In ba ni nayi mishi maganarta ba, ba ya yi mini. In na cika kawo mishi zancenta ma sai ya ce min yawaita yi mata addu’a zai fi yawaita hirarta amfani in ce mishi to.
Tunda Inna ta rasu ba mu taba dora tukunya a gidanmu da sunan yin girki ba, Babah Sumaye ke sanya mana abinci rana da dare kamar yadda ta rinka yi sanda Innarmu ke rashin lafiya.
Abin karyawa kuwa sayo mana nake yi wata rana koko da kosai, wata rana waina da miya wata rana shayi da burodi.
Kullum dai ni Babana yake tambaya me nake so? In gaya mishi ya ce in je in da kudin suke in dauko inje in saya, in na tafi kan in dawo sai in samu yayi sharar tsakar gida da kicin har da wankin bayan gida muna gama karyawar sai in tattara kwanukan da muka yi amfani da su in wanke su in kife in juye ruwan wanka in je in yi.
Innata ma mata ce mai matukar tsabta, don haka har bayan bata nan din ma ba ma iya barin gidanmu da datti, kullum ka shigo tšab zaka ganshi, kamshin turarenta ne dai a yanzu babu shi a gidan.
Gidanmu gida ne na Jama, 8, kafin rasuwar Inna amma a yanzu da bata nan wuni muke yi a ciki babu wanda ya leko mu har yaran ma sun daina zuwa dan gara gara ma Mansur jifa-jifa ya kan shigo ya gaida Babana, ni kuma ya kawo min dan wani abin lasawa.
Don haka nima ban cika zaman cikin gidan ba in Jumare tana nan in shiga gidan Babah Sumaye in bata nan in je wajen Babana in taya shi sai da kayanshi sai ya taso in debo mishi kwanduna mu dawo gida in shiga wurin Babah Sumaye in karbo mana abincinmu mu zauna muci tare a kwano daya ni da shi.
A duk ranar Juma’a kuma yakan sani in shirya in je in gaida dangin Innata mafi yawanci nafi zuwa gidan Yakunbo Halima wacce ita ce yar Inna da take bi in naje wurinta wannan Juma’ar sai wata Juma’ar, kuma in je wajen Yaya Dijah.
Babana yana mutunta Yakunbo saboda sona da take yi, sai dai duk da haka bai yarda ya bata rikona ba duk da har turowa tayi a rokar mata shi ya bata ni.
Sai ya ce a bata hakuri gani nan dai a Tsakani ai duk na ishe su. Tunda Yaya Dijah tayi arba’in kusan duk sati sai tazo gidanmu sau biyu in zata zo kuma takan zo mana da lafiyayyar miya wacce take yi mana da naman kaji ko kayan cikin saniya wata ran har ta kirbo mana sakwara wai mijinta ne yake yin cefanen ya ce tayi ta kawo mana mu rinka ajiyewa ko biredi ma rinka ci da ita shima zuwanshi biyu wurin Babana kan maganar ya basu ni.
Ya kalle shi yayi murmushi ya ce to in ba ku ita Ibrahim kai da matarka ga kuma ‘yarku sai in kara muku da ita ni fa? In zauna ni kadai? Ai ba zan iya ba.
Surakuta mai dadi Babana yake yi da Ibrahim da kawai ya maida shi saboda yayi sa’a shima Ibrahim din mutumin kirki ne ga sanin darajar surukuta.
Don haka Baba yana sonshi yana kuma son diyarshi da ya yi wa Innarmu takwara da ita ba kadan ba har ma sai yayi mata lakani yake kiranta da Inna.
Rannan ina jin Babana yana cewa Ibrahim din ka gayawa Dijah ta daina zirga-zirga da yarinyar nan a kan hanya tana diban mata sanyi, ya dan yi murmushi cikin girmamawa ya ce, Ai ba komai Baba, Babana ya ce a’a ta zauna aa dakinta kawai zuwan nata ba wani dadi ne da shi ba tunda maimakon tazo ayi wata magana da ita sai tazo ta wuni tana kuka gara ta hakura kawai ta zauna a dakinta ya ce to Baba, ya tashi ya tafi tun daga nan sai ya zama kannenshi ne suka kawo mana duk wani abin da za su aiko mana da shi ita kuwa ta koma zuwa jifa-jifa.
