Skip to content
Part 47 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Yadda Babana ya wuni karkashin dokar lilkita na kar ya ci komai ko da kuwa ruwa ne, haka nima na wuni ban iya sanya komai a bakin nawa ba, gashi babu yaya Dija sai Inna, yarta babbar da dama take zuwa tayani zama, in ita bata zo ba saboda aiki ko wani aikin sai dare suka zo ita da yaya Ibrahim idanuwanta a kumbure alamar tayi kuka har ta gaji ban iya ce mata komai ba na daga hannu ko bayanin likita na cewar za a shigar da shi Dtiyata da misalin karfe goma da rabi na dare ba.

HASBUNALLAHU WA NI’IMAR WAKL’ abinda kawai nake karantowa kenan a bakina da kuma zuciyata suka gama abinda sukeyi suka tas.

Wajen karfe taran dare Mubarak ya iso babu abinda bai zo min da shi ba wanda ya san ina so amma ban iya cin komai ba saboda tashin hankali sai kaduwa nakeyi tamkar wacce sanyin hunturu ke kadata.

Ana cikin haka har lokacin ya iso gadon likita naga an fara kawowa cikina ya bada sautin kulululu ban iya daurewa ba sai da na ruga da gudu na shiga bandaki kafin in fito na samu har an canza mishi kayan jikinshi da rigar likiten na rasa yadda zenyi da raina na rinka jin tamkar ince na fasa abar yi mishi aikin kawai, shi da kanshi babana za gane ya shiga wani hali saboda jinshi da nayi yana cewa, Mubarak na gode Ubangiji ya yi muku albarka in har ban fito ba kuma to ka rike min uwata amana. Maimakon Mubarak ya ce misbi to ko ya gaya mishi wata magana da zata yi mishi dadi sai kawai naji ya ce mishi, a’a baba ni kar kace ka bar min amanar Mero don ba zan karba ba in zaka bani aurenta kawai ka bani ga mutane can a wancan dakin inka yarda in yi hanazarin kiran mutum biyu kawai ko uku don su tayan shedawa.

Haushin Mubarak da takaicinshi suka kamani har a halin da babana yake ciki yana iya yi msihi musu da sauri na ce mishi, a’a baba daina cewa ka baiwa wani amanata ai lafiya zaka shiga ciki ka kuma fito lafiya babu abinda zai sameka sai alheri, kai në zaka fito ka ci gaba da kula da ni mu ci gaba da zamanmu babu abinda zai sameka sai alheri, babu abin da zai sameka sai alheri, nayi ta nanate fadin hakan tamkar dai shi ne abidna zai sa hakan ya zamo ya yiwu.

Ni da shi muka bi bayan gadon da ake tura Babana, babana yana ta salati ni kuma sai kuka nakeyi shi kanshi Mubarak ya shiga wani hali, watakila don ganin babu kowa a wurin daga ni sai shi saboda hatta su anti safara da na tuntubesu kan aikin basu bani goyo baya ba balle inji daiin gaya inusu cewar yau da daddare za a a yi, don haka babu wani wanda yake da cikakkiyar masaniya na abinda ake ciki.

Suna tafiya muna biye da su har muka kai inda aka tsaidamu shi kuma aka wuce da shi ciki.

Kwanciya nayi a kasa ina kuka, tashi-tashi ki gani?

Tashi ki zauna, kin taba ganin inda kuka ya yiwa wani amfani ko ya zama sanadin samun biyan bukatarshi? Addu’a ai itace ta kamace mu tashi ki zauna.

Da irin wadannan kalaman nashi ne na mike na zauna kan daya daga cikin kujerun da ke wurin shi, kuma ya fita ban san inda ya je ba jifa jifa dai yakan shigo ya zo ya sameni ya gaya min kalmomi na karfafa zuciya da kara tuna min muhimmancin tsayawata kan addu’a maimakon kuka ko yawaita damuwa ba zan iya tuna irin addu’o’in da nayi a ranar ba, fatana da burina da a yi nasara ne a fito da shi yana raye don in aka samu akasi kan hakan to ban san abinda zan cewa yaya Dija da sauran wadanda suke da hakki kan rayuwar tashi ba gaba daya

Saboda tsananin kidima da damuwa bana iya tantance dadewar da sukayi a ciki gaba daya in banda duk abinda ake yi a cikin duhun dare ne guda daya da nayi zaton anyi adadin kwanakin da basu kidayuwa saboda dadewarsu da na gani.

