Skip to content
Part 34 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Rarrashi, banbaki da wayon da Yakumbo Halima tayi tayi min ya sani kwashe bayani duka na yi mata.

Dama ashe zancen da nake ji a gari na har yanzu baku rabu da juna ba gaskiya ne? Tsuru na yi ina kallon Yakumbo ashe kuskure nayi da na yi mata wannan bayanin, ashe da ma kadan take jira da ni, to kuwa ba zai barki ki yi aure ba kin ji na gaya miki ke ya hanaki aure ya tsareki a waje a cikin gida kuma yana tare da matarshi duk tsiyar da yake yi mata wanda ke sanyata zirga-zirgar yaji tun da dai yana kusantarta ya biya bukatarshi a tare da ita ai aikin banza ne karyar iya shege kuma yake yi wanda bai son mata ai baya kusantarta indai har da gaske yakeyi yanzu da ta tafi kwanan nan iyayenta suka aiko a gayawa Alhaji Muhammadu cewar tana da ciki wata biyu yayi musun cikin? Ba cewa sukayi sun janye sakin da yayi mata ba suka je suka dawo da ita dakinshi kuma suna nan tare su na zamansu ana tarairayarta ana murna zata haifar musu da ko ya, shi ne ke ba za ki yi zuciya ki kama mutuyncin kanki ki fita harkarshi ba sai ki je kina biye mishi kuna lalacewa tare… Ta kama kuka irin wanda bai kwatantuwa.

Jikina ya kama bari hankalina ya yi mummunan tashi ganin irin kukan da Yakumbo ke yi, na rantse aiki Yakumbo… Kan in fadi abinda nake nufin gaya matan tuni ta rufeni da duka da hannaycnta duka biyu, rantsuwar karya zaki yi min saboda kin maidani shashashar uwa to ai ni da yaya Ramatu duk daya muke uwa daya uba daya muka tasha nono ta bani da kike nema ki maidani mara mutunci. Tana kuka take wannan bayanin.

Tuni nima na shiga nawa kukan, ba don dukan da tayi min din ba sai don bakin cikin al’amarina da bakin cikin yanda na zamo gaba daya iyayena da jama’ar gari suka yarda da cewar lalacewa mukeyi ni da Mubarak, yaya Dija ce kawai na tabbatar ta yarda da maganar da nayi mata na babu komai a tsakanina da shi don ta babana kuwa ba zan iya cewa komi ba tunda ban taba jin ya bude bakinshi ya fadi wata magana ba balle in san a wane hali ya dauki lamarin.

Ban san abinda ta gani ba ko abinda ya faru ba naga maimakon dukan da take ta kai min da hannayenta duka biyu ta jawoni jikinta ta kankame da karfinta kuka mai yawa ta yi kafin daga bisani ta sakeni, ki yi aure Maryamu ki yi aure abinda kawai zan gaya miki kenan. Maganar da ta fara yi kenan bayan ta gama kukan nata.

Cikin sauri na ce mata to Yakumbo ba tare da na san wanda zan auran ba sai dai kawai don in kwantar mata da hankali.

Alkawarin da na yiwa Yakumbo Halima na cewar zanyi aure ya san himmatuwa wajen ganin na fidda mijin aure ko da kuwa wane iri ne babu maganar tsayawa duba cancanta balle a yi maganar zabe, aure kawai nake so in yi ko zan samu in fita daga zargin da ake yi min na akwai wani abinda ke faruwa tsakanina da Mubarak na lalacewa sannan yin auren nawa zai zamo dailin da zan bar unguwarmu in yi nesada ita in daina ganin Mubarak wanda a yanzu na tabbatarwa kaina da cewar in har akwai wani mutumin da na tsana a rayuwata a halin da nake ciki to shi ne na tsani Mubarak, na tsani duk wani abinda ya shafeshi, na tsani duk wani labari da ya danganceshi, musamman ma labarin matarshi da cikin dake gareta wanda kuma ya zamo shi ne labarin Baba Lantana da take wuni tana bayarwa ta rinka fadin karyar banza karyar wofa, yana kinta yake kwabewa a gabanta? Sai kuma ta ja wani mummunan tsaki ta ce, ku dai da ya mayar sakarkaru ke da ubanki sai ku yi tayi ya rinka samunki yana rage gajiyarshi ta rana a kanki tunda haka kuka zaba.

Rabon da in tankawa baba Lantana ko wani nata wata magana har na manta saboda abinda nake ji yafi karfin duk wasu maganganun na ta ciwo a raina.

Rannan ina tsaye tare da wani sabon saurayi da nayi wanda inda ya biye min da ko kwana goma bai yi da fara zuwa wurina ba ya turo iyayenshi aka daura mana auren saboda irin karbar da na yi mishi da kuma za a tsareni a tambayeni dalili na na yin irin wannan bare-baren a kanshi abu guda da zan iya fadi kawai shine ba dan unguwarmu ba ne ina son aurenshi ne kawai don in samu in yi nesa da unguwar in banda haka babu wani dalili.

