Wajen karfe goma sha dayan safe na isa kauyen nan inda daga shine muka soma yin tafiyar kafa, nayi tafiyar kafar har na raina kaina sai da na soma kaiwa matuka wajen gajiya ne ma na tuna ko sunan malamin da zani wurin nashi ban ji ba balle kuma na kauyen da zanin, abin ace na bata hanya ban san yanda za a yi inyi tambayar da zata zamo mai amfani a gareni ba, sa’a kawai nayi da na ci gaba da tafiya sai kawai na ganni a mararrabar nan wacce daga ita ne muka dauki hanyar da ta nufi gidan malam.
Tsayawa nayi cak! Na zubawa hanyoyin nan ido ina kallonsu tare da tunanin wacce muka hau ne a ranar? Na gaji da dubawa na yankewa kaina bari kawai in hau kan guda daya tunda ba juyawa baya zanyi ba don haka na kama ta tsakiyar nayi ta tafiya a kanta banga komai ba banga wata alama da na gani wacce ta karfafaa min guiwa ba don haka na juyo da baya zuwa inda mararrabar nan take na sake zabar wata hanyar na hau nan ma nayi iyakacin iyawata nayi tafiya sai da na fara debe tsammani ina cikin tunanin komawa da baya kawai in koma gida inje in gayawa Yakurmbo Halima cewar ban gane hanyar ba tazo kawai ta karbar min maganin da kanta ko ta tasoni a gaba mu zo tare kamar yanda tayi min rannan tunda ni na kasa gane wurin da kaina sai kawai naga mutum tsaye cif a gabana tamkar daga sama aka jehoshi, tsoro ya.yi matukar kamani ba tare da ya ce min komai ba sai naji ya ce min, wuce mu tafi malam ne ya turoni in kai mishi ke saboda an gaya mishi cewar kin kauce hanya don haka ya kwatantamin inda zan sameki shi yasa na yanko ta cikin bishiyoyin can, nabi hannun nashi da kallo don inga can din da yake magana akai, wani irin surkukui ne da sunkurun duhun bishiyoyi da ban taba tunanin dan adam zai iya shigarsu ba ban iya buda baki na ce mishi komai ba haka nan duk da tsananin tsoron da nake cikin ba zai yiwu in yi musu binshi ba tunda ban san inda zan dosa ba.
Tasani kawai yayi a gaba muka kama hanya ‘yar tafiya “yar kankanuwa sai kawai gamu mun isa gidan.
Shiga nan, yana bani umarni nayi maza na shiga sai ga malam zaune daram a kan buzunshi cikin manyan kaya ga hularshi a kanshi yayi kwalliya irin wacce ta dace da shi.
Maryamn Daso ya kira sunan nawa yana mai kallona, ina babar taki? Na isar da gaisuwarta gareshi bayan na gama gaisheshi ya ce, alheri ya gareta, ai ga kwaryar da na hangoki a ciki can, nayi maza na waiwaya na kalli kwaryar da ya ce min daga cikin nata ya hangeni babu komai a ciki in banda ruwa, na sake juyawa gareshi na kalleshi don jin bayanin da yake yi, yayin da zuciyata ke ta faman harbawa bal bal bal, daga nan din ne na kira wanda ya daukokin don kar ki je ki yiwa mutanen hanyar da kike ta kakkaucewar wani ta’adi tunda su din mafi yawancinsu ba hakuri ne da su ba.
Wani mutum ya shigo rike da zangarniyar dawa a hannunshi ya tsuguna ya mikawa malam, bai kalleshi ba ya ce mishi, kwaya bakwai nake bukata, ya mika mishi kwaya bakwai din ya fita da zaugarmiyar a hannunshi.
Malam ya jawo wani tsohon kasko fasasshe ya debo kasa tafin hannunshi uku ya zuba a ciki ya dauki tulun dake gefenshi ya jika kasar da ruwa ta jiku sannan ya shuka kwayoyin dawan nan guda bakwai a ciki kan kace meye wannan sai kawai naga dawar nan da ya shuka a kan idona ta kama tsirowa a cikin kaskon, nan na zuba ido ina kallon abin mamaki wanda ban taba ganin kwatankwacin makamancinshi ba, na yi matukar kokarina wajen boye halin da nake ciki na tsoro saboda ganewar da nayi ina cikin wani babban al’amari, don haka nayi maza na soma karanto addu’o’i na neman tsari.
Kina da wani wanda ya dameki ne a yi miki maganinshi? Na’am na amsa ina kallonshi don ban fahimci abinda maganar tashi take nufi ba, eh abinda nake nufi kenan in kina da wani wanda ya dameki kawo sunanshi mu gwada miki aikinmu a kanshi ta hanayar kashe miki shi nan take.
Kalululu, sautin da cikina ya bayar kenan a lokacin da na ji maganar tashi, da kyar na iya girgiza kaina don nuna mishi alamar babu, cikin zuciyata kuma tarnbayar kaina nake yi me yasa malam yake yi min irin wadannan abubuwan tunda ni ai ba abin da ya kawoni wurinshi kenan ba, sannan me yasa bai yi ba rannan a gaban Yakunbo sai yau da ya ganni na zo ni kadai. Kina saurarona? Na yi maza nace mishi eh, ita babar taki ta yi miki bayani a kan ka’idojin aikinmu ko?
