Gabana yayi mummunan faduwa nan take kuma jikina ya dauki rawa nayi matukar tsorata, tsoro kuma matsananci irin wanda ban taba jin irin shi ba a rayuwata saboda gane muryar Babah Langana da nayi a cikin masu maganganun nan.
Wayyo! Wayyo!! Jikina sai rawa yake yi. Mubarak ya zuba min ido yana kallona cikin tashin hankali saboda shima a tsorace yake amma duk da haka kokari yake ya rarrashe ni ya kwantar min da hankali kan irin tsoratar da yaga nayi. Kai ku bar dukan kofar nan haka ina ganin kamar babu kowa a ciki, wata daga cikin matan da ke wurin ne suka fadi haka.
Babah Lantana tayi maza ta ce, a’a ai babu maganar bari a tunbuke min kofar gaba daya sai na shiga na gani da idona na gaji da iya shegen da ake yi min ina kallo duk wanda yayi a baya bai ishe shi ba sai yayi a yau dinnan na daren aurenta masu bugun kofa suka ci gaba saboda a umarnin da Babah Lantana ta basu ga dukkan alama kuma so suke su tunbuke kofar dakin da gaske.
Kai haba wane irin hauka ne wannan? Umma ce ta iso wurin take yin tambayar kai ku bar wannan abinda ku ke yi in ba so kuke ta jawo muku abinda zai dame ku ba.
Me zai dame su? Ai in abinda danki ke yi bai dame shi ba wannan ba zai dame su ba tunda shi da yake kwana da matar wani bai ji tsoro ba sa masu tun6uke kofa? Mero ai matar wani ce tunda gari na wayewa za a daura aurenta in kuma takamarka iya shege to bari in gaya maka, shi mijinta ya fi ka sanin kan tsiya don shi wannan in yaga dama zai iya kasa tsiya a tire ya saida ita saboda saninta da yayi.
To ta shafe ku ku kadai in ji Umma, kai ku kauce ku bani wuri in yi magana da shi, in kuma bata ciki to zan yi maganin rashin mutuncinki, za ki gane ba ki da wayo zan nuna miki ke din mahaukaciyar tsohuwa ce sau uku kenan kina kulla mishi irin wannan sharrin, to daga yau ba za ki sake ba.
To in aka same ta a ciki fa? Uwar banza mai daurewa danta gindin yayi lalata da matar aure. Da kyar a ka shiga tsakanin Umma da Babah Lantana ba don yawan mutanen da ke wurin ba da ba karamin gwabzuwa suka yi ba don kuwa su dukansu biyun majiya karfi ne.
Umma ta matso kusa da kofar ta jijigata ta ji ta a kulle kana ciki ne Ahmad Mubarak? Da sauri ya amsa mata da eh Umma, ina ciki. To zo ka bude min kofar mana don wannan azzalumar taji kunya ta gane kai ba irin abinda take zato ba ne.
Ya mike ya nufi bakin kofar duk da sanin ina cikin saboda ta ba shi umarnin budewa, ina ganin ya kama hanyar fitar jikina ya kama rawa kar-kar-kar saboda sanin da nayi bude kofar yana nufin Babah Lantana tana da mutanenta su ganni.
Masharranciyar mata kawai wacce ta rasa wanda zata tasa a gaba da cuta sai marainiyar ‘yar mijinta, ai kin ji kunya za kurma ki kara jin kunyar tunda baki da aiki sai na kullawa ‘ya’yan Jama’a sharri ba kin haifa ba ke ma?
Bude kofar Ahmad Mubarak ya sake cewa to Umma abinda na tabbatar kuwa shi ne shima ba son bude kofar yake yi ba, iyaka dai kawai ba zai iya bijire mata ba ne.
Kar wanda ya shigo min daki, kar wanda ya matso min nan in baso yake ranshi ya abinda naji ya fara fadi kenan daga bude kofar tashi, ga dukkan alamu kuma kashedin nashi ya shige su don ban sake jin wani yana yunkurin shiga ba.
Uhun yasan ba shi da gaskiya yasan in an shiga za’a fito da ita ne shi yasa yake wannan zare idon, Babah Lantana ce mai fadin hakan.
