Ai ba ku yi kuka ba tukunna sai randa kuka yi mishi farat daya ko kukayi mishi sanadin hannu da kafa ranar ne zaku gane kunyi kuskure, ai kun san ni dai ba-zan yi zaman jinya ba ko balle inje ina hidima da dawaniyar najasa.
Yaya Dija ta mike tsaye ta kalleta rike da labulen dakin nata-da tayi tace mata, matan arziki ai su ne masu hidima da jinyar mazajensu don neman albarka da rahamar ubangiji ai ke ubangiji ba zai yi miki wannan alherin ba ba zai jarrabi wani da jinyar da za ki yi hidimarshi ba balle ki samu wannan alherin.
Yaya Ibráhim ya shigo ya samesu nan take ya soma yiwa yaya Dija fada, ke da kika zo kika samu wannan al’amarin kumą mre ya kaiki tanka wata magana. Ya juya ya fita bayan ya bamu umarnin kintsa baban namu don tafiya asibiti.
Muna kokarin kintsa shin baba Lantana bata fasa magana ba ba, ba dai ke ce mai daure mata gindi ba?
Yarinyar da ta san taje kwanan gida gidan saurayi an kamata tana yin hakan yafi a kirga anyi nufin aurar da ita don neman mata rufin asiri kin sata ta gudu taje wajenki kin boye ta? To da albarkar masu albarka sai ta durkusa a tsakiyar dakinku ta haifar muku dan shege kuma kun goyashi a bayanku ke da ubanku da yake biye muku, babu wanda ya sake tanka mata.
Gwajin farko a asibiti likita ya bayar da tabbacin hawan jini ne ya yi mishi yawa yake nema ya taba mai zuciya kan haka ya bashi gado aka kwantar da shi a dakin masu cutar hawan jini.
Yaya Dija da mijinta suka koma gida ni kuma na zauna tare da shi, ban san yanda akayi ba cikin dare sai ga Sallau ya zo, sannu Mero. Na ce mishi yauwa, ba tare da na daga kai na kalleshi ba, yaya mai jikin?
Nace da sauki. Ya ja ya tsaya yana kallon baba nima na ci gaba da al’amurana, na ce ko zan karbe ki ne kije gida ki huta in kwana tare da shi in yaso da safe sai ki zo ki karbeshi? Lokacin ne na san na dago na kalli Sallau da nufin tanbayarshi shi kuma a waye dinshi da za mu yi irin wannan canjin ji da shi?
Yanayin da na gani a tare da shi ne ya hanani yin hakan cikin natsuwa sai na ce msihi a’a Sallau jeka gida kawai abinka na gode. Bai tafin ba sai ya tsaya muka kwana tare a asibitin, yanda kuma banyi bacci ba haka shima bai yi ba.
Da sassafe yaya Ibrahim ya zo duba mu ya kuma kawo mana abin karyawa da zai tafi ya kawo kudi ya ba ni ya ce in rike a hannuna ko za a nemi wani abu, nace mishi to tare da godiya. Yaya Dija bata zo ba sai da ta kammala abincin ranar gidanta ta zo mana da shi hakan Yakubo Halima ta kawo mana tuwon dare.
Mutanen unguwarmu makwabta, abokan zaman Baba na kasuwa suka yi ta zirga-zirgar zuwa don dubashi duk wanda yazo kuma zai kawo wani dan alheri ya bayar sai dai kalaman da suke fürtawa ne basa yi min dadin ji kai rashin yan uwa ko wani tsayayye bai da dadi in banda haka yaushe za a ce yarinyar da ta ja maka irin wannan tozartar tayi maka sanadin wannan mumnunan ciwon ita ce kuma mai yin jinyarka to yaushe ma kuma zaka warke?
Hankalina tashi yake yi a duk lokacin da na ji suna fadin hakan in kasa fahimtar abinda na yi na tozarta Babana, kamo ni da aka yi a gidan su Mubarak ne tozartawar da suke magana a kai ko kuwa watsa taron masu daurin auren da yara suka yi? To ko ma dai menene sai nake ganin tamkar in har da adalci cikin almarin ba laifi ne da ya dace a daukeshi a doramin ni kadai a kaina ba.
