Skip to content
Part 42 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

To ga shi nan na gaji da zaman gidan na fara gudu ina tafiya abinda kake yi a boye zan fara fito da shi fili. Ko kula zancen ban yi ba, balle in samu wata matsala, tunda an yi wadanda suka fi ta, na kuma ga wucewarsu lafiya.

Abu guda daya da yafi bani mamaki shi ne, kowa ko kuma in ce ko wadanne mutane a gidansu sukan yi al’amarinsu shiru. Babu mai cewa komai, amma ni da Babana komai muka yi sai an ce mun yi. Da ana tsayawa á iyakacin abinda muka yin ma to da sai in ce da sauki, amma ina sai an kara.

Ta gidan Yaya Dijah na bi da muka tashi don tasan naji sauki har na fara zuwa Makaranta. Na same ta cikin farin ciki an kawo mata adashenta da tayi wanda dama tàci alwashin kashe kudin gaba daya a hidimar auren da za’a yi wa Babana.

Dadi ya kama ni, amma ko kusa ban kai Yaya Dijah murna da dokin auren ba, duk da kudinta take kashewa. Ina dawowa naje na samu Babana a rumfarshi, na zauna ina shan timatir din da na dauka saboda sha’awar da ya ba ni, muna ‘yar hira ina ba shi labarin irin kąratun da aka yi a kwanakin da ban je ba.

Ya ce min “Eh, ai shi karatu haka yake, in dai har kullum kana zuwa ana yi da kai, to ba ka gane yawan abinda ake yin ya dame ka ba, sai in ka yi fashin zuwa.

Na ce,   Eh Baba.” A hankali sai na shigar da bayanin abinda na tarar Yaya Dijan tana shirin yi, shi ne hada kayan aure don maganar tana kara karfi tana kuma kara matsowa.

Wani irin shiru Babana yayi, ya kafawa kwandon alayyahun da ke gabanshi ido ba ya ko kiftawa. Har tsoro ya fara kama ni, kar dai ya ce ba ya so. Cikin natsuwa sai na tambaye shi “Me ya faru kayi shiru haka Baba?

Ya ci gaba da aikin shirya alayyahun nashi yana daurewa saboda ma su zuwa saye yana yi min bayani, wato ba wai bana son auren ba ne, fitina nake tsoro.

Ta zo ta kashe kudinta da tayi ta tattalawa bata yi wa kanta ko ya’yanta wani abu sun ji dadi ba, in zo ni kuma ban ji dadin abin ba, wannan ta gidan må ya ya aka kare da ita kullum tana raina abinda ake kai mata, balle kuma a ce an je an dauko yarinya an kawo, alhalin ba wani abu nake da shi ba.”

“Kai ai ina ganin kama wannan ba za ta yi wata fitina ba Baba. Tare muka je gidansu dazu cikin maganganun da naji Yaya Dijan tayi mata, har da na daki ta ce mata guda daya ne kuma bai da wani girma.

Sai naji ta ce, “Ai babu komai, shi aure in aka yi shi zaman lafiya ake bukata ba wani abu ba. 

Babana ya ji dadin kalamin nata da na gaya mishi, nan take ya ce “To babu laifi, sai kuyi.” Ya mike yaje ya dauko wani tsohon bankinshi na karfe ya kwakulo makullin a inda yake boyewa ya ba ni ya ce min bude ki dibi abinda yake ciki na dai san babu yawa, amma jeki ki kai mata ko sabulu sai ta saya.”

Na ce mishi, “To Baba.” Na kuma yi mishi godiya cikin farin ciki, don kuwa hakan alama ne na shima yana son auren.

A natse kwarai na yiwa Sallau bayani, ko ban gaya mishi abinda za ayi da dakin bá, amma nayi kokari na fahimtar da shi ya gane cewar bukatar dakinne ya taso, ba son korarshi nake yi ba.

Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min “To, tunda haka ne Mero, in rinka kwana a zauren gidan nan mana kawai, ai shima wani babban daki ne, in na rufe kofar waje na rufe ta ciki ba shi kenan ba?”

Nayi maza na ce “Kwarai kuwa Sallau, to ai ma shi kenan tunda ka samarwa kanka wata dabara.”

