Skip to content
Part 45 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ina yin wannan tunanin na sake rushewa da wani sabon  kukan na nadama da bakin ciki. Isyaku ya shigo da sauri. Ga mota Anti na samo.” Ya wuce cikin dakin ya gaya musu. Babana bai iya takowa da kafafunshi ya fito ba, saboda karfi ya tafi sai da aka rirriko shi aka fito da shi muna isa asibiti aka ba mu gado.

Dama kuma shi kwastoman asibitin ne, fayil dinshi aka dauko aka dora bayani akan wanda yake ciki.

Mun kwana muka wuni a asibiti babu alama na samun sauki a tare da Babana, hankalinmu ya kai matuka wajen tashi, har gara nima akan Yaya Dija.

In ban da kuka babu abinda take yi, ni na tayar mishi da ciwon. Na ce, A’a Yaya Dijah, dama bai da wata lafiya, ba ki ji bayanin da Anti Safara take fada ba, na cewar ya dade ba ya bacci da daddare.

A’a amna ai bai tsananta ba sai bayan da nayi mishi maganar duk kalaman da nake gayawa Yaya Dijah bai sa ta samu nutsuwa a tare da ita ba.

Likitoci ne suka yi ta zuwa duba jikin Babana, kusan duk wanda yazo duba shin kume ya kan tafi ne a yanayi na tausayawa da fadin kai lalle Mallam Habu yana jin jiki, Ubangiii yasa kaffara ne.

Wai kuma a wannan lokacin ne da ake cikin wannan al’amarin naji Baba Lantana tana yiwa wata mata da in banda a zuwanmu asibiti ban yi zaton ta taba ganinta ba tadin Baban da al’amarinsu.

Ai ni don dai kar a ce ban zo ba ne kawai amma in ba haka ba ai ko mutuwa yayi bani da wata asara mutumin da yake daukan girkinka yana kaiwa kishiyarka kana ji kana gani ba ka da yadda za ka yi.

Yaje yana yin abin nan da ita. Ni kam ai alhakina ne ya kama shi yanzu ba sai suje suyi ba in gani? Kin ga tun kafin yayi auren nashi sai ya yi wata biyu wata uku ba kula ni ba, a hakan…

Ganina da suka yi ya katse hirar tasu ganin da nayi in sallami Baba Lantana in ce ta koma gida ita kadai ba zai zamo mai sauki ba, zai kuma kara bayyanar da rashin adalcinmu mu da Babanmu da ke fama da kanshi.

Wanda ita take kokarin baiyanawa koya ya zama sheda akai, bisa haka sai na hada ta ita da Anti Safara nayi musu magana akan su koma gida wanda da kyar suka yarda hakan.

In na tsaya cewa mun shiga wani hali ni da Yaya Dijah dama duk wani, wanda yake tare da mu a tausayawa to na tsaya bata bakina kawai nake yi.

Ina zaune kan kujerar roba ina tashe da Babana bayan tafiyar Yaya Dijah da mijinta, in banda kuka babu abinda nake yi na roke ka ka yafe min abinda nayi maka.

Baba abinda kawai nake iya fadi kenan ban ji lokacin da ya shigo ba saboda shagalar da nayi da abinda ke gabana sai ganinshi kawai nayi a tsaya ta daya gefen kusa da Babana.

Na daga ido na kalle shi Mubarak ne yana cikin natsuwa mai yawa yanayin da ke fuskarshi ce ta kara bayyanar da hakan.

“Ubangiji ya baka lafiya Baba, yasa kaffara ce. Shi ciwo ai rangwame ne, domin kaffara ce ga zunubai sannan jikin naka ma da sauki ba haka nayi zaton ganinka ba.”

Babana ya dan daga ido ya kalle shi saboda jin kalamin nashi, ya sake yi mishi sannu kafin ya sake daidaita tsayuwarshi, ya karanto addu’ar da ake yi wa mara lafiya.

Kafin yayi mishi sallama ya juya da nufin tafiya. To zo mana, ban iya yi mishi musu ba duk da mun dade kwarai ba mu ga juna ba ban da haka ma mun dade da fita hanyar juna.