Tunda baba Lantana ta gane irin zirga-zirgar da mutane suke yi wajen zuwa asibiin sai itama ta soma zuwa kulum ta kan zo ne da tabarmarta ta shimfida a hanyar da ta san itace ta shigowar mutane tana ganin an zo sai ta tari masu zuwan tayi musu jagora zuwa inda babana ke kwance in suka gaisheshi suka ba da abin da zasu bayar tayi amza ia karbe ta saka a cikin yar fos dinta ta koma kan tabarmarta ta zauna ba kuma zata sake tasowa ba sai wasu bakin sun zo daga ni har yaya Dija babu wanda ya daga ido ya kalleta balle ya ce mata kanzil.
Kwana tara baba ya yi kafin aka sallameshi a hakan ma matsawar shi ce ta sa aka yi ta saboda yawan maganar da yake yi bai son zaman asibiti bai taba zuwa asibiti don kanshi ba sai dai don ya zo duba mara lafiya, yaya Ibrahim ne ya yi duk wata dawainiya har da biyan kudin sallamar muka dawo gida.
Likita ya sallame mu ne bisa dokoki na a kiyaye bacin ranshi a kula da abincinshi banda gishiri banda barkono banda farin maggi banda kanwa banda yawan cin man gyada.
Tun likita yana bayanin baba Lantana ta soma fadin, hu un wannan banda bandan ai ya yi yawa.
Yaya Dija ta kalleni cikin natsuwa bayan munje gidanmu da Baba tace min debi kayan da zaki diba mu tafi nace mata a’a je ki kawai ni zan zauna a gida, da sauri ta sake källona za ki zauna fa kika ce? Nace e, amma ai kuma kin san gidan ba zai zaunu miki ba a yanzu a yanda take fusacen nan ina nan ma kina jin irin maganganun da take furtawa balle kuma ace na tafi na barki ke kadai.
A hankali na daga ido na kalleta kafin na tambayeta, to in muka tafi dukanmu muka bar baba a yadda yake din nan wa zai yi mana jinyarshi? Wa zai bashi magani? Wa zai kula da abincinshi balle ya tsaya yaga an tsare dokokin da aka sa mishi? Tace to kuma haka ne ta bude jakarta ta fito da kudi ta bani tare da fadin, to rike wannan a hannunki kafin inje gida in ga abinda zan iya hadawa nace mata to.
Na koma zaman gida tare da baba Lantana da ya’yanta biyu ga kuma babana a kwance yana jinya tunda ko fita runfarshi baya iyawa balle a yi maganar kasuwarsu, dan garama dai Sallau don shi kam yayi mana mutunci kwanakin asibitin baba duka tare da shi muke kwana.
Duk lokacin da na zo shiga dakin baba Lamtana don yiwa babana wani abu ko bashi magani sai tace wai bata yarda ba ina shiga ne ina ganar mata sirrinta shi ba zai sha da kanshi ba sai an bashi kamar wani dan yaro? An wani tasashi a gaba ana shagwabashi ita bata son gulma da iya yi.
Babana kuwa shan maganin yake yi a kan dole sai na yi ta rarrashi ina bashi hakuri kafin ya yarda ya sha.
Ganin da nayi takurar ta kai inda ta kai ya sa na shiga dakin da Sallau ke ciki yana kwance kan katifarshi na ce mishi, Sallau kawar da katifarka ka .koma can gefe zan yiwa baba shinfida anan don a samu saukin mu’amala, cikin sauri ya ce min to, nan da nan kuma ya mike ya soma yin abinda nace mishin har ya tayani na shiga dakina na dauko katifar da nake kwanciya a kai na dawo mishi da ita nan na shinfida mishi ita naje na samu Babana na ce mishi tashi Baba mu koma dakin Sallau don zai fi mana saukin zama, ya ce min to.
