To wai ni ina abinda ya dameka da ni ne? Kaga ni na damu da kai e? Kaga ina. daga ido ina kallcka ne balle in san abinda kake ciki? Ina dalilin da kake nema ka maida mahaifina abokin wasanka, kullum ka ganni sai ka san abinda ka fada a kanshi.
Ban maidashi abokin wasa ba Mero amma gaskiya zan gaya miki yana bata min rai don me zai hanani ke? Don…
Na yi maza na katseshi, in ya hanaka ni sai ka rinka gaya mishi magana a kan ido na wane hurumi ke gareka na yin hakan? Nace bana sonka nace ka fita harkata nace in akwai wani mutumin da zance na tsana a yau to kai ne don me ba za ka yi zuciya ka fi ta hanyata ba?
Ranshi ya yi matukar baci da kalarman da nayi mishin, wani irin kallo ya yi min irin wanda shi kadai ya san abinda yake nufi da kallon, kina ganin kamar ba za a iya fita harkar taki bane? Kina ganin kamar in an fita harkar taki wani abu zai faru ne da kike wannan cika bakin? To ni don na fita harkar ki ma menene Maryamu? Ai ni ina da mace a gida har da ya’ya, kece kike zaune ke kadai kece kike rayuwa cikin kewa da kadaici, duk sanyin da ya taso ya kare a kanki kina zaune kan kujerar dinki, ni ai da aurena sannan karya kikeyi kice bakya sona in bakya sona me ya hanaki yin aure? Fitar da wani ki aura mana ki zauna kema a dakinki ki dandani dadi da zumar dake cikin auren sakarya kawai sokuwa shashsha wacce babu halin a batawa mutum rai ya gaya mata ta tausaya mishi, sai ta ce zata bishi da bakar magana, sau dubu nawa yake so in turo mishi mutane kafin ya yarda ya ba ni ke? Me nayi mishi a rayuwa i banda rashin adalci.
Sauri nayi na tari mashin babur na dale kai muka tafi don kar bakin ciki da dacin da nake ji a zuciyata ya sa in fara yin kuka a gabanshi.
Zagin da ba a taba yi min ba yi min, yayi min gorin aure da ‘ya’ya da… na kasa karasa bayanin nawa na shiga yin kuka sosai da sosai, tana ta bani hakuri, jimawa can kuma sai ta nisa ta ce, nima dai abin yana damuna ina mamakin yanda baba ya ja ya tsaya ya ki baiwa Mubarak aurenki bayan nima nayi iyakacin tunanina ban gano laifin da ya yi mishi ba to inma ya yi a yafe mishi mana, Umma ma fa kwanaki tazo gidan nan maganar kuma ce ta kawo ta na kuma san ba dadi ne ya sa ta yin hakan ba, to ya bashi ke din mana kawai a huta, zan sake zuwa wajen baba in sake rokonshi inji..
Kan ta karasa na yi mata wata irin rantsuwa mai karfi kafin na ce mata, ba zan taba aurenshi ba har abada ba zan taba aurenshi ba bana sonshi bana son shi ko da sunanshi ne a kusa da ni da in aureshi gara ma in yi ta za…
Ta dakamin tsawa na kame bakina na bar maganar na koma yin kuka, tun ina yi ni kadai har itama ta shiga tayani muka yi tayi sai da muka gaji muka yi shiru.
Mubarak ya saba zagina ko tsareni ya gaya min bakaken maganganu iya son ranshi a duk lokacin da ya turo maganar aurena wajen babana ya ce ba zai bashi ni din ba, to ni yake tsarewa ya gaya min duk wani abinda yake son fada, in yi bacin ran in hakura amma bai taba gayamin maganar da ta daki zuciyata ta sani bakin cki na yi kuka mai tsanani irin wannan karon ba.
Na gaji, na gaji, na gaji da irin wulakanci da cin zarafin da yake yi min a kan aurena don kawai ya ga ba ni da auren, da ina karkashin inuwar aure ai shima da bai isa ya yi min irin wadannan abubuwan da yake yi min ba don haka ya zame min dole in tsaya in yi duk wani abin da zanyi don ganin na yi auren saboda in huta da wannan wulakancin da kuma cin mutuncin kan haka yasa washegari da sassafe na yi shiri na tafi gidan Yakumbo Halima wacce ta dade tana kirana inzo muje wurin malaminta da take ta faman bani labari.
Ina shiga gidan ta fara murmushi, ‘yar halal kin ki ambato yanzun nan nake maganarki a zuciyata. Na tayata murmushin kafin na tsuguna na soma gashcta tana amsawa tana kallona cikin wani irin yanayi dake baiyanar da jin dadinta.
Kai wannan yarinya da iya kwalliya kike wannan kuma wane irin dinki ne? Mu ganshi.
Na numa mata ta gansi sosai, to me sunanshi? Na gyara na koma na zauna cikin natsuwa, kwalliya tafa ke kadai take burgewa.
