Skip to content
Part 27 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Yaya Dija ta zo duba jikin babanmu samuna da tayi cikin wani irin hali ya yi matukar bata mata rai, saukin abin ma shine da muka san ba ku yi komai ba amma da ya karbi wanna mahaukaciyar kyautar da kikayi mishi ai da bamu san iyakacin bala’ in da muke ciki ba a yanzu amma yanzu kina yin aure shi kenan mijin da ya aurehi da duk wani wanda ya danganceshi zai ce karya ne sharri kawai aka yi mana mai yin sakamakon kuma zai yi mana wato da Mubarak ya taba ni da musibar ta wuce haka kenan bata tsaya ba ni amsar maganar ba sai ta ce min Umman Mubarak ta aiko da kayaiyakinki da suke wajenta ciki kuwa har da wani bakin karfe, ta tsareni sosai da idonta kafin ta buda baki ta tambayeni kin gane abinda hakan ke nufi? Nace mata eh, bata bar ni ba sai ta ce min me yake nufi? Cikin natsuwa na ce mata kar in sake shiga gidansu tayi maza ta ce to madalla gara da kika gane hakan, da ya karbi kyautar da kikayi mishin ma da irin korar da sukayi mishi kenan koma su yi wadda ta fita.

Ko yake ko dan Umma bata yiwo min irin wannan aiken ba nima ba zan sake dosan gidansu da nufin wata mu’amala ba saboda abin kunyar da ya faru ga kuma irin abinda hakan ya zamewa Mubarak amma kuma sai naji tamkar ba ta yi min adalci ba ko kadan ban ji dadin abinda tayin ba don kuwa ita din uwa na dauketa duk da da itama na sani don Mubarak din take yi min duk wani abinda take yi min.

A wannan lokacin sai na rinka iin tamkar tubeni aka yi sirara aka jefar da ni cikin taron jama’a da bani da kowa a cikinsu balle wani mai taimako amma kuma ban yarda na munawa yaya Dija tsananin damuwata ba don kar in kara mata tata damuwar tunda har itama marasa atunanin yaran unguwarmu in suka hangota rera mata wakokin suke yi kasa-kasa amma ba da karfi ba kamar yanda suke yi min.

Sannu a hankali sai babana ya samu sauki har ya soma fita kasuwarshi saboda tababbacin da likita ya bayar na jinin nashi ya sauka amma ba ana nufin ya warke ba ne shi jini in ya riga ya soma hawa to ba a daina sha mishi magani don ko wane loakci zai iya tashi, wannan shi ne bayanin da likitan ya yi mana a ranar da mukaje ganinshi ni da baban nawa.

To Dr. me ke kawo ciwon hawan jini? Na yi mishi tambayar don in kara sani, sai ya ce min akwai jinsin mutanen da ke da jini wanda yake da irin wannan matsalar su ne masu yin ciwon a  dalilin sun gajeshi, sannan wasunyakan samu a dalilin tsananin damuwa ko kuma yanayin abincin da ake ci shi yasa yake de kyau mu rinka kula da abincinmu mu kiyayi abubuwa marasa amfani irinsu gishiri, barkono, kanwa da makamantansu, sannan mu rinka yawan motsa jiki, motsa jiki yana da amfani kwarai ga lafiyar jikinmu kin gane? Nace mishi eh Dr. Na gode.

Rike wannan bayanin da likita ya yi min da nayi sai na jiyewa kaina ya zama ka’ida kullum in baiwa Babana magani kwaya daya da kuma yayi min korafi kan maganin yana sashi yawan taba ruwa sai na mayar mishi da shan amganin nashi a lokacin dare haka nan jin saukin babana baisa na fita hanyar kula da abin karyawarshi ba ko da kuwa iyakar abinda nake da shi kenan saboda na ga na gane har da yunwa cikin rashin lafiyar tashi, ina kuma yawan gaya mishi cewar  Baba ka rinka shan timatir in ka gansu masu kyau kana kuma cin danyar kubewa kar kuma ka rinka yarda mai kankana ko ayaba yana wuceka baka saya kaci ba komai kankantarshi ya ce min to.

Baba Lantana dake yawan kasa kunne wajen sauraron maganarmu ta ce eh ‘yan kudin da yake kawowa wadanda dama ba isar mutane suke yi ba su ne kike koya mishi yanda zařtinka cinyesu a waje ba saboda sharrinki kankana da ayaba kuma maganin me suke in ba iya shege ba.

