Skip to content
Part 33 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

To menene kuma na kukan hakan? Ya soma yin maganar a yanayi na sanyin jiki alamar bacin ran da ya zo da shi din ya kau, to ni me nace miki da kike wannan kukan? Kinga share hawayen nan ki ji abinda zan gaya miki, to ai kuma na gane so kawai kike yi raina ya baci shi yasa kike ta kukan, in ba haka ko ma menene nace ki yi hakuri ki yi hakuri ina ce shi kenan zance ya kare.

Kinga tunda abin nan ya zama haka ana nema a rinka kai kawon maganganu a tsakani to ina ganin gara kawai a kawo karshen al’amarin gaba daya in kina dakina da wani wanda ya isa ya zo yana kananan maganganu ne a tsakani? Don hakan ni in kin yarda kawai a shirye nake in je in samu babana ya dawo ya sake yin amgana da baban nan gidan a daidaita a sanya lokacin auren mu kome kika gani.

Lokaci mai tsawo na dauka ban ce mishi komai ba har ta kaima ya sake tambayata, ba ki ce komai ba Mero ko kuna da wani tunani ne? Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi, kai ne dai nake ganin kamar ya kamata ka kara tunani akan maganar tunda ka sani sarai an fadi maganganu da yawa a kaina har yanzu ma ba a daina ba tunda ga ma wanda aka je har gidanku aka fada kwanan nan in…

Ban karasa zancen nawa ba ya yi maza ya katseni, yanzu ina amfanin wannan maganar da kikeyi in dai ba so kike sai döle kin sa raina ya baci ba?

Shiru nayi bance mishi komai ba, kar ki sake kawo min irin wannan maganar bana so.

A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to kayi hakuri. Dadi ya kamashi saboda hakurin da na bashi, ya dan gyara tsayuwa kafin ya ci gaba da magana, shi Baba yana dawowa zanje in same shi da maganar. Na ce Ubangiji ya dawo da shi lafīya, yayi maza ya ce amin Maryam.

Kafin babansu Mansur ya dawo wata irin lafiyaiyar soyaiya muka shiga, ka’ida ne kullum sai ya zo ko da rana ko da daddare, wataran ya zo ya sake dawowa, in na ce mishi baka riga ka zo ka dazu ya ce ai wata magana ya tuna da ya manta dazu da ya zo din bai gaya mini ta ba.

Rannan muna hira ni da shi tattaunawa muke yi irin ta fahimtar juna, ra’ayinshi yake fada kan irin tsarin da yake ganin zan gudanar a gidanshi wanda hakan yake matukar taimakawa ma’aurata bayan an yi aure.

Kin fa san ‘yan uwane da ni masu yawa ina fata zaki yi hakurin zamada su. Na yi murmushi na ce, insha Allahu. Can cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ni da nake rayuwa cikin kewar ‘yan uwan miji zasu isheni har in kasa yin hakuri da su? To kuma ba zan barki yin aiki ba don kar ki ji ina cewa za ki koma makaranta don ki samu takardarki ki yi tunanin ko har da aiki cikin lissafin nawa.

Na yi murmusih na ce nima ban damu da yin aiki ba amma cikin zuciyata ina sha’awar yin sana’a, da sauri ya ce wonderful tamkar ace kin shiga zuciyata kin gani ai ni mai sha’awar taimakon mace yin sana’a ne, Maryamu ina son ganin matata ta tsaya da kafafunta tana dogaro da kanta saboda karki samu damuwa akan wannan wacce irin sana’a kike son yi?

Na ce a’a ban sani ba tukunna ni dai kawai cikin zuciyata ina son yi amma ban zabi wacce zanyi ba, to ai kin gani ma shi kenan sai in duba in ga abinda zaifi dacewa da ke ina ganin ma kawai dinki za ki yi domin shi ya fi bani sha’awa ko kuwa? Na ce mishi to.

