Skip to content
Part 53 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ina cikin haka sai ga Anti Safara ta shigo dakin da nake nayi maza na mike na zauna na tare ta da murmushi cikinta ya fito ta kuma kyau ba kadan ba.

Amarya ta ango, anya da wata amaryar dá ta fiki morewa kuwa Yahcuwuna? Nayi maza na katse murmushin da nake yi kafin na tambayeta, wacce irin morewa kuma anti bayan duk wannan kwararmniyar?

Ta ce kin auri mijin da yake sonki ban taba ganin so irin wanda Alhaji Amadu yake yi miki ba kwaramniya kuwa ina ruwanki da ita tunda dai kinyi sa’a Ubangijin mu ya rufa muku asiri ke da babanki duk abinda akayi nufin ya same kun bai sameku ba.

Nayi maza na ce haka ne anti, to zuwa nayi yanzu don in ganki in gaya miki kisa hannu biyu ku karbi al’amarin mijinki kar ki yarda ki tsaya sakarci ko tunanin wai ko ke amarya ce a’a yi hidimar aurenki kawai ke ko iya shegen nan amare a yi ta tsiya ana wani iface-iface ban yarda ki yi mishi ba kin ji na gaya miki, hannu biyu na saka na rufe idona tare da fadin ki yi min irin tuwon da kike yi min jiya anti. Zanyi miki ma yafi na jiya dadi ki ci tare da angonki don nasan ba wuya ace ya wuce yau din nan bai dawo ba, kisa hannu biyu ki karbe shi in yaso babu kuma ruwanki da kwaramniyar da take cikin gidanshi kar ki daga ido ki kallesu balle su ganekin san abinda suke ciki, ita mace da kike gani ko wace da halinta tak zama, nace to na gode anti, tayi min sallama ta tafi har cikin zuciyata sai naji dadin iin kalaman da ta yi min.

To haka akayi wunin bikin ranar cikin wani irin cikar da ba zai ki atantu ba ta wurin mu ma dai muna da yawa ga yan uwan babana da suka rakoni daga Gaidan ga dangin Inna ta wadanda su ma masu yawa ne babu laifi ga gaiyar yaya Dija na kawaye da dangin mijinta masu kara nan gidan su Mubarak ma ba a magana uwargida kuwa kai kace tamkar da gadara yan uwanta suka zo don su nuna su din masu yawa ne.

A wancan lokacina Amarya boye kanta take yi saboda kunya da kawaici, ba kamar yanzu ba da amarya ke kai kawo a tsakanin yan bikinta sai dai hakan bai hanani tsala ado, wuni nayi ina kwalliya ta burgewa kwalliya kuma mai tsada da kowacce nayi sai kaga kamar kar in cireta saboda ina tare da gwanayen kwalliyar irinsu malama Hindu da malama Basma ga kuma anti Asiya wacce ita dama babbar sana’arta kenan gyaran amare ciki da waje, in nace ciki da waje kema sai ki gane abinda nake nufi.

A gabadaya sashinmu a wancan lokacin biki nane bikin farko da mutanen mu suka sheda video coverage ana daukar su ana kuma yi musu tambayoyi, me zaku ce game da wannan aure na Alhaji Mubarak da amaryarshi Maryam? Wasu su yi magana wasu kuwa kunya da rashin sabo ya hanasu cewa komai in banda kyalkyalewa da dariya wasu kuwa da abin yayi matukar burgesu duk da sun kasa cewa komai fadi sukeyí yau ku zo ku gani bin mutnae akeyi ana yi musu tambayoyi da irin abin nan na masu rahoto.

Malama Basma itace tayi magana ta ilimi har ta samu jan hankulan mutane gaba daya aka koma sauraron bayanin nata tayi magana ne a kan matsayin aure da kuma’ menene kishi a musulunci, tayi magana sosai ta kuma karfafa maganganun nata da ayoyi da hadisai tare da kawo misalai na manyan mata magabata yadda suka tafiyar da rayuwarsu tsakaninsu da mazajensu da kuma kishiyoyin nasu duk da ba wai basa kishin bane ya sa suka yi hakan a’a sai dai su fahimtarsu a kan kishi daban mu ma a yau tamu fahimtar daban.