A haka al’amura suka ci gaba har na kai ga fita daga dakina na koma na Sallau na kira mai gyara ya yiwa dakin gyaran da ya dace kafin mai fenti ya zo ya yi.

Ita bata yi tunanin ba don a ranar da ake aikin ma wuni tayi tana fadin, To tunda babu tsayayyen da zai tsaya ya kwasa ya kai gidanshi, can inda ake ta harin kuma uwar yarinya taja tayi damara ba dai a shiga ba, sai dai a kare a titi.

Ai sai kiyi ta gyara kina fenti don ki ji dadin zama tunda ba ki da ranar tashi.” Ban kalleta ba ma balle tasan naji abinda take fadi.

Da daddare ma da Babana ya dawo naji shi yana tambayarta ni ina butar nan ne? Sai naji ta ce mishi, Ni fa Mallam na wanke butocina na tura su a karkashin gado, don na fara gajiya da wannan auren na zuba ruwa a buta.

Kai baka da wani aiki sai na a baka ruwa a buta, don haka rinka yi da na roba kawai ga su nan a bakin famfo suma a wanke suke nayi maza na tashi na fito na ba shi butar da nake amfani da ita, na koma dakina can ciki na zauna.

Ina jin ta tana cewa, To, ni in ban da na san in ta kasance a kanka dolensu su bani ciki da falon da nake ciki zan yi wannan susutaccen zaman ne? To dadin abin duk tsiyarsu su din mata ne, mata kuma ba wani karfi ne da su ba da dai suna da namiji a cikinsu ne ai da anga tsiya to babu shi.”

Ranar Laraba da sassafe bayan an idar da sallar Asuba aka daura auren Babana da amaryarshi Safara a Masallacin unguwar su Baba Baidu ne yaje ya karbar mishi auren.

Yana dawowa daga daurin auren Baba Sumaye ta rinka rangada guda tana fadin, “Kai, wannan ya da jaruntaka take, to ashe ma tana da irin wannan kokarin ta bar ubanta yayi ta rayuwa a cikin wannan fitinar?

Ubangiji ka yi wa Hadiza albarka.” Da yake Baba Lantana bata tunanin komai game da Babana musamman kuma da yake tasan mu’amalah tayi matukar ja baya tsakaninshi da Baba Baidu balle iyalinshi, bata kawowa ranta komai ba sai kawai ta rinka jan tsaki tana fadin “Munafukan unguwa, ko ina ta samo wata Hadiza kuma oho.”

Sai tayi maza ta sake jan wani tsakin don ta tsani Baba Sumaye, ta tsani kuma ta jiwo muryarta tana wata magana sai tayi tsaki tayi ashar ko ta ce munafukan unguwa.

Tsohuwar aminiyar aminiyarta Delu, ita ce tayi sallama ta shigo gidan, rabon da in ganta kuwa an dan kwana da yawa, ina jin tun lokacin da ta shirya aurena da surukinta Alhaji Muhammadu Nalami, ta gaiyaci tsofaffin abokai don su tayata sheda isowar ta da mallakarta shekaru hudu kenan da suka wuce.

Delu ce yau a gidan? Tayi mata tambayar cikin wani irin yanayi na wulakanci da shirin tozartawa, “Kun gama zagaye-zagayen gulmarmakun naku ne kuma ki ka gaji ki ka zo wurina? To ai babu abinda bana ji, duk maganganun da kuke fada suna dawo min, musamman ma ke.

Tunda ke kam ai butuluci ne yake sa ki fadar magana a kaina, ko ma menene a tsakanina da Nalami ai aure ne tsakaninsu da Asabe gashi nan kuma tana zaune tana ta haihuwa ‘ya’yanta. Delu tayi murmushi ta ce, tana ta yawo dai wannan haihuwar tata ta ukun ina ce a unguwa ta yi ta? Ko menene ba a sani ba? Ita kam Asabe ai abin tausayi ce ita don kuwa mugun abin ki ne ya shafeta, ni tausayinta nake ji tunda ko jiya tazo wurina.”