Ta yi maza ta ce wane mutum ai duk wanda ya kalleki ya san ke din gwanar kwalliya ce Mero ai rashi aurenki ba yana nufin ke din kina da wani aibu a tare da ke ba ne a’a lalura ce dake wani aljani ke gareki wanda yake biye da ke bana baki labarin abinda wannan maiamin ya gaya min a kanki ba, ai nace miki ki zo muje wurinshi don ya ce min akwai abinda zai yi ya rabaki da shi kika ki zuwa.
Na ce to ai gani na zo yau Yakumbo zuwa nayi don ki kaini inda duk za ki kaini na gaji, na gaji da wulakancin da Mubarak yake yi min, na kwashe
bayani duka na yi mata.
Maimakon yau ma ta nanata maganarta da kullum take fadi cewar shi ne ya yi min sihirin da na kasa yin aure sai naga ta yi murmushi kafin ta ee, ja’ira, shagwaba da gata ne suka sashi yin abubuwan da yake yi su ma iyayen na shi ai sun yi nadamar hanashi aurenki da suka yi yanzu tunda kwanaki ai ance korar matar tashi ya yi ya ce a barshi kawai ya yi zamashi shi kadai tunda dai suna kallo an hanashi ke sun kuma yi ko oho da hakan, saboda su basu damu ba, ai shi ne dalilin da ya sa ita Hajiya Ummulkhairin ta kama hanya taje gidan Dijan to shi kuma babanki shima ya kafe akan ba zai basu ke ba.
Na ce wannan ruwansu ne Yakumbo. Ta yi maza ta ce ruwan su ma mai ma ya kare musu bari in yi maza in shirya mu tafi tun rana bata yi zafi ba don akwai ‘yar tafiyar kafa da za a taba.
Nace mata to Yakumbo ai ma ni tafiyar kafa ba mas’ alata ba ce na riga na saba da ita, tayi amza ta ce, aifa na tuna kin yi ta ba kadan sanda kike zuwa wajen koyon sana’ ar nan gashi ya zama tarihi sai amfanin shi ake ci ko ince muke ci tunda yaushe rabon da raina ya baci a kan dinkuna? Ace jaruntaka babu dadi? Bari ki gani in shirya yanzu mu tafi ba ma sai na tsaya wanka ba tsaka tsami kawai zanyi in mun dawo in ban ji kuiya ba na yi wankan.
Nan da nan Yakumbo ta shirya muka kama hanyar fita, gani bata tambaya ba ya sani tambayarta, dama kin gayawa kawu ne? Ta dan yi murmushi, mu yan tsofaffini nan da auren mu ya riga ya tsufa yaushe za ace komai za mu yi sai mun tsaya wani tambaya ai shima yasan sabgogin iyali yawa ne da su. Shiru nayi na ja bakina na tsuke tunda nasan babu halin in tsaya ina tambayarta Yakunbo shi aurenn yana tsufa ne a dalilin masu yinshi sun tsufa?
Bayan mun sauka a mota tafiyar kafa sosai mukayi a ciki jeji muka wuce wasu rugage muka mika cikin wani irin surkukin daji Yakumbu damun san wurin nan haka yake ai da hayar babura muka dauko a dan kauyen nan da muka wuto.
Hararata tayi, kufa yaran yanzu bakuda wata jaruntaka wai ke kina so ne ki nuna min kin gaji da tafiyar kafar da ake yi ko? Na yi murmushi kawai na yi shiru muka ci gabada tafiya da kyar muka iso wata mararraba da ta ce min wannan da muke kai yanzu ita ce mai kaimu gidan nashi nace mata to.
Mun samu yan daidaikun mutane da ke jiran a sallamesu amma ana sanar da shi isowar Yakunbo yace a shiga da mu.
Na yi mamakin ganin mutumin da ta ce min shi ne malamin na zaci ganinshi dattijo amma sai na ganshi matashi ma’abocin tsabta da natsuwa ga sutura tamkar dai ba a cikin dajin nan yake zaune ba.
Hajiya barka da zuwa, ya yi maganar cikin murya mai cike da kamala suka gaisa nima na gaisheshi.
Maryamu ko? Ta yi murmushi ta ce haka aka yi kuwa malam, idonshi a kaina ya ce, ai mun gani shi mutum ai kowa da sunanshi yake yawo, gabana ya fadi jin da nayi ya ce ya gani kar dai irinsu ne kullum malamanmu suke yi mana wa’azi a kansu? Cikin Zuciyata na ke wannan tunanin.
Ya jawo wani littafi ya bude yana karantawa na dan samu saukin damuwa a tare da ni ganin littafi yake karantawa su kuma malamanmu kulum suna yi mana wa’azin ne akan masu buda kasa suna masu duba ko bokaye to tunda wannan ba kasa bace littafi ne kenan ba duba bane yinshi kuma bai zamo laifi ba.