Babana ya fara fita kasuwa sai dai abin mamaki shi ne ashe wai har shima bai tsira daga wakar da ake reramin din ba in an ganshi sai a yi tayi wasu ‘yan iskan su rinka nunashi suna fadin shi ne mutumin da aka kama’ yarshi a dakin saurayi har a dalilin hakan mijin da zai aureta ya ce ya fasa auren shi sauranyin ubanshi ya koreshi a gidan shi amma shi yana tashe da tashi ‘yar a gabanshi sai ma kara sonta da ya yi.

Wasu su ce to ance duk abin da take samowa shi take ba wa, ai mafi yawancin iyaye yanzu in dai ya’ya zasu basu kudi to magana ta Kare sai su yi abinda suka ga dama suna kallo kai amma kuwa to tir, wato shi yana can yana kici-kici da tashi matar itama ana can ana kici-kici da ita kenan? Sai a kwashe da dariya.

Suma yaran dake cincirindon sayen timatirin babana har ana layi ba a barsu a baya ba sun daina yayensu ne suka hanasu ko su suka hana kansu saye sai su saka sauri hatta rijiyar gidanmu da bata kafewa wacce kullum baba Lantana ke fada da masu zuwa diban ruwan cikinta su ma yanzu ba a zuwa diba.

A wannan lokacin kusan kullum sai anyi kwashen timatir babana ya zama bage tuni sai jarinshi ya soma rushewa sai mai kawo kwandunan timatir attarugu tattasai albasa alaiyahu kubewa masu yawa sai ya zamo da kyar ake hada kudin daidai don haka in tsaya fadin an shiga wani halima a gidanmu na tsaya bata baki ne kawai.

A wannan lokaci saboda samun wuri Asabe abinda ta ga dama talke yi min ina kallonta bana cewa komai saboda  yanzu yanzun nan ne zata fara rera min waka in taga fuskata ta canza ta ce ba ni na kar zomon ba rataya kawai aka bani, bana tanka mata don nasan bani da yanda zanyi da ita in karfin dambe ne ta jinni gatan da nake da shi din da yasa ake tsorona babu shi, banma san inda yake ba ga kuma aiken da Ummanshi ta yi min daga gidansu wanda nasan na nuna karshen mu’amalata da su ne.

Asabe tana cikin tatamin irin tsiyar da taga dama ne rannan na farka cikin dare na ganta tana kwarara amai a cikin wani kwano duk da tsananin tsoratar da tayi da ganin da nayi mata ban gane abinda hakan ke nufi ba, na hadaki da girman Ubangiji kar ki gayawa Baba kin ganni ina amai ba zan sake yi miki wakar da nake yi miki ba.

Nace ki yi mana ni ance miki wakar ta dameni ne? Amai kam ai sai na gaya ma ta na ganki kina yi a kwano. Tayi ta bani hakuri mamakinta yayi ta kamani ko ina ruwana da ita da uwarta da zanje ina cewa na ganta tana amai oho?

Tun daga rannan Asabe ta daina nemana da tsokana a fita hanyata da abubuwa iri-ii abin sai mamaki yake ta bariï sai a ranar da yaya Dija ta zo gida ne ina rakata take tambayata hain da muke ciki da Aabe na bata labarin abinda ya faru sai naga ta ja ta tsaya tana kallona cikin natsuwa kafin ta ce min, ko dai ciki ne da yarinyar nan? Kai haba gashi yau na ganta ta canza to ita uwar ta ta ba zata ganc ba sai an gaya mata wacce irin shashashar uwa ceh aka? Shiru nayi cikin tsananin faduwar gaba, ciki? Na yiwa kaina tambayar a cikin raina.

Ai baka cima masharranci sai ka yiwa kanka mafi yawancin lokaci ai abin da ake yiwa dan wani shi yake samun naka ki ja bakinki ki yi shiru karki yarda ki yi abinda uwar ta ta zata gane tunda ita mahaukaciya ce nace mata to…

Rannan ina zaune a tsakar gida ina hidimar wankin kayan babane bayan na gama nawa a yanzu bana fada da kowa saboda Sallau dai mun dan shirya da shi tun daga kwanciyar asibitin baba da kuma lura da nayi naga yana mutuntamin baban nawa, Asabe kuwa tsoro take ji karmu yi fada in fadi abinda ta roke ni kar in fada bata san ma ni ko munyi fadan ba fada zanyi ba tunda yaya Dija ta ce min kar in fada.