Tun ranar da Mubarak ya zo gidanmu ya rokeni alfarmar fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba, ya dauki mataki in ya ganni bai kulani ko yana fara’a ya hangoni sai ya yi maza ya tsuke fuska, a zuciyata na ce nima gara irin haka, abu guda daya dai da na kasa fahimta ko dalilin yin shi shi ne wunin da Isiyaku yake yi kan dakalin kusa da gidanmu a zaune bana dai ko amsa gaisuwarshi balle-wani abu ya hadamu tunda kowa ya san dan gidan Mubarak don haka na kara kiyaye mu’amala da shi don Mansur ya kara samun kwanciyar hankali.

Ni da Mansur muka zama bamu da wani fata ko buri sai na jiran dawowar babanshi daga tafiyar da ya yi. Mansur da kullum yake ce min ai kawai kwana daya zan yi mishi in ya dawo da rana in barshi ya kwana ya wayi gari kafin inje mishi da maganar. Sai gashi baban Mansur ya dawo har ya kwana bakwai babu wani motsi ko yunkuri daga gidan nasu shi da kanshi ma sai nake ganin shi tamkar a sanyaye yake ban dai ce mishi komai ba tunda dama can ba ni ce mai zumudin maganar ba ni yar tayawa ce.

Wurin Baba Lantana mai yada maganganu a tsakar gida na samu labarin wai ashe da baban nashi ya dawo ya kai mishi maganar sai ya ce mishi ba zai sake takowa ya zo wurin babana kan maganar aurena ba, ya dai yi zuwan farko ya kuma isheshi haka don haka in har auren yake so da gaske to ga ‘yan mata nan bila adadin tun daga na dangi har bare yaje ya duba gida na mutunci ya zabi yarinya zai tsaya ya aura mishi ita ko da kuwa nawa zai kashe, amma bani ba in ba rashin hankali irin nashi ba ko iyayen Mubarak da suka san da dansu na rinka lalacewa ai ba su bar shi ya aureni ba balle shi.

Wannan bayanin da naji a bakin Baba Lantana ba karamin dukan zuciyata yayi ba, don kuwan a riga na sakankance na saki jiki zuciyata ta riga ta amince da maganar aurena da Mansur sai dai duk da haka ban bari yanayin da na sanu kaina a ciki ya baiyana ba, saboda na riga na koyi shanye bacin rai ba komai ya taba zuciyarka sai na kusa da kai ya gane ba, haka nan bacin ran da na samu bai sa naji haushin iyayen Mansur ba to balle kuma shi Mansur din da na tabbatar shima bai ji dadin hukuncin da aka zartar mishi ba, sai dai ya yi biyaiya kamar yanda kowane da na kirki yake yiwa iyayenshi biyaiya kan umarni ko hani da sukayi mishi, bai dai ce min komai ba nima kuma bance mishi na ji ba sai dai kuma biri yayi kama da mutum gaba daya ya canza fara’arshi, kuzarinshi duk sun sauya mainakon zuwa kullum ya koma yin fashi in yau ya zo gobe ba zai zo ba watarana ya yi kwanaki na yi kamar in ya zo in rinka kin fita sai kuma na ga to a na me?

Rannan dai ya gaji shi da kanshi ya zaunar da ni ya yi min bayanin komai, hakuri mai yawa ya bani ya kuma rokeni kan kar gaya min gaskiyar da ya yi ya kawo karshen mutuncin dake tsakaninma, na ce mishi a’a ko kadan ba za a yi haka ba sai dai ma a kara nima nayi mishi godiya kan alherinshi a gareni.

Ko ban tsaya yin bayani nayi bacin rai ko ban yi ba an san nayi saboda na riga na so aure na kuma so Mansur don haka fadama batawa ne kawai.

Tunda Mubarak ya taso ya zo gidanmu ya rokeni in fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba na tura al’amura sun sauya a tsakanina da shi amma ban kara sanin irin tsananta da lamarin yayi ba sai a ranar da nayi shiri da niyyar zuwa gidan Yakumbo Halima saboda dadewar da nayi banje ba har na samu labarin korafinta wajen yaya Dija.

