Skip to content
Part 22 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Wani shirun na sake yi ban tanka mishi ba, to tunda ban taba cewa ina sonki ba, yanzu a wane matsayi ki ka ajiye ni ke nan? Ban kalle shi ba na ce mishi kayi hakuri, ina gaya mishi hakan fushin da yazo da shi ya gushe.

Rannan ina kwance a dakina cikin dare idona biyu bacci ne ya gagare ni, in ban da sakar zuci babu abinda nake yi, in saka wannan in kwance, in saka wancan. Aurena da Nalami da kullum Yaya Dijah ke cewa bata tabbatar za’ayi shi ba saboda jikinta da zuciyarta ba su ji kamar za’ayi shi ba.

Kullum kara matsowa yake yi, Babah Lantana da kawayenta tare da ‘yarta sai shirye-shiryensu suke tayi ko a ina take samun kudin a take ta kashewa oho.

Ni kam cikin zuciyata ban tabbatar da maganar ta Yaya Dijah ba tunda ban hango wani juyi da zai zo ya hana aukuwar auren ba, in dai ba wata kaddara ta Ubangiji ba ne tunda dai komai na auren Babah Lantana ta sayo irin wanda taga yayi mata daidai.

To haka zan zauna in yi ta zuba ido ina kallo har ranar auren yazo a daura a kai mishi ni? In har aka yi haka kuma to me zai faru? Me zai biyo bayan hakan? Wanne hali zan shiga? Wacce irin rayuwa zan yi a gidan Alhaji Nalami?

Rayuwar aure da Alhaji Nalami to a ya ya zata kasance ke nan? Wadannan sune jerin tambayoyin da suka addabi zuciyata, da na zurfafa cikin tunani mai tsanani sai naga aurena da Nalami kamar ba ya cikin jerin biyayyar da ya kamata in yi wa Babana, domin shima sa shi aka yi ba ra’ayin kanshi ba ne yin shi.

Ita kuma wacce ta hada din da ta hango wani alheri a ciki komai kankantarshi to da bani ta tura ba tunda ni kam ai bata nufina da wani alheri, to haka zan zauna in yi ta yarda kullum Babah Lantana sai ta cuce ni ta cuci Babana?

Ina kawowa nan na mike na sauko daga kan gadon na tsallake shimfidar Asabe da ke kwance a kasa na bude kofa nayi waje ko ban tafi na bar gida ba a yau ina son ganin yanda duhun dare yake in da hali ma kuwa ina ganin tafiyata kawai zan yi in yaso bayan wucewar ranar auren na dawo.

Sannu a hankali cikin sanda na nufi kofar gidanmu, zare sakatar na sake jawo kofar a hankali na rufe don kar in bar musu kofa a buda bayan kuma dare ne kasancewar dama kudina a kulle suke a bakin zanina yasa ban tsaya tunanin komai ba na kama hanya, hanyar baya na yi nufin bi don kar wani tsautsayi yasa in gamu da wani don in yi nisa da gida kafin gari ya waye in san in da na nufa.

Ban yi wata tafiya mai yawa ba naja na tsaya cak saboda muryar da na jiwo a bayana tana tambayata ina za ki cikin daren nan?

Kadan ya rago in karta da gudu saboda tsananin kaduwar da nayi in ban da kawai a kowane hali na kasance ko na samu kaina muryar da na jin ba za ta taba bace min ba, in dai ba Mubarak ba ne wannan to Aljani ne abinda naji zuciyata tana gaya min ke nan, to shi kuma me zai fito da shi waje a cikin duhun daren nan a kuma daidai wannan lokacin na karfe biyu da rabin dare, in ban manta ba abinda na gani ke nan a dakinmu kafin fitowàta.

Ina kike nufin zuwa a wannan lokacin? Kina nufin tana da asara in ki ka aikata wani abu makamancin wannan da kike shirin aikatawa? Ai bata da asara, watakila ma abinda tafi son gani ke nan.

Kalaman nashi suka sanya zuciyata ta sakankance cewa lalle shi ne ba wani aljani ba, don haka na juyo muka fuskanci juna, hasken farin wata yayi dalilin haduwar idanuwanmu nan take na soma kuka.

Kawo hannunki kiji, kawo hannunki kiji irin abinda kirjina ke gaya min, kawo hannunki ki taba nan din nan ban ba shi hannun nawa ba sai dai na dcga idona na kalli nan din da ya ke nuna min, mazaunin zuciyarshi ne.

Kwana nake yi ina zaune Maryam ban samu nutsuwar da na iya dora kafadata a kan shimfidata ba shi yasa nake barin dakin in fito waje in yi ta zirga-zirga tsakanin gidanmu da naku, tsoro nake kar su fake ni su sace min ke suyi sanadin shigata cikin halin da yafi wanda nake ciki.

Tunda na gane abin da suke son ganinn nayi kenan to amma yanzu da ki ka fito din nan za ki tafi ban sani ba yar uwarki bata sani ba, me ki ke nufi da yin hakan’? Kina nufin za ki iya bada kanki ga wani ne?