Tun bayan abinda ya faru a tsakaninmu, sai muka shiga kiyayyar juna, ai ba nisa za ki yi ba, ya gaya min hakan don kara karfafa min in zo din.

Ke haka ake yin jinya ne? Nayi maza na kalle shi don in ji ta inda kuskuren nawa yake in gyara, kin tasa shi a gaba sai kuka ki ke yi, kina rokonshi gafara?

To a kan me ki ke yin hakan, ki, kara kashe mishi jiki ko ki kara-tsoratar da shi, ki karya mishi zuciya?

Shi majinyaci karfafa shi ake yi da kalamai na karfafa zuciya, ba yi tayi mishi kuka ba, shi ciwo ma da kike ganinshi be shi ne mutuwa ba fa.

An yi yafi a kirga mai laifiya ya mutu ya bar mara lafiya a kwance, kin gane? Nayi maza nace mishi eh.

Yanzu ke menene damuwarki da kike wannan kukan? Ban iya boye mishi ba ko in ce zanja mishi aji saboda halin da nake ciki, sai kawai na gaya mishi Babana bai da lafiya.

Gashi an kawo mu wurin da kowa ya zo ya ganmu sai ya ce uh’ uh hh lalle Mallam Habu yana jin jikı, a dakin da yake din ma na gobe da nisa ne kusan kullum sai an yi mutuwa a dakin dazu ma an yi wata mutuwar.

A hankali ya ce min, to kiyi hakuri ba ni in yi magana a canza muku dakin a kaiku inda za ki dan samu natsuwa shima Baban ya samu kulawa ta musanmman.

Koma wajen shi ina zuwa, ban ce mishi komai ba na tashi na tafi na dawo na samu Babana a yanayi na canji.

Nan take na tuna da addu’ar da Mubarak yayi mishi wacce na taba ganin bayanin da Manzon rahama yayi a kanta cewar duk sanda mai duba mara lafiya ya karantawa mara lafiya ita, Ubangiji zai saukar mishi da wani rangwame a halin da yake ciki, ko da kuwa cutar ta ajali ce. Nayi maza na matsa kusa da shi.

“Sannu Baba.”

Ya amsa a hankali “Sannu Yachuwuna, kina ta wahala da ni, Ubangiji ya yi muku albarka.”

Na dauko kofi na tsiyayo kunun gyada na zauna kusa da shi ina gauraya kunun da cokali don ya yi sanyi. “Bari in kurkure maka baki ka dan sha kunu Baba, ka dade ba ka ci komai ba.” Ya dan sha kunun kadan kafin ya daina karba nima na kyale shi ban matsa ba tunda dai ya dan sha. Na gyara zama a kan kujerar da nake zama tare da jingina a jikin gadon nashi ban san yanda aka yi ba, sai ji kawai nayi ana tashina.

Nayi maza na bude idona da gaske ashe bacci nayi, ga dukkan alamu kuma yayi nauyi, don na dan ji canji a tare da ni.

Na kalli Nos din da ta tashenin bisa zaton ko lokacin shan maganinshi ne yazo, sai naji ta ce min “Bari mu canza muku dakin ko?”

Nayi maza na kalleta duk da bayanin da Mubarak yayi min akan canjin dakin ban dauka da sauri ne haka ba.

Yayanki ya ce a maida Baba privater ward. ” Na ce mata To. Aka dauke mu aka maida mu private ward.

Mu kadai ne a wurin ga tsafta ga kulawa ta musamman sai dai maimakon saukin da Babana ya dan samu ya dore sai kuma jikinya: kara táshi, kasancewar likitoci baba tsinkewa a wurin sai suka yi ta kai kawo suna bincike kan al’amarin nashi, ina daga gefe ina kallonsu cikin natsuwa yayin da zuciyata take ta faman karanto addu’o’i iri-iri, kafin gari yawaye har an canza mishi magungunan da yake sha gabadaya.

