Na ce to shigo màna in ji shawarar, cikin natsuwa ya shigo ya nemi wuri ya tsuguna kamar wani mai shirin biyan bukata. Da ka zauna ai kamar zai fi yi maka dadi, a’a babu damuwa, na ce to shi kenan me ya faru?
Ya danyi kame-kame kadan kafin ya iya fitowwa sosai ya yi min bayanin rumfarn an ce ta baba da kullum in bashi da lafiya ake rufeta babu kowa tumatirin ciki dama duk wani abinda ake da shi su yi ta lalacewa tunda ba masu jirar zaman bane shi ne nace ko zan rinka bude ta ne ina zama a ciki? Sanin da nayi da gaskiyar magana Sallau din ya fada na kuma san in ma ban barshi ya bude rufmar ya zauna ya dan taba abinda ya taba na cikina ba to duk ranar da aka budeta za a kwashe komai ne a zubar tunda za su gama lalacewa to da a yi irin wannan asarar kuwa gara ko ba zai baiwa baban koami ba ya bude ya sayar, nasan shi zai dan samu wani abu don haka sai na kalleshi na ce mishi, to ai hakan yana da kyau Sallau gobe da safe sai kaje ka bude tunda shi baba goben zaije ganin likita, ya ce to Ubangiji ya sa mu gani lafiya, na ce mishi amin.
Washegari da yamma mun dawo daga asibiti bayan sallar La’asar a dlailin dogon layin da muka tarar daga nesa na hango Sallau a cikin rumfar baba yana tashe da yan timatirin da suka saura muka wuto shi muka shiga gida sai kusan magariba ya dawo ina kallonshi bance mishi komai ba baya ga gaisuwar da muka yiwa juna sai da ya tabbatar baba Lantana ta shiga dakinta ta kwanta sannan ya turo kofata ya shigo a hankali gaba daya cinikin da ya yi ya zube min a gabi.na na zuba ido ina kallo nace a’a ciniki mai kyau aka yi ne haka Sallau? Ya ce eh an dan taba kadan, to madalla na fada ina mai sauraron bayaninshi sai da ya gama na ce mishi, to su wadannan kudin sai ka rikesu kawai a wurinka ba ka ce kayan bai karasa karewa ba? Ya ce e, na ce to daga nan zuwa biiba ya gama jin sauki sai mu ga abinda za a yi, ya ce min to sai da safc ya fita.
Kwana uku bayan nan baba ya fara bude rumfarshi bayan ya saro wani sabon timatirin a dalilin saukin da ya samu ban san yanda akayi ba sai na ganshi tare da Sallau suna zaune a rumfar tare shi yana can ciki a zaune Sallau yana salalmar masu zuwa saye, ni ma kasuwar zai tafi sai ya tasashi a gaba su tafi tare.
Rannan ina kwance a kan dan gadona na bono da hantsi bayan na yi wanka na shafa man basilin din babana saboda gaba daya kayan shafana sun kare bani da komai in banda man wanke baki. Ina cikin tunanin halin da nake ciki ne sai kawai na ji an kwala sallama, ina jin sallamar na gane wanda ya yi ta nan take na shiga lissafin rabonshi da gidan yau zuciyata ta tunamin kwanaki tara ne cif.
Sallama dai sallama dai, na fa iso na kuma san ana jina yauwa ita rana ai bata karya sai dai ko uwar diya ta ji kunya, to ni don kar a ji kunyar ma sai na mutunta na kara kwanaki har biyu kan alkawarin da aka yi min din, ga zatona za a biyoni da su har rumfata a mutunce to da ban gani ba kuwa gani na taho karbar halali na.
Baba Lantana ta fito daga dakinta dankwalinta a hannu fuskarta kuma a daure abinda na tabbatar shi ne bata yi azton zuwan nashi ba a yau don kuwa jiya da shekaranjiya da ta yi tsammanin zuwan nashi tun sassafe take barin gidan bata dawowa sai cikin dare.
Ah naso karbar halalina ya yi maganar cikin wani irin yanayi yana mai kawar da ido daga gareta, watakila saboda mummunan kallon da ya lura tana yi mishi.