Kin san abinda barin gida ke nufi kuwa musamman wurin ‘ya mace? Kina nufin za ki iya tafiya inda za ki rayu ba tare da ni ba yar uwarki ba? Kina nufin in akwai alheri a cikin tafiyar taki ni ba zan baki wannan shawarar ba?

Don me ki ka shirya tafiya ba tare da kin nemi mu tafi ni da ke ba? Ke ce ba kya sona ki ke cewa ni ne saboda kawai ban ta6a buda baki na gayamiki ba, ban taba zaton sai na furta miki da fatar baki ba, baki ai yana furta karya Maryamu, zuciya kuwa takan tilasta gabobi suyi bayanin abinda ke cikinta.

Ban iya cewa Mubarak komai ba saboda kukan da nake tayi. Yi min alkawari a yau a in da muke tsayen nan a cikin sararin nan na Ubangiji cewar ba za ki taba fita ki tafi wani wuri ba tare da kin gaya min ko kin gayawa ‘yar uwarki ba.

Ki kuma yi min alkawarin ba za ki taba auren wannan mutumin ba ke ba shi kadai ba Maryamu yi min alkawari na wani ba zai taba taba min ke ba.

Nayi maza na gyada kaina tare da furta Kalmar nayi da bakina, duk kuwa da ban san yanda zan yi in cika alkawarin da yake tasa ni ina yi mishin ba, to muje in maida ke gida ki kwanta.

Nayi maza na girgiza kai nuna alamar a’a, cikin nutsuwa ya dago idonshi sama na tsawon lokaci kafin ya dawo da kallon nashi gare ni, kina ganin zai yiwu muyi ta tsayuwa a nan har gari ya waye? Da sauri na ce mishi eh, ya girgiza kai a hankali nuna alamar a’a mutane za su yi mana mummunan fahinmta marasa tunani daga cikinsu su zarge mu da abinda bai kamata zargin zai fi tsanani a kanki ba zan so ayi hakan ba, don zai iya zamowa bata suna zai iya zamowa dalilin da Baba zai yi fushi da ke, ba zan ji dadin hakan ba, ina so ki rabu da shi ne lafiya kin gane? Na gyada kaina nuna alamar na yarda.

Muje in kai ki gida, ban sake yin musu da shi ba ya tasa ni a gaba sai da yaga shigana cikin gidanmu har sai da na maida kofar na kulle sannan ya juya ya tafi.

Na sake yin wata sandar a hankali zan shiga dakinmu, sai kawai naji kofar dakin a kulle, abinda ya tabbatar min da cewar Asabe tana Kallon fitana daga dakin bata dai yi min magana ba ne, kawai sai da taji na fita na bar gidan ta mike ta rufe kofa ta koma tayi kwanciyarta.

Yaya zan yi? Abinda na tambayi kaina lokacin da na taba naji kofar dakin a kulle, fita zan yi in koma inda na baro Mubarak ko kuwa zama zan yi a nan in jira gari ya waye ta tashi ta bude in shiga? Ko kuwa sa hannu zan yi in buga kofar don taji na dawo ta tashi ta bude min in shiga? In yaso kowa ma yasan na fita da daddaren.

Har na matsa jikin kofar da nufin fara bugawa sai kuma naga kai to in Babana ya fito ya tambaye ni ina naje a cikin tsohon daren nan in ce mishi me? In yi sanadin da zai yi bakin ciki? Kai ba zan iya ba da in yi haka gara kawai in kwana a tsakar gidan in jira gari ya waye a bude in shiga in yaso ko don in kaucewa bata mishi sai in ce fita fitsari nayi Asaben ta kulle kofar.

Don haka na shiga kicin na hau kujera na zauna ina kallon irin berayen da ke zirga-zirga daga kicin din zuwa tsakar gida da wurin wanke-wanke wanda yawan ta’adin abinci ya kara haddasawa.

Wajen Asuba naga fitowar Babana zai wuce ban dakin gidan, nayi maza na kauce daga inda nake zaune na koma lungu sosai ya gamå abinda zai yi ya fita ya tafi Masallaci, sai ga Babah Lantana ta fito daga ita sai zani a kirji tana ganin kicin dinta a bude ta leko cikinshi tana haskawa. Satar min naman miya za ki yi? Kamar in tambayeta ko ta taba ganin inda da ya zamaa barawo a gidan ubanshi? Sai kawai naga to a na me zan tsaya ina irin wannan cacar bakin da ita, bayan ta riga ta buge ni tayi nasara a kaina tasa Babana ya dauke ni ya baiwa mutumin da babu wanda yasan me ke tsakaninsu sai su biyun suka san abinsu.

Ba fa satan miki naman miya taje yi ba, iskancinta ta tafi shi ne ni kuma na maida kofar na kulle ta dawo ta same ta a kulle shi ne ta shiga kicin din ta zauna don kar ta buga kofar a ji ta a tambayeta daga ina take? Iskanci kamar ya ya? Ta bukaci sani.

Asabe ta tsaya tana yi mata bayani, ai dama rana dai-dai ne bata bude kofa cikin dare ta tafi can wajenshi sai sunyi abinda za su yi sannan ta dawo ta shigo ta kwanta gajiya nayi jiyan na rufe mata kofar.