Ke matsa ni ki bani wuri ja’ irar mata kawai da tun zuwanta unguwar nan take haddasawa Jama’a da ‘ya’yansu fitintinu iri-iri da sharri daban-daban sai ya koma miki kanki.
Babah Lantana ta ce eh fadi duk abinda za ki fada naji ba kuma zan bar nan wurin ba sai an fito min da ita sai an fito min da ita kin daurewa danki gindi yana lalata ‘ya’yan Jama’a, wannan dai ya isa haka wanda a ka yi a baya ya isa na hana kumna tunda nayi mata miji zata je gidanshi ta zauna a can sai kuma ki sake neman mishi wata tunda da saninki yake yin komai.
Ban sani ba ko Mubarak yayi yunkurin yiwa Babah Lantanan wani abu ne naji Umman tana ce mishi a’a-a’a kyaleta a kanta sharrinta zai kare ba dai kin iya hawa kan laifin ‘ya’yanki ki hango na ya’yan wasu ba ai kina da shirin shan mamaki.
Kai Mubarak gaya min gaskiya kawai kasan inda Mero take? A natse ya ce mata eh, da sauri ta sake tambayarshi tana ina nc? Ban ji yayi wata magana ba kafin na sake jin Ummanshi ta tambaye shi tana wurinka ne?
Ya ce mata eh Umma, tana wurinka fa ka ce? Ya sake cewa eh Umma, da dukkan alamu Umma ta firgita kwarai da jin da tayi Mubarak ya amsa ina cikin dakinshi.
Ahaha, da kin ce bata ciki gashi tana ciki kin ce ke danki na kirki ne gashi ya bayyana miki cewar yafi na kowa lalacewa kin ji kunya kin ji kunya abinda Babah Lantana ke gaya mata ke nan.
Da kyar ta iya buda baki ta ce mishi to fito musu da ita, kan ya ce komai sai Babah Lantana ta sake café zancen da fadin to ba dole ba, ba dole ba ma ya fitowa mutane da matarsu ba, matar mutane ce fa ya samu yana tur…kai tir da wannan baki naki kin girma ba ki san kin girma ba?
Ke kin san kin san, kin girma da ki ke daure mishi gindi yana lalata ‘ya’yan Jama’a shiru Umma tayi bata tankawa Babah Lantana ba to fito musu da ita ta sake ba shi umurnin, in fito musu da ita Umma? Bata tsaya ba shi amsar tambayar tashi ba sai kawai naji shigowarta.
Kan ka ce meye wannan sai gata tsaye a kaina hannu da sakata kama ni ta jawo ni muna isowwa falon muka gamu da Mubarak ga dukkan alamu biyo ta yayi yaga abinda zata yi kar ki ba su ita Umma muna gamuwa abinda ya fara cewa ke nan.
Na roke ki kar ki ba su ita yana nata rokon nashi saboda ganin alamar ba za ta saurare shi ba, tana jin haka ta saki hannuna ta juyo gare shi a fusace tau! Tau!! Tau!!! Wasu irin zafafan marika ta sakar mishi a jere cikin sauri har guda uku.
Jikina ya sake daukan wani rawan kar-kar-kar na kara tsorata wani irin matsanancin tsoro ban taba ganin dan gata kuma shagwababben da irin Mubarak ba, amma ga abinda Umman tayi mishi a yau a kaina kuka sosai na kama yi yayinda Mubarak ya kai guiwowinshi duka biyu kasa kiyi hakuri Umma bata saurare shi ba ta sake kama ni muka yi waje ta dankawa Babah Lantana ni a bannunta, to yi waje ku bani wuri.
Yanzu kuwa kin taba ganina a gidanki in ban da yau? Kin taba ganin kafata ta tako cikin gidanki? Gidanki ai ba gidan zuwa ba ne, gidan da uwa ke daurewwa danta gindin ya rinka lalata ‘ya’yan Jama’a? ai kukan karya ki ke yi.
Duk abinda Babah Lantana ke fada Umma ba ta ce mata komai ba kuka kawai take yi sai dai bansan asalin dalilin kukan nata ba na ganina a dakin Mubarak ne ko na tausayin al’amurana ne oho.
