Baba Sumaye tana rufe baki Baba Lantana ta yi zumbur ta maike da sauri ta sake shigewa cikin dakin namu inda Asabe da dan jaririnta suke tamkar dai ace dama kasake tayi tana sauraron bayanin nata ban san yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina abinda na gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya kuma sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su. Na shiga dakin nayi sallah na hau gado na kwanta cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin ubanku.
Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take ko ita da su wa take yi oho.
Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake ba mu ji komai ba illa iyaka dai na muryarshi yana ce mata to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi, lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don sallar asuba bai sake dawowa gidan ba.
Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana don ba dabi’arshi bace wucewa kasuwa daga masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata, kin ganta ko Baba, kin ganta ko baba kinga halin Asaben ko? A gabanki ta ce min Agogo ne ba?
Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin to an je anzo da Agogo ya zo ya zare mata ido yana tambayarta’ shi kadai ne su sauran me yasa bata ambaci sunansu ba sai shi? Maimakon taja ta tsaya a kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji Nalami ne.
Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi, nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami kuma? Wannan abin mamaki da ban tsoro da yawa suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuhuma da yi mata ciki, ita kuwa wane batan basira ne ya kaita yin hakan?
Tsawon lokaci ina tunanin tsakanin biyun wanne ne dama dama? Agogo dai shi ne mutumin da ya jagoranci abinda Mubarak ya sa aka yiwa Sallau wanta da suke uwa daya, shi kuwa Nalami ba sai na tsaya ina wani dogon bayani a kanshi ba ko da yake dai baba Lantana tayi nufin badani gareshi ta kuma yi mishi tayin Asaben don ta samu warware masalar kudin da suka shiga tsakaninsu to amma tunda hakan bai yiwu ba wane birgewa ko sha’awa wannan mutumin ya baiwa Asabe da har ta yarda da shi har take tuhumarshi da zamowa uban danta? Na yi maza na bar wannan tunanin na shirme tunda gani nake tamkar bai shafeni ba na amsa sallamar da naji ana kwalawa a kofar gidanmu da sauri na fita don ganin masu sallamar, tunda na jiwo muryoyi da yawa alamar ba mutum daya bane.
Ina fita naga an ciccibo babana rabe-rabe wai faduwa yayi a kasuwar timatirin su nan take na kama salati, ina yin kuka, wani daga cikin mutanen dake rike da baban nawa ya dakamin tsawa, kaice ki ba mutanc wuri munafuka kawai duk ba ku kuka jawo mishi ba, ita ce fa wacce kwanaki aka yi tsiyar nan a kanta ran daren da zan daura mata aure da wani aka kamota a dakin wani kato wanda shi babu yanda ba a yi da shi ba ya auretan ya ki amma don hauka da rashin zuciya taje ta kai mishi kanta shi kuwa wanda zai auretan da ya ji labari ya ce to ya fasa.
Wani daga bayan yace, a’a to zai fasa mana da ka auri budurwa fanko ai gara ma ka auri bazawara da ma kasan abinda ka aura, ni da aka bada labarin haihuwar yar tashi ai na dauka ita wannan din ce ta haihu, ashe wata ce kuma daban? Wato shi ‘ya’ yan nashi duk haka suke? Su matan lalacewa ta bin maza, shi kuma namiin kana ganinshi ba sai an yi maka bayani ba, baki a rube ko ina kuma a fuska tabon adda, to amma dai dan gara shi tunda ba zai dauko mishi irin wannan maganar ba, lalacewar ‘ya mace ai babbar musiba ce ko ba komai kuma gashi ya fara dawowa kan hanya tunda yana binshi kasuwa yana kuma taimakonshi ba kadan ba.
Kukan da nake yi bai hana zuciyata tuna min maganganun nasu ba wannan wane irin rashin adalci ake yiwa babana wato su Asabe su Sallau din ma duk ya’ yanshi ne? Ban kai karshe ba na ji wani ma ya kama bayanin ‘ya mace, nifa shi yasa ma ban cika son haihuwarta ba na kuma yi sa’a ‘ya’yana bakwai gaba dayansu maza ne babu mace ko daya.
Wani kuma daga can gefe ya ce kai ba fa duka matan ne haka ba in akayi sa’ar su aka dace da na kirkin dadin al’atmari ne da su saboda su din masu tausayi ne, shi malam Habu har da laifinshi cikin lamarin iyalinshi don kana da hakuri ba dalili bane da zaka zuba ido ka barwa matarka da’ ya’yanka sai yanda tayi da su ai cewa akayi ku kare kawunanku da iyalanku daga shiga wuta to shi ya zuba ido a kan komai ya bar mata tafi karfinshi, yaushe ake yin haka? Haka ne haka ne suka amsa.
