Skip to content
Part 5 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Nayi maza na ce mata gashi nan saboda taimakon nata yazo min ne a daidai lokacin da nake bukatarshi.

Duk da taimakon da Jumare ta kawo min da aiken da Babah Sumaye tayi-tayi na ayi kaza kar ayi kaza abincin da muka girkan yawanshi ba kadan ba ne, dandanonshi kuma ba wani mai gamsarwa ba ne ko in da aiken nata da zuwan Jumaren wane irin kwaba zan yi? Oho.

Duk da min karbi girkin abincinmu Babana bai daina bada kayan miya a gidan Baba Hodijo ba babu kuma wani abinda ya canza a tsakani ni kam ma dai ban daina zuwa karban abincina ba ina shiga gidan Babah Sumaye zata ce min ga abinci can in za ki ci jeki ki diba in ce mata to dama kuma hakan take yi min.

Haka nan duk wani abu na kulawa da take yi min bai sauya ba, ina dawowa daga Makaranta wurinta nake fara zuwa in tube kayana in canza da wanda ke nan a wanke a goge in ci abinci in yi wanka in yi sallah in yi shirin tafiya Makarantar allo bayan na karbo cefane na kawo.

Zan iya cewa kwanon Babana ne kawai aka cire shi ne kuma mai cin abincin da nake kwabawa da sunan girki sai ko yaran da nake turawa a cikin gidan wadanda rasa uwata da nayi ya koya min lura da sa ido wajen sanin ‘ya’yan da ba su da uwa a dalilin suma mutuwa ta daukan musu ita kamar yadda ta daukan min tawa ko kuma a’a sakin uwar tasu aka yi aka bar su watse a tsakar gida.

Duk.munin abin da na girka Babana bai cewa komai, bayan sannu da kokari sai yayi bisimillah yayi komai uku yayi hamdala ya ce in kawar ko in nemi wadanda zan ba, in ce mishi to in je in kawo mishi ruwa.

Zuwan da nayi gidan Yaya Dijah ne na bata labarin dukkan abubuwan da suka faru har da bayanin da Babah Sumaye tayi ina ji, shiru yaya Dijan tayi cikin wani yanayi na nuna tsananin tausayi ta ce uh’uhummn, Baba ina jin tausayinshi in na tuna Inna na tuna halin da na samu kaina a ciki a dalilin rasata da muka yi.

Sai in tambayi kaina to shi kuma fa yaya yake ji? Ta dan yi shiru cikin wani irin nazari da tunani mai zurfi, jimawa kadan sai ta dago ta kalle ni idanuwanta sun kada sunyi jazur alamar suna shirin fara zubar da hawaye, sai ta ce min dama yayi auren kawai zata debe mishi kewa zai samu abokiyar mu’amallah zai kuma huta da cin wannan danyen abincin naki da ki ke kwabawa ba kya ci nayi maza na ce ina ci mana ai ba danyen ba ne kuma kullum ya ci zai yi min addu’a.

A wannan lokacin zan iya cewa bani da wata matsala ko kuma damuwa da ta wuce ta bani da uwa mahaifiya in ban da wannan ban rasa komai ba, ban nemi wani abu na rasa ba, Babana yana matukar sona yana kula da ni yana tattalina, komai nake so yi min yake yi duk wani abinda ya ba shi sha’awa saya min yake yi.

Fura da nono, kankana, gasasshen nama, wannan kadan ne kusan kulllum zai saya min sai in ni ce na ce ba zan ci ba. Babah Sumaye ma a tsaye take a kan al’amarina, kitso, wanki, kula da kai, tsaftace jiki, lura da tarbiya bata gaji ya min kan komai ba.

Ga dangin Innata da kusan kowane lokaci hankalinsu a kaina yake, don haka ina yawan tuna Innata ne a dalilin tsananin kauna da shakuwar da ke gare mu amma ba don na samu kaina cikin wani hali na wahala ba.

Rannan ina tare da Babana a gida yana kishingide yana jan carbin shi a hankali cikin natsuwa tare da sauraron kira’ar karatuna da nake yi a gobe, sai da na kammala komai na maida Alkur’ anin nawa mazauninshi.

