Skip to content
Part 46 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Kai kam ai dama baka son laifinta ban taba kawo maka zancenta kan abinda take yi min ka goyi bayana ba sai ka ce wai sa ido nane ya yi yawa.

Bai sake tanka mishi ba sai ya juyo gareni, ke rabu da shi kin ji Maryam daina kuka ki share hawayenki kin ji? Ni zan tafi. Nayi naza ma share hawayen nawa kamar yadda ya bani umarni na kuma yi mishi godiya, Mubarak yabi bayanshi nayi maza na koma wurin babana. Ba a wani dade da yin hakan ba sai na hango shi yana dawowa alamar rakiyar ba mai yawa ya yi mishi ba, don haka na yi maza na sake fitowa daga dakin na tare shi a dan dogon falon da kofofin dakunan ke ciki a hankali cikin natsuwa ta yanda babu mai jin abinda nake fada na ce mishi, ko zaka daina zuwa ne don kar mu zo muna batawa juna rai? A yanayin da nayi mishi maganar a irin shi ya bani amsa, ranki ya zo yana baci dai amma ni me zai bata min rai? Ai ina ganin somi somin hakan na daga wurinki zan yi maza in yi maganin abin don gaba daya zan hana ki zuwa asibitin kamar yadda kika hana matan gidanku zuwa. Gabana ya yi mummunan faduwa na yi maza na daga ido don in kalleshi saboda mamakin maganar tashi in ga irin karfin halin da ke gareshi da zai yi min irin wannan hukuncin alhalin ni da mahaifina ne, wani irin lalataccen kallo naga yana yi min, kina nufin kinfi kowa kusa da shi ne ko kinfi kowa sonshi ne? Ki yarda in ga wani abinda bai yi min ba ki gani? In gani in zan hanaki zuwan ki zo ki ga wulakancin da zan yi miki baki iya rashin kunya ba? Kar ki dauka kuma wai kishinki nake yi kamar yanda Amiru yake fada ko daya.

Rasa abinda zance mishi nayi na soma yi mishi kuka saboda sanin da nayi cewar zai iya aikata abinda ya ce din. Sakarya kawai sokuwa wacce ko ciwon kanta bata sani ba sai rashin kunyar tsiya.

Ya wuceni zai tafi nayi maza na ce mishi, to bana son aikin da kake son sawa a yi mishi. Maimakon ya ce min to kamar yadda na yi zaton ji daga gareshi sai naji ya ce min to ai bake ke da shi ba yana kuma da bakinshi don a cikin hankalinshi yake. Ya wuceni ya shiga ciki na share hawayena nabi bayanshi a kan kujerar da nake zama na sameshi yana tashe da babana da ke kwance yana fama da kanshi.

Sannu Baba ya soma yi mishi gaisuwar cikin natsuwa, da yardar Ubangiji zaka samu saukin wahalar numfashin nan nan ba da dadewa ba tunda likitoci sun gano kan al’amarin sun kuma yi bayani da cewar dan karamin abu ne ya sameka don haka za su yi aiki su gyarashi in aka gano kan ciwo Baba to ai shi kenan magana ta kare sai kawai a yi addu’a Ubangiji yasa a dace da abinda za a yi don haka nake so in rokeka ka yi hakuri ka kuma kwantar da hankalinka kar ka ce zaka sanyawa ranka wani damuwa don kar jininka ya zo ya hau aikin da za a yin ba wani mai wahala bane. Ya zubawa Babana ido tare da sauraron abinda zai ce, yayin da nima na yi hakan tare da fatan in ji ya ce baya son aikin tunda mu kam ni da yaya Dija ba ma so gashi kuma ba shawara da mu ya yi ba kafin ya zartar da hukuncin sai kawai na ji babana ya ce mishi na gode Ubangiji ya yi maka albarka. Ya ce amin, ya mike ya fita ba tare da ya nuna alamar ya san da tsayuwata a wurin ba.

