Skip to content
Part 43 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kafin ta taso tuni har ya gyara zaman rigarshi ta daidaita a jikinshi, yayi sallama kofar dakin Amarya ta amsa, ya shige ciki.

Ka fito Malam tun muna shaida juna da kai, tun tun muna girma da arziki da kai tun ban shigo nan din na same ka ba. Ta zabura wai zata shiga dakin Amarya, ban san yadda aka yi ba na dai ji Amaryar tana cewa.

A’a haba wannan kuma ai neman wuce iyaka ne, koma dai daga can wurin zaman naki kawai in yana son ganin naki zai zo inda kike ya same ki.”

Ke har wata iyaka ce da ke? Ta soma zage-zage sai dai kuma ta kasa shiga dakin ta same shin, ana cikin haka naji an turo kofa an rufe gurin an kuma sa sakata an kulle ta ciki.

Buga kofar yayi matukar razana Baba Lantana, nan take ta kurma ihu mai karfi, ni kuwa nayi maza nima na sawa tawa kofar sakata, don kar ta fado min dakina, na hau gadona nayi kwanciyata aka barta a tsakar gida ita kadai tana ta faman sambatunta.

Washegari kuwa farkawa nayi a dalilin an kwankwasa min kofa saboda makarar da nayi, saboda Baba Lantana bata bar ni na samu natsuwar da nayi bacci da wuri ba, shiga da fita ta rinka yi tana buga kofa kamar zata ballata, ban sani ba ko ni kadai ce kai kawon nata ya hana bacci.

Ina bude kofar dakin nawa naga Amarya tsaye da murmushinta ga kamshinta na amarci a tare da ita, kai Yaya Dijah ba karamin ladan Babanmu ta samu ba, abinda zuciyata ta fada kenan sanda na karewa amaryar kallo.

Gajiye ce ta saki makara ko? Na tayata murmushin da take yi nin, to in kin idar da sallar sai ki zo, na ce mata to. Ina shafa fatiha na shige dakin nata don kuwa dama na kosa inga Babana in ga yanayin da yake ciki.

Yana zaune kan wata shimfidaddiyar darduma, kai da ka ganshi ka san yana cikin farin cikı, an tasa mishi abin karyawa a gabanshi.

Na tsuguna na gaishe shi, farin cikinshi a bayyane yake, me kike so ki karya da shi? Tayi min tambayar bayan ta gama amsa gaisuwar da nayi mata. Akwai tea, akwai kunu, ga kuma farfesun kayan ciki.

Na zuba musu ido ina kallo, can cikin zuciyata kuwa nasan da abinta tazo, ga kuma kayan tsarabar bikinki zan. Na ce, Na gode, a bar min nan sai za ni makaranta zan karba in kaiwa ‘yar ajinmu.

Babana ya ce, “A’a karbi kici abinki in za ki je makaranta ki diba a nawa.” Na ce, To.

Hu’un, lalle namiji sai a bar shi, na kuma yarda lalle Mallam ba karamin algungumi ba ne, ashe duk halin naza shima ya iya, ina kallonshi sumu-sumu abin tausayi, ashe ba abin tausayin ba ne, ai inda nasan haka ne da ba karamin gasa shi nayi ba. Ashe dama lafiyarshi kalau?

A zuciyata na ce da kin kashe shi dai ba gasawa ba, in dai gasawa ne kawai ai dukanmu mun gasu. Ni da kaina ba karamin mamakin Babana nayi ba, gabadaya kwanaki ukun nan na dakin Amarya ko rumfarshi baya budewa, yana nan a gida a kuma cikin dakinta, yana kishingide akan darduma duk lekawan da zan yi kuma zan hango shi an tasa mishi wani dan abin motsa baki a gaba.

In kuma ya fito don yin alwala zuwa Masallaci, sai kaga tana biye da shi tana rike mishi da butar tamkar dai ace gadinshi take yi.