Inna ta rasu ne cikin watan Jimadah Thani, sannu a hankali sai gamu mun iso cikin watan Sha’aban har shima ya kusa zuwa karshe mutane sai shirye-shirye da dokin isowar Ramadan suke yi mukam a gidanmu ba a shirin komai.
Da Inna tana nan da mu ma muna nan muna ta shirye-shirye abinda zuciyata take ta gaya min kenan sai dai ban gayawa Babana ba saboda yawan ce min da yake yi mata addu’a yafi yawan hirarta amfani.
Ana gobe za a fara Azumi Babana ya bani sugar mudu bibbiyu da madarar (Peak) dozin dai-dai ya sani na bi yayun Inna mata da ke gidan aurensu na kaiwa kowacce nata na gidan Babanta kuwa shi da kanshi yaje ya kai musu haka nan gidan Baba Hodijo.
Yaya Dijah kuma mu ma ta aiko mana da abubuwa masu yawa kala-kala kuma masu dadi na kamun Azumi.
Washegari kuwa mai alfarma Sarkin Musulmi ya bada sanarwar ganin watan Ramadana mai albarka don daukacin Musulmi maza da mata suka yi niyyar daukan Azumi.
Sanda Inna ke raye na kan yi Azumin amma ba mai yawa ba, ban san dalili ba a wannan lokacin sai Babana ya ki yarda sai da nayi tayi mishi kuka ya bar ni na dauka har watan ya kai ashirin kuwa ban yi abin da yafi guda bakwai ba.
Shiga goman karshe da aka yi ne ya nuna gabatowar sallah karama daga ko’ina sai aiken kayan sallah ake yi min dangin Inna maza da mata zai wuya a ce ga wanda bai yi min ba, sai dai kawai na wani yafi na wani haka kawayen Inna da Iyayen ‘ya’yan da ta saba yi wa Kitson sallah da lalle kyauta, Babah Sumaye ma Yaya Dijah da mijinta kam ba a maganarsu ga kuma Yakunbo.
Babana ya tara kayan a gabanshi yana dubawa, idanuwanshi suka cicciko da hawaye ya ce, Wannan duk arzikin Ramatu ne Ubangiji ya gafarta mata na ce mishi amin Baba.
Mun wayi gari a gidanmu ranar sallah kamar yadda ta kasance a gidajen sauran Musulmi baki daya, sai dai mu kam maimakon walwala da farin ciki irin na sallah samun kanmu muka yi cikin matsananciyar kewa.
Mutuwar Inna ta zamo mana sabuwa saboda ganin babu kowa cikin kicin din gidanmu, da yanzu tana nan tana fama da cincirindon yaran dake karbar abincin sallah a kofar kicin dinta wanda yawanci burabuskon gero take yi da miyar yakuwa saboda shi ne mafi soyuwar abinci a wurin Babana, sai kuma tayi masar shinkafa da miya don rabo na sosai da sosai wanda ni zata yi ta aika ina mikawa sai wadanda suka san da burabuskon nata ne zaka ji suna aiko ni ki gayawa Ramatu ta sanmun burabuskon nan ina so, in ce musu to.
Yau kicin dinmu shiru babu kowa a cikinshi, na shiga cikinshi har na gaji ina ganin kamar zan ganta a mazauninta ban ganta ba, babu ita babu dalilinta.
“Ga fa kwanukan abinci nan an tara mana zo ki zabar mana wanda zamu ci ki fitar da saura ki samu masu ci ki basu don kar ya lalace” nayi maza na ce to Baba.