Ganin haka ne ya sani matsawa kusa da shi sosai lokacin da wani lokaci ya sake shigowa don duba yanayin jikin nashi da safe, sannu da aiki doctor. Ya juyo ya kalleni, yauwa sannu ko? Ya ya jikin nashi? Na yi màza nace da sauki, yanayin da na gani a tare da shi ya karamin kumarin yi mishi tambayar da nake son yi mishi, Dr. An gane wani abu ne a tare da shi da yasa aka canza mishi magu agunan nan? Sai dai ya daga ido ya kalleni kafin ya maida kallonshi ga aune-aunen da yake yi, mara lafiyan mene ne dinki? Na yi maza na ce mishi, babana ne mahaifi, to me za ki yi in kin sani? A hankali na ce babu komai, nayi shiru ban sake ce mishi komai ba, ya ci gaba da abinda yake yi har sai da ya gama zai fita sai ya sake kallona ya ce min, me sunanki, na ce mishi Maryam, har ya yi kamar zai juya ya tafi sai naji ya ce min, menene aikin zuciya a jiki? Cikin nutsuwa na ce mishi harba jini zuwa sassan jiki, to daya ko biyu daga cikin jijiyoyin da sukeyi mishi wannan aikin ne ya samu matsala. Jikina ya yi sanyi sosai da jin bayanin nashi amma da yace min kin gane? Sai na yi karfin halin ce mishi eh kamar in sake yi mishi wata tambayar sai naga to kar ya ce na dameshi don haka na hakura nace mishi, na gode, ban san tunanin da ya yi ba wanda ya sashi ci gaba da yi min bayani, bangaren hagu na zuciyarshi ne ta samu matsala har ya dan kumbura kadan saboda jjiyoyin wurin basa aiki sosai shi yasa numfashi yake yi mishi wahala.

Bayanin da ya yi min ya sani tambayar shi, to yanzu menene abin yi Dr? Za mu yi mishi aiki nę mu gyara Jjiyoyin bai gama yi min bayanin ba sai ga Mubarak ya shigo duk da sanin likita ne ko kallonshi bai yi ba balle ya ce bari ya gaisheshi na juyo da kallona gareshi da nufi gaisheshi saboda mutuncin da nake ganin yayi min na kulawar da nake -ganin ya nuna a kan rashin lafiyar babana, wani irin lalataccen kallo naga ya yi min, jikina ya kara yin sanyi cikin zuciyata ina tunanin laifin me nayi mishi, sai kawai na ji ya ce min, shi ma wannan din saurayinki ne? Gabana ya yi mummunan faduwa nan take kuma na ji mummunan bacin rai a zuciyata, wacce irin mummunan magana ce wannan, ina fama da jikin babana ya kalleni ya ce, wai ina samartakan, me ya maidani? Nayi maza na kawar da maganar tashi daga cikin zuciyata na dai kudurawa raina kamewa in daure mishi fuska sosai watakila don yaga na dan sakar mishi ne yasa yake so ya yi min wulakanci irin wanda ya saba.

Yaya Ibrahim ya iso tare da yaya Dija kamar yadda suka saba yi kullum ta zo ta tayani mu yi mishi abinda ya dace sai su tafi sai kuma ta gama abinda zatayi sai ta zo mana da abincin rana daga gida kuma Anti Safana take zuwa mana da kunun gyada da baba yake sha sai da daddare Yakumbo Halima ta kawo mana abincin dare ita kam Baba Lantana ko tazo da wani abu bana yarda ta baiwa babana saboda na riga na jita tana fadin alhakinta ne ya kamashi banda wannan ma na ji ta tana fadin’ ko ya mutu bata da asara, ashe Alhaji Mubarak ya zo? Nayi shiru ban amsa mata ba to me ya sa kika yarda ya dawo da mu nan? Ban tsaya yi mata wani bayani ba na ce mata ki yi hakuri mu ne zamu biya, bata sake yin maganar ba sai ta tambayeni, to yaya kuka kwana da jikin nashi? Ban boye mata ba sai nayi mata gaba daya bayanin da likita ya yi min, dama ana yin irin wannan aikin ne? Ta yi min tambayar cikin wani irin yanayi, na ce nima ban sani ba, tana jinn a ce ban sani ba ta soma kuka, ban iya bata hakuri ba kukan nima na shiga yí muka hadu muka yi sai da muka gaji muka yi shiru don kanmu.

