Littafi Na Uku
Kartawa nayi da gudu cikin duhun daren nan na rinka bi cikin kwararo da lunguna ba tare da ina jin tsoro ko duhun daren ya dameni ba, ji nake tamkar gudun da nake yi din gudu ne na ceton rai, ban tsaya a ko ina ba har sai da na isa kofar gidan su yaya Khadija duk da nisan dake tsakanin unguwannin namu.
Sau daya kawai na taba kofar gidan nasu na jiwo muryar Yaya Ibrahim yana tambayar wanene? Alama dai na su ma ba su yi bacci ba.
Ni ce na amsa cikin wata irin murya mai tsananin rawa saboda barin da jiki na ke yi.
Nan da nan na ji yana kokarin bude kofar, bai tsaya yi min wata magana ba ya kauce daga hanya ya bani wuri alamar wai in shiga, sai dai ban iya motsawa ba sai da ya yi min magana da bakinshi, to shiga mana maganar ta shi ta zamo tamkar nuni ko tunatarwa a gareni.
Falon yaya Dija na shiga saboda ganin da nayimishi a bude ban ganta an an ba don haka na wuce can cikin dakinta akan sallayarta na ganta tana sallah yayin da hawaye ke gudu a kan kumatunta, na nemi wuri na zauna har ta idar ban mtosa ba shima yaya Ibrahim bai shigo ba wurinshi ya shiga sai da ta shafa fatiha bayan ta kammala addu’o’inta sannan ta juyo gareni.
Wannan musiba ta kai inda duk ta takai, sai dai duk da haka ban fidda tsammani ba zata wuce wata rana har ki ga kina bayar da labarinta, babu abin da ya kuma jawo mana wannan fitinar irin rasa uwar mu da mukayi karo na farko da yaya Dija ta fito fili ta fadi hakan da bakinta tana gama fada kuma ta kama kuka nima na shiga tayata kukan da take yi.
Yaya Ibrahim ya turo kofa ya shigo, ke Dija wane irni rashin hankali ne wannan? Yaya zaku hadu kuna yiwa mutane kuka a cikin wannan tsohon daren, wai a kanku aka soma ganin irin wadaanan abubuwan ne balle ku ce naku yayi daban da na kowa? Ina ce ga ta nan a gabanki in kuma kaddarar ta ce aurenshi kina da wata hikima ne na hana hakan faruwa ni bana son rashin hakuri.
Fada sosai yaya Ibrahim ya yi kafin ya juya ya tafi wurinshi, nima na mike na shiga bandaki nayi wanka na fito nazo na sanmeta kwance a kan gadonta, na hau muka kwanta tare kowa ya yi shiru lokaci mai tsawo har ta kai ma na soma tunanin ita kam ta samu tayi bacci sai na jiyota tana tambayata, kin yi bacci ne Maryam?
Na ce mata, uh uh. Yaya aka yi kika fito? Ban boye mata komai ba na kwashe bayani na duk abinda ya faru a daren na gaya mata.
Zumbur ta mike ta zauna a tsakiyar gadon kika bashi kyautar budurcinki fa kika ce? Kan in san amsar da zan bata kan subutar bakin da nayi nayi mata wannan bayani tuni har ta rufeni da duka duka kuma ba mai sauki ba, kina nufin saboda Mubarak sai ki yiwa kanki sanadin tsiya, tana dukan tana kuka, ke wace irin yarinya ce wane irin so kike yiwa Mubarak?
Tsananin tsoratar da nayi da abinda yaya Dija ta aikatamin shi ne ya yi dalilin dana shanye duk wata azaba da ta gana min abinda bai taba faruwa ba a tsakaninna da ita.
Shi waye da zaki kai mishi budurcinki? Haba wacce irin fitina ce wannan? Ke wacce irin shashashar yarinya ce da bata san darajar rayuwarta ba? Bayan ta hakura ta bar duka da kukan ne take furta irin wadannan kalmomin abin da tayi min din ne ya yi dalilin da bai karasa gaya mata sauran abubuwan da suka faru ba na nemi wuri na makure wuri daya yayin da ita kuma ta ci gaba da tsaki tana fadin, mahaukaciya kawai da kin cuci rayuwarki da kinja mana bakin ciki da tozarta a cikin jama’a. Har gari ya waye bata sake kwanciya ba bata kuma daina yi min fada ba, namiji aka ce miki ana yi mishi irin wannan kyautar ne? Ai ni ban san haka kike ba.
