Na dai san kawai ba karamin farin ciki nayi ba, saboda ganin da nayi nima zan samu kani ko kanwa, in musu nima irin abinda Yaya Dijah take yi min na kulawa da tausayawa.
Muna cikin wannan halin sai ga Baba Lantana tana shigowa da kayanta kwararam-kwararam tana ajiye su a tsakar gida, tana komawa tana shigowa da wasu. Ta rame tayi baki tanfar wacce ta tashi daga jinya mai tsanani.
Yaya haka kuma naga an shigar min daki? Wannan wane irin neman magana ne? ba sakina aka yi ba, ba komai ba sai kuma kawai daga na fita. . .