Na girgiza kai nuna alamar a’a, to muna da ka’idojn da karyasu yake da hatsari kwarai shi yasa muke bayani a kansu don kar mutum ya jawa kanshi wata fitina da zata zo ta dameshi ta damu duk wani wanda yake tare da shi, ba a yin musu da umarnin da ake bayarwa anan ko mai tsananinshi, sannan ba a yin gardama ko jayaiya domin nan din wuri ne da ake mu’amala da nau’o in halittu guda uku wato jinsi mutane da na aljanu sai kuma rauhanai don haka ba wurin wargi kika zo ba, yin daya daga cikin ukun can dana ambata miki ina nufin musu, gardama ko jayaiya sakamckonshi yin hauka ne hauka kuma irin wacce bata warkewa.
Cikina ya sake bada wani sautin na kulutuiu har ma ya fi na farkon karfi saboda tsananin tsoro da na samu kaina a ciki din.
Kin taba ganin aljani ko rauhani? Na yi maza na ce mishi a’a, to ai za ki ganshi yau din nan. Na ji kamar in zabura in mike in karta da gudu in shige cikin dajin nan in huta.
Ya gyara zama ya soma yi min bayani, kin san akwai jinsih mutum da na aljan da raunahni kafin mala’iku ko? Na yi maza na ce eh ba tare da na fahimci komai ba da yake nufi ba. To mu nan fadar rauhani kika zo kin gane? Na sake yin karfin halin cewa eh. Ya zuba min ido yana kallona ban sani ba ko shima ya gane halin da nake ciki na tsoro ne.
Yanzu kafin rauhanin da zai yi miki aikin ya iso tunda mum riga mun kirashi yana can yana dawafi ne in ya gama zai taho, kin taba yin sata? Tambayar tashi ta zo min a bazata, na yi maza na kalle shi don inji ko abinda aa jin daidai ne, ya ce eh abinda na tambayeyi kenan, kin taba yin sata? Na ce mishi a’a, sata ko wacce iri baki taba ba? Kin san fa ba a karya a nan, in ka riga ka shigo nan to gaskiya da gaskiya ne kawai, in kayi karyar ma za su gane ka don haka yi tunani sosai don kar su kamaki da laifin yin karya.
Na gama tunanin da zanyi sai na ce mishi, sai dai ko na abinci ko naman miya a wurin matar babana. Ya yi maza ya ce, a’a ai wannan ba sata bace bari kawai a gaya musu baki taba sata ba ko da yake ma suna nan tare da mu suna jinki, ko kina yin karya? Na dan yi shiru cikin nazari kafin shima na ce mishi wani loakci na kan yi amma ba ko da yaushe ba.
Ya gyada kai tare da fadin, to babu laifi ya yi kya, kina da kiyayewa kenan? Na ce mishi ch, to ai shi kenan sun jiki, tambaya ta karshe ki fa yi hakuri ba daga ni bane kaidarsu nake bi don haka suke bincike kan kamewar mutun kafin sù shigar mishi, kin gamsu? Na ce eh. Kin taba yin zina? Na girgziza kai na nuna alamar a’a, to ai ma shi kenan aikin naki mai sauki ne tunda baki da kazanta mai yawa a tare da ke sai ta kananan zunubai wannan kuwa dukkanmu ne don haka ki kwantar da hankalinki shi wannan aikin naki mai sauki ne kwarai an yi irinshi yafi sau nawa anan in dai kin bada hadin kai ai shi ke nan tsanani kwana uku ne zuwa bakwai magana ta kare don haka bari ya iso ya sallameki, na riga na ji tasowarshi don haka bari in yi miki tuni ka’idojinshi banda musu banda gardama banda jayaiya ba abokin wasanki bane sakamakon yin hakan hauka ce da babu nagani kin gane ko? Na ce eh, can cikin zuciyata kuwa addu’o’i nake ta yi na neman rabuwa da rauhani lafiya.
Ana cikin haka naji wani abu ya fara bayar da wani sauti na shuuuuuw sai dai ban san daga ina yake fitowa ba, wata irin iska’mai sanyi ta fara shigowa dakin.
Yauwa gashi nan ya doso mu gashi nan ya dunfaro gashi nan zuwa kar ki mance da abinda na gaya miki don ni kaucewa zanyi in baku wuri banda musu banda jayaiya banda gardama, dif sai kawai naga wutar fitila ta mutu duhu mai tsanani ya baiyana, na yi matukar tsorata irin tsoratar da ba zai yiwu in kwatanta ta ba.
A firgice kwarai na shiga furta kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, shiiiii sautin da ke ta karuwa a cikin dakin kenan sai kuma tsananin sanyin da ya fara kadani, na shiga cikin wani irin yanayi mai tsamanin firgitarwa baranma dai da na ji wani abu ya sauka a jikina wanda ya yi min kama da hannun mutam, rauhanin ma yana da hannu ne irin na mutane?
Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan, ban daina furta kalmomin da nake firtawan ba sai ma karawa nayi zuwa can naji abin nan da ya tabani mai kamar hannu ya cafko kullin da na yiwa zanina a ta bayana yana kokarin kwanceshi, kici-kici da kokawa mai tsanani ya kaure tsakanina da rauhani saboda ganin da nayi rauhani yana kokarin gwadamin karfi, ya yi min illar da bazan laminta ba, ganin da nayi kamar rauhanin zai yi galaba kaina yasa na sa hannu da kafa na kuma bude baki na kurma ihu da iyakacin karfina ina bana so, bana so aikin a kyaleni, ban sani ba ko maganar da yaji nayin ne ya sashi bude bakinshi shima ya yi min magana da irin nashi zancen.
Gyaaraaahhhh ki budee kafahfuh mu sah miki albarrkah…
Mu sake bin Maryamu cikin littafi na hudu don mu
ji karshen labarin na ta tare suka fito.