A wannan lokacin ba ka iya kwatanta yanayin da Baba Lantana take ciki, in ban da uhun maza? Babu abinda za ka ji ta tana fadi. Namiji? Kai lalle sai a bar su, ashe dai babu wani dan kankani a cikinsu.

A haka aka koma dakin Baba Lantana ina daga dakina ina jiwota, “Oh, Mallam ashe lafiyarka kalua kake yi min irin wannan abin? Gabadaya kwanan nan uku ba ka yi fashi ba ko daya, ina kallonka yau din ma ba za ka yi wani motsi ba ne ina yi maka magana kayi shiru ka lullube kai da bargo.

Ko kana nufin a kaina ne ba ka da lafiya, amma in a can ne lafiyarka kalau? To ai ba zai taba yiwuwa ba, nayi maza nasa yan yatsuna shabbaba na toshe kunnuwana da su don in samu in daina jin maganganun nasu, ko zan samu in yi bacci.

Komai na Safara a tsare yake, kullum girkinta yazo zata ba mu lafiyayyan abinci da irin kudin da ake baiwa Baba Lantana tana rainawa, tana kin yin girkin.

Ga ta gwanar iya abincin gargajiya ce iri-iri.

Su burabusko, su gwate, su dan wake su danbu su gauda su gurasa, su sunasir su wasa-wasa, balle ayi maganar tuwo, sai tayi sati biyu tana girki bata maimaita abinda ta girka ba.

Haka nan abin karyawa tuni muka daina sanmakon fito nemanshi, ganin da tayi ina fita nemo mana ranar girkin Baba Lantana, yasa ta kirani ta ce min rinka zuwa nan kullum da safe muna karyawa kin ji, shi dai da ya ajiyeta ranar girkin nata su san wanda suke ciki, na ce mata to.

Baba Lantana ta tsunduma cikin wani irin abu da bata taba zaton zata tsunduma cikinshi ba, a zamanta da Babana, ga kishiya dai kwatsam wacce kuma ta haife ta, ga shi tasa hannu ta kalallame shi, in ban da Baban nawa ba dan gayu ba ne, don su wanka da shafa man nan da duk sai tayi mishi, to ba zai yarda ba.

Gashi tana ganin wadansu irin al’amura a wurinshi wadanda bata taba tsammanin yana da su ba, sai ta zama kamar wata zararriya, babu abinda take so irin ta samu abokin hirar da zata yi zance da shi don ta rage damuwarta babu.

Saboda babu mai zuwa wurinta duk ta kore su sanda ta samu daular gidan miji ita kuwa Amarya sai kai-kawo take yi da ‘yan uwa da abokan zama, dan muguntan da take yi mana na kin yin girki muyi takai kawon neman abinda zamu ci yanzu duk ta kau.

Ko kadan Safara bata kallon abincinta in ta gama ta ce su zo su ci ta ce to, tunda tare suke ci in bata gama ba ma oho. Za ta ci wani abu nima zata ba ni.

Bakin ciki ne ya ishi Baba Lantana, taga kamar in ta tayar da wuta zata iya korar Amaryar nan saboda taga komai take yi ba ta ce mata komai.

Ta karbi kudin cefane ta ki yin girki, ko taga shanyarta a igiya ta zube. Rannan an tashi da safe naji Anti Safaran na cewa Yaya ina kwana? Ko dama a lalace take amsa raata gaisuwar, amma bata daina ba.

Yaya ina kwana? Ta sake maimaitawa, sai naji ta ce mata, ke raba ni da wani yaya, yayan munafurci, ki kira ni yaya a bayan idona kina yi min munafurci, rike yayarki bana so tunda ai ni ban ma ga wani abinda na girme ki da shi ba.

Ta ce, To kiyi hakuri. Taja bakinta tayi shiru bata kiranta Yayan ba ta kuma kiran sunanta, ana cikin haka ta sake cewa kicin nata ne a ranar girkitita bata yarda wani ya shiga ba. Nan ma ta ce, to, sai ta fito da risho dinta in zata dan yi wani abu ta tura a bayan kofarta tayi.

