da na gada a wurin Mahaifiyata, ban saida shi ba kuma ai babu mai sayar da shi ko kuwa?

Yayi maza ya gyada kai tare da fadin in dai haka ne kam babu shi na ce a to, na leka na kira wani yaro na ce mishi gudu kaje ka kira min Isiyaku, yaron ya tafi da gudu, ni kuma naja na tsaya a kofar gida ina kunkuni, to an zo da gado gidanmu ne balle a jawo gado a ce za a sayar ayi canji?

To ku sasanta dai sai mai gadon ta gaya min kudin gadon in biya, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi amma ai nace maka ba na sayarwa ba ne za ka bar wurin nan ko sai na kira yaran can sun rakaka? Sum-sum ya kama banva ya bar wurin.

Babah Lantana tayi kwafa ta kama gado zata mayar ciki na ce a’a ai tunda ya fito ba zai koma ba a zo a sayar da shi bana nan, katifar ma don dai ba zan bar Babana ya kwanta a kasa ba ne da na shiga na fito da ita na hada su.

Ai sai ki fito da itan kawai ta ju ya ta shiga gida Isiyaku ya iso na ba shi gadon na ce ya hadu da yara su kaui shi gidan Yaya Dijah.

A wannan lokacin ne Babah Lantana ta rasa yanda za ta yi da ni a dake dai ba zai yiwt ba in zagi ne ba zai gamsar da ita ba, tunda nima nayi rikan da bana rama zagin amma ina komawa gefe in yi kunkunan da bata jin abinda nake fada wanda nasan yafi komai bata mata rai.

Ga shi ta fito da gado da niyyar sayarwa ta karbi kudin wai-ita zata yi canji na kwace gadon na tura wa Yaya Dijah shi babu kuma yanda zata yi dani, ina jin ta tana rattabawa Babana bayani na karya da na gaskiya don dai ta samun ya sa baki cikin maganar bai ce mata komai ba.

Takaicinshi ya kama ta, ta kalle shi cikin yanayin bacin rai tare da jan tsaki kai kam ai gaya maka magana ma ba ta da wani amfani sai ayi a gama kana ji ba za ka ce komai ba, kayi wani gum da baki kamar na mai cin najasa.

Bai ce komai ba nima ban ce ba, cikin zuciyata dai cewa na yi in ma kin yi ne don ki cuci wani to kanki zai koma.

Ban sani ba ko takaicin sane  yake yawan damunta ko kuma ta mantá ne cewar dasa hannunta cikin shirun na Babaha yasa naji ta tana mita ita kadai’ a dakinta, a ce maigida duk abinda aka yi a gidanshi ba zai ce komai ba, sai yayi gum da bakinshi kamar na mai bubu? To ina zance? A hankali na buda baki na ce babu, sai dai nasan bata ji ni ba.

Tsaraba mai daraja sosai Mubarak ya aiko min da ita, sai dai hakan bai sa da muka gamu da shi a hanya na daga ido na kalle shi ba, balle in je ina kula shi saboda na gaji da yanda yake tafiyar da ni ba kuma zan lamunci miskilanci da jan aji irin nashi ba.

A wannan lokacin mu’amallata da Ahmad Mubarak sai ta kara ja baya sosai mafi yawancin lokaci ko yana dan murmushi ya ganni daure fuska yake yi, ko yayi kamar bai ganni ba, nima bana kallonshi in ba a kan kuskure ba.

In na san yana gida ma bana zuwa sai in bari sai baya nan in yi maza in je in gaida Umma in dama abin da zan yi mata ma in yi mata ina ganin ya dawo zan yi maza iu îta in bar gidan.

Umma da kanta ta ganc mun yi ‘yar tsama ni dashi don sau biyu tana tambayata ni me ke faruwa ne tsakaninki da Ahmad Muuarak Maryamu? Ina jin ta soma irin wadannan tambaycin sai kawai in gudu in barta.

Sai dai irin wannan zaman da muke yi da shi bai sa ya canza komai ba na daga abubuwan da ya saba yi min kowane lokaci a cikin yi min aike yake, kayayyakin bukatar rayuwa irin su mai, sabulai, na wanka da wanki, under wears, audugar al ‘ada, kudi babu abinda ba ya baiwa Isiyaku ya kawo min.

Ana cikin haka watan Azumin Ramadan ya iso, don dama su Mubarak sun yi umarar su ne a watan Rajab, Isiyaku ya turo yazo ya tambaye ni me da me nake so a kawo min? Na ce yaje ya gaya mishi bana bukatar komai har cikin zuciyata ban jina kamar ina bukatar wani abu nashi a wannan lokacin tunda abinda nake so yayi min bai yi ba abinda nake nema a wurinshi ban samu ba.