Bakin Baba Lantana ya dan rusuna a dalilin cewar da Delu tayi ko jiya Asabe taje wurin ta watakila taso ne yadda ta yanke ta share tsofaffin aminan nata, itama yar tata tayi haka.

Delu tayi amfani da damar da ta samu na shirun da Baba Lantana tayi ta ce mata “Kinga ni fa ba fada ma ya kawo ni wurinki ba, zuwa nayi in ji dalilin da yasa hidima irin wannan ta taso miki, ba ki neme mu ba.

Cikin natsuwa Baba Lantana ta tambaye ta hidimar me kuma nake yi yanzu in banda ta fama da tsohon mijin da bai iya hassala komai. Delu ta ce, Kai haba bai iya hassala komai aka daura mishi aure? Ko kuwa dai don ya yi aurenne yasa ki ke fadin haka akan shi don ki bata shi?

“Aure?” Tayi tambayar a wani irin yanayi, “Wane aure kuma? Wace mata ce zata yarda ta auri Mallam a yanda yake din nan?”

Baba Sumaye da ke cikin gidanta tana jiwo hirar tasu, kasancewar a tsakar gida suke, don ko dakinta bata kaita ba sai ta takarkare ta rangada wata irin matsiyaciyar guda mai ratsa kunne da jiki.

Kafin ta ce “Ubangiji na gode maka, na kuma roke ka ka yi wa Hadiza albarka da ta raba ubanta da wannan musiba da ya dade yana rayuwa a ciki.

Kar dai dama da ni wannan matsiyaciyar matar take yi? Aure? Wane irin aure kuma. Mallam zai yi? Wace mata ce zata yarda ta aure shi? Ai kuwa da taci…”

Baba Sumaye ta kwashe da dariya tare da fadin yau fa za a ga hauka tunda an yiwa mahaukaciya kishiya, aiyururururii.” Sai ta sake rangada guda. Gabadaya Baba Lantana ta birkice, Delu kuwa ta yi maza ta suri takalmanta ta kama hanyar fita, tana fadin Ke ni fa ban san ba ki ji ba da ban zo na gaya miki ba, alhalin maganar take yi fuskarta cike da murmushi alamar bukatarta ta biya.

Baba Lantana ta kama fadin maganganu tamfar wata zararriya, “To Mallam ma har wani namiji ne da za a yi kishi a kanshi, sullutu a cikin maza, shi in ana kiran maza har zai buda baki ya amsa?

Ai karyarsu ta kai karya, a ce ya yi mata biyu bai isa ba, Baba Sumaye tayi maza ta ce to na náwa? Wai an tambayi tsuntsuwa sunanshi? Ya ce na nawa? Ta bar wannan ta koma durawa Baba Sumayen ashar, ita kuwa ba ta amsa ba.

Ta yi ta gaji ta koma kan Babana da baya nan zuwanta rumfarshi biyu bata samun shi ta dawo tazo ta zauna ta zagi Innata ta hada da Yaya Dija da ni da makwabta ta gaji rushe da kuka ita kadai.

Ana cikin haka sai ga Asabe ta shigo gidan, rabe-rabe da ‘ya’yanta uku biyu suna biye da ita, daya tana goye ganin uwar tata a yanayin da take ciki yasa jikinta yayi sanyi kiyi hakuri Mama.

Tamfar tuna mata zaman nata tayi ta juya kanta da zagi da tsinuwa ba dai kin ce ke wurin makiyana za ki rinka zuwa ba? To ki daina zuwa wurina na yafe musu ke kije can ku karata na bar musu ke. Ta rufe mata ya’ya da duka gaba daya gida ya kaure da koke-koke.

A A zuciyata na ce, “Kun gamu da mahaukaciyar kaka, sai ga Yaya Dijah ta shigo ita da Aminanta, Anti Kubra da Anti Asiya. Na yi zaton zata rufe Yaya Dijah da duka, sai naga ba haka ba, sai da Yaya Dijan ma ta mika mata ‘yan kayan da tazo mata da su a matsayin kayan fadin kishiya, shi ne naji ta ce mata je ki ki kaiwa Ramatu kin ji ko ba ki ji ba? Munafukai ke da yar uwarki.”

