Tunda kika zo wurina ban taba ganin wani al’amari daga gare ki ba sai na alheri.” Shiru Inna tayi tana sauraronshi sai da ya gaji ya canza zancen don kanshi ni nafi zaton canjin da kike ji din watakila da namiji ne ai kin san gaba daya haihuwar nan da a ka yi in ban da na farin sauran shidan duk mata ne amma tunda kin ce kina da ndamuwa to tashi kawai muje asibiti.”
Ta yi maza ta ce ka ji Mallam kuma shekaran jiya ne fa naje awo suka kuma ce min babu matsala, iyaka dai in dan rage cin gishiri da barkono.”
Haka rayuwar Inna da Babana take kullum a cikin ganin alherinta yake, bai daga ido ya kalli wani al’amarinta ba balle ya gano kuskurenta baida wani labari wanda ya wuce na fadin alherin mahaifinta saboda ba shi ita da yayi ba tare da shi din ya neme ta ba ya kuma ba shi ita tana da shekaru goma sha biyar a duniya, bayan kuma gata da manema masu yawa da suke fatan ganin an ba su aurenta.
Kullum Babana a cikin sayayyar haihuwar Inna yake komai ya gani ya bashi sha’awa zai sayo yazo da shi gida, rannan ina jin ta tana ce mishi wannan kayan fa Mallam yawansu ya isa haka.
Kuma ma ni sai nafi son a hakura da sayayyar haka sai an ga an yi haihuwar tukuna saboda ni dai Mallam zuciyata a tsinke take game da haihuwar nan.
Ya yi maza ya dago ido ya kalleta za ki fara ko Ramatu? Kin san irin fadar min da gaban da kike yi kuwa idan kina furta irin wadannan kalaman? Kin sani sarai ai kin kuma san abinda kike yi in yi kike yi don in ji dadi kin sani, in ma don me kike yi kin sani.
Kin sani sarai bani da kowa bani kuma da yan ‘ya’yannan naki amma sai ki rinka gaya min maganganun da zan rinka hawa gadona da daddare ina kasa yin bacci saboda lissafe-lissafen al’amura. Tayi murmushi ta ce, “To ka yi hakuri Mallam bari in je in kawo maka abincinka.”
Bai saki fuska ba ya ce, To wane abinci kuma zan ci ni yanzu bayan kin gaya min wannan maganar.”
Ta sake yin wani murmushin ta ce, “Kayi hakuri Mallam ba zan sake yin ba amma da wannan katon cikin nawa da wannan kwalliyar da nayi don ka ji dadi in girka abinci don kai ka ce ba za ka ci ba ai kai ma kasan in na soma fushi zan dade ban huce ba, burabusko fa nayi maka da miyar yakuwa, ta kuma sha kashi da tantakwashin ga kuma nama ka gani?”
Ta zauna kusa da shi tana nuna mishi in zuba maka? Ya ce To ko don tsoron kar kiyi fushi ai zan ci Ramatu amma in don yunwar da na dawo da ita ne ai ta tafi tunda taji irin kalaman ki tayi maza ta ce ai ba zan sake ba kayi hakuri ya ce ya wuce Ramatu.
Anyi hakan bai dauki wasu kwanaki da suka zamo masu yawa ba na farka cikin dare naga kofar dakin Innata a bude alhalin sanda zamu kwanta ni da hannuna ne na rufe kofar har na sanya mata salanta nayi kamar in gyara ruhuwata da na fahimci zamewanta ne yayi dalilin farkawar tawa saboda tsananin sanyin da a ke yi har na juya da nufin komawa baccina sai kuma na tuna ai ban ga Innata a wurin kwanciyarta ba da sauri naji baccin ya sake ni nayi mika na bude idanuwa sosai a kasa na ganta a durkushe da gwiwoyinta a kasa ta dafa wata kujera ‘yar tsugune wacce dama ta zamanta ne a kicin nan take na karan wartsakewa ina kara bude ido don in ganta da kyau har nayi nufin saukowa in da take sai ga Babana ya shigo dakin cikin sauri rike da kwanon sha karami a hannunshi alamar rubutu yaje ya yiwo mata daga wannan rubutun dai Ramatu in bai yi ba sai kawai mu tafi asibiti kin ga nakudar tayi tsawo kar muzo muyi irin na
wancan karon shima asibitin yana da amfaninshi ai duk rahma ce ta Ubangiji ta kawomasu bata dai tanka ba.