Ai kai baka taba cin halal ba a rayuwarka tun daga kuruciyarka har kawo ga halin da kake ciki na tsufa a yanzu.
Duk abin da za ki gayamin dai ba zan tanka miki don kudi ne dai sai kin bani su ko girma da arziki ko tsiya tsiya duk wanda kika zaba tunda dai na ma yi sa’a kawarki bata taimakeki kika samu miji a hannu ki ka yi mata alkawari kika saba saboda ganin bukatarki ta biya kika wulakantata kika barta tana bara bara karuwa karuwa ta yardaer munje kotun zata bada sheda a kanki kyauta ba sai na biya ba ai da sauki.
Wacce kawa ke gareni da mukayi haka da ita in banda sharrinka? Da sauri ya ce mata Delu. Ni da kaina da babu ruwana a cikin maganar na san baba Lantana tayi amfani da kawayenta wajen neman babana a malamansu da kuma taga kamar ta samu yadda take so ta koresu ta hanyar yi musu wulakanci ba tare da ta cika musu alkawarin da ta yi musu ba cikin irin wadannan kawayen nata nata har da Delu.
Jikin baba Lantana ya yi sanyi kwarai da jin cewar Delu zata bayar da sheda a kanta ta kuma san sauran ma zasu iya yin hakan koma fiye da haka, to su je su yi ta bayarwa mana, ya yi murmushi ai fa za su je.
Takardar fili nake da ita zan baka kaje ka sa filin a kasuwa ka sayar ka karbi kudinka, takardar fili kuma? Ya yamutsa fuska ni da na bayar da kudi na tsaba a hannu sai kuma a ce za a hadani da wata takardar fili? In filin na arziki ne me yasa ke baka saida shi kin karbi kudin kin bani ba? Da kyar Alhaji Nalami ya yarda baba Lantana ta fito da ta takarda ya karba yana dubawa tana yi mishi bayani, filin ya kai shekara uku da saye tun a wancan lokacin kuma jaka uku na sayeshi zuwa ina ganin zai iya kaiwa jaka goma in an saida shi a kawomin sauran kudin.
A hankali ya matsa kusa da ita ya ajiye mata takardar tare da fadin, saidashi da kanki ki bani kudina kawai abinda nake so kenan shi ne kuma zai fiye miki rufin asiri a kan wannan neme nemen maganar da kikeyi da ni ai ke ma kin sani sarai tunda aka saida gonar mage aka saiwa bera daddaawa to kuwa tsugu ne ta kare mishi ni za a kawowa iyas hege filin da aka saya shekara uku bayan ne za a yiwa wannan bayanin ba ku yi magana a kan irin ginin da za ki yi a kai ba saboda sanin kullum darajar kasa raguwa take yi ba karuwa ba sai a ce ana neman kari?
Darajar kasar ce take raguwa a garinku ake yin hakan ko? Ai sau dubu in kika zage ni nace miki ba zan rama ba, itama Delu shawarar da ta bani kenan, ambatar sunan Delun yake yi kamar da gangan tamkar dai ace ya san hakan yana bakanta ran baba Lantana.
Tun yaushe aka daina cin ribar fili saboda yadda darajarshi take ta faduwa ai kudi a hannu ana juyawa su ne wani abu. Da kyar Nalami ya karbi filin Baba Lantana a jaka ukun da ta sayeshi tun shekara uku da suka wuce ya kuma tasa Sallau a gaba don ya kaishi inda filin yake yana yi kuma yana yi mata bayani, yo so take in banda tsohuwar sanaiya da mutuncin dake tsakani zan karbi wannan filin ne a haka? Ai da sai ince sai masu saye sunje sun gani sunyi mishi kudi tukuna to babu irin wannan a tsakaninmu. Ya tasa Sallau a gaba suka fita.
Cikin zuciyata na ce uhm uhn kudin babana ne da aka yi ta titsiyeshi ana tarawa yau Nalami ya zo ya karbe su a karin banza. Hausawa suka ce wai, Garin banza a farau farau din wofi yake karewa.