Ta ci gaba da zage-zagenta tana watsi da kayan. Ba su ce mata komai ba, sai lekowan da Anti Asiya tayi dakina ta ce min “Ke je ki ki karbo mana kayan cefane a wurin Baba, aiki muka zo yi don yanzu ‘yan jere za su iso, na ce mata to.

Ban dawo na samu Baba Lantana ba, kofarta a kulle itama Asabe ta tasa ‘ya’yanta sun yi gaba sai kawai muka sake a gida muka yi ta hidimarmu, ‘yan jere suka iso suka yi ta jerensu, makwabta ma suka yi ta shigowa suna yiwa Yaya Dijah murnar auren da ta yi wa Babanmu, sai hira ake yi ana aikin ana bada labarin haukar Baba Lantana ana kwashewa da dariya. Da yamma yan biki suka tafi, bayan sun gama kintsa komai a kan sai da daddare masu kawo. Amarya za su kawo ta. Suna barin gidan sai kawai naga Baba Lamtana ta balle kofar dakinta, ta fito, ashe wai duk abin nan da ake yi tana ciki ta kulle kanta, tana jin duk abinda ake fada.

Muna hada ido da ita, ita ce ta ce min “Dukkanku kuma za ku ci ubanku, har da shi uban naku zan ga yadda za a yi ya yi mata biyu a cikin gidan nan da ni ku ke yi.”

Tun kafin Baba Lantana tayi min wannan bayanin a tsorace nake da ita, balle kuma da ta gaya min hakan, ko dama can kuwa mafi girman tsoron nawa ya yi tafiya ne ga  tunanin yadda za a yi Babana ya shigo dakin wata mata a gabanta, tana kallonshi, to balle kuma yanzu da tayi maganar da bakinta.

Magriba kawai aka idar sai kawai jama’ar amarya suka dawo wai har sun kawo ta, nan da nan gida ya gauraya da kamshi, ba su wani dade ba kuma sai suka watse suka yi tafiyarsu.

A ka bar amarya ita kadai a dakinta, nima ina nawa dakin, ina fama da faduwar gaba saboda tsoron abinda zai faru tsakanin Babana da Baba Lantana in ya shigo gidan nan yau, tunda ta ji maganar ba su yi ido hudu ba.

Kan turmi ta fito ta zo ta zauna da damara a kugunta, tana fadin “To duk wani iya shegen mutum ni kam ai kallonshi kawai nake yi, ni kam ai iyaka ce ai ni nafi tsumma lalacewa, yau zanga yadda za a yi Mallam ya zo ya ce min yayi aure a gidannan zai shiga, wani daki, ai sai dai kowacce ta aura mishi ke din tazo tayi gadinshi, in har ta matsu sai yayi abinda take so yayin da ke, munafukan banza munafukan wofi.”

Tana cikin wannan sambatun sai gashi ya shigo da gyaran muryarshi da ya saba, da kuma sallama. Da sauri ta taso ta tare shi tana fadin Munafuki, na ce maka munafuki.

Ina lekensu ta jikin kofa, na ganshi a tsaye yana kallonta, ai babu inda za ka je zan ga yanda za a yi ka shiga wani wuri ba nawa ba, kai nan ma har wani namiji ne? nayi kamar in tashi in fita in taya Babana, sai kuma naga kai bari dai kawai in zuba ido in yi ta kallo, in har ta hana shi shiga dakin amaryar tashi shi kenan in gari ya waye in taga zata zauna ta zauna, in taga zata tafi ta tafi.

Wane dadi ne ya kwaso Baba Lantana? Oho. Sai kawai na ganta tasa hannu biyu ta cukume wuyan rigar Babana tana fadin “Kai din me? Me kuma aka yi…”

Bata gama ba sai kawai naga tamfar an dagata sama ne kafin aka yi faro da ita ta tafi can nesa ta fadi.

Mamaki yayi matukar kama ni, na ganin abinda yayin, nan take kuma sai na tuna ai duk iya shegen da Baba Lantanan ta rinka tsulawa a gidanmu bata taba gwada sa hannu ta shake wuyan Babana ba sai yau.

<< Halin Rayuwa 41Halin Rayuwa 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×