A sallameshi kawai, nayi maza na kalleta a sallameshi” yaya Dija mu yi yaya da shi da wannan numfashi nashi? Ai ba gida zamu maidashi ba wani asibitin zamu sake mishi in da za a bashi magani ya ji sauki ba tare da an yi mishi aiki ba, kin taba ganin wanda aka yiwa irii wannan aikin dą suka ce za su yi mishi ná gyara jijiyoyin zuciya? Nayi maza na ce mata uh-uh ta ce to.

Gaba daya muka sake tsundurma cikin wani hali na kunci da damuwa. Mubarak ya sake dawowa shi da abokinshi Amiru kulawarshi da tsayawarshi kan al’amarin babana abin sha’awa ne don kuwa gabadaya ma’aikatan wurin sun dauka shima dan babana ne komái yake yi baya sauraron kowa duk abinda aka ce za a yi sai ya ce a yi sau biyu ina zuwa wajen sayen maganin da aka rubuta sai su ce kudinku da kuka ajiye bai kare ba na kuma san shi ne ya ajiye kudin amma a kame kwarai nake da shi in ba shi ne ya tambayeni wani abu ba bana tanka mishi, shima kuma ba sosai yake shiga harkar tawa ba sai ta kama ina dai kaffa-kaffa da shi saboda na riga na sanshi na kuma kara ganeshi shi mutum ne mai iya wulakanci a ko ina kuma a kuma ko da yaushe a shirye yake ya yi min in ba haka ba banga dalilin da zaisa ya kalleni a halin da nake ciki na rashin lafiyar babana ya ce wai a asibitin ma samari nake yi.

Cikin natsuwa da girmamawa na gaida Amiru, yaya mai jikin? Na ce mishi da sauki, ashe aiki za a yi mishi ko? Na dan yi jim kadan cikin tunani kafin na ce mishi, anya? Anya wane iri? Ya yi min tambayar cikin wani irin yanayi na tsarguwa mai yawa, na sunkuyar da kaina saboda yanayin da yake kallcna a ciki sai naji ya ci gaba da yin magana, ba yanzu muka fito daga wurin likitocin da za su yi aikin ba ni da Alhaji Ahmad? Ai ya riga ya gama maganar da su har ya yi setting din bill din da suka bayar baki san komai bane a kai? Ban iya cewa komai in banda sa hannun da nayi na soma share hawayen da suka soma zubo min.

Ban sani ba ko ganin hawayen nawa ne ya sashi saurin juyawa wajen Mubarak din, kai baka yi mata bayanin komai ne? Ya ya za ka tsaya kana yiwa mahaifinta aiki irin wannan ba tare da ka yi shawara da ita ba? Koma me ke tsakaninka da ita tunda dai ka hadiycshi ka zo ai sai ka bar komai ka fuskanci maganar rashin lafiyar kawai in ya koma gida sai ku dora daga inda kuka tsaya.

Har a mu’amalar da take yi da samari sai in yi hakan dai ta? Gabana ya fadi saboda jin mu’amala da samarin da ya ke ikirari, ba sha’anin gabanta take yi ba, ba sai in kyaleta nima in yi nawa ba?

Wani irin mummunan tsaki Amiru ya ja kafin ya ce mishi, kai fa halinka kenan a ko ina a ko wane hali a kuma kowane irin yanayi wai kana iya yin kishi. Ran Mubarak ya soma baci da jin maganar tashi a fusace ya soma ce mishi, a’a kai Amru kar kaja ta raina ni fa wane irin magana ne wannan? Ni kishi nakeyi a kanta? Yanzu kai baka ga irin abinda suke yi ita da wannan likitan da muka samu a nan ba tana yi mishi magana tana wani yauki tana wani kakkashe mishi murya shi kuma sai zirga-zirga yake yi yana kaiwa da kawowa don ya gane abinda take nufi.

Amiru ya ja tsaki kafin ya saki wani lallausan murmushi ya ce, ban ga komai ba Alhaji kai ne kaga hakan ni dai na san a halin da Maryam take ciki a yanzu in ma kaga tayi wani abu makamancin hakan to sai dai tayi don ya zama dabi’arta amma ba don ta burge wani ba don haka kayi hakuri ka rage sa mata ido ku fuskanci juna kai dai ta don ku fi jin dadin mu’amala a tsakaninku.

<< Halin Rayuwa 44Halin Rayuwa 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×