Da daddare kawar Babah Lantana ta sani a lalle saboda babu wanda ya tako cikin gidan, cikin dangin Innata da Yaya Dijah don sun ce babu ruwansu da bikin.
Ni da mai sakun lallen kallon juna muke yi da ido zuru-zuru ta juya tana fadin oh’oh amaren yanzu suna da abin mamaki babu ruwansu da kuka don an saka musu lalle.
Babah Lantana ta taso daga inda take tana fadin ai bata yi kukan sakun lallen ba, ita wannan ai tata rashin kunyar ta daban ce, ni kuma ba a wannan abinda ni bari ka gani, in na zo na sharara mata mari ai zata yi mai dalili.
Ta zabura ta taho cikin saurinta da nufin shararan min marin, wasu cikin kawayenta masu dan hankali suka tare ta tare da fadin a’a haba mai shararawa Amaryar tana cikin lalle ki sharara mata mari me yayi zafi haka?
Ina ruwana ni da lalleta tunda dai bata da mutunci a sa mata lalle ta ki yin kuka saboda ta matsu a kaita gidan mijin ko me? A haka dai ana wasa ana dariya a ka cimma burinta na dukana a cikin taron kawayenta da ta tara a gidanmu.
Wata daga cikin kawayen nata da naji suna kira da sunan Lari baby duk da kokkodewarta wai baby take amsawa, ta matso kusa da ni cikin natsuwa ta ce min kin gani ko Amarya ” yanmata ke yarinya ce don haka zan gaya miki lamarin duniyar nan sai a hankali, kar ki yarda kiyi abinda za ki cuci kanki.
Zauna wuri daya kawai ki nutsu kar kiyi abinda zai je yazo ya dame ki shi lallen nan da ki ke gani ba karamin al’amari ba ne, wasa da hakkokinshi wurin amarya al’amari ne babba. Shi ke sawa kiga wasu amaren sun zama wasu, kar ki yarda ki ce za ki fita daga dakin nan ki fita waje kin ji ko?
Amarya mai fita da lalle haukacewa take yi kin ji ko? Na ce mata to, saboda tsoratar da nayi da irin bayanin da tayi min din.
To ina ruwanki ne da ki ke rattabo mata wannan bayanin? Tayi tambayar tare da galla mata harara kai ke daima da dogon baki ki ke, taja tsaki ta juya ta fita.
Uh’uh Anti Lantana gara in gaya mata ta sani shi da ai na kowa ne, ai sai kiyi ta fita ta fita. Duk da bayanin da matar nan tayi min zuciyata bata hakura ta bar ni na zauna lafiya ba, kai-kawon da take yi yayi tsanani ko mikewa a gadona gagarata yayi ina zaune ne kawai ina sauraron abubuwan da take gaya min.
Daren nan na yau shi kadai ne yai saura min gari na wayewa za a daura min aure tunda daurin auren ma na safe a ka ce za’ayi kenan daga nan zuwa wayewar gari ne yai saura min, to haka zan zauna shi ke nan magana ta kare ko kuwa ya ya zan yi?
Shi ke nan sai in zauna a daura min aure da mutumin da Babah Lantana ta kawo min? da Babana ne don ra’ayin kanshi yaga zai bada ni gare shi da ba zan yi jayayya da auren ba tunda ni din mallakinshi ne, to amma Babah Lantana, in zauna in karasa waycwan gari a cikin gidan nan yana nufin na yarda da auren da za’a daura min.
In sa kai in fita kuma ina tsoro saboda bayanin kawar Babah Lantana tayi min, ina cikin wannan kai kawon sai kawai na tsoro matsayar da ta sanya ni mikewa tsaye ita ce ta da in zauna a daura min aure a kaiwa Alhaji Nalami ni gara kawai in fita in bar gidan in yaso duk abinda zai faru da ni ya faru dani a can gaba.
Da wannan tunanin cikin zuciyata nasa kai na fita daga gidanmu sai dai ban san yadda aka yi ba ganina kawai nayi na kama hanyar zuwa gidan su Mubarak.
Ina dosar gidan na hango shi zaune a kan dakalin kofar gidansu yayi zaman dirshan a kasa kanshi a sunkuye, har na isa kanshi bai ji motsi ba saboda ya riga ya shagala kan abinda yake yi.
Na kasa ce mishi komai don ban san me zan ce mishi ba, kusan mintoci biyu zuwa uku kafin ya dago kai daga sunkuyon nashi yana ganina ya dan kadu bai ji isowar tawa ba da sauri ya shiga goggoge fuskarshi da tafukan hannayenshi duka biyu.
Me ya fito da ke a cikin daren nan? Tambaya yayi min cikin wani irin yanayi na nuna karfin hali da jarumtaka ban tsaya ba shi amsa ba sai kawai nasa kai na nufi cikin gidansu, maimakon in wuce can ciki kamar yanda na saba kofar wurinshi na tura na shiga nasa kai na wuce falon na shiga har can cikin dakin nashi abinda bai taba faruwa ba a rayuwata hasalima yau ne shigana wurin Mubarak na biyu.