Wulakanci irin na Mubarak yawa ne da shi ga dukkan alamu kuma watakila shima ya san shi din gwani ne tunda shi da kanshi ma yana barazanar zai yi shi don haka sai nà kudurawa raina in ma za a yiwa babana aikin to ba shi ne zai dauki nauyin abinda za a kashe ba kamar yadda na lura yake nufin yi yan kadarorina zan sayar da na samu na tara da kudin da nake samu a sana’ata ta dinki zan sayar in baiwa yaya Dija kudin ta hada da abinda ke hannunta ta mikawa mijinta ya hada tunda naga alamar aikin zai ci kudi masu yawa.

Yaya Dija ta iso na bata labarin duka binda ake ciki da wanda ya faru tsakanina da Mubarak, fada ta rufeni da shi a kan wai ai ni nake jawoshi ta hanyar sakar mishi fuskar da nakeyi mishi amma in ba haka ina ruwanshi da mu da har zaizo yana yi mana irin wannan shisshigin?

Aje ya ji da harkokinshi ya barmu mu ma mu yi namu sannan ta riga ta gaya min bata son aikin ba za a yi ba ban ce mata komai ba har ta yi ta gama har ma ta tafi iyaka dai kawai addu’a nake yi da kara gayawa Ubangiji halin da mahaifina yake ciki wanda kuma nasan ya fini sani.

Ana idar da sallar magariba sai ga Amir ya sake zuwa dubamu na ji, dadin ganinshi saboda ganin shi kadai ne ya zo ya duba babana ya juya zai fita nayi amfani da baccin da ya tarar baban nawa yana yi na biyoshi waje muka tsaya a dan tsaye a wajen da muka tsaya da Mubarak.

Cikin natsuwa na soma yi mishi magana wanda roko ne na ya taimakeni ya gayawa Mubarak cewar ya fita hanyar jinyar da babana yakeyi ya daina zuwa asibitin bana kuma son duk wani taimako nashi.

Wani dan siririn murmushi ya yi mai hade da ajiyar zuciya a hankali cikin natsuwa ya tambayeni, wai ni in sani mana me Alhaji Ahmad yake yi miki ne? Ni dai nasan tun kina yar kankanuwarki yake tare da ke tun baki isa komai ba tun baki ma san ke wacece ba, amma har zuwa yau din nan bai samu matsayin da ya dace dashi ba a wurinki.

Nayi maza na kalli Amiru cikin ntusuwa saboda jin kalaman nashi kan in san abinda zan budi baki in gaya mishi sai naji ya ci gaba da cewa, saboda kawai kin san yana sonki saboda kin gane ba zai iya fita harkar ki baa duk motsin da za ki yi idonshi yana kanki iyayenshi sun bashi aure amma kin hanashi natsuwa da zai zauna lafiya da iyalinshi lafiya ya iya jaruntaka kan komai amman in akan ki ne sokancinshi yawa ne da shi, ni da kaina na sha bashi shawara kamar yadda nasha yi mishi gori a kan ki wai dan ya yi zuciya ya kawar da kai daga gareki amma ya kasa ya yi aike gidanku ace an hanashi yafi a kirga kullum kuma ya zo kusa da ke sai kin san abinda kika yi kika bata mishi rai amma yana biye ba zan ce mishi ya fita harkarku ya daina zuwa ba don ko na gaya mishi ba ji zaiyi ba, don haka in ya zo ke da kanki ki kara gaya mishi in ya ji shi kenan in kuma bai ji ba sai ya yi tayi na dai san har da alhakin abubuwan da yake yiwa matarshi uwar ‘ya’yanshi da take matukar sonshi cikin wadannan abubuwan da kike yi mishi. Ya wuceni ya yi tafiyarshi ba tare da ya tsaya ko da don yi min sallama ne ba.