Ya isa gare ta ya durkusa a gabanta shi ma kan gwiwoyinshi karbi ki sha rubutun nan Ramatu, bata motsa ba daga yanayin ta na sunkuyar da kan da tayi tana kallon ‘yan yatsunta.
A hankali cikin matsananciyar taushi da laushin murya ta ce mishi ka yafe min abubuwan da nayi maka Mallama.
Ya kara zuba mata ido watakila ba wannan ne karo na farko da tayi mishi irin wannan rokon ba saboda jin da nayi ya ce mata, To ni wai me kika yi min ne Ramatu da ki ke ta nanata min wannan maganar? Ai ni ban san komai ba game da ke in ban da alherinki shekaru ashirin din aurena da ke sune shekaruna na jin dadi da samun farin cikin rayuwa in ban da ke da wata kila ban taba sanin jin dadi ba, na zauna da ke kina yi mini biyayya kina tattalin farin cikina, kina kyautata min, ban taba yi miki umarni kin ki bi ba, ban taba cewa ga yanda za ki yi kin ce a’a ba.
A kullum cikin kiyaye bacin raina ki ke, to me zan ce miki? In har akwai abin da ki ke yi min da ki ke kuntatawa rayuwata ai bai wuce irin wadannan kalmomin naki ba, tunda kin san me suke nufi a gare ni, kina yi min nuni ne da zan iya komawa in da na baro har gara ma wancan lokacin ban taba danddanar wani madandani da ya kwadaitar da ni son rayuwar duniya ba kamar yanzu, to suma na yafe miki tunda nasan kina cikin wani hali ne yasa ki ke yi mini hakan. Ubangiji ya raba ki da wannan ciki lafiya.
Ni da nake kwance shiru a kan gado nake ta faman kukan sharbe na kasa saukowa daga kan gadon saboda tsoron kar a ce min in fita waje ba wai don tsoron daren ba sai don tsoron kar a hana ni ganin halin da Innata ke ciki saboda nasan a duk lokacin da Babana ya shigo dakin Innata ba a barina in shiga in ma ina ciki zan yi sauri in tashi in fita tunda nasan ko ban yi hakan ba ita Innan zata sani ni ce cikin zuciyata na amsa addu’ ar tashi na ce amin.
Mallam yayi maza ya ce na’ am Ramatu me ki ke son gaya min? me ki ke so in yi miki? A hankali ta ce mishi Mama ce. Gabana ya yanke ya fadi jin ta ambaci sunana. Cikin natsuwa ya ce mata “Eh, me Maman nawa tayi? Ta sake rage murya kafin ta ce mishi, ka baiwa Innata rikonta zata rike maka ita kamar ina raye.
Cikin nutsuwa ya ce mata, In har ina raye to a’a duk inda zan shiga zan shiga ne tare da ita, zata rage min kewarki yayi maza ya share wasu zafafan hawaye da suka zubo daga idonshi. Ita din ai kama da ke take yi, kina raye ma nakan kalle ta in yi mamakin kamanninta da ke balle kuma in kin tafi kin bar ni.
Wasu hawayen suka ci gaba da zubowa daga idanunshi har suna jika rigarshi, ban taba yi miki karya ba, ba zan yi miki a wannan lokacin ba, zan dai yi miki alkawari a duk lokacin da na hango wata alama ta katsewar rayuwata, to cikin taimakon Ubangiji zan mika mata ita.
Yana gama fadin hakan yayi maza yà miko wata Jaka ya dauko wacce yasan nan Inna take tara kayan haihuwarta yana cikin haka sai ga Babah Sumaye da Baba Hodijo sun shigo alamar kofar gidanmu ma a bude take sun kuma san da abinda Inna ke ciki.
Mallam Bukar ga motar nan fa a waje mun samota, da sauri Babana ya ce, To mu tafi.”
Yasa hannu ya daga Inna ya tsaida ita, Babah Sumaye ta daura mata zani tana fadin “Iko sai mai shi.” Gaba daya cikin ya tattara ya dawo kirjinta.