Can cikin dakin nashi a kayace yake matuka ga kamshinshi da na saba ji a tare da shi katuwar katifa a yashe a kasa tasha shimfida mai daraja ga tarkacen takardu tare da laptop a gefe sai wardrope wacce na tabbatar kayanshi a ciki. Gabana sai faduwa yake yi yana harbawa da sauri da sauri, me ke shirin faruwa ne? me ya shigo da ni nan wurin? Abinda ke ta kai-kawo cikin raina ke nan.
Mubarak ya biyo ni har can cikin dakin yaja ya tsaya a bayana cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da tsorata da abinda yaga nayin me ki ke so a kawo miki Maryam? Ban tanka ba ban kuma waiwaya na kalle shi ba, na kai guiwowina duka biyu kasa na durkusa a kansu, ya sake biyo ni kasan yayi yanda yaga nayi muka fuskanci Juna.
A hankali cikin nutsuwa cikin wata irin murya mai laushi da taushi a dalilin karaya da tsoratar da tayi na soma yi mishi magana, zuwa nayi a yau don in yi maka godiya bisa dawainiyoyinka da alhairorinka a garce ni.
A sanina ban taba sanin wani mutumin da ya kai ka yawan alhairi ba ka taimaki maraicina ta hanyoyi daban-daban da ba zai yiwu in fade su ba.
To me ya kawo wadannan maganganun Maryam? Yayi min tambayar a sanyaye idanuwanshi kuma suna kafe a kaina. Na kawar da kaina daga kallon da yake yi min kafin na soma ce mishi Babana yayi nufin aurar da ni ga wanda yayi niyyar bada ni gare shi bana zaton akwai wani dalili da zai hana shi yin abinda ya shiryan in dai ba wata kudura ba ce ta Ubangiji.
Ban ki auren don raina maganarshi ko bijirewa umarninshi ba, naki auren ne a dalilin sanin dalilin kulla shi da aka yi a yanzu ina cikin wani hali da ba zai fadu ba, don haka nazo wurinka in roke ka kayi min wani alheri tunda kai mai alherin ne kullum a gare ni.
Da sauri ya tambaye ni me ki ke so in yi miki Maryam? Gaya min shi ko menene shi zan yi miki.
Na sake sunkuyar da kaina kasa sosai kafin na soma ce mishi, ni din budurwa ce nafi zaton daren yau shi ne dare na bankwana a tsakanina da kai, don haka nazo wurinka ne in yi maka kyauta daa abinda nake ganin tanfar naka ne.
Muryata ta soma rawa jikina ya soma kaduwa, hawaye suka soma gudu daga idona suna zuba shar! Shar!! Shar!!!! Gabadaya hankalin Mubarak ya sake tashi, ya tsunduma cikin wani hali da ya fi kama da kidima.
To menene na wannan kukan? Me ki ke so in yi da ki ke wannan kukan yanzu a gabana? Na ce ki gaya min kawai ko menene zan yi miki shi, kiyi shiru. Nace kiyi shiru.
Kwan! Kwan!! Kwan!!! Muka jiwo kwankwasa kofar falon nashi, lokacinne na san bai shigo ba sai da ya kulleta da sauri ya mike wajen kofar ya bude.
Me ke faruwa ne Ahmad Mubarak? A hankali naji Umma tana yi mishi tambayar, me ki ka gani Umma? Ta dan yi shiru kafin ta ce mishi ji nake kamar ba kai kadai ba ne. Ya sake cewa me yasa ki ka fadi haka Umma?
Ta canza tambayar da tambayarshi to me ka ke yi har yanzu idonka biyu? Bakin ciki ne ya dame m Umma, ina bakin cikin raba ni da Maryam da a ke son a yi.
Rabuwa kam ai an raba ka tunda gari na wayewa za a daura aurenta, kai dai kayi hakuri. Kamar yau ne za ka ga ya wuce wata rana kuma ai sai labari, ko ma ka kwanta kar in sake Jin ka a waje, ya ce mata to.
Ta juya wurinta shima ya maida kofar ya kulle ya dawo har lokacin ina durkushe a inda ya bar in ya sake kai guiwowin nashi kasa ya sake durkusawa kamar yanda dama yayi muka fuskanci juna.
Da gaske ne Babana zai raba mu don haka nake so in yi maka kyauta ta alfarma don ta zamo girmamawa ga al’amarinka da ke cikin zuciyata.
Yayi ajiyar zuciya mai karfi kafin ya tambaye ni mecece kyautar taki Maryamu? Ban kalle shi ba na ce mishi ‘BUDURCINA’ yayi matukar kaduwa da jin kalmar da na furta, don kuwa sai da hakan ya bayyana a fuskarshi, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi karbi budurcin kawai a wurina bani da sauran bukatarshi bada shi zan je gidan nashi ba shi yasa nazo’ yanzu don in kawo maka shi.