Nazo na dudduba na dauko kwanon Yakunbo, tuwon shinkafa ne miyar kuka da man shanu da yaji, ga kuma naman da nayi zaton na Talo-Talo ne a ciki na ce mu ci wannan Baba ga kuma masa da miya.
Mansur ya kawo na Yaya Dijah, kwan doya ne da cincin mai nama da gasasshiyar kaza, sai miya a wani kwano su na adana mana sauran zan fitar in baiwa yaran da suke so ya ce, To.
Duk da lodin kayan sallar da ke gare ni ban wani yi kwalliya ba,bayan wankan da nayi sai da Babana ya ce min to gyara jikinki mana Yahcuwuna kiyi kwalliya kamar sauran yara, sannan naje nayi.
Nayi kyau ba kadan ba, ga kitsona da Babah Sumaye tasa a ka yi min sun sauka har kafadata na shiga gidan taga kwalliyata ta kuma aike ni gidan su Jumare na kai musu abincin da tayi har da gidan Yakunbo saboda mu’amallah sosai suke yi a tsakaninsu.
Kwalliyar sallah sosai na rinka yi muka kuma yi yawon sallah ni da Jumare wacce take ganin ita din budurwa ce tunda ‘yanmata a wancan lokacin sha hudu ne sha biyar in an yi tsanani sha shida wacce ta makara sosai sha bakwai.
Har gidan zoo Jumare ta kai mu muka kuma samu goron sallah sosai wurin dangi da kuma masu son Jumare.
Tun sanda Innata ta rasu ban sake zuwa Makarantar boko ba, ko kuma ta Alkur’ani, ina zaune ne kawai a gida bana komai tanfar dai a ce da gani har Baban nawa mancewa muka yi da ana zuwa Makaranta. Sallah da sati guda ina tare da Babana, labarin yawon sallarmu da Jumare nake ba shi yana jinjina kai cikin yanayi na nuna alamar murna da gamsuwa don dai ya kara min jin dadi da na gama sai ya kalle ni ya ce min, gobe kuma ina za ku ke nan?
Nayi dariya na ce babu, ai hidimar sallah ta kare tunda yau sallah na da kwana bakwai.
Ya sake kallona ai kuwa dai haka ne hidimar sallah ta kare kenan, na ce eh Baba. Ya ce, To ai ina ganin sai kiyi shiri ki soma zuwa Makarantarki, kin ga kin dade ba ki je ba, in ma kin ga ba za ki ta bokon ba shi ke nan amma ta allo kam da ta Asuba sai ki rinka zuwa na sake ce mishi to Baba.
Jimawa can ya sake kallona cikin natsuwa ni a ta bokon aji nawa ki ke ne? A wancan lokacin da ba a cika sanya yara a Makaranta kafin cikarsu shekaru bakwai ba, saboda bin ka’idar hannun dama ya taba kunnen hagu kafin a dauki yaro a Makaranta sai na ce mishi aji uku.
Yayi maza’ya ce, A’a to ashe ma kin fara nisa ina ganin har ita sai ki koma don ki samu ki gama aji shidan ki koyi karatu da rubutu da dan turancin kai yara asibiti.
Ban amsa ba saboda jin nauyi a dalilin gane in da maganar tashi ta dosa, iyaka dai nayi shiru don komawa kan karatuna da na bari nima yafi min don zai rage min zaman kadaicin da nake ciki.
Kwana biyu bayan nan na soma zuwa Makarantar boko wanda sai da naje ta allo kafin nayi hakan gab ake da fara jarrabawar canjin aji, a lokacin da na koman sai dai da yake dama can ina cikin yaran ajin masų fahimta gashi kuma ina da kawata da muke benci daya Hasiya Jibrin, sai na samu hayewa zuwa aji hudu.
Rannan na dawo daga Makaranta na shiga wajen Babah Sumaye karbar abincina na zauna a nan wurinta ina ci muna hira tana bani labarin al’amuran da take ganin ya kamata in sani, na gama na mike na kai kwanon gun wanke-wanke na hada da kwanukan da na samu a wurin na wanke su tas, na kife na wuce bandaki nayi wanka na fito na wanke uniform dna na shanya.