Babu wata alama kuma da take nuna zan samu yanda nake so din a wurinshi, to ana me zai yi ta hidima yana ta dawainiya dani bayan shi ba sona yake yi irin son da nake yi mishi ba, in taimakona wake yi don kyakkyawar mu’amallar da yayi da Innata a shekarunshi na kuruciya to ya kyautata ya taimake ni a bayanta har na kawo munzalin da nake ciki yanzu.

Don haka na gode ya bari haka, in don tausayi ne ma dai to na gode yanzu nayi girman da shi bai lura ya gane ba, don haka ya bar ni kawai in ci gaba ni kadai in ma wahalar ce in shata kawai. A yanzu abinda nake so ya so ni ne kawai irin son da nake yi mishi, soyayyar da zata rikida ta zama ta aure, aroma ba kullum a ji tausayina ba.

A duk lokacin da irin wadannan abubuwan suka dawo a cikin raina zama nake yi in yi ta kuka wani irin kukan da sai nayi na gaji kawai nake yin shiru.

Ban san dalili ba cikin zuciyata babu abinda nake so irin aure, ban sani ba kowace yarinya ta kawo munzalin da nake abinda take ji ke nan ko kuwa ni don ina tare da Babah Lantana ne? Matar da kullum burinta ta cutar da ni ne in kaga bata yi min hakan ba to abin ya gagara ne kawai.

Sannan kullum hirar kawayena ke nan samarinsu da ranar aurensu, sai na samu kaina nima a irin wannan yanayi da matsayin sai dai kuma na kasa sakin zucivata in so wani ban da jin dadin wata magana in dai a hakin wani ta fito ta in da nake so ta fito din kuma abin ya gagara, to ya fita mana ko zan samu in saba da wasu irin sabon da nayi da shi in so su irin son da uake yi mishi ko na rinka jin dadin kalamansu.

Gaya mishin da aka yi bana bukatar komai shi ne yayi dalilin da ya gangaro da kanshi yazo har kofar gidanmu sai dai yau ma cikin rashin sa’a tare da Mansur din yazo ya same ni, sai dai maimakon ya juya ya tafi bayan tafiyar Mansur din kamar yanda yayi wancan karon tsayawa yayi ya tsare ni da ido yana kallona, yayinda ni kuma na sunkuyar da kaina kasa nayi kamar ban san da tsayuwar tashi ba.

Ni me ke tsakaninki da wannan ne? A hankali na ce wa’? Yayi shiru ya ci gaba da kallona ba tare da ya sake cewa komai ba, saboda sanin da yayi nasan wa yake nufi, na mike tsaye a hankali cikin natsuwa tare da karkade jikina a sakamakon zaman dirshan din da nayi a kasa sanda nake hirar.

Cikin natsuwa na kalle shi na ce Mubarak, ya ce uhh, ya amsa ba tare da ya buda bakinshi ba watakila bai ji dadin yanayin da na ambaci sunan nashi a ciki ba.

Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi yau ne ka ga ya dace ka tambaye ni abinda ke tsakanina da Mansur? Ya sake cewa uhhm, ba tare da na dago ido na kalle shi ba, nace to ai ka makara, na juya na shiga gida na bar shi a wurin yana tsaye.

Na hau gadona na zauna a dalilin na kasa kwanciya jikina sai faman bari yake yi, yayin da Zuciyata ke ta faman harbawa a dalilin sanin da nayi na batawa Mubarak rai.

Hankalina yayi matukar tashi na kasa jin dadin al’amarina.

Tsawon lokacin ina cikin wannan hali kafin naji zuciyata tana rarrashina tana bani hakuri kalamai masu karfi take gaya min, ya zama dole in zama jaruma a kan lamarinshi in har ni kadai ce na ke sonshi shi tausayina yake ji to ya tafi ya bani wuri mana kawai ya gani ko ba zan rayu ba.

Ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni tare da masu sona irin son da nake bukatar ayi min a yanzu, ya tafi ya bani wuri mana ya bar ni in yi harkokin rayuwata menene na tsare ni da tambayoyi? Na mike cikin kuzari saboda jin da nayi zuciyata ta gamsu da abinda na aikatan naje na debi ruwan sanyi nayi wanka na dawo na zauna goge jikina ina shafe shi da man shafawa na 10.0-6 man da Mubarak ya saban min da shafawa.