Cikina ne ya yi wani irin kuka na tunanin da irin dadewar da nayi ban bashi wani abu na hatsi ba, na waiwaya a hankali na kalli Asabe da baba Lantana da suke zaune cikin rana wai suna shan hantsi su ma zazzare idanu suke yi nuna alamar yunwar su ke ji kamar ni tunda a yanzu duk mun zama daya ni babu su ma babu, yanda nake kaiwa Azahar ban karya ba haka su ma suke kaiwa har gara nima yunwa bata cika gigitani ta fitar da ni cikin haiyacina ba don kuwa da ana sabo ko wani kawance da ita to da na ce munyi ba a yi ne kawai yasa ba zan fadi hakan ba amma duk da haka zan iya cewa na saba jinta haka nan a duk halinda nake ciki bana rasa wani dan canji kulle a bakin zanina wanda nake dan tsakura ina baiwa Babana abin karyawa in ayso ni in hakura don bana yarda ya fita su kuwa nasan da kyar ne in suna da wani abu.

A wannan lokacin a gidanmu rashin yin girki bai zamo komai ba tunda baba Lantana tana kin yin girki da gangan yanzu mai dalili ya sameta, kasuwar Babana ta yi kasa jarinshi ya yi matukar karyewa tun yana kawo mata dan cinikin da yake yi tana rainawa tayi watsi da su ko tayi ta zage-zage tana tambayarshi wadanann me za su yi mata har ta hakura ta zuba ido don ta gane abin bana kare bane tunda kullum raguwa yake yi sai da ta kai ma tana tambayama ace mata ta yi hakuri tayi ta maganganu to yanzu babu kawai yake cewa ya ja bakinshi ya yi shiru ya barta ta fadi duk abinda take son fada.

A wannan lokacin sai ta zama bata da aiki sai na fushi ko mita ko ka ji ta tana baiwa Asabe labari irin zaurawan da suka nemeta wai ta kisu ta auri babana sai ta yi kwafa ta ja tsaki tace, to rabon wahala ni kuwa sai in kyalkyale da dariya tayi ta zagina, Asabe tana kallonta bata tsoma baki nima bana cewa komai baya ga dariyar can cikin zcuiyata ina kiranta da sunan da na saba jin Alhaji Nalami yana kiranta wato Butulu.

Muna cikin wannan zaman ne muka ji an kwada wata irin sallama a kusa da kofar shigowa gida gabana yayi mmmunan faduwa arnma kuma nasan na Baba Lantana yafí nawa faduwa saboda yanayin da na gani a tare da ita tun kafin ta kai ga amsa sallamar tashi sai gashi ya fado tsakar gidan.

In ce ko da ba za a amsa sallamar tawa ba ne? Ta soma kame-kame tana rantse-rantsen wai bata ji sallamar tashi ba nan da nan ta shiga yi mishi oyoyo tana sannu da zuwa cikin sauri ta shiga ta dauko mishi shimfida tana yi tana, habawa yaya za a yi inji sallamarka in ki amsawa to a wanne dalili? Ta gyara zama, yana fadin a dalilin cuta mana aike tsunma ce.

Na mike na soma tsince kayana da suka soma bushewa na wuce na nufi dakina cikin zuciyata ina kokarin danne dariyar rawanin da naga yayi wanda yafi kama da na waziri aku.

Rawani kuma Alhaji ya koma yi? Tayi tambayar cikin yanayin sakin füska da fara’a, ko an baka wata yar sarauta ne ban šani ba Alhaji Muhammadu? Ta sake janshi da watą rahar.

Ya kara tsuke fuska saboda watakila fara’ar tata ta yi mishi yawa, kinga bana son irin sunayen da kike kaka ba min ni, naje Makka*ne da kike ce min sunana Muhammądu? Nalami kawai sunana kenan shi na fi so shi nafi sani.

Ta yi murmushi Alhaji ai sunan mai niyya ne bana wanda ya je bane, Muhammadu kuwa ai sunan maza ne menene aibi don an kiraka da shi tunda Nalami ai ba sunan gaskiya ba ne.

To ni shi nafi so da shi aka yanka min ragon suna ko sai ace bai yanku ba? Ta ce ya yanku, ya ce to ni ba ma wannan ne ya kawoni ba. To ka cire rawanin naka mana ka sha iska. Ya yi maza ya ce na ki din in cire yaran unguwarku da basu da tarbiya su hangoni su zo su kara sani ko? Ko da yake an gaya min cewar ke kika biyasu kika ce musu su kasheni in nazo wurin daurin auren to ta Allah ba taki ba gani nan daram gabanki da raina da lafiyata.

Da sauri ta tambayeshi ni? Insa a kasheka akan wane dalili? A dalilin dukiyata da kika karba man tunda ai an gaya min komai ba kudina ni kadan kika ci ba, tayi murmushi, wanda ya gaya makan bai gayama ka gaskiya ba, niikam ai ina nan a kan bakana tunda dai kaima ka ganta da idoka tana nan ba…

Ba ta karasa ba ya ji maza ya ce ma ce a’a bana so ina? Ai wautar tawa ba ta kai haka ba ai ni kuma kin sanni ba a cutata: sau biyu ko da yake dai ke zatiddawahice ko gamsheka bata kaiki sharri ba wato in sake dawowa da sunan karbar aure don ki samu su karasani ko tunda burinki bai gama cika ba a kaina to naki bana son auren shiga kawai ki fito min da abinda kika sani nawa sauri nake yi.

