Na sake kallon Baba Sumaye saboda tsananta mamakina yayin da ita kuma ta ci gaba da bani labarin da ban sani ba.
Shi Alhaji Muhammadu ai ya auri mata da yawa a sanina nama akan idona ina ganin sun kai biyar, iyaka dai mafi yawancinsu basu haihu da shi ba daga ita Ummulkhairin ce sai Hindatu su ne masu ‘ya’yan, ita Ummulkhairi ya’ya mata uku su ne su Kaltume ita kuwa dama ba budurwa ya aureta ba bazawara ce ta ma haifi ‘ya’ya biyu a can wani gidan, a cikin jikokin ta na can gidan nema yanzu aka baiwa Mubarak din guda daya, ai Rumasa’u ce yarinyar da zai auran.
Ban san yanda akayi ba sai kawai na tsinci kaina da tsanar Mubarak da Ummanshi da babanshi da ma ita Rumasa’ un tunda na santa na saba ganin tana To Yi gidan sai dai ban taba sanin alakar dake tsakaninsu ba da ya wuce na ‘yar babbar yarsu ce na fassarasu a matsayin wadansu irin mutane mayaudara marasa adalci wadanda basu san kowa ko komai ba in banda kansu.
Shi da ai darajanta shi ake yi a adanashi a yi tattalin darajar shi da mutuncinshi baka barin shi ya wulakanta a gaban jama’a ba, balle ya je yana lalacewa, masoya da makiya suna kallo wasu na bakin ciki wasu na madalla, shi Alhaji Muhammadu ya yi nufin adana danshi ne don ba zai yiwu ya zuba mishi ido yana nema ya shiga wani al’amari ba, ita kuwa Ummullkoiri sai tayi amfani da damar da ta samu wajen bashi jikarta ya aura, kunga ai ya kara zama nata a hakan kuma sai ta kara samunshi a hannunta kamar yanda hikimarta tasa ta samu mijinta, to shima malam Habu da samun wani yayi ya daura miki aure da shi ya kaki dakin mijinki da ya fi ye mishi barinki da da ya yi ana yi miki wannan wulakancin da tozartarwar, to bai yi ba bai kuma da mafadi abokiyar shawararshi daya ce matarshi ita kuma bata taba shawarta mishi wani abin ariziki ba sai na sharni za kuma ta ga yanda abin zai juya mata.
Sallama nayi da Baba Suimaye na fita na koma cikin gidanmu na fasa zuwa gidan yaya Dija.
Ina shiga gidan naga baba Lantana tare da Asabe a zuciyata na tabbatar labarin auren Mubarak da ta ji ne ya dawo da ita.
Baba Lantana sai farin ciki take yi tana kyalkyalewa da dariya irin wacce ta dade bata yi ba, ita mace kowacce ai tana da kufu’in aurenta in kana da hankali kaima ba sai an gaya maka ba ni dama can nasan wannan yaron mubarak ba zai aureta ba yaro dan gata irin wannan ya rasa matar da zai aura sai ita, ai kema kin san ba zai yiwu ba, a yanda yake da irin arzikin ubanshi da îrin gatan da yake da shi habawa?
Timatiri ne fa sana’ar ubanta kowa ya sani to ko basu lalace tare ba yaushe zai aureta? Ita ba kyau ba ita ba gata ba, ita ba dangi ba, ita ba asali ba haka kawai? Ai idonsu ya rufe ne kawai kan sun duniya ba don haka ba da tuntuni suka gane gaskiya da akayi abin nan da sai malam ya bi bayan Alhaji Muhammadu Nalami ya bashi hakuri a daura’ aure to baiyi ba saboda shi agwagwane bin ya’yan shi yakeyi yanda suke so haka ake yi don haka nunawa ido ne. dama kuma ina addu’a na kuma san alhakina ne ya fara kamasu, nayi nufin yi musu abin arziki in rufa mata asiri duk da cikin da na san tana da shi na hadata da wanda nasan zai aurcta duk da cikinta don asiri ya rufü itæ da ‘yar uwarta da taimakon ubansu suka watsa min kasa a ido, to ai mu na nan da su.
Ta yi kwafa ta mike ta nufi dakinta.
Asabe dai ba ta ce mata ba to balle kuma ni can cikin zuciyata dai mamaki ne ya kamani na yanda ita da bakinta ta zauna tana bayanin gata irin na Mubarak a yau alhalin kullum abinda ta saba fadi shi ne karyar banza karyar wofi mu za a kawowa barazana, daga karyar ziki kawai haka masu kudin suke.
A wannan lokacin sai baba Lantana ta zama bata da wata hira sai na Mubarak da iyayenshi tayi ta bada labarin arziki da irin alherin Alhaji Muhammadu a wurinta a kuma bakinta naji wai ashe sabon gini aka yiwa Mubarak din a can cikin gidansu banda haka kuma aka saya mishi sabuwar mota, don ya yi angwanci a ciki, ai kwarya tabi kwarya in tabi akushi sai ta fashe, karin maganar da baba Lantana ke wuni tan ayi kenan a yanzu.