Babah Lantana ta damko ni tamfar zata karya kashin hannun nawa saboda tsananin rikon da tayi min bayan kuma ni ko nuna alamar jayayya ban yi ba.
Muna tafiya sauran Jama’a suna biye damu a baya duuuw! Ita kuma tana bayani duk da daren ba mai boye sirrin magana ba ne, tun bata isa komai ba yarinyar nan take bin maza, nan in da ku ke kallonta babu irin lalacewar da bata sani ba in a kan namiji ne babu kokarin da ban yi ba a kanta abin ya faskara, a ce yarinya kamar wannan ta iya bin namiji har gidanshi taje kwanan gida? Ai kuwa randa ta rika akwai magana kenan, ni wannan tana da aiki ko in ce mijinta yana da aiki in ba a dace ya zamo irin ta ba.
Ga dauke-dauke ko bera bai fi ta sata ba, ni fa yanzu da lalita nake yawo saboda duk inda zan ajiye zata dauka tanfar mai wankin ido take tayi na kudi tayi na naman miya, bani da halin in motsa a gidana sai tayi min ta’adi bani da sakat.
Bayanin nata ban sani ba ko ya gunduri wasu daga cikin Jama’ar tata ne naji wata mata daga bayanmu ta fara cewa ba a yi wa da irin wannan tonon asirin Lantana musamman ma da yake ke din uwarta ce ba a bakinki ya kamata a ji wadannan kalmomin ba ai tsakaninki da ita addu’ ar ce Ubangiji ya shirya mana musamman ma kuma da yake yau din nan shi ne darenta na karshe a tare da ke zata gidan mijinta gobe kamar yanzu fa ita din matar aure ce tana can a gidan mijinta.
Cikina ya bada wani irin mummunan sauti na kulululu! Saboda jin da nayi ta ce, gobe kamar yanzu ni din matar aure ce ina gidan mijina.’
Addu’a ya kamata ki dage kiyi tayi mata na Ubangiji ya shiryeta ta bari fiye da haka ai anyi an kuma bari kawo ki ka gani yana rayuwa yana da kuskuren da ya aikata lokacin kuruciyar wanda in da za a sake dawo mishi da kuruciyar tashi a yanzu ba zai maimaita wancan abin ba don ya gane bai yi wa kanshi daidai ba.
Wata can daga gefe ta sake cafe maganar itama maganar take yi shi sabulun wankan aure ma wani irin siddabaru ne da shi saboda sabulu ne mai albarka wanke dauda yake yi yayi tas, ya wanke duk wani mugun hali ya zama mai kyau mara hankali ta zama mai hankali kiga an kai yarinya daki ana tsoron al’amarin ta sai kuma kijita shiru ta zauna sai wanda yasanta yasan kuruciyarta shine kawai zai san ta taba yin wani abu.
Babah Lantana taja wani mummunan tsaki wato nan duk bayanin nan da nake yi muku haushina ku ke ji da sauri dayar ta ce ba haushinki ba ne muka ce kiyi mata addu’a ta sake jan wani tsakin to da addu’arta zan ji ko da ta nawa ya’ yan? Gaba daya suka hada baki wajen cewa aiya kin yiwa wani addu’a kin yiwa kai ne don kuwa ita addu’ar yana daga cikin sharadin karbanta in ka yi wa kanka ka hada da sauran Musulmi baki daya da kuma za ka bar yiwa kanka ma ka koma ba ka da aiki sai na rokarwa al’ummar Musulmi ko wani dan uwanka to kai ma da kaga biyan bukatunka cikin sauri.
Babah Lantana ta ce, ai sai kuyi tayi ina jinku wannan dai babu abinda zai sa in zauna ina bata lokacina kan wannan ba don ni kadai ni nasan irin abinda ta guma min iyaka dai tunda zaman namu tare yazo karshe shi kenan magana ta kare, zata je gidan mijinta nima ta bar ni in zauna da nawa mijin lafiya a gidana, aniyar kowa kuma ta bishi, kowa yayi shiru yana jinta babu wanda ya sake ce mata wani abu.