‘Yar madaidaiciyar kwalliya nayi a dalilin tsala kwalliyar ta daina burgeni ta daina sanyani nishadin da ta saba sanyani a baya, sai dai kuma bai hana kwalliyar tawa zamowa mai ban sha’ awa ba.

Ina tafiya cikin natsuwa ba tare da na damu da kallo ko sanin su wa nake wucewa bisa hanya ba har na kai ga shiga lungun da fita daga cikinshi zan bulla kan layin da gidan su Yakumbo Halima yake.

Kasancewar lungun a matse yake gashi kuma da yawan kwata ‘yar hanyar da ake bi din ba wata mai fadi bane ya sani ai hanyar waiwayawa in ga wanda ke biye da ni yana taku cikin sauri dan in kauce mishi in bashi hanya ya wuce in har naga alamar akwai bukatar hakan, abin mamaki Mubarak na gani gabana ya yi mummunan faduwa bisa dalilin guda biyu dalili na farko shi ne faduwar gaban da na saba samu a duk lokacin da na ganshi ko na ji muryarshi wanda kwanakin baya nake murnar na rabu da shi to ya sake dawowa, daliil na biyu kuma shi ne mummunan kallon da ya tsiri yi min a tsakanin nan ko yana walwala ya hangoni sai ya yi maza ya daure fuskan wani irin daurewa kuma mai tsanani.

Na maida kaina kan hanyar nufin ci gaba da tafiyata, yayin da wani bangare na zuciyata yake bani shawarar in karta kawai da gudu don in samu in yi nesa da shi tunda ga dukkan alamu zai kamoni saboda dogon taku: da yake amfani a tafiyar ta shi.

Tsaya mana mu yi magana, na yi kamar ban ji abinda ya ce ba na ci gaba da tafiyata sai kawai na ji caraf ya kamo gyalena ya rike, ina yi miki magana kina ji nakina tafiya.

Raina a bace saboda fusatar da nayi na rike min gyalena na juya da nufin yi mishi tuni kan hana shi yi min hakan da na taba yi in da hali ma in yi mishi tuni cikin tsiwa den kar gobe ya yi tunanin sakewa.

Muna hada ido da shi gabana ya sake faduwa na yi maza na sunkuyar da kaina kasa saboda wani irin kallo da yake yi min wanda ban saba da shi ba.

Kina nufin ko saurarona ba ki da lokacin yi da nake kiranki kina ji na? So nake in tambayeki yaya naji maganar aurenki da masoyin naki tayi sanyi kamar ma babu ita? Sakarya kawai sokuwa mara wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya kamace ta in taso in zo in rokeki ki fita hanyar shi ki ce min wai ba za ki yi ba? Ai nayi hakan ne don ina zaton ina da matsayi a wurinki saboda kin yaudareni kin yi min abinda na yi zaton ni din daban ne a wurinki saboda kin yaudareni kin yi min alheri wanda na yi zaton bani da abokin gami a wurinki, ashe ba haka bane to amma kuma na gode shi da akayi mishi hani a kanki ya hanu.

Gabana sai harbawa cikin sauri yake yi, bakaken maganganunshi sun yi tsanani da nauyi cikin zuciyata kokari mai yawa nayi kafin na danne hawayen da ke shirin zubowa a idanuna na hanasu zuba don kar in yi kuka a gabanshi don haka najuya da nufin ci gaba da tafiya, sai naji ya ce, ni babu inda za ki sai kin bani amsar tambayar da na yi miki.

Cikin natsuwa na bude baki wanda bai ma san zan bashi amsa ba dan ya san ban cika yin hakan da shi ba na ce mishi, kayi hakuri ba yaudara ya sani yi maka hakan ba kuskure ne.

