Skip to content
Part 38 of 38 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Yaya Dija na baiwa labarin kalaman nata ita ce ta faiyacemin abinda take nufi, kasar kullum sai ta tasa babana a gaba tana yi mishi hirar gidan mijinta na baya, haushi da takaici ya yi ta kama ni na yanda sau daya babana ya kasa cewa ya sauwake mata nashi auren taje ta koma gidan mijin nata na bayan, yawan fadan da take sashi a gaba da yi  kullum ya sani bashi shawarar dawo da kwana dakin Sallau don ya rinka samun wadataccen bacci saboda mas’alar hawan jininshi, kamar bai ji shawarar tawa ba daga baya kuma sai naga ya koma dakin.

*****

Wata goma sha daya cif nayi ina zuwa makarantar koyon sana’a ta Markas kafin aka yayemu saboda yarda da aka yi cewar mun iya mu goma sha biyar aka yiwa yayen aka kuma yi mana kyautar keken dinki saboda gamsuwar da akayi da kwarewarmu, ko kafin nan kuwa nikam na dan dau lokaci ina taba dinkina a gida a keken da yaya Dija ta saya min don haka dana samu wannan kyautar sai kekunana suka zama guda biyu.

Naso kwarai in koma Markas in sake shiga wani ajin daga cikin azuzuwan sana’o’in dake wurin in kara koyon wata sana’ar haikan bai yiwu ba saboda karatun da nake yi a makarantar asidini mai zurfi, karatu ne dake bukatar sadaukarwa mai yawa banda haka kuma ga lalurar babana ta yawan rashin lafiya don haka sai na hakura.

Tunda aka yaye mu a wurin koyon dinki na soma yin dinkin sosai a gida sai mas’alolin da suka danganci babu suka yi matukar yi min sauki bana rasa na sabulun wanka ko wanki bana rasa ta yin break a makaranta wani lokaci ma nakan raka babana asibiti ne ba tare da na shedawa yaya D1ja ba balle inje ina jiran abinda zata bamu wannan shi ne abinda yafi komai faranta min rai na.

Shekaru uku ne yau tun bayan faruwar abinda ya faru tsakanina da Mubarak cikin shekarun nan kuwa nayi abubuwa masu yawa wanda kasancewata a yau ni din kwararriyar tela tace gani a fada a kuma kwaikwaya, ni din kuma gwanar girki ce saboda na koma makarantar Markas na sake shiga ajin koyon girki nau’o’inshi kuma malamaina na Markas irinsu malama Hindu da Basma wadanda mukayi matukar shakuwa a dalilin kulawar da suka nuna a kaina sunyi min taimako mai karfi wanda a dalilinshi na samu shiga exam center dake kusa da Markas din na samu rubuta jarrabawar dana samu mallakar takardar shedar gama karatun secondary indana samu credit guda hudu da pass biyu saura f9.

A bangaren da nake ganin kamar na yi nasara kenan, a daya bangaren kuwa Ina nan kamar yanda dama nake aure ya gagara babu kuma yadda banyi ba in yi shi hakan bai yiwi ba, zan iya cewa garama da, da yanzu a lokacin da kuka sanni samarin sukan dan zo auren ne basa tsayawa a yi saboda wasu dalilai to a yanzu babu bani da wani wanda zan ce wannan saurayina ne.

Mutanen unguwarmu tun suna nunani suna yin bayani a kaina zuciyata tana lissafi ta karyata maganar ta su har na hakura na fita harkarsu ta barsu su fadi duk abinda suka ga dama.

Tun ban kama maganar mutane irin su Yakumbo Halima da suke fadin cikin biyu dai akwai abu daya ko dai anyi min sihiri ne ko kuma ma aljani ne ya aureni ya hanani yin aure har na soma shiga rudani ina tambayar kaina to menene mas’alata, tuni dai na daina yin kawaye don na gaji da aurar da su da akeyi ana barina a wannan lokacin in har ina da wata kawa to kekena ne da kuma dinkina sai ko kwalliyar da nakeyi don kuwa ba sai an gaya min ni da kaina na san mu’amalar da nayi da malamaina na Markas irinsu Malama Hindu da Basma ya koya mina abubuwa iri-iri da suka damganci mace kwalliya, kamewa, mutunta kai, iyaka dai har yanzu hakan baisa na samu mijin da ya tsaya ya aureni ba su ma kamar yaya Dija sukan ce min wai lokacin auren nawa ne bai zo ba sai in yi murmushi kawai in yi shiru cikin zuciyata kuwa tambayar kaina nake yi ko yaushe ne lokacin oho?