Ba a gama da wannan ba sai kuma ta fito da wani salon in Safara ta gama abinci ta kawo ta kira ta ba za ta ce ba za ta ci ba, sai ta dauko kujerarta tazo ta zauna tasa hannu ta gutsuri lomar tuwon ta kai bakinta, sai ta fara tauna shi.

Sai tayi wuf ta dawo da shi ta tofar tare da fadin, kai tir, wannan tuwon ai danye ne ke ba ki iya komai ba ne a rayuwarki sai jarabar bin miji? Ba ta ce mata komai ba, rannan dai sai ta gaji ta ce mata da dai kin daina irin wannan abin, tunda kema kin san baida amfani, shi hatsi ai ba a yi mishi haka.

Sai kuwa Baba Lantana ta zabura ta sake gutsurar wata lomar ta kai bakinta, tayi mishi tauna daya ta maido shi kan asalin tuwon da ke cikin kwanon wanda ita take ci, anyi din an yi wa hatsin rama mishi.

Haka kawai sai ki rinka yiwa mutane danyen abinci kice sai an ci dole? To an yi an kuma karawa.

Ta sake gutsura ta kai baki ta sake mayarwa cikin kwanon, ina daga dakina ina jin su ban san yadda aka yi ba sai kawai naji an kaure da dambe.

Dambe kuwa ra gaske, tunda dukkansu karfafa ne, ko motsi ban yi ba balle in yi tunanin raba su, sai kawai naga an daga Baba Lantana an nanata da kasa, Safara ta haye kan ruwan cikinta tayi ta kirbar bakinta da duka, da ta ga hakan ma bai yi mata ba, sai ta shaketa har sai da wuya ta sa ta bude baki tayi maza ta kwaso gwajaljelon tuwon da ta tauna ta mayar ta warba mata shi a baki ta matse bakin sai da ta hadiyo shi.

Sannan ta saketa ta mike tayi tafiyarta tare da fadin “Haba, ina amfanin babban da bai san ciwon kanshi ba? Ina kyale ki ba ki san kyale ki nake yi ba, to mu zuba shege ka fasa ni da ke.”

Da daddare Babana ya dawo, ta zaunar da shi ta rattaba mishi bayani, kala bai ce mata ba. Ta sake tunzura zata tasa shi a gaba da masifa, ya fito yazo yayi shimfida a tsakar gida yayi kwanciyarshi, duk da sanyin da ake yi bai tashi ba sai da lokacin zuwa Masallacin shi yayi.

Wannan zaman ai ba dole ba ne, kai Mallam ai dama ba mijin mata biyu ba ne, muturmin da baya iya buda baki yayi magana yaya za ayi ya iya ajiye mata biyu? Kullum baki a rufe kamar na mai ciwon bubu.

Gara kawai ka sauwake min ka sake ni ka ji ko ba ka ji ni ba?

Bai kulata ba, ta gaji da fadan ita kadai ta shiga dakinta ta kama fitar da kaya, ai na ce na daina wannan matsiyacin auren, yau na daina shi ko ka bani takarda ko kar ka ba ni tafiyata zan yi. Ina ganin ta gama kwashe kayanta ta tafi na shiga dakin na share yana, na share dattin dakin tas na cewa Anti Safara bari in taya ki ki kwashe kayanki ki koma can, da sauri ta ce min au haba? Na ce mata eh.

Nan da nan muka bar komai muka koma aikin jidan kayanta muka maida su dakin Innata, dakin da nake ganin kamar babu wani daki da zan so kamar shi, muka gyara komai yayi tsaf gwanin kyau.

Gidanmu yayi matukar yin dadi, Anti Safara tayi ta tattalinmu ni da Babana, har ma da Sallau. Sai dai shi kam bai iya zama ba, yana ganin Baba Lantana ta kwana biyu bata dawo ba, sai yayi wa Babana sallama ya tafi sai dai bai fadi inda za shin ba.