Muna shiga gida naji ta kai min wani irin wawan dukan da ban zata ba sai da na kife a kasa saboda tsananin buguwan da nayi nan take kuma ta biyo ni ta sake dannewa tana duka tana fadin har a daren ranar auren naki ma sai kin je kwanan gida duk wanda ku ka yi a baya bai ishe ku ba sai kin sake kai mishi kanki a yau saboda ki samu kaiwa dan uwana kazantarku ko?
Tana yi tana duka tana mintsini tana bugun kai a kasa, ga kuma bayanin da take yi fatanki da bai wuce ki sa mutanc su zage ni su ce ban iya tarbiya ba, toaniyarki zata biki dadin abin kuma shi ne ba ke kadai ba ce a gidan ga yar uwarki nan Asabe ita ce gaba da ke ko da yake ba sosai ba ne amma sai ki tsallaketa tana kwance kije wurin iya shegenki tana kallo babu ruwanta saboda bata gaji wannan tsiyar ba.
Mafi yawancin mutanc suka fusata da dukan da Babah Lantana ta rufe ni da shi fadi suke yi haba a ina ake wannan abin amarya kuma ayi mata duka tun a wurin sakun lalle take burin dukan yarinyar nan a ka hanata shi ne yanzu ta fake da wannan abin tayi mata irin wannan nagazawar.
Aka kwace ni da kyar daga hannun Babah Lantana a ka kai ni daki a ka zauna da ni na makure wuri daya cikin tsananin takaici da bakin ciki ga masifar 6acin ran auren dolen da tasa ayi min ga bakin cikin azabar da ta gana min ga wulakantani da tayi wurin mutanen da ba su sanni ba, babu ma kuma abinda ya hada ni dasu balle su san sharri ta kulla min na maganganun da ta fadi a kaina.
Ina zaune ina kuka yayinda mutane a tsakar gida suka yi cincirindo suka zagaye Babah Lantana suna sauraron karin bayanin da take yi musu a kaina na game da mugayen halayena sai kawai naga wata mata da ban santa ba ta fado cikin dakin tana shigowva tasa hannu caraf ta damke hannuna.
Nayi kamar in kurma ihu saboda tsananin tsoro don nayi zaton ko bayanin da Babah Lantanan ke yi musu ne ya kara fusatata har taga bari tazo ta ja ni kawai zata kai ni a sake yin rubdugu a lakada mini wani uban dukan.
Sai naga tayi maza na dora dan yatsanta a baki tare da fadin shhhhi alamar kar in yi wani motsi mai karfi da zai jawo hankalin Jama’a gare mu, don haka na mike cikin nutsuwa ina biye da ita sannu a hankali cikin hikima da kulawa ta fitar dani daga cikin tirmitsin Jama’ar nan ta nufi kofar gida da ni.
Muna fita waje ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce min kama hanya kiyi tafiyarki kin ji yarinya, wannan fitinar tayi yawa je ki abinki babu wani abinda zai same ki sai alheri shi da ai na kowa ne babu mai yi mishi sharri sai wawa.
Zuba mata ido nayi ina kallonta a tsorace gani nake tanfar wani sharrin take so ta sake kulla min don gani nake tanfar duk wani wanda yakc tare da Babah Lantana mugu ne sai naji ta ce min, ke fito da ke nayi fa don ki samu kiyi ta kanki, yi maza ki bar wurin nan tun bata ankara ta gane ba kya nan a cikin gidan nan ba.
Kallon da nake yi mata cikin tsananin tsoro ne wata kila ya sa ta maimaita cewa yi ta kanki na ce don ki samu ki kubuta daga sharrin wannan muguwar ja’irar, ta sake maimaita kalmar shi da na kowane babu mai muguntarshi sai wawa, jeki duk inda ki ka ga yayi miki daidai kin ji wata rana in kina raye sai kiga kin bada labari.
Ina jin haka na gane da gaske tayi nufin taimakona ban sake tsayawa wani bata lokaci ba yankawa kawai nayi a guje duk da kasancéwar lokacin, lokaci ne na nisan dare ga kuma duhu.