Babah Lantana ta tabe baki ta ce, ki ka sani ma da ba ki rufe mata ba kin barta ta shiga tayi kwanciyarta ta huta ni kam yanzu ai bani da sauran matsala da ita balle har in je ina kai kararta wajenshi a kan tana zuwa kwanan gida, to a na me?

Kwanaki tara ne fa kacal suka ragewa zaman nata a cikin gidan nan, gidan da kullum sai ta yi wa mutane gorinshi sai kuma ta koma gidan Nalami, Nalami kuwa wannan matar tashi in dai tana nan a yanda nasan ta tooo ta dan yi murmushin iya shege ta wuce ta shiga bayan gidan tana fadin, dama in mutum ya ce ba zai yi sharar masallaci ba ai zai yi na kasuwa.

Duk abinda suke fada ina jin su shiru kawai nayi saboda ba ni da wani abinda zance musu in huce bakin cikin da suka sanya ni a ciki.

A haka muka kasance a çikin gidan nan har a ka wayi gari ana cewa saura kwana biyu ne daurin  auren nawa abinda yayi dalilin da na zama tanfar mara hankali saboda tsananin kidima da gigicewa, babu abinda bai zo ya roki Babana ba amma yayi shiru bai ce komai ba.

Babah Lantana sai hidimarta take yi, babu abinda yafi komai daga min hankali irin tsananin farin cikin da take ciki, wuni take yi tana Dariya bata gaji ba, kan abinda bai taka kara ya karya ba ma sai ta kyalkyale da dariya ta bugi cinya tare da shewa kafin ta ce sai ni Lantana ‘yar Babanta, mata a gidan Mallam Habu mai timatir, kowa yaci tuwo tare da ni miya yasha.

In rasa in da zan tsoma raina in dan ji dadi nayi kuka a wannan lokacin har na fige na fita cikin hayyacina, ga shi bana ci ba na sha nayi mummunar ramar da na zama tanfar majinyaciya, wai a irin wannan halin da nake cikin kuma sai manya su rinka zaunar da ni suna cewa wai in yi hakuri wata rana sai labari.

Ba don dai kar in yi wata magana na ce na fadi ba daidai ba ga shi ni kuma a’ yanzu nema nake in rabu da kowa lafiya don gani nake tanfar ba zan wuce wannan lokacin ba, bakin cikin da ke addabar zuciyuata zai kashe ni kowa ya huta, da na tambaye su ni yaushe ne wata ranar nan da kullum a ke gaya min amma ban taba ganin tazo kan al’amarina ta mayar min da shi abin bada labarin ba?

A wannan lokacin ko gidan Yaya Dijah ba na iya zuwa saboda rashin kuzari na wuni nake yi a kwance kamar yadda nake kwana a kwance don haka ban san abinda take ciki ba amma dai itama na gaya mata na gaji da jin zancenta na bata tabbatar za’ayi aurena da Nalami ba saboda wai jikinta da zuciyarta ba su yardan mata za’ayi hakan ba.

Na ce to sai yaushe za su yarda? Sai sun ganni a dakinshi? Daina gaya min haka Yaya Dijah, bar ni kawai in fuskanci abinda yake gabana, ina fadin hakan ta kama kuka nima ban tsaya bata hakuri ba nasa kai na fita na bar gidan, ban sake komawa ba.

Mubarak kuwa sai yazo kofar gidanmu sau biyu sau uku ban iya tashi na fita ba saboda bani da jarumtakar yin irin wadannan abubuwan kuma a wannan lokacin sai nafi sha’awar a ce kowa ya fita harkata a bar ni kawai ni kadai in yi ta kwanciyata ina tunanin Innata da sauran abubuwan da sukai saura.

Bikin nawa ba wani biki ne da Babah Lantana tayi wa wani sayayya na abin arziki ba, amma ta shirya kawatashi ta hanyar tara tsofaffin kawayenta da suka yi gwagwarmayar rayuwarsu tare har ma da Dafau Mai kalangu naji tana cewa zata kira.

A al’ada ranar sakun lalle rana ce da Amarya tare da kawaycnta kan tafi yawon ban kwana, sai cikin dare take dawowa in an je an kamo ta a kawo ta gida a sa mata lalle, a irin wannan ranar ni na wayi gari ne a kan gadona ina kwance babu wata kawa a tare da ni ba a kira min ita ba nima kuma ban nemarwa kaina ita ba.

Ina daki a kwance ina kallo Asabe ta sha kwalliya ta fita itama Babah Lantanar hidima sosai take yi tare da ‘yan bikin da suka fara zuwa mata.

Ina daki ni kadai in saka wannan in warware in saka wancan wai Nalami Babana ya yarda zai bada aurena gare shi in zama mallakinshi?

To zai yi hakan a dalilin ya daina sona ne ko kuwa dai da gaske abin yafi karfin nashi ne? Wannan shi ne abinda yake ta kai kawo a cikin zuciyata.

<< Halin Rayuwa 21Halin Rayuwa 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×