Ina tarę da shi muna hira a kofar gidanmu sai kawai ga Mubarak tamkar daga sama aka jehoshi, gabana ya yanke ya fadi saboda ganin inda muke zaune ya tunkaro gadan-gadan nayi maza na kawar da kaina daga gareshi saboda irin kallon da na lura yana yiwa wanda muke tare da shi din wanda shima na gane ya tsargu da Mubarak din.

Yana isowa sai na ji ya ce mishi, malam lafiya na ganka anan wurin? Da sauri mutumin ya daga ido ya kalleshi lafiya? Ban gane tambayar taka ba, ya zuba mishi ido cikin natsuwa yana kallonshi, wannan iyalina ce baka ji abinda ke tsakanina da ita ba ne? Ya shiga waige-waige hankalinshi a tashe jin da ya yi Mubarak ya ce mishi ni din iyalinshi ce.

Ai ban san matar aure ce ba ni a sanina…

Kan ya karasa bayanin ya yi maza ya ce mishi, bar nan kawai tun kafin abin ya kai ga ranka ya baci.

Yanzu kuwa in ji mutumin, ko raina ba zai baci ba ma ai da sanina ba za ni wurin iyalin wani ba, ita ta ha’ince ni ta boye min gaskiya, ya kama hanya ya yi tafiyarshi, nima na mike na shiga gida na barshi a wurin ban tsaya jin wata magana tashi ba.

Ina gida akan gadona a kwance ina tunanin al’amarin cikin zuciyata dai nasan babu mutumin da yake shiga harkokina yake takuramin yake bata min rai yake sanyani bakin ciki a rayuwata irin Mubarak sai daiban san yanda zanyi da shi ba tunani mai tsanani na shiga ciki har daga karshe na yankewa kaina hukuncin komawa gaban Yakumbo Halima in gaya mata abinda ke faruwa don kar ta dauka ban ji maganar da tayi min ba na fito da miji ba. Na gyara na yi kwanciyata da tunanin na kaiwa Yakumbo Halima bayanin abinda Mubarak kc yi min.

Ina kokarin tilasta kaina yin bacci kenan sai na ji Asabe tana kwalawa sunana kira, cikin irin muryar tsoro ne ya kanani saboda sanin da nayi cewar ni da Asabe bama ko ga maciji.

Waiyo-waiyo dama dai kawai in mutum in huta da wannan wahalar. Zumbur nayi na tashi na zauna saboda jin maganar ta ta, me ya same ki haka Asabe?

A tsorace na yi mata tambayar. Bata tanka min ba, waiyo-waiyo, abinda kawai take ta faman fadi kenan.

Na sauko gareta ina kokarin riketa don in tsaida murkususun da take yi a kasa cikin yanayi na tausayawa ina isowa garéta na gane lamarin ba karami bane, ya kuma wuce duk yanda ake zato don haka nace mata bari in kira miki baba Lantana don tazo ta ga halin da kike ciki in ya so a kaiki asibiti. Tayi maza ta ce min u’u barta kawai kar ki kira min ita ke dai kawai ki taimake ni ki kaini cikin kankon bola ki barni a wurin in ma mutuwar zanyi in mutu a can.

Tausayin Asabe ya yi matukar kamani, haba Asabe daina fadin irin wadannan kalaman kankon bola a cikin tsohon daren nan ko mahaukaci ai ba zai dunfari wurin ba, na shiga share mata gumi da majina da hawayen dake ta dalala.

Ki yafemin abubuwan da na yi tayi miki Mero satar kayanki da na rinka yi ina sayarwa da kudinki da sharrin da na… Kai haba Asabe bar irin wadannan maganganu ai zanman tare ne.

Ana cikin haka naga Asabe tayi rigingine ta bankade komai babu sauran kunya a tare da ita, tsoro ya sake kamani jikina ya dauki rawa cikin muryar kuka nace mata Asabe, don naga alamar bata cikin haiyacinta, kan in kai kkarshen bayani na hango wani abu yana shirinf itowa da gudu na nufi kofa na balleta cikin rawar jiki da karkarwa na buga kofar da take ta baba Lantana da babana, tana jin bugun kofar da nayi sai na ji ta soma cewa, yauwa ai ga ranar da nake jiran zuwan nata nan ta zo ranar da asiri zai tonu, ranar da zaka gane shirunda kake kame bakinka kana yi a kan komai ba dabara bace, ai tun dazu nake gaya maka wannan zirga-zirgar da ake yi ana ziryar bayan gida da kyar ne in ba nakuda ake yi ba, ni na dade ina fatan ganin an haifar maka shege a gidan nan, ba dai kwadayin abin duniya ya sa ka zuba mata ido tana yin abinda taga dama ba? Yaro ya ki aurenta ya kai gida amma a waje ya maida ita matarshi? To muje ka karbi haihuwar da hannunka don kar ka ce sharri aka yi mata ba a jikinta ya fito ba don haka nuje a yi kornai a kan idonka, kaga ta inda yake fita muje mu je.