Mubarak ya sake shigowa ya sameni a inda ya barni a zaune.

Sannu Maryam, da kyar na iya buda bakina na ce mishi, yauwa saboda jin da nakeyi tamkar labban bakin nawa a manne suke, cikin yardar Ubangiji za a yi nasarar aikin da ake yiwa baba Ubangiji kuma zai yi miki sakaiya kan al’amuran rayuwarki gaba daya bance mishi komai ba ya nemi wuri ya zauna yana kallon agogo in dai komai ya tafi daidai ai sun kusa fito da shi.

Cikina ya sake bada wani sautin na kululu saboda jin da nayi ya ce in komai ya tafi daidai kenan in bai tafi daidai ba ma an kusa sanin abinda ake ciki kenan.

A haka muka ci gaba da zama a wurin babu mai cewa wani komai, idona yana kan agogo in banda tafiyar lokaci babu abinda nake dubawa, zuciyata kuwa tana ta karanto addu’o’i haka, a haka a irin wannan yanayin da awowi suka zama tamkar kwanaki a hakan kuma dai har muka kai lokacin da suka ambata na kammala aikin da za su yiwa baban nawa sai kuma gashi an fito da shi kwance a kan gadon babu wata alama ta motsi a tare da shi, muka sake biyo bayansu zuwa dakin da dama muka bari aka dorashi a kan gadonshi aka kwantar da shi, abu guda daya kawai da ya dan kwantar min da hankali shine tabbacin da naji suna ta baiwa Mubarak na anyi nasarar aikin da aka yi mishin.

Amma ban samu natsuwa a tare da ni ba har sai kwanaki biyu bayan nan da naga babana ya soma wattsakewa daga mummunar wahalar da ya sha har kuma gashi numfashin nashi ya daidaita saura ya samu karfin jikine kawai.

Mutane suka yi ta zuwa duba babana saboda jin labarin aikin da aka yi mishi kai kace ahi kadai ne mara lafiya a asibitin nan,  ina jin wani daga cikin yan kasuwar tumatirin nasu yana gayawa abokin tafiyar tashi,  kaga ja’irar yarinyar nan yar gidan Malam Habu mai tumatir,  kai wannan yarinya da jarumtaka take bata gajiya da hidimar mahaifinta kullum a cikin kai kawo da dawainiyarshi take shi yasa duk iya shegenta sonta yake yi.

A to ba dole ya sota ba Malam ko da na mijine ya ke irin hidimar da yarinyar nan take yi akan mahaifinta ai yaci a yaba mishi balle ita yara irin wadannan ai haka suke sunada halin tsiya da na arziki,  kai ba duka ba inji wani da bansan ko waye ba ita dai wannan anyi dacentane Ubangiji kuma zai saka mata ya shiryar da ita ya bata mijin da zai sota ya riketa duk da iya shegen nata.

Babana bai cika kwana biyar da yin aiki ba sai da kowa ya gamsu da aikin da ak yin ya kuma ce gwara da akayi hakan ciki kuwa harda yaya Dija.

Tun kwana biyu da aikin babana sanda ya soma dawowa cikin hayyacinshi Mubarak ya dauke kafa ya daina zuwa asibitin baya zuwa da daddare balle kuma da rana,  ko dama can kuwa mafi yawancin zuwan nashi kan  zamo cikin dare ne lokacin da zirga-zirgar dubiya tayi sauki in dai ba wani dalii mai karfi ne ya kame na yazo da ranar ba.

