Ana cikin haka watan azumin ramadan ya iso sayaiya sosai Mansur ya yi min, ina zaune a dakina ina buda baki mun kai azumi na biyu ina jin baba Lantana tana cewa babana wai ita din ai rabon wahala ne ya sa ta aurenshi in banda haka ai shima ya san irin zaurawan da tayi, cikin zuciyata na ce o oh kowa da irin yanda babu take zuwa mishi, wata ta kara mishi natsuwa wani kuma ta yi sanadin wargajcwarshi, wata mai daraja irin’ na azumi bai sa ta dan rusunawa al’amuranta ba.
Isiyaku ya yi sallama a kofar daki ya shigo, Anti ina wuni? An sha ruwa lafiya? Na amsa gaisuwar tashi ina mai kallonshi. Ya yi fes da shi ya yi kyau kamar in tambayeshi ka samu wani abin yi ne Isiyaku, sai na yi maza na fasa a dalilin ba wani shiri muke yi ba a yanzu saboda gaba daya al’amuranshi na Mubarak ne.
Ya karkata ya zaro envelop daga aljihun shi ya ajiye a gefena, wai gashi in kawo miki. Da sauri na ce mishi, Isiyaku ashe ban ce maka kar ka sake karbo wani abu daga wurin mutumin nan ka kawo min ba?
To dauki maza-naza ka tafi mishi da shi ka kuma gaya nishi inji ni na ce ya fita hanyata ya daina shiga harkokina in bai sani ba ko bai gane ba to bari ni da kaina in gaya mishi na tsaneshi, na tsani al’amuranshi, na kuma tsani duk wani abinda ya shafe shi, in ya kuskura ya sake aikoka da wani abu wurina to zan karbi abin in aikawa matarshi don tasan yanda zatayi da shi, ya daina kula al’amarina.
Wani irin lalataccen kallo Isiyaku ya yi min da ya yi dalilin da nan take na warware hannu na sheka mishi mari mai kyau a kumatunshi har sau biyu, ina wasa da kai ne da zaka yi min irin wannan kallon? Bai ce min komai ba sa hannu ya yi ya dauki envelop in ya sa kai ya fita ya bar gidan, ya barni ina huci da tunanin haka zan rinka yi mishi duk lokacin da ya kawo min wani sako tunda nace mishi ya daina yaki.
Washegari mun taso daga wurin tafsir nufina in tafe gidan yaya Dija don in yi mata barka da shiga ramadan mai albarka sai kawai naga Mubarak ya yi fakin din motarshi kusa da hanyar da muke wucewa bai ji tsoron cincirindon matan da suke wucewa su na hangenshi ba ko don kar su gayawa matarshi.
Yana ganina zan wuce ya yi maza ya fito daga cikin motar tashi ya tsareni, magana yake yi cikin natsuwa ta yanda na nesa ba zai gane bakar magana yake yi ba.
Malamin naki ne ya koya miki rashin kunya da rashin mutuncin da kike yiwa mutane ko? Na daggo ido na kalleshi saboda ambaton malamina da ya yi.
Eh ai kafin kullewarku ke da shi rashin kunyarki ba ta kai haka ba, ki mari Isiyaku, gansamemen saurayi kamar Isiyaku ki mareshi dame kika girmeshi? Kina nufin in banda shi din yaro ne mai mutunci za a yi hakan’? Kina mace ki mari namiji kina nufin in ina da iko da ke ba zan yi miki hukunci mai tsanani na ladabtarwa ba? Sakarya kawai sokuwa, shashasha wacce rashin mafadi ya hanata sanin abinda ya dace da ita.
Wani lalataccen kallo ya yi min gami da jan mummunan tsaki kafin ya wuce ya tafi ya barni, ance miki matata irinki ce.
Haushi da takaicin kaina suka hadu suka kamani kan yanda akayi ya gama gaya min bakaken maganganun shi ya wuce ya tafi ba tare da na iya ce mishi koami ba, babu kuma abinda yafi komai kona min rai irin cewar da ya yi wai matarshi ba irina ba ce, to wacce iri ce? Me yake nufi da wannan maganar ta shi? Babu irin alkawarin da ban yiwa kaina ba a kan ba zan sake barinshi ya gayamin magana in kyaleshi ba amma gashi na kasa gaya mishi komai.
Baba Lantana a wanann lokacin tsula tsiyarta take yi irin yanda ta ga dama, da yake Asabe mai imani ce da tayi cikinta sai ta reni abinta ta haifi abinta ba ta je ta zubar da shi ba balle ta je tana dauka wani zunubin na kisan kai, gashi kuma a sanadin hakan ai ta yi aurenta tanan an goye da danta tukarballa ta bar wasu a titi suna ta tanbele basu ga tsuntsu basu ga tarko.