Tuni na sauko daga kan gadon ina ta faman kuka ina rike da hannun Innata wacce itama ta kama nawa hannun ta kankame a cikin nata.
“Sake ta mu tafi, muje ki shiga gida ki samu Jumare ku kwanta tare tazo tana nan a ciki, ki kuma daina wannan kukan da ki ke yi, kiyi mata addu’a kawai in Ubangiji ya kawo saukin lamarin da sassafe sai ki ga mun dawo tare da sabon yaronmu ko yarinya. Ki samu wata ‘yar uwar.
Wadannan duka kalaman Mama Sumaye ne don haka na dan samu natsuwa har na wuce na shiga cikin gidan nasu naje na samu Jumare muka kwanta mu kuma namu gidan aka sa kwado a ka kulle shi.
Jumare ‘yar kanwar Babah Sumaye ce da ke yawan zuwa wurinta, ta girme ni da shekarun da suka kai hudu, don haka ta fini wayo tana ganina ta ce min ke share hawayenki kizo muyi kwanciyarmu haka ake yi in za a haihu gobe za ki ga sun dawo da sabon yaro ko mace ko namiji, wanne ki ka fi so?
Na dan yi shiru wai zan yi zabi, nan da nan kuma naji bani da wani zabi bana ma dokin abinda za a haifan tunda naga wahalar da take ciki, bukatata kawai in ganta ne ta dawo gida lafiya.
Duk da kalaman da aka yi min na Inna haihuwa zata yi ba daga kwanciyata nayi bacci ba saboda na riga na tsorata da abinda na gani, daga baya ne kawai da yake shi bacci barawo ne ya sadado yazo ya dauke ni.
Farkawa nayi daga baccin nawa a dalilin nayi ya ishe ni ga kuma hasken rana da ya cika dakin da sauri na diro daga kan gadon na fito dakin da gudu, gidanmu nake nufin zuwa inga ko zanga Inna da sabon yaron da aka ce kan safiya zata haife shi Jumare na gani a zauren gidan ta rabe tana leke.
Nima na tayata yin leken don in ga abin da take gani, cincirindon jama’a ne gaba dayansu kuma maza babu mace ko daya gashi kuma yawan nasu yakai inda ya kai.
Can gefe ga yara ‘yan saffa suma maza mafi yawancinsu kuka suke yi. Da sauri na kalli Jumare meye a ke yi? Ta kara lekawa tana kokarin tantancewa kamar fa rasuwa a ka Yi amma ban sani ba.
Muna cikin haka sai ga makara an fito da ita daga cikin gidanmu da mutum shimfide a ciki, ina kallo a ka yi sahunan sallar amma wai ban gane Innata ce a ciki ba, ina ji Jumare tana gaya min wanda ya rasunne a ciki, na kuma ga zanin Innata lullube kan likafanin amma kwata-kwata ban kawowa kaina cewar ni ce na rasa Innata ba saboda ban taba zaton zan rasata a wannan lokacin ba, ban taba zaton zata daukan min mahaifiyata ta raba ni da ita kamar yanda tayi wa daruruwan yaran da ba za su kidayu ba.
“Waye ne ya rasu Jumare? Na yi tambayar cikin tsananin tsoro da firgita ba wai don ina zaton abin ya kasance ne a kan Innata ba, sai dai kawai don naga abin da ban taba gani ba, wanda kuma yayi matukar tsorata ni.
Na sake yi mata tambayar mai yawa na sake yi mata tambayar, da sauri ta ce min, “Ke ban sani ba. Saboda itama ta shiga wani yanayi na kuma yarda har a yau din nan na yarda Jumare bata san Innata ake sallata ba.
Ban san yadda aka yi ba ina ganin an dauki makarar nan an tafi da ita,dumbin Jama’a sun bi bayanta cincirindon yara suka yi ta dalewa kan manyan motoči za su bi don yi mata rakiya na kama kuka sosai da sosai Jumare tana ba ni hakuri.
Daga baya ne kawai na soma jin matan da ke wucewa ta bayan gidan za su shiga gidanmu, suna fadin “Ikon sai Ubangiji! Ashe Ramatu ce ta rasu?