Ban taba sanin duk wata fitina da nake ciki ko damuwa ko bacin rai nafila ne ba sai a ranar da Isiyaku ya zo min da labarin cewar wai Mubarak zai yi aure.
Samun kaina na yi rannan cikin wani irin yanayi da ba zai yiwu in tsaya ma kwatantawa ba, kwana nayi rannan idona biyu a zaune daram a tsakiyar gadona, ban kwanta ba balle in samu halin yin gyangyadin da zai zama dalilin runtsawa.
Mubarak zai yi aure? Maganar dake ta faman kai kawo kenan a cikin zuciyata wacce kuma ita ce ta hanani sakat ta hanani jin dadi ta hanani natsuwa ta hanani zaman lafiya balle in yi maganar kwanciyar hankali, don saukin abin ma shi ne ni kadai ce a ciki dakin tunda Asabe ta tafi har yau din nan bata dawo ba, don haka zagewa nayi nayi kuka sosai kuka irin na bakin ciki da tausayin kai sai da nayi na gaji don kaina nayi shiru, ina cikin share hawayen nawa ne naji zuciyata tana gayamin cewar ai kukan dadi kikeyi a yau da dai ace da kikayi mishi kyautar budurcinki kyautar wauta da shashanci ya sa ki kikayi ya karba hakan ta auku a tsakaninku to ya karbi budurcin naki to da yau kin yi kuka na gaskiya kuka iin na nadama da bakin cikin rayuwa, nayi kasake ina sauraron abinda zuciyar tawa take gaya min, lokaci mai tsaho ina sauraronta kafin daga bisani na yunkura cikin natsuwa na sauko daga kan gadon nawa na zo na soma binciken cikin kayana, hotunan da Mubarak nayi ta cirowa ina yagawa tare da konawa saboda tabbacin da zuciyata ke bani na shi kenan na rabu da Mubarak rabuwa kuwa ta har abada.
Na kosa kwarai gari ya waye don in je in shedawa yaya Dija labarin aurcn Mubarak da naji, garin ya ki wayewa nisan daren ya kai matukar nisa duhun daren ma ya kai iyakacin duhu, gani nake tamkar in naje na gayawa yaya Dija tana da wani taimako da za ta yi min ko wani amfani da zata yi min, ko wani amfani da gaya mata zai amfanar da ni, waiyo waiyo waiyo abinda kawai nake iya ji yana fitowa daga cikin bakina kenan, saboda tsananin zafin da zuciyata ke yi, da kyar na samu garin ya waye.
Muna hada ido da Baba Lantana a tsakark gida ta saki wani irin lallausan murmushi wanda rabon da in ganta tana fara’a tun ranar da Nalami ya karbi takardar filinta ya tafi, muna hada idon sai ta yi Dariya ta ce, anya ashe kema kin ji labarin, ta sake sakin wani lafiyayyan murmushin kafin ta ce, uhun in dai da namiji ne ai kuka ba ki ma fara shi ba tukun balle ke da kika wulakanta jama’a a kanki ai kadan kika soma gani. Ban tanka mata ba na sa kai na fita gidan yaya Dija nake nufin zuwa. Ina fitowa daga gida na kara rudewa na kidime jikina ya dauki rawa karkar kar, cikin hanzari na juya da baya don in koma gida, amma saboda tsananin firgitar da nayi maimakon in shga gidanmu sai na samu kaina a zauren gidan su Baba Sumaye, tsugunawa nayi a zauren cikin wani irin rudani, cincirindon mutanen da na hango a kofar gidan nasu Mubarak ne ya yi matukar razanani tafiya daurin auren nashi za a yi ko kuwa har sunje sun dawo ne?
Ban kara sanin irin rudewar da nayi ba sai da na ganni durkushe gaban Baba Sumaye ina kuka alhalin ba abinda nayi nufin yi kenan ba.