Ina jin hakan nasan fitowar zasu yi tare don haka na tsaya a inda ana bude kofar babana zai ganni.

Abin kunya ina jin gadonshi kukeyi malam tunda ba haka ai nayi ta gudun makashi baka yarda da shawarat bane yasa baka koreshi ba sai da ya sameka saboda bai damcka ba, muje nace muje kana ji ana ta gurnanin nakuda ka ki kayi kuzari sai wani jan kafa kake yi kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki.

A na bude kofar mukayi ido hudu da babana, muje mana kayi wani kerere ka tsaya min a hanya kaki ka bani wuri in fita, abinda haba Lantana ke fadi kenan daga bayanshi saboda kasa motsin da ya yi a dalilin ganin da ya yi min a bisa da na tabbatar kuma shi ne da ni ya gani a cikin wani hali na abinda take gaya mishi watakila da ya yi faduwar da bai sake tashi ba don a haka ma tsinkewar da yayi ta kai duk inda ta kai.

Kurdawa tayi ta bayanshi ta fito saboda ta kasa hakurin ya matsa ya bata wuri, tana ganina a tsaye tayi maza ta ja ta tsaya ta yi turus cikin tsananin kaduwa nan take tsoro ya baiyana a idonta, a’a to wake zirga-zirgar da gurnanin nakudar da ke fitowa.

Ban ce mata kala ba balle kuma babana da ya zama tamkar mutum mutumi, to wane irin abu ne kuma haka mai nakuda tana tsaye kememe, da gani dai nasan kece kike wannan zirga-zirgar da gurnanin nakudar inma…

Kan ta karasa maganganun nata masu kama da sanbatu sai kawai mika jiyo kukan jariri daga cikin dakin namu.

Ina kallon yanda jiri ya debi baba Lantana ya yi wuji-wuji da ita kafin ya fyadata da kasa, tayi faduwar yan bori wato da mazaunanta, tsoro ya kamani saboda ganin irin faduwar da tayin, sai kawai na ga ta zabura da iyakacin karfinta ta yanka da gudu ta nufi cikin dakin namu. Wato da ma sharri ne abin? Wato ni za a kawowa iya shege? Dama da hadin baki ne tsakáninki da matsiyacin likitan da yace min ba ciki ne da ke, kaba ce? Ni za ki kawowa tsiya? Ni za ki jawa magana? To ai kuwa yanzu za ki gane wautar ki don kuwa kasheki zanyi murus har lahira.

Tana fadin hakan muka jiwo ihun Asabe da sauri Sallau ya fito ya fada cikin dakin; ba zaiki kasheta anan ba baba ba zaki yi mana kisan kai a gida ki jawo mana wata fitina ba, tunda dai har kin kaita gun likita ya ce miki kaba ce ai kin san da komai, lokacin baya ta kawo miki gasassun kaji kina ci, kowa ai yana girban sakamakon abinda yake aikatawa ne.

Da karfi Sallau ya jawo baba Lantana ya fito da ita waje, tana-kicin kwancewa daga gareshi tana kurma ihu da iyakacin karfinta, ka sakeni kawai in hadata ita da shegen dan nata na murkushesu kowa ya huta.

Wannan dai duk kina kokarin jawowa kanki wani abin magana ne kawai in har kika bari makwabta suka jiyoki suka gane abinda kike ciki da ma ki yi maza kin san abinda kike ciki da ita da dan nata kafin gari ya waye magana ta watsu.

Daga cikin gidan Baba Baidu muka jiwo muryar Baba Sumaye tana cewa, kar makwabta su ji na nawa tunda ni naji? Ai ko dan cikin shegen da tayi ta rokarwa ya’yan jama’a sai na baza wannan labarin, barde a gonar wani sunkuru ya rufe naka, don ke kam yayan jama’a kika sawa ido, naki ba kida lokaci balle ki gano abinda suke ciki, wai likita ya ce miki kaba ke gareta?

Ta kwashe da dariya kafin ta ce, saboda ya gane ke din mahaukaciyar uwa ce shi ya sa ya yi miki hakan, kar kumaki ji da wai ba nan unguwar ba ko a wani wuri na ji 1abarin an tsinci mataccen jinjiri zan kai rahotonki don nasan halinki kin kuma furta zaki kashe uwa da da dan kar su jawo miki abin kunya, sai kace in da ana kashewa da ke kin kawo yanzu, ai yanda kika sa su kuka da bakin ciki lokacin da kikayi naki haka kema za á sa ki ki yi abinda kukayi ne ai za a yi muku, shi kuma malam Habu Ubangiji ya yaye mishi abinda ya sameshi, yauwa duk inda naji an tsinci mataccen jinjiri nasan kece zan fada na kangon bola ma da aka gani kwanaki wa ya sani ko ke kika kaishi? Fitinannun mutane masu jawa mutane annoba iri-iri.

<< Halin Rayuwa 33Halin Rayuwa 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.