Na koma dakin da babana yake kwance na jawo kujerar robar da na saba zama a kanta cikin natsuwa na zauna zuciyata cike da tunanin kalaman da Amiru ya yi min nice mai yawan batawa Mubarak ko shi ne mai yawan bata min a sanina kullum a cikin kaffa-kaffa da shi nake matukar yana wuri bana sakewa in yi abinda na ke so kai ko baya nan bana iya saba dokarshi saboda tsoro ko gudun bacin ranshi da nake yi amma a hakan bana tsira sai ya san abinda ya ce na yi wanda ya yi min wani abinda zan raina kaina ko in zubar da hawaye a dalilinshi amma ka ji irin kalaman da abokin shi yakeyi min to babu laifi.

Har dare har washegari Mubarak bai dawo ba, maimakon in sake in ji dadin rashin ganin nashi sai na zama ko iya amsa gaisuwar likitan nan bana yi saboda tsoron kar mu na cikin gaisawar ya shigo ya ganmu ya ce ba a yanayin da nake amsa gaisuwar sauran mutane nake amsa mishi ba.

Wunin ranar nan har dare bai shigo ba sai wajen karfe goman dare a lokacin nan kuwa babana yana cikin wani hali da ya yi dalilin da sai da naje na kirawo likito ci saboda kei kawo mai tsananin da numfashin nashi ke yi.

A hankali ya turo kofar ya shigo bai nufi wajensu don gani ko jin abinda ke faruwa ba wurina ya zo ya tsaya bai yi wata magana ba har sukayi abinda za su yi suka gama suka tafi, da sauri muka isa inda baban yaku kwance don ganin halin da yake ciki gaba daya ya jike da gumi cikin zuciyata na ce ya wahala, hawaye suka sake zuba daga idanuwa na sharr, bance mishi komai ba haka nan shima Mubarak din ya juya ya fita ya barmu a dakin, na kai guiwowina kasa na durkusa yayin da na kwantar da kama a gefen gadon nashi hawaye suna ta zubo min, jimawa kadan na sake dagowa na kalleshi saboda yanayin numfashin nashi da naji ya sauya bacci ne ya daukeshi na dan ji dadi kadan saboda tunanin yanayin da zai sake farkawa a ciki.

A hankali naji an turo kofar an shigo na waiwaya don ganin wanda ya shigo Mubarak na gani cikin zuciyata na ce, ashe ba tafiya yayi ba, to dawo daga nan mana tunda ya samu ya runtsa. Ban yi musu ba na koma daga nan din da yace na zauna, a hankali ya mikomin ledar da ya shigo da ita, bude ki cinye abinda ke ciki ba hikima bane don kana jinyar mara lafiya ka yi ta zama da yunwa in ka yanke jiki ka fadi sai jinyar ta zama ta mutum biyu maimakon da ana yin na mutum daya.

Na sa hannu na karba ina ci shi kuma yana yi min nasiha shi mutum hakuri yakeyi ya koyi jarumtaka, idan al’amari irin wannan ya sameshi ba ya yi ta kuka yana kin cin abinci ba kinga irin ramar da kikayi kuwa? Na maida ledar na ajiye saboda koshin da nayi na bude robar ruwa ina sha, sai da yaga itama na maida ita na ajiye sannan ya tambayeni, amma yanzu ai kin gane ya zama dole mu tsaya wajen ganin an yiwa baba aikin nan ko?

Na yi maza na daga ido na kalleshi saboda jin dolen da ya ambata sai naji ya ce min, to zai yiwu ne mu barshi a cikin wannan halin? Kin ga haka zai yíwu? Sannan ba zai yiwu a cireshi daga nan a kaishi wani wuri ba domin nan teaching hospital ne. Kalamai da bayanai masu yawa yayi min a natse har dai na bude baki na ce mishi, to ai yaya Dija ma ba ta son aikin.