Mubarak ya zama tanfar wani mutum-mutumi sai faman bari yake yi tanfar wanda yayi wanka da ruwan sanyi a cikin sanyin hunturu, da kyar ya buda baki ya soma yin magana, a’a kar muyi haka, ba sai kin yi min haka ne zan san ina da matsayi mai girma a wurinki ba. In kin bar shi a nan ma nawa ne, ai nawa I Maryam zan kuma karbe shi ai ke tawa ce na kuma yi sa’a kin gane ke din tawa ce, kar kiyi gangancin bada shi ga kowa.
Na dan dago kadan na kalle shi a rikice kwarai yake bakinshi ne kawai mai jarumtakar furta kalmomin da yake fadin. Ba ka sona? Da sauri ya soma fadin ina sonki mana Maryamn, ina sonki, ya ya ma za ki ce bana sonki? Ina sonki, ina son ki, ina sonkki.
Ina jin ya fara furta irin wadannan kalmomin na soma cire kayan da ke jikina ina ajiyewa a gefe dai-dai da dai-dai, kan kace meye wannan sai gani na zama daga ni sai ‘yar shimin da ke jikina wacce bata ma gama sauka kasa ta cinyoyina ba, itama na saki hannayenta kirjina ya bayyana na maida hannayena baya don balle rigar nonon shima in ajiye shi a gefe.
Da sauri Mubarak ya taso yana fadin uh’uh Maryam uh’uh kar muyi haka wannan kam ba zan barki ki cire ba, ya miko hannu da nufin hana ni cireta, a wannan lokacin kaduwar da yake yi takai duk inda takai, kar muyi haka Maryan maida rigarki jikinki kiji abinda zan gaya miki. Yayi maza ya mike ya shiga wata kofa da ke cikin dakin zuban da naji ruwa yana yi ya fahimtar da ni ban daki ne.
Kusan minti biyar kafin ya fito yanayinshi ya sauya daga yanayin da ya shiga bayan gidan, a ciki can gefe ya koma ya nemi wuri ya zauna ya soma yi min magana a hankali, shiga ki yi alwala za ki dan ji sanyi a cikin ranki.
Kaina a sunkuye na ce mishi uh’uh kar kiyi tunanin bana sonki ko kin fi ni shiga cikin wata damuwa duk wami abinda ki ke zato a kan wannan al’amarin na shigo abinda yafi haka, ina sonki fiye da duk yanda zuciyarki take iya kwatanta miki, son naki kuma zan iya cewa yana daga cikin dalilan da suka sa ba zan iya yin hakan da ke ba, don kina da girnma da kinma mai yawa a wurina.
Mahaifiyarki tana dashi, iyayenmu mutanen kirki ne, yin hakan kuma ba zai rage min komai ba na daga ciwonki da nake ji cikin raina, hakika na sani an zalunce mu ko kuma in ce ana Shirin zaluntarmu tunda har yanzu ban tabbatar da daurin auren ba, ina sonki ne ba don sha’awa ba, ina sonki ne ba don kaina ni kadai ba, ina sonki tare da girmamawa da mutunta duk wani al’amari naki.
Don haka ba zan so mu aikata wani abin da zai taba mutuncinki ba, don haka mu kara hakuri da Juriya da jaruntakar da zamu kai ma cimma nasara kar mu sanya sabon Ubangiji a cikin lamarinmu, ko kin taba jin inda darajar mutanen da suka gama rayuwarsu ta duniya suka koma ga Ubangijinsu ba su taba aikata zina ba a ranar Alkiyama?
Ina yi mana fata da addu’ar shiga cikin irin wadannan manyan mutanen da muyi haka Maryam gara mu kama hanya mu bar garin ni da ke muyi tafiyarmu zuwa can wani wuri muyi zamanmu su neme mu su rasa, sai komai ya lafa mu dawo kin ga lokacin komai ya warware sai a sake gabatar mishi da maganarmu.
Ban ce mishi komai ba ban sake daga ido na kalle shi ba, saboda kunyarshi da ta kama ni, girma da darajarshi da kimarshi suka yi matukar karuwa cikin raina, zuciyata ta kara tabbatarwa tare da sakankancewa cewa tabbas Mubarak mutum ne mai girma da daraja wanda bai nuna son kai kan abinda yake so.
Bai saurari yardata ko rashin yardar ba ya mike yana fiddo kaya a cikin wardrope dinshi da yawansu kayan mata ne gaba dayansu kuma sabbi, sunkin kudi ya dauko yana kokarin adana kudin a jikinshi yana yi min bayani muje in kai ki in da za ki zauna in kuma zauna tare da ke in tsare mutuncinki har kafin wannan maganar ta lafa sai in…
Bai kai Rarshen maganar ba muka ji ana buga kofar dakin nashi da karfin tsiya, tare da hayaniya mai yawa, alamar dai mutanen da ke dukan kofar ba mutum daya ba ne ko biyu adadi ne na Jama’a masu yawa.