Muna zaune a bayan motar ni da Yakabudi bacci takeyi saboda gajiyar hidima da kuma sanyin AC da ya ratsaya, ni kuwa tunanin al’amura da yawa nake yi Innata na fara tunawa ‘yar rayuwar da muka yi tare dan sanin da nayi mata mu’amalar da nake yi tunawa a tsakanina da ita, rasuwarta da yanda hakan ya zama sanadi na la’amura masu yawa, zamana da babana, mu’amalar da ta gudana tsakanina da shi, na tausayawa da kulawa har kawo zuwan baba Lantana gidanmu al’amuran da aba Lantana tayi mana sanadinsu a zuwanta gidanmu tausayin Babana ya kama ko na ce ya kara kamani musamnan da na tuna yadda ya bar gida ya bar danginshi ya fito ya soma rayuwa tare da kulawar uwar da, da kunnena, na ji shi yana tabbatar mata da cewar ita ce bangare mafi dadi da rayuwarshi ta dandana yazo ya rasata a lokacin da bai zata ba ya yi bakin ciki irin wanda bai misaltuwa bai gama wattsakewaa daga rashinta ba da kewarta ya zo ya fada hannun Baba Lantana, alamuran da suka yi ta faruwa har kawo wannan lokacin da muke ciki, wata rana sai labari ai babu wani abinda yazo ya tabbata in dai ba kudurar Ubangiji ba ne, wannan jimlar jimlace da mutane daban-daban suka yi ta furtamin ita a lokuta daban-daban bisa faruwar al’amura daban-daban sai dai ban taba kawo tsammanin wucewar tasu za ta zo min a haka ba saboda tsananin daci da ciwon abubuwan da suka yi ta faruwar sai na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar ba zai wuce ba na rinka ganin tamkar nawa mas’aloli da damuwowin ba masu wucewa ba ne masu dawwama ne don haka şai na zamo a duk lokacin da wani babba ya tabbatar min da cewar zasu wuce wata zai wuce har ki ganki kina bayar da labari sai in samu kaina da tambayar kaina to yaushe ne? Yaushe ne wata ranar da zai wuce? To gani a yau sai na samu kaina da yarda da cewar tabbas mutum mai gaggawa ne mai sauri ne a kanki al’amuranshi, saboda ganin da nayi tamkar daurin aurena da Mubarak da aka yi kawai ya kawo karshen al’amuran duka zamana da Baba Lantana da ma shi Baban nawa a gida daya ya kare, lissafin da ake tayi min na dadewar da nayi babu aure a ce nan kusa babu sauran sa’a ta shima ya kare a yau ni din matar aure ce, matar ma kuma ta Ahmad Mubarak wanda duk kwaramniyar a kanshi aka yi ta yi haka na zurfafa cikin tunani mai tsawo nayi nazári mai zurti kan al’amuran rayuwa da kai kawon al’amuranta abubuwan da na shiga da wadanda idona ya gane min sai na kara tabbatarwa kaina da cewar rayuwar gabadaya wata rana zata kai ga kaiwa, tausayi ya yi matukar kamani har na kasa hana idanuwana zubar da hawaye.
Sannu a hankali sai gashi har mun iso garinmu har gamu muna shiga unguwarmu, bude ido ki gani Maryam nisan tafiyar da kika sanyamu ta kare gamu mun iso gida, Amiru ne yake yi min wannan magana,r ban tanka mishi ba.
Babana na hanga a kofar gida cikin kwalliyar daban taba ganin yai irin ta ba, babbar riga da ‘yar ciki da wando ga kafceciyar hularshi ta zanna a kanshi, bakin da ke fita daga cikin motocin dake tsayawa yake yiwa sannu da zuwa wadanda yan uwanshi ne da suka biyo motocin amarya sai dai nasan ‘yan daidaiku ne kawai zai iya shaidawa a ciki sauran duk sai anyi mishi bayaninsu, tunanin Babana ya sake dawo mini ban taba yin kwana bakwai ban ganshi ba don ban taba zuwa wani wurin da na bar shi na bar unguwar da aka haifeni da gidanmu naje na kwana bakwai ban dawo ba, to ina ma nake zuwa? Gidan yaya Dija ne sai ko Yakumbo Halima da sauran dangin Inna nan din kuwa ba na iya zaman da zanyi kwana bakwai nake gudowa in dawo gida sai wannan karon dai nayi tafiyar dana kwana sittin da daya.