Bayan na gama addu’o’ina na shafa sai muka shiga hira da Babana irin wadanda suka shafe mu har na shirya zan tafi in kwanta sai naji ya ce min ni fa da wata yar shawara na ce zan yi da ke.

Da sauri na dawo na zauna cikin natsuwa ina kallonshi cikin yanayin girmamawa da kuma sauraro can cikin zuciyata kuma tunani nake yi wacce shawara ce wannan da Baba bai da mai bashi ita sai ni?

Ban sani ba ko ganin irin yadda na tattara komai na mayar gare shi ne yasa shi mikewa ya zauna ko kuma a’a shi ma hakanne yaga ya fiye mishi daidai, kina jina ko Maryamu?

Na yi maza na ce mishi eh Baba can cikin zuciyata kuma na kara girmama al’amarin da Babana ke bukatar shawarar tawa a kai tunda yayi dalilin da yasa shi ambaton sunana na Maryamu’ tunda nasan ba kasafai ya kan yi hakan ba, saboda kasancewar sunan nawa suna ne mai girma a wurinshi.

Mutane ne suka dame ni da maganar in yi aure, nan da nan na tuna kalaman Yaya Dijah na cewar duk randa ya sake yi min wata magana da ta danganci aure in yi mishi in karfafa mishi gwiwa kan yayi auren don shi ma ya samu saukin al’amuranshi.

Bisa wannan dalili yasa nayi maza na ce mishi to kayi auren mana Baba Inna fa wajen shekararta uku ne yanzu da rasuwa kana ta zaune kai kadai yin auren kuma zai rage maka wasu damuwowin.

Ya bar abinda yake yi ya zuba min ido yana kallona, kalamanki ne wadannan ko kalaman yar uwarki? Don dai nasan ba ki da wannan nisan tunanin, ban boye mishi ba na kwashe hirarrakin da muke yi ni da Yaya Dijah kan rashin auren nashi. Yana ji na bai ce min komai ba sai zuwa can naji ya ce min to bari dai kawai in yi tunda kuma kuna ganin ya dace in yi amma in ba haka ba ni bani da wata damuwa kan hakan.

Tunda muka yi wannan maganar Babana bai sake ce min komai a kan maganar ba, sai kwana goma bayan nan na kammala wanke-wanke na kife kwanukan nazo inda yakena zauna saboda kiran da yayi, ga ni Baba.

Nayi mishi maganar cikin girmamawa, ya kalle ni cikin wani yanayi da na kasa tantance wanne ne yafi rinjaye a ciki? Maganar nan tamu ce nake ganin kamar zata tabbatą.

Nayi maza na tambaye shi wacce magana Baba? Yayi maza ya rage fara’ar wace magana kuma ki ke tambayata? Nayi sa’a cikin hanzari maganar ta fado min, don haka nayi maza nace mishi eh Baba na tuna ta, na tuna kayi hakuri.

Ya dan yi shiru kadan kafin jimawa kadan ya ce min, akwai wata yarinya nan da a ka nuna min tana da dan fasali kadan an kuma ce wai tana da ya’ya biyu da mijinta ya rasu ya barta da su, to kin ga maganar ya’ya tunda marayu ne, ai nima ga ki sai tazo mu hadu mu rike ku musamman da yake shi maraya rike shi ba karamin al’amari ba ne, akwai falala mai yawa a cikin al’amarinshi.

Na ce “Haka ne Baba.”

Tun daga wannan lokaçin bai sake min wata maganar ba sai a wata ranar Juma’a da safe bayan na dawo daga Makarantar Asuba. Na zauna kusa dashi na gaishe shi sai ya kalle ni ya ce min to yi maza kije gidan “yar uwarki ki gaya mata zancen nan ya tabbata an yi daurin auren yau da asuban nan.

Nayi maza na ce “Lah, har an daura Baba?”

ya ce, Eh uwata an daura to me za a jira tunda dai za ayi? Ai ita din na gaya miki yadda al’amarinta yake, don haka da ta koka min maganar aikin kafinta saina gaya mata tabi a hankali da tayi shawara dani ma da bata Sanya kanta cikin dawainiya ba balle har taje tana bacin rai, don haka ta tare kawai tazo ta fara amfani da wadannan kayan har kafin kafintan ya bata nata sai a kwashe wadannan din.