Na dawo da baya ina jiran fitowar tashi Sallau ya leko daga cikin dakin yana tambaya ta Mero wannan ai katifar gadonki ce, nace mishi eh, ya ce to ki maida ita mana kawai sai ya yi amfani da wannan ni zan rinka yin shimfidar tabarma ina kwanciya, har zance mishi a’a ya barta kawai sai baba Lantana ta taso da saurinta to ai ba tasu bace wannan din da kake neman gwaninta a kanta tawa ce da kudina na sayeta don haka ban yarda ba, ta sake kallonshi cikin wani irin yanayi da takaici yafi komai baiyana a idonta kana tsoronta ne saboda wancan dan iskan ko? Dama ka wartsake kayi hidimarka shima yanzu ta kanshi yake yi sakaraí matsoraci bani katifata ka rinka kwanciyar tabarmar da ka zabarwa kanka.
Na kalleta cikin natsuwa na ce mata, to ki fito min da wacce take kan gadonki ai wannan tamu ce tunda ta gadon innarmu ce.
Ta zabura kamar zata ki famin mari saboda hakan dana gaya mata ban san yanda akayi ba ta fasa ta kuma bar katifar ta tayi nima naja tawa na mayar kan gadona.
Dawowar da Babana yayi dakin sallau sai ya bani damar dana rinka kula da shi dama duk wani alamarinshi ko wane lokaci ina tare da shi komai naga ya dace in yi mishi bana jiran sai ya ce a yi mishi, wanka, wanki, komai a kan lokaci.
Duk wannan abinda yake faruwa baba Lantana bata cas bata as kan abinda ya shafi rashin lafiyar mijinta taja ta tsaya kan wai raina mata mukayi ya sa na zo na kasa na tsare a kanshi don haka itama ta cire hannunta kan lamarin shi tunda shi dama abinda ya’yanshi suke so yake bi baya kuma gudun abin kunya na aikata babban laifi bai ce min komai ba ya tasani a gaba yana kallona masu ya’ya maza ma sun hukunta ‘ya’yansu amma ni ya yi kamar bai san abinda na yi ba.
Yadda dama can babu mai ce ma ta komai in tana maganganunta haka yanzu ma a wannan lokacin ko wani wadataccen girki batayi sai ta ce wai ba a fita an kawo mata ba me zata girka? Don haka kullum gidan a bushe yake babu abinci ni dai ina tsare da cikin babana ba na yarda ya ji yunwa ba na ma zaton ya san Baba Lantana bata girki in dai ba ya lura ya gane. Abinda kalamanta a tsakar gida suke nufi wurin Isiyaku da ya zo gaida babana da jiki na samu labarin wai ashe Alhaji Muhammadu Baban Mubarak korarshi yayi daga gidan saboda samuna da akayi a dakinshi da kuma cin mutuncin da Baba Lantana ta je musu da shi cikin gidan tun yana tsare a wurin ‘yan sandan wai ya aike mishi cewar in ya fito ya nufi inda ya nufa amma ba gidanshi ba, ya kuma turo har abokan Baban sun zo sun bashi hakuri yaki ya hakura ya tsaya kan bai son sake ganin shi a yanzu.
Gabana ya yi mummunan faduwa saboda jin irin hukuncin da Baban Mubarak ya zartar a kanshi bayan kuma na san matsayin da yake da shi a wurin iyayena nashi na yi matukar kaduwa, tausayinshi kuma ya kamani har na rinka ganin tamkar ni naja mshi tunda ai ni naje wurinshi ba shi ya kirani ba, cikin zuciyata na ce to abinda baba Lantana ta je kenan tana fadin masu ya’ya maza ma sun hukuntasu amma nawa yana kallona saboda abin kunyar da na aikata bai dameshi ba sai wani lallangabewa yakeyi ina tarairayarshi wai shi nan ga mai ‘ya.