Za ki yi kuka mana Mero za ki yi kuka kai me sonki ma ai zai tayaki zubar da hawaye, wadannan abubuwan da suka faru dole ai ba kananan abubuwa bane ko ni din nan nayi kuka nayi addu’ar ubangiji ya jikan Ramatu da rahamarsa sanda akayi bikin Dija da yake tana raye ai ba a yi haka ba shiru akayi komai aka gama cikin rufin asiri da mutunci su na murna muna murna, kema maraicinta ne ya ja miki shi ya sa bana jin zafinki sosai bacin raina daya ne da kika je kika bashi kanki to ga abinda gari ya waya, yanzu waye a kasa? Waye kuma a wulakance? Babu amfani in tsaya ina yiwa baba Sumaye bayani kan cewar banyi abinda ake zargina da aikatawa ba, tunda nasan ba yarda zata yi ba don haka sai kawai naja bakina nayi shiru ina sauraron abinda ake gaya min.
Ahmad Mubarak zai yi aure don yana son daidaitawa da mahaifinshi, yin aure da kuma alkawari na zai fita daga lamarinki gaba daya su ne ka’ idojin da ya yarda da su kafin shi Alhaji Muhammadu ya yarda ya yafe mishi laifuffulkan da ya yi mishi, kema kuma don baki da mai taimakon kuruciyarki ya doraki a kan hanyar da ta dace ne ya sa aka barki kina wannan kai kawon ana yi miki wadannan wakokin na shakiyanci da iya shege, ni dai banga laifinsu kan abinda sukayi ba sun mutunta dansu ne shi da ai daraja ne gareshi sannan shi Alhaji Muhammadu shi kadai ke gareshi in dai a kan da namiji ne sannan ya’ yanshi duk mata ne abinda ya batamin rai kawai shine da basu tausayawa maraicinki ba in ba haka ba, komai kikayi ai kuruciya in ya hadu da maraici lamarin ba karami bane sai gyaran Ubangiji, to sunki, sunce bai zama dole a ce da dansu kadai kika lalace ba don haka a matsayinsu na iyaye ya zama musu dole su tsaya su ga yayi aure mai tsabta don neman zuriya mai albarka.
A zuciyata na ce wato ni in an aureni ba za a samu zuriya mai albarka ba saboda tunanin da suke yi na na riga na lalace? To in ni a lalacen nake ba da dansu aka ce na lalacen ba? Wato in ma da dana baiwa Mubarak kyautar budurcin nawa ya karba irin hukuncin da za su zartar a kaina kenan? Tambayoyin da suka rinka kai kawo a cikin zuciyata kenan kafin lokacin da na katse maganar zuci na koma sauraron abinda Baba Sumaye ke gaya min.
Ai ita uwar goyon nashi, nayi maza na daga ido na kalleta saboda ban gane maganar da take son yi ba, uwar goyon wa? Cikin natsuwa ta ce min shi Mubarak mana, na sake kallonta sai ta shiga yi min bayanin saboda ta gane ban san komai ba kan maganar da take nufin yi min din.
Ita Hajiya Ummulkairi ai ba ita ce mahaifiyarshi ba, na zaro ido ina kallon Baba Sumaye cikin tsananin mamaki, ban taba kawo irin wannan tunanin ba cikin raina, saboda ban taba tunanin akwai wata kyakkyawar mu’amala tsakanin matar uba da dan miji ba balle har aje ana samun dama ko shagwaba irin wacce na saba ganin Mubarak yana yiwa Ummanshi ita kuma ta bar komai da takeyi tayi ta tarairayarshi.
Mahaifiyar Mubarak ai Hindatu ce budurwa ya aureta tazo ta haifeshi shi kadai zaman yaki dadi, ta tsallakeshi ta yi tafiyarta, tunda ta tafi kuwa ban sake jin ko da labarin ance ta zo ganinshi ba, ina ganin kuma sanda ta barshi bai fi shekara guda ba a duniya, don sanadin mutuwar, auren ne ya zama sanadin yayeshi saboda shi uban ya ce ba zaa tafi mishi da shi ba, sai ya baiwa ita Ummulkairin shi da yake mata ce mai hikima sai ta sa hannu biyu ta rike irin rikon da ko ya’yanta bata yiwa haka ba, bata bari mummunan zaman da suka yi da uwarshi ya shafeshi ba.