Suna barin gidanmu nima na fita don nemana motar da zata daukar min babana zuwa asibit, a kan idona ina ji ina gani nake jin mutane suna bayani an haifi shege yau a gidan malam Habu wanda ake yiwa bayanin sai ya tambaya wane malam Habun? Sai a tsaya bayani malam Habu mai tumaturi, nan na wajen kan kwana baban wannan Maryam din da kwanakin can watannin da suka wuce aka kamota a dakin saurayin da take kwanan gida har kan haka mutumin da zai auretan ya fasa? Sai ace haka haka na tuna dattawan unguwa kuwa fadi suke yi kai malam Habu bai yi sa’ar iyali ba.
Raina ya baci zuciyata tayi zafi hankalina ya tashi, na rasa inda zan tsoma rayuwata in ji dadi, da dai ace nasan abin da zafi àru kenan to da na ja Asabe na fitar da ita daga gidanmu in ya so ko a kan titi ne ta haihu, gaba daya sai masu magana suka mance da Babana ba shi ne uban Asabe da Sallau na asali ba suka kuna mance da cewar bayanin da nice ‘yarshi ta asali yana da ya’ ya Dina in ni ban zamo mutuniyar kirki ba ita ta kirki ce don kuwa in dai biyaiyar aure shi ne kirkin mace to yaya Dija ta kirki ce.
Ina kuka na shigo gida tare da direban motar da na samo don ya tayani daukan babana, yaya Dija na gani a gidan ta zo saboda labarin da ya je mata sai dai kuma wai cacar baki na samu suna yi da baba Lantana, Asabe ai mai imani ce shi yasa ta haifi nata, dan mai rai ke sau nawa kanwarki tana cikin shege kina cire mata? Ko ance miki ban sani ba ne.
Wuceta nayi ko kallonta banyi ba na shiga dakin da babana ke kwance na cewa direban shigo daga nan kan ya shigo ta biyoni ina kuka nace mata babanmu yana kwance kina fada da ita?
Kan tayi min magana baba Lantana ta cafe tana zaton zan kyale ta ne take wani zuwa wai kar ‘ya’ yana su sake shigowa nan gidan to wannan gidan har wani gida ne da za a yiwa mutane doka a kanshi? Ban amsa ba itama yaya Dija ta yi shiru, ai a shirye nake don ni din warki ce dai dai da kugun kowa wanda duk ya shiga lamarina zan shiga nashi in ka gayamin cuta kuma zan gaya maka mutuwa, munafukan banza munafukan wofi duk sai kun ci gidanku a hannuna.
Muna jinta tana tayi muka fitar da babanmu muka tafi asibiti gado aka bamu ni ce kuma na zauna tare da shi a wannan karon ko tayani kwanan da Sallau ke yi ban yarda ya yi ba.
Ina zaune kan kujera gaban gadon babana yake kwance ina kallon babana da halin da yake ciki, tunani kawai nake yi na al’amuran dake ta faruwa da mu daga wannan mu koma wannan, sai ina ganin kamar al’amura sun soma wucewa an fara samun sauki sai kawai wani abin ya sake tasowa a sake fadawa cikin wata mas’alar da zan rinka ganin tamkar tafi wacce aka baro baya tsanani. Ana cikin haka naji motsi a kusa da ni, nayi maza na daga kai don ganin ko waye? Mubarak na gani a tsaye daga gefe kadan kuma babanshi ne Alhaji Muhammadu, cikin tsananin kaduwa da firgita nayi maza na sauka daga kan kujerar da nake zaunen na tsuguna a kasa karo na farko da na ga baban Mubarak bayan faruwaral’amuran da na daina shiga gidanshi.
Tashi maryam tashi ki hau kan kujerar ki ki zauna. Ban iya motsawa ba ban iya tashi na hau kan kujerar ba ban kuma iya buda bakinan a gaisheshi ba, kuka kawai nake yi.
Ubangiji ya bashi lafiya, Ubangiji ya sa kaffara ce, Mubarak ne ya amsa addu’ar da baban nashi ya yi da amin.
Maganar da na ji Mubarak din ya fara yi min ta tabbatar min da cewar bayan yayi addu’ar bai tsaya ba tafiya yayi don haka na mike na zauna a kan kujerar da na bari.