Da abin nata ya tsaya a kaina ni kadai da sauki, yanzu yanzun nan ne zata sa shi a gaba ta sulleshi sai dai in ba zan leka kofar gida ba ko ka ji tana cewa, to ni in banda na lissafa naga duk tsiyarka kai da ya’yanka zan iya cinye wannan daki da nake ciki tunda dai su din mata ne ai da tuni na dade da rabuwa da kai in yi tafiyata yaushe zan iya zaman jinya, to ba zan tafi ba ne in bar kasona a ce rashin hakuri, don haka nake zaune daram ina jira sai naga kwal uwar daka.
Wadannan kalaman da na ji baba Lantanan tana furtawa wadanda na tabatar ba ta san na ji ta ba su ne suka yi dalilin da na yi sammakon zuwa gidan yaya Dija na bata labari.
Shiru tayi tana kallona cikin wani irin yanayi, Jimawa can sai naji ta ce, ni tsorona ma kar ta karasa mana shi ba mu sani ba tunda take maganar gadon dan wannan gidan wato ita idonta yana kanshi ta sake nisawa kafm ta ce, nifa da baba zai yarda ma da wani auren kawai ya kara.
Da sauri na zaro ido ina kallonte cikin razana, aure kuma? Shi baba ya ce miki zai iyayin mata biyu ne? Hankalinta a kwance ta ce min to ba shi kenan ba in ba zai iya biyun mai zama ta zauna mai tafiya ta tafi, amma wannan fitina har ina? Da akwai wata yarinyar bazawara nan kusa da ma takaba ta gama tana kuma da yayanta biyu kinga in aka yi sa’a ma sai ya kara haihuwa ya ma huta da sharrin da take kulla mishi na baya iya tsinana mata komai, baba ai ba tsoho bane in ma bakan ne bakin cikin ta ne ya maidashi hakan, na dai ja bakina nayi shiru ina jinta tana maganganunta bance mata komai ba.
Rannan ranar wata juma’a da yamma bayan saukowa daga sallar Juma’a naji Babana ya karbi wasu baki a zaurenshi wadanda na tabbatar iyayen Mubarak ne wato Alhaji Muhammadu da amininshi, ban san takamaiman abinda ya kawo sun ba na dai gane su din ne kawai ta dalilin ambaton sunansu da na ji baban nawa ya yi.
Nayi maza na mike na shiga gida na basu wuri, can cikin zuciyata dai ina tunanin wanene kuma Alhaji Muhammadu? A sanina a unguwarmu Baban Mubarak ake kira haka to amma shi me zai kawoshi gidan mu? Yana dai zuwa duba babana daga baya bayan nan tare da Mubarak to amma wannan ai zai iya zama makwabtaka ne ko kuma kwadayin alherin da ake samu wurin gaida mara lafiya.
Ina ganin sanda babana ya shigo gida rike da tabarmarshi a hannu bai ma baro ta inje in hade ba, bai ce min komai ba nima kuma ban tambayeshi ba don dama can babu irin wannan mu’amalar a tsakaninmu, don haka sai kawai na ci gaba da harkokina.
Da daddare ina zaune dakina takarduna na makaranta nake dubawa lokacin da na ji sallama a cikin zauren gidanmu gabana ya yanke ya fadi saboda jin da nayi tamkar muryar Mubarak ce da sauri na mike na fito.
Uhh lalle al’amarin babba ne har cikin zaure kuma yanzu kake shigo mana? Ta yi kwafa ta ce ko baka yi haka ba ai an kuma hade.
Tsayuwar da Baba Lantana ta yi a wurin wai sai ta ji abinda ya kawo shi ko zai fadi ya hanani tafiya in barshi don ba zan bata mishi rai a gabanta ba, wucewa na yi nace mishi muje daga waje mana, don haka muka fito.
Tun kafin in tambayeshi abinda ya kawo shi gidanmu ta tsareni dai danuwanshi wai ni me baba yake nufi da ni ne? Tambayar tashi ta sanyani yi mishi tambayar wane baba? Da saurinshi cikin wani irin yanayi ya ce min, babanki mana. Gabana ya yi mummunan faduwa jin yanda ya ambaci baban nawa, cikin zuciyata na ce, lalle mutumin nan yau yana jin rashin mutunci amma babu laifi, na kawar da tunanin nawa na mai da hankalina wajen sauraron abinda zai gaya min kan Baban nawa wanda na tabbatar ba mai dadi bane.
Na rasa me nayi mishi, na rasa wane irin laifi na yi mishi wanda ya wuce ga bai yafewa, tun aurena bai wuce wata uku ba na turo aminin babana ya zo wurinshi kan maganar ni da ke bai saurari maganar ba na koma na sake rokon babana ya zo da kanshi ya yi mishi magana don ya fi ganin abin da muhimmanci ya zo ya sameshi bai ji kunyar idonshi ba ya ce mishi ba zai bani ke ba yau ya sake dawowa saboda na sake komawa gabanshi na rokeshi ya dawo ya sake rokonshi to ya sake dawowa shi kuma ya sake cewa matukar shi ne zai daura miki aure da kanshi to ba zai daura auren da ni ba, saboda na ci mutuncunshi na keta mishi haddin yarshi nayi sanadin da shi dake kuna wulakanta shi ne na ce bari in zo in ji me na yi? Me nayi miki na haka ni na taba ki ne? Ke baki gaya mishi babu komai tsakanina da ke ba sharri kawai matar shi ta kulla mana.