Asabe dai bata shiga harkata ba nima ban shiga tata ba ta dai dawo gidanmu gaba daya har da kayanta da na watsar sai dai kuma a yanzu ba abinda yake gabana kenan ba ina ji da kaina, ina cikin wani irin tashin hankali da rudanin da ban san yanda zanyi in fita daga cikinshi ba.
Gaskiya ne duk wani abinda baba Lantana ta fada akan Mubarak da irin gatan da iyayenshi suka shirya mishi tunda aka fara bikin ummanshi ke bin gidajen makwabta da abinci dana sha ko kaje gidan bikin ko kar kaje za a kawo maka nau’o’in abincin da aka girka kala kala, ina ganin tamkar a unguwar nan gabadaya gidanmu ne kawai bata yiwa irin wannan aiken ba.
A ranar da aka kammala bikin kuwa ina kwance a kan gadona ina jin dirin motocin abokan Mubarak da suka rakoshi wurin babanshr ya şa mishi albarka kafin su rakashi dakina maryarshi don ance wai tunda aka yi abin yau ne ranar farko da Baban nashi ya yarda zai ganshi.
A wannan daren bana iya kwatanta komai game da halin da zuciyata ke ciki, iyaka dai kawai na san kasancewar Asabe a dakin nan ba ya hanani yin kuka ba tare kuma da na damu da ta ni ko bata ji yi kawai nake yi don in samu in samu saukin ciwon da kirjina ke yi. Ban san abinda take ciki ba sai jinta nayi ta ce, uhun dama kin hakura kim yi shiru tunda taki mas’alar ma ai mai sauki ce. Ban kulata ba itama bata sake ce min komai ba.
A wannan lokacin sai na zama babu abinda nake sha’awa irin in ga mutane masu yan uwa da dangi a wasu garuruwan na nesa sai in rinka jn tamkar inama dai nice da tuni na tattara kayana na koma can inda suke dan in samu saukin bacin ran da nake ciki, wani lokacin kuma nice ina ma dai dai babana yayi min irin abinda baba Sumaye ayi sha’awar ace ya yi min na aurar da ni ga duk wanda ya ga damada yanzu nima ina can gidan mijina ko ina son shi ko bana sonshi kuma ai zan zauna darajar shi baban nawa ne ya bani shi sannan ko bana son nashi kuma ina ganin ba zan gamu da bacin ran da ya kai wanda nake fama da shi ba a yanzu.
Ana gama bikin Mubarak kuma sai na sake zama abin nunawa wurin ‘yan mata da samarin da dama na rike musu wuya sai da ya gama da ita sannan yaje ya auro gal a leda, abinda suke ta fadi kenan ko naji suna fada suna dariya bana kulasu ko kuma su yi ta rera wakokin da makada da mawaka suka yi ta rerawa Muberak din da iyayenshia wurin bikin, sai da ta kai ma na sake daina fita waje saboda tsananin dana shiga cikin zuciyata na rika tambayar kaina sai mace?
Kullum in za a yi maganar ta nashi bangaren da ya gama da ni din akan furta a yanayin da bai yi kama da aikata wani laifi ba sai dai ma kaga tamkar ya yi wani alin gwaninta ne ko bajinta, a nawa bangaren ne za a yi ta a yanayi na wulakanta ko tozarta ko kuma muna ailkata wani abin kunya da wuiakantar, kai da nal ura da kyau da yanayin da ake bayar da labarurrukan sai na gane shi Mubarak ma sha’awa yake baiwa mutane ga kuna gatan da iyayenshi suka yi nishi wanda mutanen unguwar basu gajiya da bayar da labarin, bisa wanan lurar da nayi da abinda ya sameni sai nima da kaina na yardarwa kaina da cewar ita mace ita ce mai yin abin kunya in har abin kunyar ta zo, ita ce kuma mai tozarta in abin tozartar ya zo, ita ce mai shiga ta wulakanta saboda ita ce mai rauni komai ya faru a kanta yake karewa, ita ce a kasa, ita ce take bukatar mutunci da kunya don su zamo sutora a gareta, shi namiji karfi kawai yake nema.
Dana kara tsunduma cikin tunani sai na tuna da wasu kalmomi da na taba gani a cikin wani littafi a hannun Mubarak, ga abin da suka ce: MAN IS BORN FACE AND EVERY WHERE HE IS IN SHAKKLE”
Da na natsu na dawo cikin haiyacina sai na samu kaina a yanayi na godiyar Ubangiji da ya taimakeni ya rufamin asiri ya hana Mubarak karbar kyautar da na yi mishi, in tuna kaina in tabbatarwa kaina ni din budurwa ce gal a leda, shi ne abin da yafi komai sanyaya min zuciyata a wannan lokacin.
Bikin Mubarak da kwana goma na hangoshi tsaye a kofar gidansu a dalilin fitowar da nayi za ni shago don sayawa babana ruwan swan din da nake amfani da shi wajen bashi magani, ban san yadda akayi ba ina tsaye a shagon nan cikin bari saboda kaduwar da nayi a dalilin hangoshi da na yi wanda shi ne ganina da shi na farko tun bayan faruwar abubuwan da suka faru a tsakaninmu.