Ganin da nayi za a wuce kofar gidanmy bayan nayi zaton nima a nan za’a saukeni yasa nayi maza na cewa Amiru, a’a a’a ba a nan za a saukeni ba? Gaba daya shi da mai tukin suka hada baki wajen tambaya ta gidanku? Ai furta kalmar na bayar na karar mishi da baba suka yi tare da baba Abba Gana ya rabaki da shiga gidanku ba tare da izinin angon ba yarinya shi kuwa tuntuni aikina jin wayoyin da yake tayi jaddadawa yake yi lalle ne a wuce da ke gida kar a ce za a tsaidake a ko ina, ban san dalili ba ina jin bayanin na Amiru na soma yin kuka hawaye suna ta gudu a kan fuskata, a hakan aka shigar da ni gidansu Mubarak sashin Umman shi aka fara kaini itace ma ta jagorance mu ta wuce gaba muna biye da ita a baya zuwa inda tace can din ne wurina muna tafiyar ina tunanin shekaru biyar ne cif har da wasu watanni ba shiga gidan ba da nake shiga irin shi tafiyar da muke yi kafin mu isa inda zata kaimin ya sani fahimtari rin canjin da gidan ya samu a shekarun da nayi ban shiga ba.
To ga nata wurin nan bismilla ina jin ta fadi hakan na soma karanto addu’o’i iri-iri ko dama can kuwa tun isowata kofar gidan nake addu’ar ban fasa ba man tarar da su anti Kubra, anti Hindu, Hasiya Jibrin da mutane da yawa wadanda ba zai yiwu in yi ta lissafinsu ba, aikin jere suke ta yi daga ganin jama’ar dake wurin dai kai kasan ba karamar gaiyata yaya Dija tayi ba.
Mun kuma shigo. ne muka samu su Yakumbo Halima da su baba Sumaye da suka rigamu isowa suna fadin, kai masha Allahu tubarakallahu Ubangiji ya yiwa Hadiza albarka mafi yawancin mutanen dake wurin suka yi amin, amin, ita kam ai uwa ce ba ya ba.
Wani daki da babu komai a ciki daga labule sai katifar da aka yiwa shinfida mai kyau aka kaimu ni da Yakubudi ina shiga anti Kubra ta biyomu ta yiwa Yakubudi sannu da zuwa ni kuwa kallona tayi ta tsuke fuska kafin ta ce min, maza share hawaye ki hadiye kukan da kikeyi ya ishen haka na gani a wurin Hadiza jiya tun da akayi waya akace an daura auren ki da Alhaji Ahmad take kuka tun ina rarrashinta ina bata hakuri har sai da ta kureni nayi mata kaca kaca nace ina dalilin da za ki tara jama’a irin wannan ki yi ta kuka a cikin su, to maza kema sharesu ni ma ina nan kika tuna in na naki kukan na dadin ganin burinki ya cika ne kin auri mijin da kike so duk daya kar in sake ganin hawaye a idonki.
Ban tankawa Anti Kubra ba iyaka dai dama nasana halinta na kuma san tana cikin mutanen da suke san yaya Dija.