Washegari da sassafe yaya Ibrahim ya yi shiri cikin kwalliya ta burgewa gidanmu ya nufa don halattar daurin aurena da Alhaji Nalami kamar yadda dama aka shirya ya shigo ya yi mata sallama ya fita.
Gabana ya yi mummunan faduwa kamar yadda na san itama yaya Dija ba ta ji dadin tafiyar tashi ba sai dai ta shanye saboda har yanzu fuskarte a daure take alamar wai bata daina fushi da ni ba kan maganar da nayi mata, a zuciyata na ce to da Mubarak ya karbi wannan kyauta da nayi mishi ko da yaya muka kare da yaya Dija oho?
Ina tayata aiki ina kokarin ganin tą wartsake don mu koma kamar yadda muke, yaya Ibrahim da ya sani da baije wajen daurin auren nan ba cikin matsuwa ta ce min, ai ba zai yiwu ba sai a yi zaton da wani abu a kasa a gane ya san inda kike sannan ko ba don haka ba ma zai yiwu ace babanmu ya kira shi hidimar gidanmu bai je ba, ai kuma sai ya zama karnar da raini a cikin lamarin, nace to kuma haka ne.
Ina zaune a gefen gado cikia natsuwa duk da hucewar da na ga kamar yaya Dija tayi bai sa ni jin wani dadi a tare da ni ba, a takure kwarai nake zuciyata sai harbawa takeyi da sauri sauri saboda tsananin tsoron da nake ciki.
Tashi ki yi wanka ki gyara jikinki ki karya kafin ya dawo mu ji abinda suke ciki sai mu ma mu san menene abin da za yi. Nace mata to.
Muna zaune a falnota bayan mun karya, jikina sai faman bari yake yi tamkar wacce sanyin hunturu ke kadawa babu abinda yafi komai kadani irin Kallon agogo da nayi naga karfe tara saura minti gonan safe, alhalin daurin auren kuma an ce ne za a yi shi da karfe bakwai da rabi na safe, to kome yaya Ibrahim din ya tsaya yi a can oho? Da ya dawo ai da mun san abin da ake ciki.
Muna nan zaune a wurin muna jiran dawowar nashi lokaci sai tafiya yake yi, yaya Dija ta gaji tace ko me ya tsare babansu har yanzu bai dawo ba oho?
Daurin auren da aka ce tun safe za a yi shi har yanzu ba a dawo ba. Tana yi tana kallon agogo don kara tabatarwa kanta da lokaci.
Muna cikin hakan sai yaya ibrahim din ya shigo gaba daya muka tsareshi da idanuwanmu sai dai babu wanda ya iya buda baki ya ce mishi kala saboda tsananin tsoratar da muka yi.
Yanayin shi yana nan a tsakani wato baina-baina ko kuma kadahan-kadahan arn yi daurin auren kenan?
Zuciyata ce ta raya min hakan. “Lafiya dai babansu na ji ka shiru gashi kuma duk jiinka yayi dabbare-dabbare bayan sanda ka fita bar daukan ido kayanka suke yi saboda farin su. Ya gyara zama akan kujera bayan ya kwabe babbar rigar tashi da ya tube ya jefa can gefe.
Lafiya dai babansu? Ta sake yin tambayar a yanayi na zuba mishi ido. Wannan al’amari ai yana da ban mamaki gaba daya muka sake zaro idanuwa muka zuba mishi, yayi shiru, me ya faru Baban su? Rashin hakuri ya sa ta sake yi mishi tambayar.
Tun barina gidan nan fa ba wani abu da na sawa bakina. Ina jin haka na mike na nufi kicin don kawo mishi abin karyawa na shigo dauke da tiren abinci a hannuwana sameshi yana yi mata bayani, samarin unguwar ne suka watsa taron mutane da duwatsu da goruna, sanduna ba a samu damar yin daurn auren ba.
Da sauri yaya Dija ta sake tambayarshi ba a samu yin daurin aure ba kace Babansu? Cikin natsuwa ya ce mata, eh ai rikici babba abin ya zama.