Cikin natsuwa na tambaye shi to in baka yi komai ba sai me? Dole ne sai ya baka aurena da za a je ana ta yi mishi zirga-zirga a gida? Sauran iyaye da suka yi hukunci a kan ya’yansu haka aka yi musu? Naga shima shi ya haifeni ko kuwa don an ganshi yana saida turmatir sai a ce bai isa ya zartar da hukunci a kan tashi ‘yar ya zaunu ba sai an canza mishi?
Bai nuna bacin rai da jin maganar tawa ba sai ya ce min, iyaye suna zartar da hukunci mai tsanani a kan ya’yansu, Maryam yin hakan ba laifi bane amma kuma da yawansu sukan ciza ne sai kuma su hura a mafi yawancin lokaci ma su kan taya ya’ya son abinda sukc so matukar sun gane babu cutuwa a cikin lamarin, me yasa shi ba zai yi hakan ab? Me ya sa ba zai tayaki son abinda kike so ba ya baki mijin da kika rayu kina so?
Na ce, ai abinda nake son yake taya ni shi din ya san ban taba sonka ba ya kuma san duk wani abinda ya gudana tsakanina da kai ya faru ne a dalilin kuruciya da kurna kuskure.
To babu laifi, ya fadi hakan cikin wani yanayi don haka nayi maza na juya da nufin shiga gida sai naji yayi maza ya ce min to, dan dakata mana ki ji abinda zan gaya miki.
Na dan ja na tsaya ba tare dan na waiwaya na kalleshi ba, sai naji ya ce min, to amma ai shi Baba yana da labarin rabo yana kashe mutane ko?
Gabana ya sake yankewa ya fadi jin da na yi ya ambaci mutuwà a tsorace kwarai na tarabaye shi, me kake nufi da wannan maganar?
A natse ya ce min, abinda nake nufi kenan ki buda baki ki yi mishi magana ki gaya mishi gaskiya babu komai tsakanina da ke ban taba mishi ke ba, na ce to in ba haka ba fa?
Ya ce shi kenan sai ki yi ta zama sau goma in za a kawo miki kaya sau goman kuma za a zo a karbe.
Gabana ya sake faduwa, kar dai a ce Mubarak ne ya yi dalilin fasa aurena da Halliru? Kar dai a ce Mubarak ne dodon da Halliru ke gayawa Yakumbo Halima wanda ita ta dauka dodon dodanni ne ko wani aljani.
Rasa abinda zan cewa Mubarak nayi in dan ji saukin abinda ke cin zuciyata don haka sai na ce mishi, a sanina dai baba na shi ne mahaifina yana da iko a kaina kamar yanda kowane uba yake iko da danshi saboda wanda ya yi sanadin zuwana duniyar nan babu wanda ya taya shi don haka in har rabon wani ya zama sanadinshi to na rantse har abada ba zan auri wannan din ba sai dai ni ma rabon nashi ya sa yanda zai yi da ni kuma karka sake kulani.
Ina fadin haka na yi maza na shige cikin gidanmu na barshi a nan wurin yana tsaye. Ko badan ban ji haushin hana Mubarak aurena da babana yayi ba, saboda tuni ya riga ya fita min a rai bana kallonshi inji zuciyata ta rayamin abubuwan da ta saba raya mina game da shi a baya sai dai in ganshi in ji faduwar gaba ko in ganshi in ji haushi da takaicin shi sun kamani.
A wannan lokacin ne kuma baba Lantana ta fito da wani irin salo a gidanmu duk wani wanda ya zo wurinta in suna hira bata kai karshen hirar sai ka ita tana gaya mishi cewar ita wannan zama da take yi ma ai ya kusa ya zama haramtaccen zarna, abokin hirar ta ta ya ce, haramtaccen zama kuma, Lantana sai ta ce eh to haramtacce mana tunda abinda ake yiwa zaman yayi karanci ace miji kana kallonshi yana kallonka, shimfidarku daya amma sai ya shafe kwana da kwanaki babu komai, babu wani motsi a can babu a tukunya ma babu ana yin zaman haka ne ai ni yanzu kiris nake jira don ma dai kawai kar ka tafi ne ya zama ka tafi ka bar ladanka.
Haba Lantana haba Lantana yanzu ke a yanda kike din nan sai kin yi korafi kan irin wadannan al’amuran, mutumin da ko lafiya bata isheshi ba, tace a’a ni ban wuce ba sannan tun a can baya ma da yake da lafiyar me aka yi ne da za a ce yanzu in hakan ta faru kar in yi magana?