Rannan da safe ni da yaya Dija ne kawai a tara da shi bayan mun goggoge mishi jiki mun gyarashi mun tsabtace komai na dakin sai kamshi yake yi yaya Dija ce a kusa da shi tana bashi ruwan tataccen kabeji da karas yana sha a hankali yayin da ni kuma na gama tattara kayan wanke-wanken mu na mikawa Inna nace taje ta wanke sai kawai mukaji an turo kofar dakin a hankali tare da yin sallama, gaba daya muke amsa sallamar tare da maida hankalinmu wajen kofar.

Gabana yayi mummunar faduwa saboda ganin mai sallamar, Umma ce ko ince Umman Mubarak tare da Rumasa’u da Rukaiya, kadan ya rage in dibibice in rude saboda rabon da muyi gaba da gaba da su haka an dade ko ince tun daga ranar da abinda ya faru tsakanina da Mubarak na samuna da akayi a dakinshi da al’amuran da suka biyo baya wata mu’amala bata sake hadani da wani daga cikin mutanen gidan ba, wacce tayi dalilin haduwarmu a wuri daya kamar hakan ba dan gara-gara Rukaiya in ta kure mana a makaranta mukan gaisa saboda munyi karatu tare.

Sannu da zuwa Umma yaya Dija ce ta fara yi gaisuwar daidai tana mikawa Umman kujerar zama, na mika hannu don karbar yarinyar da take hannun Rumasa’u duk da yanayin dake fuskarta tamkar dai ace mu din ba wasa tare muke yi ba, gaba daya aurenta da Mubarak ya canza al’amuran dake tsakaninmu ni da ita kowa ya fi jin zafin wani oho?. Ko da yake dai nikam can cikin zuciyata na sani bana jin zafin Rumasa’u kamar yadda nake jin zafin Mubarak da wadanda suka sashi aurenta.

Gaba dayansu na bisu na gaishesu kamar yadda naga yaya Dija tayi, yaya jikin na malam? Yaya Dija ta sake amsawa Umma zancensu ni kuma na dawo da hankalina wajen sauraron abinda Rukaiya ke gaya min naga Hasiya jibirin shekaran jiya ta tabaye ni ke na gaya mata tace in gaisheki itama zata zo, nayi murmushi na ce mata ai jiya tazo nan ta kusa wuni muna zancenmu ban sake Juyawa na kaili Rumasa’u ba saboda bata bani fuskar da zan iya fuskantarta in kakalo wata naganar da zanyi da ita don haka na ci gaba da wasa da ‘yarta da kuma hira da Rukaiya, ko kadan dai banji dadin sammakon da sukayi mana ba an saukin abiıma sun zo sun samu babana da kuma dakin da muke ciki cikin tsabta.

Bayan tafiyarsu yaya Dija ta kalleni tayi murmushi ta ce, kai kishi babu kyau mata suna kokari, ban tanka mata ba balle zancen ya yi nisa na kalli Inna na ce mata, jeki ki yi mana wanke-wanke kin ji? Ta ce to ta tashi ta fita ba fa zuwansu bane ina jin Alhaji Mubarak ne ya turosu.

Na sake kin amsawa don kuwa ban san dalili ba sai naji bani da ra’ayi a kan zancen nasu.

Sati biyu da aikin babana aka sallatmo mu muka dawo gida bisa dokoki da aka jaddada mana binsu. Ranar wuni nayi ina aiken Inna gidajen mutanen da sukayi ta zirga-zirga suna ta dawainiya da mu irinsu Jumare gidan baba Hodije Yakubo Halina, Hasiya Jibrin, malamaina na Markas irin su Malama Basma da Hindu abokan karatuna na makarantar mu ta ilimi addini mai zurfi musamman wadanda mukayi aji daya da su wadanda har karo-karon kudi suka yi suka kawo min don taimakawa zumunci irin wanda mutane suka nuna mana a wannan. Lokacin babu abin da zamuce musu sai dai addu’ar Ubangiji ya sakawa kowwa da alherinsa amin summa amin.