Mas’alar aure ko? Ya yi tambayar ba tare da ya kalli kowa ba idonshi a kan littafin shi, ta yi maza ta ce mishi eh malam aure ne damuwar kullum sai manema sun fito mata gasu gasu kamar za a yi auren sai kuma a nemesu a rasa sun gudu, tun ina ganin laifinta ina ganin kamar ita ke korarsu har na daina jin zafinta na koma tausayi saboda na gane babu hannunta cikin lamarin.
Ya girgiza kai cikin natsuwa tare da fadin, ai ba zai bari a aureta ba, wa kenan malam? Ta yi tambayar tana mai kallonshi. Ya ce mai ita mana ai wani maketacin aljani ne yake tare da ita shi ya sa babu halin tayi aure don ba zai bari ba shi yake korar mata samarin da siddabaru iri-iri suna tare da ita su rinka ganin ta caccanza musu tanayin launi launi, su ganta fara, su ganta baka, su ganta ja, su ganta bulu ko kuma su rinka ganin fuskarta tana rabuwa biyu sai ta koma ta hade ta sake rabewa ta sake hadewa, to kinga kuwa ai babu lafiya.
Yakumbo tayi maza ta ce, ko kadan cikin sanyin murya ni da kaina da ba sosai nake yarda da irin wadannan abubuwan ba jikina bari yake yi jin bayanin malamin.
To yanzu yaya za a yi kenan malam? Ya ce eh to da yanda za a yis ai dai kumaaiki ne babba sai an rabata da shi gaba daya in ba a tsaya an yi hakan ba ko anyi auren kashe mijin zai yi don haka sai an yi juriya da jarumtaka.
In dai za a rabata da shi ai duk wani abin da za a yi ba zai gagara ba malam a gaya mana kawai abin da za a yi.
Ya ce to babu laifi akwai aiki da za a yi wanda za a bukaci sadaka mai karfi ko dai shekararrun zakaru guda bakwai ko kuma rago sannan zata rinka zuwa nan muna yi mata wani aiki har kwana bakwai in har komai ya tafi daidai to kafin cikar kwanaki bakwan din nan mijin da zata aura zai baiyana ana gamawa sai a daura auren mu kuma in ya zo to shi ne zai biya ladan aikinmu baku ba.
Nan da nan Yakumbo ta shiga yi mishi godiya tare da tambayar to wanne ya yi tsakanin rago da kajin? Ya ce a’a ao na za a hada ba rago yafi sai dai in babu hali sai a yi da kajin duk daya ne.
Ta ce to bari mu bada kudin ragon nawa ne zai yi? Ya ce daga fan goma zuwa sha biyar ko ashirin duk wanda kika bayar zai yi.
Na yi kasake ina tunanin ta inda kudin da ya ambata zasu fito sai kawai naga Yakumbo ta jawo lalitarta ta ciro kudi ta kirga fam goma sha biyar cif ta mika mshi, ya ce zuba nan cikin wannan kwaryar, ta bi umarnin nashi ta zuba muka yi mishi sallama muka fito.
Babu abinda yafi komai yi min dadi irin cewar da ya yi kafin a kammala aikin mijina zai baiyana ana gamawa kuma sai a daura auren shi ne ma wai zai biyashi kenan nima zan yi aure babu sauran a tareni a zageni babu sauran a yi min gori, babu sauran a rinka nunani a unguwa ana fadin babu sauran sa’ata a’ yan matan da ke yawo a unguwar.
Washegari da safe naje na samu babana a rumfarshi bayan na kammala shiri na dan zauna kamar zanyi mishi hira sai da na bari Sallau ya dauki kwanduna ya nufi kasuwa sai na kalli babana na ce mishi baba yaya Dija ta aiko ni wurinka wai ince maka akwa wata yarinyar bazawara mai hankali kusa da su ko za a yi magana da ita.
Gabana yana faduwa na yi mishi bayanin, sai na ji ya ce to ina da kudi ne da za a yi min magana da bazawara? Sannan da girmana da komai ita mace ace miki tana son tsoho ne a shekarun kuruciyarta.
A hankali na ce mishi, baba ai ita yaya Dija ina ganin kamar sun fahimci juna ita da matar tace min ne in yi maka magana in ka yarda ta turo maka ita don ka ganta, a hankali ya ce a’a ni kam ai ba sai na ganta ba in dai ku tayi muku ai shi kenan fitina ce dai kawai ni bana so.
Nace mishi to nayi mishi sallama na tashi na tafi, can cikin zuciya ta kuwa mamaki nake yi ban taba zaton haka amsar babana zata zamo ba, na kama hanyar tafiya wurin malam don karbo alkawarin da akayi duk da wata zuciyar tana nuna min in fara ganin yaya Dija tukunna sai kuma naga to bari dai kawai inje can din in yaso in na dawo sai in biyo ta wurinta in yi mata bayanin yadda muka yi da babana daga nan kuma taga abin da na karbo wurin malam.