Saboda a wannan lokacin har na gaji na soma tambayar kaina to koma dai ni din ina cikin matan nan ne da ba a halitta musu mazan auren ba?

Tun ina kin yarda in yi amfani da abubuwan da Yakumbo Halima take bani in yi amfani da su na farin jini da wai maganin sihiri da kullum take zargin wai Mubarak ne ya yi min in yi murmushi in ce mata Mubarka bai ma yarda da irin wadannan abubuwan ba Yakumbo shi fa dan boko ne ma digiri biyu ne da shi ya ma sake komawa karatunshi don neman na yau, yaushe zai zauna yana irin wadanann abubuwan? Sai ta ja tsaki bayan ta gallamin uban harara ta ce, ai sai ki yi dama in kana son mutum ai baka iya ganin laifnishi, ince mata ba haka bane Yakumbo ai ni yanzu bana son Mubarak abin da na sani ne kawai nake gaya miki, ta ce to baki san komai ba ince mata to na yarda.

A wannan lokacin ta kaima ina zama in yi kuka in share hawayena tun ina yi ni kadai har ta kaima ina yi a gaban yaya Dija, menene mas’alar da ta hanani yin aure? Bani da fasali ne? Ta girgiza kai uh uh kina da shi daidai gwargwado, bani da tsabta ne? Ta sake cewa uh h kina da ita kin kuma iya kwalliya kina kuma yi iina da kamun kai da natsuwa gashi kin yi karatunki kina ma kai tunda har yanzu kina yi to amma lokacin auren bai zo ba, Maryam mijin naki ne baizo ba don haka bani da yanda zai yi sai dai in yi ta baki hakuri in kuma kara rokon ki ki kara tsare mutuncinki komai zai wuce har kiga kina bayar da labarin al’amarin, ni dai nasan duk waenda ya yi dace da samun babbar mata mai aikairori iri-iri, in yi murmushi ince yaya Dija kenan, kenan kina dai gaya min hakan ne kawai don in ji sanyi a raina.

Ita dakanta yaya Dija duk da irin wadannan kalaman sanyaya zuciyar da take yi min ta sha gaya min cewar rashin aurena ya katse mata baccinta ya gusar mata da nishadinta ya sanyata ta ji zuciyarta ta kutata don haka mu yi ta istigfari muna rokon gafarar Ubangiji, in ce mata to wataran kuma in dan zolayeta ince mata ba kince zai wuce ba? Ta yi maza ta ce, kamar yanzu kuwa in har muna raye to zamu sheda wucewarshi.

Yaya Dija ya ce a wurina da ta zame min uwa ita nake kallo a matsyain uwa saboda duk abinda take yi min yi take yi da iyakacin iyawarta tana da ya’ya maza da mata amma bata hada su da ni ba, na sha jin matan gidansu suna cewa ai ita wai kanwarta ta fiye mata kowa tunda ita ita kadai ke gareta ba kuma zata sake ‘yar uwa irinta ba tunda uwar da zata haifar mata wata bata nan ba wadannan kalaman ne suka sa zuciyata yarda da yaya Dija bata hadani da kowa ba a aiyukanta ne a kaina shi yasa nima bana wasa da ita duk abinda tace min to káwai nake cewa bana yi mata musu.