Mun dawo gida da Babana a dalilin saukin da ya samu kowa murna yake yi muna farin ciki musamman da yake a yanzu yana da mata mai kula da tattali da kokari ganin asirin gidanta ya rufu sai dai kuma hakan bai hana hankalina da zuciyata tafiya wajen tunanin abinda ya hana Mubarek zuwa yiwa babana murnar dawowa gida ba rabonshi da zuwa asibiti tun kwana biyu ko uku da yin aikin bai sake takawa ba to yanzu kuma mun dawo gida ga mu ga shi ba zai shigo ya gaisheshi ya karasa ladanshi ba bayan duk irin hidima, dawainiya da ya yi da rashin lafiyar tashi, to ko dai matarshi ce ta hanashi zuwa? Tanbayar da ta zo cikin zuciyata kenan, nayi kokarin in kawar da hakan ta hanyar tambayar kaina anya Mubarak yana yiwa matarshi irin wannan tsoron kuwa? To amma me akayi mishi? Da dai naga damun kaina kawai zanyi sai nayi maza na cire wannan tunanin daga cikin zuciyata na maida hankalina kawai wajen lura da halin dà babana ke ciki ina kuma rama bacci da gajiyar zaman asibiti tunda muka dawo matarshi ke kula da shi ga anti Safina ga baba Lantana ba a je ko ina cikin kulawar ba na soma jin maganarshi daga dakin baba Lantanar yäna cewa uh’uh ba fa zan iya irin wadannan abubuwan ba a yanzu in kin ga da matsawa kawai jeki ni bani da wata damuwa a yanzu.

Mamakin babana ya kamani cikin zuciyata nace kar dai ace babana zai fara yin magana ne.

Ba a dauki wani lokaci ba baba Lantana ta fito da halayenta da akafi saninta da su na kin yin girki da sauransu saukin abin kawai anti Safana tana nan tana kuma tsaye kan al’amuran mijint adama ni kaina da take matukar ji da ni batama ko kiran sunana a yanzu wai sai Maman Baba wani irin ji da ni takeyi ban sani ba ko gani take tamkar don ita da abinda ke cikinta na yi jinyar Baban nawa.

Rannan da sassafe na idar da sallar asuba na shafa fatiha na shiga dakin anti Safara inda nasan ya kwanaa don in gaisheshi in kuma bashi magungunanshi da naki yarda wani ya bashi, yana shan magungunan muna yar hira magana kadan kadan.

Baba kana cin zaitun din an kuwa? Magani ne fa ba kadan ba. Kafin ya bani amsa sai kawai naji muryar yaya Ibrahim yana sallama tare da shigowa cikin gidan, shigo mana Ibrahim, baba ya yi mishi umarni don haka ya shiga har cikin falon.

Kan maganar zuwan mutumin nan ne likita na ce a kira min kai inji kayi binciken a kan nashi ne? Na mike na fita saboda ganewar da nayi maganar a kaina ne tunda na ji ana ambaton likita wato Dr. Bello wanda ya biy mu gida da kai kawo da hidimomi iri-iri.

Ni fa baba binciken da’nayi kan mutumin nan ba wani mai yawa banc saboda ga Alhaji Ahmad a kusa da mu wanda aka dade ana tare yaushe za a je ana bincike kan wani sabo kuma? Gabana ya fadi jin da nayi ya ambaci sunan Mubarak, babana yayi maza ya ce, Mubarak kuma? Cikin zuciya na ce, a to ai gara dai da ko tambayeshi.

Cikin natsuwa va ce mishi, eh baba i ni a wurina banga wani wanda ya fishi ba, babu ma wanda ya kaishi cancanta in dai har za a bada auren ne bisa cancanta da dacewa babu wanda ya fishi dadewa a cikin neman kullurn kuna a tsaye yake a kan al’amarinta ga zaman tare da makwabtakar dake tsakani, don haka in har ba shi ne ya ce bai da bukatar auren ba to babu wani dalili da zaisa mu je muna binciken shi likita, to yaushe ma muka sanshi?

<< Halin Rayuwa 46Halin Rayuwa 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×