Tana jin haka ta fadi a kasa tana sujada alamar godiya ga ubangiji. Ya bita da kallo ana tasowa ta shiga furta kalmomi na godiya da shukure baiyane ta matso gabanshi tana shirya mishi abin karyawa tana sauraron bayanin da yake yi mata, nima ina gefe ina ji jiya ashe wai da suka ankara suka gane Maryamu bata cikin gidan sai sukayi zaton ta sake fita ne ta sake komawa wajen Mubarak tunda dama a can suka kamota don haka suka sake yin gaiya guda suka koma musu har cikin gidansu har wajen iyayenshi da aka duba ba a sameta ba, maimakon a hakura a yi neman a wani wuri tun da Babansu da kanshi ya fito yayi mishi magana ya ce bata wurinshi, sai ita babar taku ta nufi ofishi ‘yan sanda ta debo su mota guda tana fadin wai iyayen nashi ne suka daure mishi gindi yana lalata ‘ya’ yan muytane a gidan don haka ba zata yarda da maganar baban nashi ba, a cikin daren suka kama Mubarak suka tafi da shi suka tsare bayan dattawan unguwa sunyi kokarin shiga tsakani ta ce wai bata yarda ba aje gaban hukuma kawai don su din dukansu munafukai ne don haka su kuma samari suka fusata suka ce ta wulakanta musu iyaye banda haka kuma dama shi Mubarak mai mu’amala da su ne, don haka suka ja suka tsaya cewa zasu ga yadda za a yi a yi daurin auren, sai da suka bari jama’a sun taru har an sanar da isowar wakilan ango sai kawai suka firfito da sanduna da gorori suka fadawa jama’a musamma tawagar angon da jama’ arshi wasu kuma daga can nesa suka yi ta auna mutane suna yi musu Ruwan duwatsu, gabadaya suka tarwatsa jama’ a, shi dai angon nan in dai ba karyashi suka yi ba to sun turgudashi a wani wuri don da kyar muka kwaceshi a hannunsu, sai faman nishika yake yi yana neman taimako.
Assha assha namiji da neman taimako kuma Babansu lallai fa da gaske ne abinda ake fadi akanshi cewar shi din ba namiji bane daudu yake yi.
Yaya Ibrahim ya daure fuska, wane irin zancen wofi ne wannam daga nace yana ihun kiran maza su yi taimako kuma sai ki dangantashi da daudu kin san ma’anar daudu kuwa? Wuya tana da dadi ne? In ka ji fa kayi ihun kuma taimamko ai ba laifi bane.
Ta ce haka ne, daidai lokacin da ya mike ya nufi waje don tafiya wajen harkokinshi.
Daga ni har yaya Dija babu wanda ya iya cewa wani komai bayan fitar tashi kallon juna kawai muka yi cikin wani irin yanayi da ba zan iya kwatantawa ba, da kyar na iya bude bakina na ce mata wato dai duk wani al’amari yaya Dija na ubangiji ne. Tayi maza ta ce ai shi ne madogara ta dindindin in har ka dogara da shi din kuma to baka tabewa.
Duk da wannan labari mai dadi da yaya Ibrahim ya zo da shi saukin damuwa kawai muka samu amma ba wai mun fita daga cikinta bane muna te addu’a tare da sauraron abinda zai biyo bayan abinda aka yi.
Ina nan zaune a gidan yaya Dija har adadin kwanaki hudu jinin jikina har ya fara dawowa na soma farfadowa daga mummunar gigitar da na yi sai ga Yakumbo Halima ta zo gidan don dama ta san ina nan saboda aiken da yaya Dija tayi na a gaya mata saboda ta samu kwanciyar hankali.
Muna zaune gabanta muna hira bayan ta gama cin abincin da na kawo mata tana kara bamù labarin abubuwan da suka faru ko ince suke faruwa sai naji ta ce, shi kam malam Habu ai ya shiga mas’ala koma ince ya shiga uku ina amfanin ace namiji baida katabus komai sai yadda akayi da shi.