Ya yi maza ya gyara tsayuwa tare da kara tsareni da idanuwanshi cikin saurarona binda zai kara fitowa daga bakin nawa, ni kuwa ban fasa ba na ci gaba da yi mishi bayani, kuskure na yi nayi maka abinda na yi makan wanda ya sanyaka yin tunanin kana da matsayi na daban a wurina da har zaka ganni da masoyina ka roki alfarmar in fita hanyarshi, ko Mansur ya rabu da ni ba zan zamo wani sabon al’amari a wurina ba don sunnar magabata ya bi zan kumaci gaba da girmamashi tare da soyaiyar da muka yi wa juna saboda mun yi ta mun gama ta ba tare da ta yi min wani sanadi na wulakanci ko tozarta ba a wurin jama’a, na kuma gode maka da baka yi amfani da kuskurena da wautata da sakarcina da sokoncin da na rayu a ciki a dalilin bani da mafadi ya sani nayi a kanka ba da ka yi amfani da damar da wadancan abubuwan suka sanyani na baka a kaina da ka yi dalilin da na kara zama shashasha sokowa sakarya waçce ta aikata kuskure a rayuwarta, kuskure kuma har abada, don haka duk abinda ya faru tsakanina da kai tun daga farkonsa har zuwa karshensa kus…

Ban kai karshen maganar da zanyi ba sai kawai na ji kafafuwana sun zurma cikin kwatar dake bayana, nayi maza na kalleshi cikin tsananin bacin rai nan take kuma na sake dago idanuwan nawa suka hadu da na Mubarak dake yi min wani irin kallo, yanayin da na gani a tare da shi ya tabatar min da cewar ba ji nayi kama ba shine ya hankadani cikin kwatar da na zurma.

Kar ki sake yin kuskuren kallon idona ki ce za ki yi min rashin kunya irin wanda kika yi min yau in kuwa ba ki ji kashedin na yi miki to za ki gane baki da wayo, sakarya kawai sokuwa shashasha mara wayo wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita.

Yana gama fadin hakan ya ja wani mummunan tsaki ya wuce yayi tafiyarshi ya barni cikin kwatar ko a jikinshi.

Da kyar na iya zare kafafuwana daga cikin kwatar takalmana kuwa asararsu nayi don kafafuwan nawa kadai na iya zarewa, a hakana rinka diddingisawa na doshi gidan Yakumbo Halima cikin zuciyata dai ni kadai nasan abinda nake ji game da Mubarak, na tsaneshi na kishi na rinka jin wani irin ciwo a zuciyata game da shi, babu abinda ke kai kawo a zuciyata in banda na tunanin yanda zanyi in dau fansa a kanshi kan irin wulakancin da ya yi min, da dai ace so shi ne samu to da na tashi daga wannan unguwar na koma wata don in yi nesa da shi in daina ganinshi dan ya daena shiga harkokina.

A haka na shiga gidan Yakumbo Halima, tana ganina ta kama yin salati, wane irin rashin dabara ne wannan Mero? In zaki fada kwata sai kuma ki fada da kafa duka biyu kamar wata yarinya ‘yar karama?

Ban iya ce mata komai ba kuka kawai na kama yi don daman daurewa kawai nayi na hana kaina soma kukan tun daga waje. Cikin hanzari ta tsame hannunta daga cikin kullin danwaken da take jefawa da sauri ta iso inda nake tsaye ina ta faman kuka.

Haba Mero haba Maryamu daso don kin shiga kwata kuma sai ki tsaya kina kuka? Ai tsautsayi ne shi kuwa kin ji ance bai wuce ranar shi ba, bari in kwara miki ruwa a kafar in wanke miki dagwalon sai ki shige bandaki ki yi wanka ki canza kayan jinki da wasu.

Har nayi wanka na fito na gama abinda zanyi duka na zo wurin Yakumbo Halima na zauna ina tayata jifan danwakenta idanuwana basu daina zubar da hawaye ba, na kasa gane dalilin bakaken maganganunshi musamnman gorin da yayi min kan fasa aurena da Mansur ya yi sunyi min ciwo da yawa.

<< Halin Rayuwa 32Halin Rayuwa 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×