Ban san yadda a ka yi ba, ganina kawai nayi a cikin gidanmu Yaya Dijah tana kankame dani a jikinta tana ta faman kuka, bai yiwuwa in tsaya kwatance ko bada labarin abinda ya faru. Illa iyaka dai kawai an yi zaman makokin Ina na kwana uku cikin matsananciyar kewa da jimami da addu’o’i ba daga wurin mu ya’yanta ko mijinta ko danginta ba kawai. Har daga wurinJama’a masu yawa da suka santa ko suka ji labarinta wurin kira da mutanen da suka san rayuwarta.
An watse daga zaman makokin Inna, ‘yan uwa da abokan arziki duk suka watse aka bar mu daga mu sai mu a gidanmu, ina nufin daga Babana sai ni sai ko Yaya Dijah da take nan bata koma dakinta ba.
Muna zaune gaban Babanmu ni da Yaya Dijah da take tashe da tsohon cikinta in ban da kuka babu abinda take yi, ni kam nayi kukan na gaji na bari watakila don ban gama fahimta ba ko gama gane girman abinda ya same ni shi yasa na hakura da kuka na koma zare ido.
To yaya za ayi ai sai hakuri kawai, ita kam ai ta huta wajen haihuwa ta rasu banda haka kowa alherinta yake fada, dubi kuma irin mutanen da ta samu, kiyi hakuri kawai ki bar kukan muyi ta addu’a Ubangiji ya gafarta mata, muka ce Amin.
Duk da hakurin da Babana ke ta bayarwa na muyi hakuri sau biyu ina ganinshi ya buya a dakinshi yana nashi kukan.
Rannan da safe Yaya Ibahim yazo gaishe mu dama kuma tunda a ka watse zaman makokin bai taba fashin zuwa gaisuwar ba, suna gama gaisawa da Babana yayi tasa mishi albarka.
Da zai tafi kuwa sai ya ce mishi in ka taso daga kasuwar ka biyo ta nan ka tafi da matarka taie gida ta huta a dakinta, sai kayi ta hakuri da ita.
Ya ce, To Baba yayi mishi godiya ya tashi ya tafi, rannan da yamma Yaya Dijah ta koma dakinta ba a wani dade ba kuwa ta haihu, ya mace ta haifa, Yaya Ibrahim ya sanya mata sunan Innarmu daga mu har Babanmu muka yi murnar alherin da yayi mana.
Babah Sumaye ce taje ta zauna mata tayi mata biki har tayi arba’in saboda Yaya Ibrahim da iyayenshi sun ki yarda da dawowanta gida suka ce tunda babu, Inna to me za ta dawo gida kuma tayi?
Sannu a hankali sai mutuwar Inna ta rinka shigarmu tana ratsa tsoka da kashi da bargo da zukatanmu, gaba daya ta makurkusa mu ta canza mu daga yanayin da duk muke tun ma dai ba Babana ba.
A farkon al’amarin ni kam ma gani na rinka yi tamfar karya ne tana can asibitin ne kawai watarana zata dawo wani lokaci kuma in rinka jin tanfar wani mummunan mafarki ne da zan farka in ga al’amarin ya sauya in da duk abin ba haka ba ne amma ina?
Sannu a hankali sai kwanakin suka fara tafiya daga daya har a ka je uku a ka yi bakwai har aka kwana arba’in ban ga Inna ta dawo ba, babu ita babu dalilintà sai dai yan uwanta da abokan arzikinta su dan zagayo su duba mu a duk sanda za su tafi kuma hakuri ne dai suke ba mu tare da fadin Ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa, ya kuma sa alherinta ya bita, amma ita kam shiru kake ji.
Wannan shi ne abinda yafi komai ba ni tsoro, a wannan lokacin sai na zama babu abinda nafi so irin in zauna in yi ta kuka saboda na riga na fidda ran sake ganinta tunda ban taba ganin randa tayi tafiyar da ta wuni ta kwana ba tare da ta tasa ni a gaba ta tafi dani ba.
In ban da kewarta da kadaicin babu abin da yafi komai damuna, ko ina yayi min fadi gani nake tamkar ni kadaice a raye babu wani abinda nake ji in ji na gani su balle in ji dadinshi in tsaya bayani, na kewar da Inna ta bar mu a ciki ma to na bata bakina ne na kuma san duk yadda nakai da jin wani abu’ kan rasata da aka yi to Babana yafi ni, illa iyaka dai kawai shi baya cewa komai.