A hankali ya ce min to ai baban naki ne Maryam kin fita iko da shi, ke kika fi kowa shan wahalarshi in yana cikin rashin lafiya kamar kina ciki ne dubi yanda kika zama a dan tsakankanin nan, kece kuma baki da kowa sai shi in aka rasa shi kinfi kowa rashi ita tana aure tana da mijinta da iyalinta ga ya’yanta ke ce baki da kowa sai shi, Ina jin ya fadi hakan na soma kuka saboda yarda da zuciyata tayi cewar ni ce bani da kowa sai babana in aka rasashi ni nafi kowa rashi. Kukan da nake yi bai hanashi ci gaba da yi min magana ba, ke madadin da namiji ce a wurin shi duk kuma abinda da namiji ke yiwa uban a kulawa da taimakawa shi kikeyi mishi ke kinfi wani da namijin ma jaruntaka don haka tsaya kawai a matsayin da ya dace da ke ki taimaki mahaifinki ya samu lafiya in kuma aikin ya zo da akasi to kar ki ji zafin kanki ki dauka kawai kaddarar kenan kin kuma rasashi ne a kokarin da kikeyi na nema mishi lafiya.

Kalaman Mubarak sukayi matukar shigata ta yadda har naji na yarda da magamar yin aikin nan take kuma sai naji zuciyata ta daina tsoro, addu’a kawai nake yi a yi aikin a sa’a.

Da safe yaya Dija tana isowa ita da mijinta a gabanshi nayi mata maganar ina ganin mu bar neman sallama don komawa wani wuri mu tsaya a nan a yi msihi aikin kawai don ba zai yiwu ya yi ta zama a cikin wahala irin wannan ba.

Tayi maza ta ce min, a’a ba zai yiwu don ba zai yiwu mu yi abinda zaum sanyashi cikin hatsari ba ban taba ganin inda akayi irin wannan aikin ba ba kuma zai yiwu a fara a kanshi ba.

Ai hatsari bai wuce ciwo ba yaya Dija gardama mai tsanani ta shiga tsakaninmu, saboda taja ta tsaya a kan bata son aikin tunda itace babba kuma itace zata fadi yadda za a yi, nace mata a’a ni ya kamata in fada saboda nice tare da shi a wuri faya ni nafi ki tsoron rasashi saboda nasan zan fiki maraicinshi ni ce ni kadai bani da Uwa bani da… ban iya karasawa ba kuka na soma yi mata.

Yaya Ibrahim ya kalleni cikin natsuwa ya ce min, kece mai fadin abinda za a yi mishi Maryam tunda kina so a yi mishi aikin za a yi ké Dija ki yi akan wannan ra’ayinta za a yi.

Karo na farko a rayuwarmu ai da yaye Dija da jayaiya irin wannan ta shiga tsakaninamu bata taba cewa ga yadda zaa yi nace mata a’a ba, hankalina ya yi matukar tashi da abinda ya farun musamman da na ganta tana ta kuka saboda ta riga taki aikin da za a yin sai fin karfinta kawai akayi bata yarda ta zauna ba ma a  asibitin kamar yadda kullum take yi kama hanya tayi ta tafi,

To in aikin nan bai yi nasara ba me cewa yaya Dija? Tambayar da na yiwa Mubarak kenan a lokacin da ya zo don jin yanda mukayi da ita, bata fuska ya yi sosai kafin ya ce min, to in kama suka yi nasarar fa? Ke ba za ki yi addu’ar yin nasara ba sai ki zauna kina barin zaciyarki tana raya miki munanan abubuwa? Da wani wanda yake rike da rayuwar wani ne ko kuwa da wata hikima ne da za ta sa mutum ya tsallake wa’adinshi? Da irin wadannan kalaman na yarda na sanya hannu a kan takardar aikin da za a yiwa babana.

Cikin tsananin tsoro da fargaba ina gama ganya hannun na koma gefe ina kuka yana rarrashina.

<< Halin Rayuwa 45Halin Rayuwa 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×