Kina ganin kamar akwai wani dauwamammen abu ne a rayuwa? Duk wadannan abubuwan da kike gani wata rana za su wuce don hakaki rinka yin hakuri. Ya ciro kudi masu yawa ya ajiye a gefen gadon, ki rike wannan a wurinki ni zan tafi baba yana jirana:
Na yi maza na ce mishi bana so dauki kudinka ka tafi da su, bana bukatar komai daga gareka. Ya yi kamar bai ji ba ya juya da nufin tafiya, nayi maza na ce mishi, da ka yardar ka dauká don kar su zamo maka sanadin bacin rai saboda zan iya ba da a kaiwa ma…
Ban san yanda aka yi ba naji ba zan iya karasa abinda na yi niyyar gaya mishin ba, wucewa yayi ya yi tafiyarshi ba tare da amsa min ba, nima na zubawa kudin ido ina kallonsu: lokaci mai tsawo kafin nasa hannu a kansu na daukesu na ada nasu.
Kwananmu uku kafin a ka sallamomu muka dawo gida.
Mutane suka sake tasa babana da gidan mu da ni ma a gaba kai kace nice na haifi dan shegen.
Ina dakina ina zaune cikin damuwa da tunani iri-iri na ji Sallau yana cewa, baba Lantana ai Asabe ta kamanta ruwa ido batan bakatantan zata yi tayi dalilin da dan nata zai rasa madogara kamar….
Da sauri baba Lantana ta wulwulo ashar ta antaka mishi, ya ce to shi kenan baba nayi shiru na kuma ji ni mahaukaci ne to na rokeki ki taimakeni ki daina tunani wajen maganar Asabe da samarinta da danta. Ki samu masu hankali su rinka zuwa miki.
A wannan lokacin wata irin rayuwa na tsunduma yi da ba ma zai yiwu ince zan tsaya ina bada labarinta ba, abinda dai na sani kawai shi ne ina wuni ban kai wani abu bakina ba saboda kwata-kwata yunwa ta rabu da cikina mafi yawancin lokaci ruwan kawai nake sha saboda bushewar makogaro dake yawan damuna.
Rannan an wayi gari da safe wankin kayan babana nake yi saboda ya dan fara samun sauki ya yi amfani da tsabtataccen kayaya dan ji dadi, ina cikin yin wankin ne naji anyi sallama a kofar gidanmu, Sallau baya nan don haka na yi maza na leka tun da nasan babana bai mallaki karfin yin hakan ba.
A hankali nayi leken don ganin mai sallamar a dalilin ban cika son hada ido da yaran unguwar ba, malamina na makarantar islamiyya na hanga malam Yahuza da sauri na karasa fita wajen naje na tsuguna kasa cikin wani irin yanayi na kunya da kuma girmamawa, sannu da zuwa malam.
Haba Maryamu shirun naki ai yayi yawa shiru-shiru shiru da ba zai yi auren ba ai sai ki dawo karatunki, ai ba haka rayuwa take ba komai kika gani yana da lokacinshi shi aure lokaci ne in har lokacin shi bai zo ba babu yanda za a yi a yi shi, watakila mijin naki bai zo ba, ita kuma mace bata aure sai mijinta don haka ki dawo karatu kin gane ko? Nace mishi to malam.
Kar fa kice min to ki zo baki dawo makarantar ba don sau biyu ina turo yara abokan karatunki su zo su kiramin ke ba ki zo ba.
Kamar ince mishi babu wanda ya zo ya kirani sai naga bari in yi mishi shiru kawai. Ai ba a girman da ake wuce yin karatuna addini, shi dan adam yana rayuwa ne a kan neman ilimin sanin nahalicci don haka ki dawo makaranta kin gane? Na sake ce mishi e malam.
Muka yi sallama ya tafi nima na shiga gida, a zuciyata na rinka tunanin ko su waye malam ya turo su kirai oho, ina cikin tunanin hakan sai kuma na watsar na bari saboda na gane sanin ko su waye din ba zai amfanar da ni da komai ba.
Zuwan da malam Yahuza ya yi ya sanya ni na ji wani canji cikin zuciyata saboda irin nasihun da ya yi min, kwadayin karatu ya sake dawowa cikin raina, sai dai kuma yaya zanyi in sake fuskantar yan makarantar bayan duk irin kwaramniyar da na yi ta fama da ita? Da wane idon zan sake kallonsu?
Wannan shi ne abinda ya fi komai tsaya min a rai. Kwana biyu bayan zuwan malam har lokacin ban fara zuwa makarnatar ba sai dai kuma bana jin dadin hakan da nayi, in na yi tunanin menene ya dame ni wanda ya sa zuciyata take yi min nauyi? Sai in tuna malam Yahuza ya tako har gidanmu ya nemi in koma makaranta in yi karatu abin yi hakan ba, abinda ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba yin hakan rashin girmamawa ne ga na gaba musamman malaminka.
Rannan dai na daure na tafi gabana kuwa sai faman bugawa yake yi, kirjina yana ta faman harbawa da sauri-sauri, a tsarge kawai nake zaune a ajn motsi mai dan karfi in akayi sai inji na kara takura in yi kamar ni ake nunawa ko ake bada labari na.