In har da wani lokacin da naji dar ko wani faduwan gaba kan maganar auren na Babana to a wannan lokacin ne ban san dalili ba sai naji ban ji dadi ba, a ce amarya tazo ta shiga dakin Innata tana amfani da kayan Innar tawa da dai ace yau ne yake neman shawarata to da na ce mishi a gaya mata kawai ta jira kawai kafintan ya gama mata aikin nata to amma babu halin in ce komai.

Yi sauri kije ki gayawa Dijah ki dawo sai mu dan yi kwalimar da zamu yi wa gidan kar baki su zo su ga kazantarmu ko kuwa? Na ce mishi haka ne Baba.

Gidan Babah Sumaye na fara shiga tana hidimarta cikin kwanciyar hankali iko sai Ubangiji yau sai a ka wayi gari da maganar daurin auren Mallam Bukar na ce haka al’amari yake in kaga ba a yi abu ba to lokacinshine bai yi ba Ubangji ya bada zaman lafiya na ce amin Baba.

A maganar da muke yi ne nayi mata hirar bayanin da Babana yayi min.

Cikin sauri ta dago ta kalle ni anya ayi haka kuwa? To ko da yake dai duk yadda a ka yin daidai ne fata dai a zauna lafiya amma kuma ai ita Halima a sanina akwai akwatinanta da nasan akwai muhimman al’amarinta a ciki a dakin an fita da su ne? Na yi maza na ce mata a’a suna ciki, ta ce, to maza je ki ki fito da su ki kawo nan in Dijah tazo sai ta tafi muku da su gidanta.

Na ce, Mata to, da sauri na koma gida cikin sa’a Babana ya zaga nayi maza na fitar da su na kai mata, haduwa muka yi da shi zai shiga ni kuma zan fita ina rungume da hotunan Innata guda biyu a jikina, ina za ki kai wadannan?

Cikin natsuwa na ce mishi zan fitar ne a dakin, tsawa ya daka min nayi maza naje na maida su nazo na wuce shina tafi aiken da yayi min.

Dawowa gida nayi na samu tuni har Babana ya gama kwalimar da ya ce zamu yi tare, dan karamin gadon bonon Innata shi ya kawo min daya dakin wanda da na baki ne dan akwatina kuma yana karkashinshi.

Duk abubuwan da suke faruwa ina bi ne kawai da kallo ba sosai suke yi min dadi ba, to amma kuma har cikin zuciyata murna nake yi Babana zai yi aure da za a tambaye ni abinda ke sosa min ran kuma ba zan iya vin wani cikakken bayani ba.

Anyi hidima su girke-girke da dafe-dafe saboda isowar amarya da ‘yan rakiyarta Babah Sumaye ce kuma ta jagoranci duk wani abinda aka yi tunda shi mijinta ne ma ya zamo wakilin Babana da ya karbar mishi auren itama Yaya Dijah ba a barta a baya ba, don har da sayayya tayi ta kawowa Babana wai a kara a cikin kayan aure.

Yayi murmushi ya ce, wane kayan aure ne ma? Ke dai tunda kin kawo wadannan din a bata a ce mata ‘yarta ta ce tayi kwalliya, to Baba ta fadi tana murmushi, ya tayata murmushin tare da yi mata addu’ar Ubangiji yayi mata albarka, ya kuma jikan Mahaifiyarmu da rahamarsa muka yi maza muka ce amin.

Ban fara gane irin fasalin auren da Babana yayi ba sai bayan da ‘yan buki suka watse mu kai saura daga ni sai Babana sai ko Amaryarshi a gidan, lokacin ne na soma gane wani canji ya same ni.

Dakin Innata dakin da nan ne a ka haife ni, a cikinshi muka yi rayuwarnmu ni da uwata bayan rasuwarta kuma nan ne wurin zamana, komai zan yi a cikinshi nake yi, sai na zamo ba ni da halin shiga cikinshi in zauna in sake, ina shiga na dan zauna sai a ce min to je ki waje ko.