‘Yan kwanaki kadan da auran Babana, kwanakin da ko talatin ba su cika ba, sai ga Babana har ya yi kyau, ya yi fes da shi in muna zaune mu biyu kuwa zai dan rage murya ya ce min, “Oh, ashe lafiyayyar yarinya kuka samar min? Ubangiji dai ya jikan Ramatu da rahamarsa. In ce mishi amin.

Randa Baba Lantana ta cika sati biyu da tafiya, ranar Yaya Dijah tazo mana wuni da ita da ya’yanta duka, dama dan da Anti Safaran ta yaya Nasiru, rabon Yaya Dijah da yin irin wannan zuwan ni dai na manta.

Babana ya wuni cikin farin ciki yana ta ina yaka saka da jikokinshi, itama Anti Safaran haka. Sai wajen yamma ta shirya zata tafi, ya yi tayi mata addu’a yana sa mata albarka, ita zuciyarta gaba daya ko daga ji kuma kasan har da jin dadin abinda tayi mishi.

Da zata tafi sai naji ta ce min ga dan hira nan na kawo miki, ya taya ki zama nayi maza na ce mata to na kama hannunshi na rika nayi mata rakiya muka dawo tare da shi.

Mu’amalla ce sosai tsakanina da Safara, duk da ta same ni a shekaruna na budurci sosai wanda a lokacinmu ma ba a cika samun ‘yanmata masu shekaru irin nawan ba in dai ba a gidajen da ‘ya’yansu ke karatu sosai ba.

Amma hakan bai sa tayi wasa da kulawa da al’amurana dan kankanin canji in ta gani a tare da ni zata tsaya taga ta warware min shi. Haka nan sai aiki ya mana kaza gyara abu kaza kar kiyi kaza, kaza da ki ke yi ki daina babu kyau.

Abinda na tabbatar shi ne da ita ce ta zauna da ni a shekaruna na kuruciya, to da tarbiya sosai tayi min, kuma zan fita to bai zamo mata komai ba in ce mata za ni wuri kaza ta ce min kai a’a kina yawan fita ba dabi’ar budurwa mai mutunci ba ne yin hakan.

Sai dai in makaranta za ni, in kuwa za ni Makarantar to ko ina da kudina tunda ina sana’ata tana gani zata kawo kudi ta ce min ungo ki kara, in yi mata godiya.

A haka sai gidan namu ya sake zama wani wuri mai cike da ni’ima zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali ga kuma girmama na gaba, tana girmama Babana nima ina girmamata, tana kyautata min nima ina kula mata da danta. Gabadaya sai muka zamo muna son junanmu sosai.

Rannan aka wayi gari Safara tana yin mashasshara da mura, ban kai gane kan komai ba, saboda ban taba kawowa raina cewar wani abu zai iya faruwa ba, na dai ga Babana yana ta kaiwa da kawowa cikin wani iri yanayi na tsananin farin ciki, bai iya zama a runfarshi ya wuni kamar yadda ya saba, sai ya dawo gida dubata.

Wani lokaci sau daya wani ma har sau biyu in zai shigo kuma bai shigowa hannu haka sai yazo da wani abinda zai miko min ya ce “Karbi ki wanke muku.” In ce mishi To. In wanke in kawo mata ita kuma sai ta ce mun to dibi naki mana, in ce mata to in diba ta ce min kara in naga zan kara in kara in kuwa ya ishe ni in ce ya ishe ni.

Anti Safara da kanta ne ta gaji ta ce min ciki ne da ita saboda Iuran da tayi ta gane ban gane ba, mamaki gami da farin ciki suka taran mun, har ta gane abinda nake ciki. Mamakin me kike yi haka? Kin yi zaton ba zai kara haihuwa ba ne? Na ce, “Eh, to ai na gane kamar ya girma.”

Ta sake wani murmushin tare da fadin “Don ya haifi Hadiza sai ya tsufa ko kuwa dai dun kin ji matarshi tana yi mishi sharin bai tabuka komai? Shira nayi ban yi magana ba, don kuwa naga kamar ta wuce sanina.

<< Halin Rayuwa 42Halin Rayuwa 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×