Ina zaune a dakin ina yankan kayan da nake nufin dinkawa a wannan satin wanda na ankon wani biki da za a yi ne a unguwarsu ya Dija aka kawomin ina yankan cikin natsuwa da kwanciyar hankali saboda daga ni har dakin nawa tsab muke sai kanshi muke yi, bana tunanin komai cikin raina aiki na kawai nake yi sanda Asabe tayi sallama ta shigo cikin dakin, ashe kina ciki? Nace eh Asabe kin zo ne? Ta ce min, ina kwana? Ina amsawa ina matukar jin tausayinta gaba daya ta canza ko rigar nono a wannan lokacin na ganiyar kuruciya bata iya sakawa, tsabtar ta duk ta kare kullum ka ganta gara jiya da yau ba ita ba ba ‘ya’yanta kullum yanzu sai tazo gida kullum kuma da mas’alar da zaka ji tana fadi baba Lantana tayi tayi ta daina shiga dakina tana gaisheni ta ki dainawa, ban sani ba ta canza hali ne ko kuma sule biyun da nake baiwa ya’yanta in zasu tafi ne ya hanata daina wa oho?

A wannan lokacin wanda bai yiwa Asabe sani na hakika ba ba zai ganta ya ganerta ba ga karni da take yawo a ciki.

Kin fito daga dakin kanwar uwar taki ne? Ban ji abinda tace ba naci gaba da aikina ina istigfari kan yawan damuwar da nake yi a kan rashin aurena, na yi imani da in yi aure irin wanda Asabe tayi gara ma ina zaune a gida gaban iyayena ckin haiyacina da rufin asirina, tunda ba cewa akayi in ba a yi auren ba ba za a samu rahama ba sai dai in ba a yi aikin neman rahamar ba, ba kuma raina auren Asaben nayi ba yasa na fadi haka tunda na san darajar aure yawa ne da shi ko banyi shi ba kuma na karantashi a ganewa kawai a yanda ka’idar auren yake da bayanin shi da akayi a tsari irin wanda auren Asabe ka tafiya zai yi wuya kwarai in har ana samun ladan da ake nema din kullum a cikin korafi ake a zagi miji a zagi kishiya a gaya mata irnin tsiyar da zataje ta yiwa mijin, ni kuwa ina zaune gaban iyayena cikin rufin asiri ina addinina daidai gwargwado ina neman ilimi, ina sana’ata ina kyautatawa mahaifina gwargwadon iyawa ta, a wannan lokacin banda sutura da hidimominshi har rumfa nayi mishi sabuwa ciki da falo, kayanshi suna can ciki shi da Sallau suna wuri daya, Sallau kuma yana iyakacin kokarinshi kullum babana yana yi min addu’a yana samin albarka.

Na karaa kallon al’amarin Asabe da aurenta wanda da ni aka so a tura cikin wannan wahalar Ubangiji ya tsarcni, kullum a cikin tashin hankali da miji ake kishiya kuma ta kamata tayi mata dukan tsiya ta kaima baba Lantana da kanta tayi damara taje har gidan Nalami wai zata ramawa Asabe dukan da matarshi ke yi mata ban san yadda akai ba sai naga ta dawo kaca-kaca, da kamar akwai rayuIwar addini a gidan nasu to da komai ma da sauki to babu.

Daga tsakar gida na soma jiwo wata magana da ta katsemin maganar zucin da nake yi saboda an fara daga murya ana yinta sama-sama alamar rayuka sun fara hassala.

To ba kya cewa ya sakeki, ke wacce irin sakarya ce yaya za a ce miji ne zai auna maka hatsi abincin da ba zai isheka ba babu kudin cefane babu komai sai abinda kishiya ta baka, sannan in abincin bai isa ba sai ace kai ne ka rasa, wannan wane inn zalinci ne, sannan in dare yayi ya zo ya fada miki da yunwar da komai ba dama ki ki yarda da shi, ke ko irin ‘yar tirjiya da yangar nan da mata ke yi a rarashesu a yi musu abinda suke so baki iya ba.

Ai rufeni da duka yake yi yana ganin alamar zan yi mishi tawaye sai kawai ya tashi ya zauna ya yi ta jigbata da duka wai ladan hatsinshi da na wuni ina ci, Baba Lantana tayi shiru kamar yanda Asaben ma ta tayata yin shiru, jimawa can na ji ta ja wani mummunan tsaki da bai da dadin ji kafin daga baya ta bishi da fadin, kai Nalami dai tsinane ne.