Gashi kuma daga inda duk na fito nan nake dosa saboda kwata-kwata ban ma saba da in da aka maida ni din ba, gashi kuma sai nake ganin tamfar dakin da abinda ke cikinshi duka nawa ne ko kuma na Innata amma a ka fitar da ni a ka sanya wata a ciki.

An wayi gari da safe ina durkushe daga bakin kofar dakin gaishe su nake yi a cikin barin jiki saboda al ‘amarin da idanuwana suka gani wanda ba sabawa da ganin hakan suka yi ba.

Babana na gani kwance shame-shame kan gadon Innata me rumfa da aka canzawa shimfida a ka sanya sababbi, ita kuma zaune a gefen gadon da daurin kirji a jikinta kanta babu dan kwali jikinta babu riga sauri nayi na sunkuyar da kaina kasa, ban lura naga halin da Babana yake ciki ba balle in gane da rigar a jikinshi ko babu?

Yana fita waje ya bar gidan naji ta kwalo min kira, da sauri na amsa naje ina işa tayi maza ta cafke kunnena ta rike bayan ta dirma min wani nannauyan dundu da sai da yayi sandin gantsarewa ta.

Kina hauka ne kike shigo min daki, da fadi sunan uwar miji gara na uwa mahaifiya. Da sauri Babana ya ce mata ko? Ta langabar da kai nuna alamar girman maganar da zata yin, to wacce ta haifan maka miji Mallam? Da wani abin da yafi aure daraja ne?

Da sauri Babana ya ce mata babu shi, babu shi fa kam. Sai dai fa sanin hakan wurin mutane kadanne a wannan lokacin, ta ce Uhun ai kuwa dai wanda ya raina aure bai yi wa kanshi adalci ba.

Bakuwar ta ce tayi sallama abinda yayi dalilin katsewar hirar tasu, aka shiga barka da sannu da zuwa, a’a ke Lantana ‘yar taki ki ka tasa a gaba nan za ki koya mata son miji? Amaryar Babana da a yanzu naji an kirata da Lantana nasan sunanta shi kam Babana Malama naji yana kiranta.

Ta kyalkyale da dariya ta ce, to me zan jira ita mace ai tun daga haihuwarta ake koya mata tattalin miji da tarairayar aurenta, to ai shi ke nan. Ta juyo gare ni da dariyarta ke ‘yar amarya bakinki da maiko.

Na yi maza na soma gaisheta tunda a jiya an gaya min in rinka gaida mutane in na gansu, kafin nan ban damu da gaida kowa ba in ba ‘yan uwan Innata ba ne sai ko na Babah Sumaye.

Ke Yaacuwuna kawo musu dan abin nan mana yayi maganar daidai ya mike ya kama hanyar waje bayan sun gama yiwa juna gaisuwar gajiya da fatan Ubangiji ya sanya alheri, a zuciyata nace sai kirana da sunan Yaacuwuna yake yi sunan da ya dade bai kira ni dashi ba alamar dai yana cikin farin ciki mai yawa.

Miyar kajin da ya yi saura a aje na kawo musu, wacce Yaya Dijah ce tayi mana tare da timemen biredin da yake kai na ajiye musu, suka bude kwanon kawar tata ta fara uh’uh’uh ke da arziki cikin lamarin nan naki fa wannan karon.

Suka soma cin naman miyar suna hirarsu ni kuma ina can gefe daya a rakube saboda yanayin da na gani a fuskarta, ba ki dan tsakura kika sanma ‘yar taki ba? Ta yi maza takai tsokar da ke hannunta baki ta lankwame kafin ta sake gutsuro katon biredi ta dan na a kai, ta kora da Ruwan shayi sannan ta soma yi wa kawar tata bayani wannan ‘yar tawa a rike take nan inda ki ke kallonta bata cin komai a jikin kaza sai cinya, ai kuwa kin ga bana bata cinya ni in zauna haka ba ko kuwa?

<< Halin Rayuwa 4Halin Rayuwa 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×