A wannan lokacin ba zan iya zama in kwatanta halin da nake ciki ba na kunci, takura da kuma bakin ciki a halin dan a samu kaina a ciki, na gane ashe ba auren Alhaji Nalami kadai bane karshen bakin cikin rayuwa ko da yake dai ni a wurina ina ganin tamkar shi ne ya yi min sanadi na shiga duk wani hali da nake ciki, ban kara sanin irin cikin wani hali na shiga wata gagarumar fitina ba sai da na ji Asabe tana rera wata irin waka da na sha jinta a bakin yara ban taba kulawa na gane abinda suke fadi ba sai ko yau da na ji ta a wurin Asaben shị ne na gane ashe wai ni aka yiwa wakar.
A wancan lokacin da ko yawan kula, samari budurwa take yi yan mata yan uwanta suke rera mata wakar, mace mai wasa da maza karya nayi mamakin kaina matuka na kuma ga sakarcina da tun asali ban gane da ni ake yi ba wai sai da na ji wakar a bakin Asabe, masu gatama masu ya’ya samari basu tsallake wannan wulakancin ba balleni da bani da kowa in banda babana sannan tun can asali dama ba wani farin jini ne da ni ba a tsakanin yan mata da samarin unguwar iyaka dai tsoron Mubarak ya tserar da ni daga duk wani wulakanci ko iya shege da za a yi nufin yi min to yanzu kuwa babu shi kowa kuma ya san ta kanshi yake yi don kuwa wannan hukunci da babanshi zai yi ba sannan a yanzu bama maganar wasa da maza bace matsala ta an kamo ni ne a dakin saurayi na kai mishi kaina baba Lantana kuma ta sake rattaba bayani a gaban kowa a cikin daren da babu sirri a cikinshi cewar ba ranar na fara ‘zuwa kwana a wurinshi ba.
Na yi kuka rannan irin wanda na tababtar ban taba yi ba a rayuwata nayi bakin ciki na rasa inda zan tsoma raina in ji dadi na rinka jin tamkar ina ma dai ikon bude kasa in buya a cikinta saboda tsaranin kunya.
Duk inda tozarta ta kai duk inda wulakanci ya kai, duk inda muzantawa ta kai kalmomin da suke cikin wakar sun kai harma sun wuce gashi saboda wulakanci da raini sai aka yi anfani da sunana ta yanda kowa zai gane da ni ake yi amma shi Mubarak babu nashi sunan a cikinta, na samu kaina cikin wani yanayi da na rinka ganin tamkar babu wanda ya taba shiga cikin wannan yanayin sai ni kadai.
Da kyar na ke iya fita waje sai in dolen ta kama, dole ina nufin in zan saiwa babana wani abin in ta kama hakanma sai na yi ta leke naga mutane sun dan dauke sannan ne zan ruga da gudu inje shagon kusa da gidanmu in sayo in dawo saboda yara suna ganina suke fara rera wakar wasu suna anshi cikin tafi sannu a hankalima dana lura sai na gane ba waka daya aka yi min ba kaloli ne daban-daban kara fito da sabbima suke yi, baki ciki in ya dameni sai inji kamar in gudu in yi tafiyata in tafi can inda babu wanda ya sanni in yi zamana sai kuma ince to Babana fa, wa zai yi min jinyarshi? Yaya Dija fa ita me tayi min da zan tafi in barta? Sai in tsinci kaina dayin wani tunanin ince to ai ina ji ana cewa babu wam dauwamammen abinda ya ke zuwa ya tabbata, in dai ba ikón ubangiji bane don haka duka binda ake yi zai wuce in rudi kaina da cewar da nake yi nayi na wai watarana sai labari ina fadin hakan kuma zanji zuciyata tana tambayata to yaushe ne naki wataran zai zo? Wanda ni kaina ban sani ba ina raye ne zanga wataran ko sai na mutu ban sani ba tunda ni kam ai kullum al’amurana kara
cabalbalewa suke yi bakin cikina kuma yana kara karuwa.