Hasiyan Jibrin ta shigo na kuma ji dadin shigowar tata, kin gani abokan tasowarki har sunyi sallah suna cin abinci ke kina zaune wannan doguwar tafiya ai ko mura kike ya rage ga ruwan zafi na zube miki ki yi wanka sai ki yi alwala ki yi salla ki dan ji dadi, nace mata to kafin in idar har ta tanadar min abubuwa masu saukin ci wadanda ba za su gunduren da sauri ba irinsu strawberry grabus citrus da apple masu ban sha’awa wadanda ko don kyansu zaka iya bata lokaci mai tsawo kana cinsu basu gundureka ba, itama Yakabudi ta kai mata tare da abincinta tana ci ita kuma ta dawo wurina muna hira, ai naso in zo har Gaidan din nayi maza na ce mata gara da bakije ba Hasiya da Walid yasha wahala tafiyar tayi tsanani da yawa, ta yi murmushi ta ce, to ba biki uwarshi akeyi ba, na yi murmushi a karo na farko tun bayan da bikin ya fara na ce, ai kuwa da uwar tashi bata kyauta mishi ba don da ta wahalar da shi.
Hira kadan muka yi sai naji ta soma tambayata ina fata dai kin shigo ne da shirinki, shiri kamar yaya Asiya? A hankali cikin muryar rada ta soma yi min bayani, shirin rike mijinki a hannunki mana ko kin san yau kwana hudu kenan da dawowar uwargidanki daga yaji, gabana ya yi mummunan faduwa saboda a yanzu zaman lafiya nafi so ba fitina ba, duk da ta gane faduwar gaban da na samu bata yi shiru ba sai ta ci gaba da ba ni labarin da take son ba ni alamar dai ta matsu sai ta gaya min, ai rikici mai yawa aka yi bayan tafiyarki, ta ja ta tsaya kan in dai Alhaji Ahmad zai aureki to ita ya sauwake mata saboda wai kina waje ma baki bar aurenta ya zauna lafiya ba balle kuma a ce kin shigo gida gabadaya kuma daga ita har yan uwanta sun mara mata baya suna fadin ai da aurenki gara a ce wasu kishiyoyin ya kawo mata su zama hudu, wajen kwana talatin ta yi bata nan shi da abokanshi suka yi ta zuwa biko ana yi musu wulakanci wasu abokanshi har suka fusata suka ce ya saketa ya ce a’a shi ba zai yi aure don ya rabu da ita ba ne dukanku yana sonku ya kuma yi alkawarin matukar ba ita ta tsoma kanta cikin abinda bai shafeta ba zai yi iyakacin kokarinshi wajen ganin yayi adalcin da zai tsarevwa kowa hakkinshi.
Na yi ajiyar zuciya mai karfi ba tare da na ce mata komai ba baya ga Ubangiji ya bashi ikon yin hakan saboda iyakacin gaskiyata nake nufi nafi son zaman lafiya a kan gutsiri tsoma.
Sau biyu Anty Kubra ta kawo min kan wayar telephone din dake dakin wai in karba zai yi magana da ni ban karba ba saboda sai nafi son ya kyaleni kawai in zauna shiru ko zan samu natsuwar da nake bukata a tare da ni, tunda na soma gane cewar nan gidan nashi dana zo ma zai yi wuya in har zan samu zaman shirun da nake bukata don ina daga kwance na jiwo Baba Sumaye tana cewa, kun ga dangin uwargidan nan babu abinda suke nema in banda a yi rikicin da za a yi kaca-kaca a bikin nan to na rokeku kar in ji wani cikinku ya kulasu.
Tana fadin hakan na ji mutanen dake wurin su na ta bayaninai mu ma kaza mu ma kaza tun jiya suke yi mana wulakanci abu kaza da kaza har suna gori wai.
Yakumbo Halima ta katse masu kokarin yin bayanin kan irin gorin da suke yin tare da fadni, abin dai bai yi dadi ba da kwabar yarsu suka yi suka nuna mata muhimmancin zaman lafiya da yafi musamman ma da yake akwai sanaiya mai karfi a tsakanin mu da su, haduwarsu karkashin miji daya kuma wannan kaddara ce su dukansu biyun matan shi ne in banda haka ai da Mero ya fara aura da ya aureta a wancan lokacin kuma da ba ma zaton zai koma auren ‘yarsu to kaddara don haka mu ba ma fada da ita sai dai mu yi mata addu’a, yanzu ita wacce tayi sanadin abin ina take? Itama ba ance shekaranjiya ta tafi ba itama ta yiwa kanta sanadin nata auren saboda sharrinta, shi mutum duk yadda ka kai da kinshi ai baka iya hana shi samun abinda kaddararshi ta rubuta mishi in da hakan yana yiwuwa ai da auren Mero da Alhaji Mubarak bai yiwu ba.