Da sauri yaya Dija ta ce Yakumbo bafa haka kawai bane da abinda tayi mishi. Ke matsa can ni ki bani wuri a kanshi aka fara yiwa maza asiri? Ai shi asiri da kike gani bance miki babu shi ba amma mafi yawancin lokaci hali yake tararwa, yauwa shima kuma gashi nan ya gamu da nashi gamon, don dazu da safen nan nake jin labarin wai ya yanke jiki ya fadi cikin kwandunan tumaturi a kasuwarsu sai da aka ciccibo shi rangatanga aka kawo shi gida.
Ni da yaya Dija salati mai kafi muka kama yi yayin da ita kuma ta ci gaba da fadin, uhun menene wannan in ba bakin ciki da damuwa ba da yake nema ya haddasa mishi ciwon nan na zamani da ake fama da shi na hawan jini.
Ni da yaya Dija bamu iya daukar abinda ya samu babanmu a yanda Yakumbo Halima ta dauke shi ba, wato a’inda babanmu ya shuka ne yake girba tausayin shi ne ya kamamu nan take muka soma yin kuka muna fadin, ba laifinshi ba ne Yakumbo ba laifinshi bane kune kawai baku san abinda muguwar matar nan take yiva baba ba na asirce-asirce da sihiri iri-iri.
Yakumbo ta mike tsaye nuna alamar tafiya tana fadin, to ai shi kenan ku kuka san abin yi tunda ubanku ne ni kam ni nazo na gaya muku sai kusan abinda kuke ciki.
Yaya Dija ta kawo kudin mota ta bata. Tana barin gidan ta kalleni, daga irin wannan faduwar ne fa ake rasa wani bangaren na jiki, ni yasu baba Lantana ta cuce mu a rayuwa mu muka barta ta zama sanadin nakasar ubanmu muna kallo to ta gama damu don wa muke da shi kuma bayan shi din? A hankali nace mata babu musamman ma da yake kullum a cikin alkawarin neman mana dangin ubanmu kike sai dai har yanzu shiru. A fusace ta juyo gareni kefa ba wani hankali ne da ke ba bakya ganin kullum a cikin mas’aloli muke bamu fita wannan ba mu sake fadawa wancan? Ban sake yin wata magana ba bayan fadin haka ne da nayi.
Nan da nan muka shirya tafiya gida bayan ta tura an gayawa mijinta halin da babanmu ke ciki, a hanya sai kallonmu ake yi ana zunde ana nunamu tamkar dai ba a sanmu ba, wai dan rikicin da akayi a gidan nan ne ta ya sa mutane suke yi mana irin wannan kallon, nace mata eh tace to ai sai su yi tayi su ne abin fada baya yi musu kadan nace haka ne.
Muna shiga gida Baaba Lantana ta soma sakin maganganu ai dama da kika gudu can wajenta kika tafi ta boye ki to ai zancen bai kare ba in ma kuma yi kuka yi dan ku kunyatani in tozarta gaban mutane to ba ni kuka yiwa ba ubanku kuka yiwa shi kuka kunyata kuka tozarta kuka nunawa jama’a cewa shi din ba komai bane a wurinku bai kuma isa da ku ba ko ba komai kuma ni kam ai gani nan a zaune daram lafiyata kalau shi ne bakni cikinku yake sashi yanaa tintsirewa a cikin jama’a yana faduwa, in kuka yi sanadinshi bukatarku zata biya tunda dama fatanku kenan gashi can a kwance magashiyan ai cikin yardarm ubangiji bakin cikin ku ne zai yi sanadinshi.
Wani irin mummunan faduwar gaba na samu abinda na tabbatar kuma shi ne itama yaya Dija abinda ta ji kenan saboda zaburar da naga tayi ta nufi dakin da yake kwance.
Ku daiyi a hankali kar ku takamin leda da kafafuwanku masu datti don yanzu na gama gogeta babu kuma komai na uwarku a ciki balle ace za a shiga min da gadara.
Halin da Babanmu yake ciki yafi gaban bayani numfashi yake yi sama sama ga kuma karin ruwa ana yi mishi abinda muka tabbatar shi ne wadanda suka dawo da shi ne sukazo da wanda ya dan dubashi da gani har yaya-Dija kuka muke yi saboda bamu taba ganinshi cikin halin rashin lafiya irin wannan ba.