Motsi na ji a bayana tare da shakar wani irin sanyayyan kanshin da ya yi sanadin da na yi matukar tsarguwa da zuciyata ta yi, da sauri na juya don fidda rai daga zato saboda in samu natsuwa a tare da ni, sai kawai idanuwanmu suka hadu an yi maza najuya don karbar abinda nace a bani, jikina sai rawa yake yi har kárkarwa tamkar sanyin hunturu ne yake kadani, cikin wata irin kwalliya yake ga kamshi gashi in ba kuskure nayi ba sai naga kamar kiba ya yi, nan da nan na ji zuciyata tana gayamin shi bai da damuwa shi dadi yake ji, shi hankalinshi a kwance baida wata matsala a tare da shi, da sauri na mika hannu na karbi ledar siyayyar tawa da ya yi nufin karba, ban bata lokaci wajeu tsayawa karbar canjin ba nayi maza na bar wurin.
To tsaya mana Mero jirani mana ai wurinki na zo. Bai ji kunyar fadin hakan ba a gaban mutanen da suka cika a shagon, ina jin maganganun na shi na yi maza na kara maimakon sauri na yanka da gudu nayi amza na shige cikin gidanmu ba tare da na saurareshi ba.
Kwana biyu bayan nan na fita gida da sassafe don sayawa babana kunu da kosan da na saba siya mishi, ina zaune wurin mai kosan ina jiran ta zubamin saboda na samu wasu a gabana da yawa sai kawai na ganshi ya iso wurin, kallo daya nayi mishi nayi maza na sunkuyar da kaina na dora hannu akan guiwata yayin da na zagaye guiwar tawa da hannayena duka biyu, doguwar farar jallabiya ce a jikinshi duk da ban tsaya kare mishi kallo ba nasan ta karbeshi.
Ina kwana Baba? Ya soma gaida baba mai kosan tana amsawa, lafiya lau Amadu ya ya su Hajiya da iyalin naka? Lafiya lau. Ya amsa mata, sakun kosan bai so kan Mero baba nc? Da sauri ta ce mishi ko baizo ba ai sai a zuba mata Amadu. Nan da nan ta zuba da yawa fiye kudin da na bata ta kunsa ta mikomin nasa hannu biyu na karba na dora a kan murfin kwanon kunun na dauka na kama hanyar zuwa gida, Mubarak yana biye da ni babu halin in ruga da gudu in tafi in barshi saboda tsoron kar kunun nawa ya zube.
Ki tsaya mu yi magana mana Mero. Ban kula shi ba tafiyata kawai nake yi, ban fa yi miki laifin komai ba balle ki ce za ki yi fushi da ni, ni da ke mun shiga wani irin al’amari ne a dalilin sharrin da matar Babanki ta kulla mana, na kuma san ba zai yiwu tanshanye ta gama lafiya taga yanda take so a rayuwarta ba tunda ita sharri tasa a gaba, in ma kina da wani tunani ko kulli game da ni a zuciyarki to ki yi hakuriki sake kawai duk abinda kika gani kuma ya zama dole ne kawai ya sa kika ganshi a yanda kika ganshin, a shirye nake kuma in yi miki bayanin da zai gamsar da ke.
Ban kalleshi ba balle in tanka mishi har muka zo kofar gidanmu muna isowa kuwa nayi maza na wuce cikin zauren gidanmu na barshi a can waje.
Tun daga nan na zama bana fita daga gida kai tsaye sai na dan tsaya na yi waiwaye waiwaye in tabbatar ban hangoshi a kusa ba.
Rannan ina zaune a dakina ni kadai sai ga Isiyaku ya shigo yana sallama, na amsa sallamar tare da bashi izinin shigowa, ya nemi wuri ya zauna muka shiga gaisawa har da yin hira tun da dama can abokin hirana ne, na yi ta tunanin abin da zan dan kawo mishi ya dan taba saboda nuna girmamawa ga bakonka ban tuna ba don bani da komai a dakin don haka na hakura muka ci gaba da hirar a haka jimawa can sai ya ce min, Mero ni zan tafi. Nayi maza na ce mishi ai na gode maka Isiyaku sai dai ka shigo yau dakin nawa babu komai a cikin shi.
Ya yi murmushi tare da fadin, babu komai. Ya dan karkace kadan sai naga ya zaro wata takarda daga cikin aljihunshi ya miko min tare da takardun kudin naira ashirin ashirin cunkus a hannunshi wai gashi in kawo miki. Nayi maza na zuba musu ido tare da tambayarshi menene wannan? Cikin natsuwa ya yi min bayani, wasika ce tare da kudi ya ce in kawo miki. A hankali na sake tambayarshi, in ji wa? Ya dan yi murmushi kadan kafin ya ce min, inji yaya Mubarak mana wa zai yi mikıi irin wannan aiken in ba shi ba? Ya baka kudi ba kawo min? Ina yi mishi tambayar na soma kuka tun katin ya kai ga amsa min nan da nan ya hidime ya shiga bani hakuri yana yi min magana, to menene in ya baki kudi an shi Mero? Yanda duk kika dauki abin fa ba haka yake ba shi Yaya Mubarak.