Shi ne nace to ko zance ya sake nin ne kawai? Da sauri ta ce ya sakeki mana tun yaushe nake gaya miki hakan? Ta dan rage murya kadan ta ce, to amma fa ba zai yarda in bar mishi wannan yaron a can ba ya ce wai zaman a ya ke yi na barin gidan shima zai bari wannan dai ya yarda nashi ne tunda yana kama da ya’yanshi amma shi wannan ai bai ga ta inda ya daukoshi ba shi ne nace ko zan kawo miki shi ne kawai in bar mishi wannan din wahalar da nake sha tayi min yawa kajin mafa da yake bani figarsu yana bani sisi-sisi ina samun na sabulu yanzu ta hanashi bani ko kwabo wai…

Ni da nake kashe da kunne in ji abinda baba Lantana zata fadi kan kawo mata dan da Asabe ta ce za ta yi sai naji ta hassala ta daka mata tsawa, ke barni haka da wannan mugun labari naki sakarya kawai, shashasha sauna mara zuciya ace mutum bai da wani aici sai na bayar da mugun labari? Ki dauko yaro ki kawo min ya zama duk tattakar da ya yi miki a banza kenan ko me? Wannan yaro ai dole ne ya girma a gidanshi ladan sukurkutaki da ya yi ya maida ke wata ya mutsattsiyar tsohuwa, tsinannan mutum kawai.

Na ce oh oh ta kacame tsakanin siriki da sirika, ina zaune kan kekena ina dinkin kayan dana gama yankawa zuciyata tana tunaina al’amarina irin kokarin da baba Lantana tayi na ganin ta sa babana ya baiwa. Alhaji Nalami aurena duk da tafi kowa saninshi da duk wani al’amarinshi tunda tun a lokacin ta sha gaya min cewar in dai matar Nalami tana nan a yadda ta santa ai zata yi mata magani na to gashi abin baiyo kaina ba sai ya fada a kan yarta nan take na tuna da karin maganar hausawa da ke cewa wai, mugunta fitsarin fako, in kayi sai ya dawo maka kanka.

Kwalliya mai kyau nayi a ranar da na yi nufin kaiwa masu kayan kayansu, doguwar riga na Sanya har kasa ta farar atamfa da aka yiwa ratsi da kananan filawowi koraye da bulu, saman rigar na yi shi a matse yayin da na yiwa tsakiyar yankan umbrella ya sauka har Kasa, dankwalin yadin’ atamfar ne a kaina na yi dauri mai kyau sosai na sanya yan kunne kanana na yafa farin gyale madaidaici a-kafadata yayin da na kawata hannayena da adon awarwarai, agogo da zobuna biyu na zinari daya kuwa na azurta da aka yiwa kira mai kyau na shuri takalmana silifas masu igiya a baya yan Italy da suka kara kawatamin kwaliyar tawa, nasa garkamemen kwado na kulle kofar dakina a dalilin gajiyar da na yi da biyan mutane atamfofinsu da suke bata don haka nama canza kofar dakin gaba dayanta.

Na baro gida rike da ledar kayan dinki da kuma pos a hannuna bayan na gayawa babana inda zani, yar tafiyar da nayi ba wata mai yawa bace na ja na tsaya don tarar mashin din da zan hau.

Wai ke me yasa ba kya įin magana ne? Sau nawa nake gaya miki in zaki fita ki daina amfani da turare ki kuma daina hawa mashin bana so.

Ban kalle shi ba balle in bashi amsa iyaka dai nasan nayi mamakin ji ko ganinshi a wannan lokacin tunda nasan ya tafi Legos ban kuma san da dawowar tashi ba.

Amma shi Baba tsareki da ya yi a gida kike ta wannan zaman a gabanshi yana ganin kamar ya yi mishi daidai? Shi bai san kin kai kowane irin munzali bane, bai san kina da sha’awa ba? Ke ba za ki gaya mishi kina da mas’ala ba? A muku muku sanyin nan kin fito za ki je ki kai kayan da kika dinkawa wasu in kina gidan aurenki mijinki zai yarda da haka? Gaskiya na gaji da ganinki a haka yanzu fa Rumasa’u ya’ yanta biyu ne.

Maganar ta daki zuciyata a hankali na tunawa kaina da kullum muka gamu da shi bama rabúwa sai ya san yanda yayi ya sokamin bakar maganar da ta tsaya mina raina.

<< Halin Rayuwa 37

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×