Na zaro ido ina kallon Hasiya Jibrin don son jin karin bayani kan maganar da na ji Yakumbo Halima ta fada na wacce tayi sanadin da aurena da Mubarak bai yiwa ba a wancan lokacin itama ta yiwa kanta sanadin nata auren na kuma san da baba Lantana take nufi, sai Hasiya Jibrin ta gyara zama ta ce min, ai ai ranar da ake shirin tafiya daurin aure Baba yasa a yiwa ‘yan kasuwar timatir dinsu abinci na musamman ya ce su ci a kuma zuba musu a kula a sa musu a motar da suka yiwo shata saboda nisan tafiyar sai Baba Lantana ta ce zata yi wannan tana kai kawo tana hidimar girki ana raha ana barkwanci da ita har muna cewa a a kaga Baba Lantana abin mamaki ta sake sai hidima ake ta yi da ita, ashe ashe Baba Lantana da abinda ta shirya, kamar Baba ya sani ya ki fita daga cikin gidan nan har muna ganin kamar ya dan takura mana ashe ashe in baki labari sai kawai idonshi ya kai kan Baba Lantana tana zuba wani abu a cikin abincin nan bayan an gama shi ai kuwa dai nan da nan ya isa wurinta ya tambayeta me take zubawa a çikin abincin? Ta ce bata zuba komai ba ya yi yayi ta ki yarda da cewar ta zuba wani abu ya ce to ta diba ta ci, nan ma ta ki.
Hannu biyu na saka na dafe kaina saboda sarawar da yake yi a dalilin tsoratar da nayi ban iya barinta ta kai karshen bayanin ba na tambayeta me take zubawa a ciki Hasiya? Sai ta kuramin ido kafin ta ce, guba su ci su mutu ko ince duk wanda ya ci ya mutu, salati na rinka yi ina karawa kafin daga bisani na shiga yin hamdala ina godiya ga Ubangijin da ya yiwa Babana wannan rufin asirin bai barta ta ja mana wannan abin bakin cikin ba ko me muka yiwa Baba Lantana ni da babana ta kaimu irin wannan kiyaiyar? A in tsaya yin wannan tunanin sai kawai ma na kawar da shi na kalli Hasiya na ce, to sai aka kare a ya ya?
Ta ci gaba da takaicin abinci ta kama kuka da zage-zage wai zai kulla mata sharrin da ya saba kulla mata, ya ce a’a ai babu sauran sharri je ki na sauwake miki auren ya isa haka, za ta yi rashin mutunci su Anti Kubra suka fitar da ita daga gidan aka dauki abincin aka je aka tona rami aka juyeshi aka rufe don kar wani abu mai rai ya ci, na ce hodijan na kame bakina nayi shiru.
Rannan dai da daddare bacci ya gagara ta yayi gabadaya mutanen dake dakin sunyi bacci amma ni idona biyu.
A baya a duk lokacin da na kan zauna in yi tunani a kan yin aure na kan ga kamar yin auren hutu ne amma tunda auren ya gabato ni na samu kaina cikin wani irin yanayi da yanzu da wadannan al’amuran suke ta faruwa sai na gane lalle akwai wani babban al’amari a cikin don haka maimakon in yi ta juyi idona biyu ni kadai saboda bacci ya gagareni sai na koma karanta kalmar Lahaula wala kuwwata illa billa kalmar da Manzon rahama ya tabbatar mana da cewar tana maganin musibu kala daban-daban har guda dari daya babu wato casa’in da tara mafi kankantar musibun nan kuwa shi ne bakin ciki har gari ya waye ban daina ba da na idar da sallar asuba ma komawa nayi na kwanta na ci gaba da karantawa.