Ban san yarda akayi ba naji baba Lantana ta rage murya, tayi wata magana sai dai kuma shi bai rage muryar ba wajen bata amsa don haka na gane abinda ta ce mishi.

Asabe kuma? In zo in auri Asabe to a kan me? Ai dai kasan ba finta komai tayi ba tunda ita Asabe ma ga kirji a cike ga mazaunai ga diri ita wannan ai haka singul take tsawo ne kawai kamar sanda. Ya yi tsaki ya ce ai duk a banza gara ma singul din ita Asabe in ita nake so ai nasan inda zan same taa bani kudina kwai.

Ranta ya baci da jin maganar tashi cikin yanayin fusata sai ta ce mishi karfa ka ce zaka yi min wulakanci ina binka cikin sauki kana sake baki kana caba min ma gana da wasu labbanka masu kama da saukan markade nawa ne kudin naka?

Ya gyada kai nuna alamar gamsuwa da jin maganar ta ta cikin natsuwa ya ce basu da yawa kawo min su in tafi in bar miki gidanli jaka bakwai ne.

In banda baba Lantana a zaune take sanda ya ambaci jaka bakwai din nan watakila da ta fadi kasa warwas saboda tsananin kadirwar da tayi, a’a jaka dari zaka ce ba jaka bakwai ba in ka tsaya a jaka balkwai ma ai sharrinka bai kai sharri ba la’anannen tsoho kawai matsiyaci da ma abinda ya sa ka zo kace in baka ita kenan don ka samu damar kullamin sharrin daka dade kana son kullamin? To bani da su ban ma san su ba. Nan take kuma ta soma rusa wani irin kuka.

Ban yi mamakin ganin gigicewar Baba Lantana kan ambaton kudin da Alhaji Nalami ya yi ba saboda a wancan loakcin jaka bakwai din ba karamin kudi bane kudi ne da ake iya siyen gida da su kudi ne da akc iya biyan aikin haji da su har aje a karbi guzuri na zunzurutun kudi dalar Amcrica dubu daya a can kasa mai tsarki, haka nan ko da ban san abinda yake tsakanin baba Lantana da Albaji Nalami a kan maganar kudi ba to nasan shi Nalami zaiyi wuya warai in yana da kudin da suka kai jaka bakwai balle ya iya bada su saboda bai da kamannin wanda ya mallaki irin wadannan kudaden.

Yanzu nan banda fam hamsin Dinka guda uku da ka bani ka taba kawo wani abu bayan nan ka bani?

Sai da ya kara juya mata keya kafin ya ce, fam hamsin hamsin sau uku wasa ne? Tunda kika ambanci wadannan da bakinki ai sauranma zaki fito da su ai kin yi kokari ni kam ma ai duka nayi za ki ce ban taba baki komai ba küma in ma iyakar abinda na baki kenan to zaman nawa sukayi a wurinki? Da a wurina suke ina ta juya abina da yanza nawa suka zanma?

Sannan dukan tsiya da kiką sa aka yi min fa? A nawa dukan yake? Nawa kuma na kashe wajen yin jinyar kaina? Dankwala dankwalan kajin da na rinka sayowa ina kawo muku kuna ci ke da mijinii da su lemon gongoni da na kwalaye fa? Su a nawa suke?

Ko kina nufin za ku ci bulus ne? Sannan kwana nawa nayi ban fita kasuwa ba a dalilin jinayr? Zan dau asara ne? Ai kema kin san riba nafi ganewa ba na fahimtar asara.

A fusace ta ce mishi to asara kam sau nawa kayi ta a rayuwarka? Babbar sana’arka fa daudu ne? Yayi maza ya ce yaurwa ga kudin kulla sharri da bata suna ai hada lissafni komi na yi na rattaba wuri daya don haka ki bani kudina tun muna sheda juna dake cikin mutunci tun bamu kai ga wulakanta juna a bainar jama’a ba don ba zai zamomin komai ba in kai maganar gaban alkali in kira masu shedar zur mu yi lada da su su je su yi rantsuwa su yi min sheda gaban alkali ya karfar min kudina in biyasu ke ni na yarda ma in bar musu kudin duka su cinye zaifi min dadi akan ace na bar miki su.

<< Halin Rayuwa 26Halin Rayuwa 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×