Wani abin takaicin shi ne duk wani abinda ke kewaye dani shi ne don haka na tsayar ma raina da cewar cikin matakan da zan dauka na kamewa daga gare shi har da daina yarda da hidimomin da yake yi min.

Ina cikin wannan halin sai ga Isiyaku ya shigo dauke da wani katon kwali shake da kayayyakin amfani na hidimar Azumi, ba zan iya cewa a mayar mishi ba don kuwa yana da girma da kima a wurina.

Na karba na ajiye, Mansur ma ya kawo min nashi na sake hadawa daga gidan Yaya Dijah ma ta aiko da sako guda biyu, na Babana da nawa. Ina jin Babah Lantana tana gayawa Baba wai in ban da kar ta ce ya mayar wa Yaya Dijah da kayan kamun AZumin da ta kawo mishi ace bata kyauta ba da ta fada don kuwa ba a kan son ranta ta bada nashin ba, tunda abinda ta bashin bai kai wanda ta ba ni yawa ba.

A watan Azumin kullum na kan shiga gidan su Mubarak ne da safe in je in gaida Umma in kuma rike mata Alkur’aninta muje wajen jin Wa’azin Tafsir din da ake yi a babban Masallacin Juma’armu in a ka tashi sai na rakata gida kafin in zo gidanmu in yi alwala in yi sallah, in hau gadona in kwanta in yi bacci.

Ba na farkawa sai karfe uku da rabi, sai in yi wanka in yi alwala in yi sallar La’asar in kama shirye-shiryen abin buda bakina wanda nake yi da dan dama don bani kadai ba ce, ‘yan Almajiraina guda biyu da muka yi matukar sabo sai Isiyaku da Mansur da kuma Babana da kullum nake daidaitan dawowanshi daga wurin Tafsir tunda na dare yake zuwa in ba shi abinda nayi ya zauna yana ci, ni kuma ina gefe ina jiranshi sai ya gama in karbi kwanon ya wuce ya shiga gida kafin in bi bayanshi.

A haka har Azumin yazo karshe muka shiga kwanaki goma mafiya daraja kwanakin neman daren Lailatul Kadri daren da AIkur’ani mai girma ya ba mu labarin cewa darajarshi tafi ta watanni dubu, haka alkairorin da ke cikinshi.

Ubangiji yasa mu dace, kullum abinda Umma ke fadi ke nan in taji Mallam yana ta nanata fadin alherin daren ‘Lailatul kadri ni kuwa sai in ce mata anmin Umma.

A wannan lokacin zan iya cewa ban taba samun kaina cikin hali na kunci da farin ciki lokaci daya ba irin wannan karon, ina cikin farin ciki saboda alkhairori da suke ta zuwa min daga wurare daban-daban.

Kusan kullum gari ya waye sai an zo min da sako na kayan sallah daga wani wuri. Yakumbo Halima da ba wani karfi ne da ita ba ma atamfa ‘yar Holland ta dinka min a dalilin wai na zama budurwa, Yaya Dijah tsalelen leshi gami da takalmi da Jaka da gyale.

Umma atamfa da leshe itama da takalmi da Jaka da gyale mahadin takalmin duk da dai tace wai da kudin bankina ta saya min amma dai nasan alherin Umma bai kwatantuwa a wurina.

Mansur yayi min kala biyu masu kyau shima tare da takalmi da Jaka tare da gyale, sai kuma a ka kawo min na Mubarak, Isiyaku ya aiko ya kawo min. Na zauna ina kallonsu suma kala biyun ne sal dai shi komai nashi daban ne da na saura, bai taba mancewa da wani abu ba in dai har aiken zai yi min yadika ne masu kyau masu laushi kala biyu mai ruwan madara da kuma baki na rike su a hannuna ina kallonsu ruwan da suke yi ya kara tabbatar min da darajarsu.

An yi musu adon zare a wuyansu kalan zaren ya dace da kalan takalma guda biyu da ya saka a cikin kayan kenan kowanne da mahadinshi gyale biyu sai kayan shafa da under wears ga kuma wani dan karamin akwati mai dauke da wata ‘yar sarka mai dan madaidaicin ‘yan kunne da zobe a wata yar takarda kuma wasu siraran wararai ne da agogo babu yanda za ayi a kushe hidimar Mubarak in dai zai yi ta matsalarshi guda daya ce ita ce ta ban san in da yasa gaba ba.

<< Halin Rayuwa 18Halin Rayuwa 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×