Na shiga dakinta na shafa mai na dauki kayana da ke wurinta na fito ina rungume da allona, na ce mata za ni Makaranta Babah, ta ce a’a sai kin karbo min cefane, ajiye allon anan kiyi gudu ki karbo min cefane ki kawo min sai ki tafi, na ce mata to. Nayi yadda ta ce din kafin na tafi makarantar.
Mu’amala ta uwa da ‘yarta Babah Sumaye take yi dani, yadda take tafiyar da ni sanda Innata take raye haka al’amarin yake har yanzu sai dai ma kari.
Don yanzu tana sa ido sosai a kaina hada kayanki kiyi wanki, in ce to. Dauki kibiya ki tsefe kanki, tunda ba wani son kitso kike yi ba, in ce mata ban iya ba ta ce in gama abinda nake yi in kawo kibiyata tayi min tsifan kowane lokaci a cikin yi min fada take, sai dai in bata ga nayi laifi ba ko da kuwa a gaban waye.
Ina ganin har dan hakanne yasa Yakunbo bata dadewa bata zo wurinta ba, in tazo kuwa ta rinka yi mata godiya ke nan, ita kuwa Yaya Dijah kusan kullum in zata zo zata riko mata wani abun hasafi ko dai sabulun wanka dana wanki ko kayan tea.
A wannan lokacin a gida na daina barin Babana yana sharar tsakar gida da kicin, ina idar da sallah nake fita in yi komai in gama abin da ke bukatar wanki in wanke na gyarawa in gyara tunda ba wani kwanannen datti ba ne a gidan.
Sai kaga nan da nan nayi na gama na shiga wankana, yawan abubuwan da Yaya Dijah ke kawo mana kwana da yawan maganar da take yi min kan fita kullum aje sayen abin karyawa kowa yana gani yasa na rage sai in ce Baba mu ci abu kazan da muke da shi kawai ya ce min to.
Kullum na gama shiri zan tafi Makaranta sai Babana ya ce min matso nan in gyara miki hodar nan taki, in ce to. In matsa yasa gefen rigarshi ya goge min fuskata kafin ya umarce ni dasa hannu in dauki Naira daya a cikin kudin da suke dakin, lokacin nan kuwa Naira daya ba karamin kudi ba ne a wurin yara, don kuwa tana iya sayen waina ta sayi biskit har ta hada da kwalbar lemo wani lokaci ma har da alawa don haka kudi sosai nake zuwa da su Makaranta.
Ina tare da Babana a gida duk da Innata ta rasu yana matukar kula da ni, wai abin da yake yi min din ma sanda Inna take nan ba na samu, don kuwa ita mai kwaba ce mai kulawa kuma da tarbiya, iyaka dai kawai zama kusa da Inna da yunwa yafi zama a inda bata nan cikin daula da ba na sha.
Babana ya dawo daga Masallaci sallar asuba ya zauna ya gama laziminshi da addu’ar da zai yi ya gama ya shafa nima na shafa tunda a kusa da shi nake zaune na soma gaishe shi kasancewar ranar ta Lahadi ce ya sani gyara zama kusa dashi tunda ba Makarantar boko zani ba.
Zan gama abin da zan yi ne in tafi makarantar allo wannan kuwa sai wajen tara. Daga ido nayi na kalli Babana cikin natsuwa na ce mishi Baba, ya ce Na’ am Mamana, na tambaye shi yanzu duk addu’o’in da muke yiwa Inna suna zuwa inda take?
Yayi maza ya gyada kai tare da fadin da yardar Ubangiji kuwa, kin san ai akwai wasu ayyuka na sadakatul jariya masu gudana da dan Adam kan bari a duniya ladar ta rinka kaiwa a gare shi a bayan rayuwarshi daga cikin irin wadannan ayyuka da ladansu bata yankewa akwai ‘ya’ya na gari.