Da ta kawo karshen jawabin nata sai tace ya ku yan uwanamu ina kira garemu da mu yi gyara a kan yadda muke tafiyar da al’amuran da suka danganci kishinmu a yau mu daina kishi na jahilci kishi na rashin sanin ya kamata mu koma yin kishi irin na shari’a wanda shi ne ibada.

Wassalamu alaikum wa rahamatullah, gabadaya wuri ya kaure da kabbara malama Ubangiji ya saka miki da alheri abinda kowa ke fadi kenan.

Ana gama wannan aka shiga yin hotuna wai duk ribibin da kaeyi nayin hotuna da amarya ita Rumasa’u da kyar ta yarda aka yi mana hoto guda daya ni da ita da aka kawoni dakinta kuwa kamar yadda aka saba bisaal’ada na kai amarya wurin iyayen miji da uwargidanta ba, in har tana da ita yan uwanta basu ji kunyar fadin babu wata amana tsakanina da ita ba tundai ta din ba wani girmana tayi ba banda haka kuma ai banbancin dake tsakainta da ni kadan ne iyaka ita tana ciki ne ni ina waje ba manyan dattawan da suka kaini ba wadanda shekarunsu suka kai fassara musu al’heri ko da kuwa da kafa ka kadeshi ba da baki ba ko ni da nake lullube a gabansu na gane abinda suke so, to balle kuma su a haka muka tashi muka fito aka dawo da ni dakina tunda dama sai da aka kaini wurin Umma kafin a kawo ni wurinsu mun dawo daki muka ci gaba da harkokinmu sai a wata yar uwarta ta shigo wai ga kudin sayen bakina Amarya an manta ba a bayar ba, anti Astya ta ce, baki haba, babu komai mayar masu kawai, ita wannan amaryar ai ba sai an sayi hakinta ba.

Ana cikin haka aka soma rade-radin ango ya dawo ango ya dawo kan kace meye wannan har labarin ya bazu ko ina ango ya dawo, ai kuwa dai dama na san da kyar ace bai dawo ba yau, kai wannan ango da zumudi yake, maganganun mutane daban-daban ne wannan.

Kan kace meye wannan sai na jiwo muryar tsiyaku a falo yana gaida jama’a, wani abu kake so ne suna tambayarshi ya ce a’a yallabai ne ya ce in shigo in gani in mutane sun danyi sauki ya shigo, kar ata mai iya shege ta ce mishi, jeka ka gaya mishi bamu yi sauki ba muna nan cike a wurin. Gabadaya suka kwashe da dariya suna fadin, ke dai baki da dama, ita kuwa tana dariyar tana fadin, a’a to haka kawai da rana tsaka ba zai jira abokai su kawoshi ba? Ba fa saurayi bane ta ce, eh ko ba saurayi bane ba zai shigo yanzu ba.

Wajen karfe hudu da rabi aka soma walimar maza a masalaccin unguwarmu wanda dama yafi kusa da gidan Alhaji Muhammadun don shi ya gina shi walima sosai aka shirya don saniya sukutum aka yanka dominta banda ciye-ciye da abubuwan sha iri-iri malamai kuma daga wurare daban-daban aka gaiyatosu.

Ana cikin haka Isiyaku ya sake shigowa falon, wai ina anti Asiya, tayi maza ta ce mishi gani nan, wai ince miki in babu matsala yana so ya shigo.

Ta ce, to to kaje ka ce mishi ya danyi min hakuri kadan, Isiyaku yana fita ta mike tace, kai jama’a surukuta fa ba wasa bane bikin nan ai munyi shi mu dan ragu mu koma gidan Hadiza, wasu suka ce ka nufi gidanka ma kai ai yamma ta riga tayi, a can gefe kuma wasu suna korafin wane irin rashin hakuri ne wannan ko bai yi hakan ba ai za a tafi a bashi wuri.

Isiyaku ya sake shigowa, anti wai gashi duk wacce zata tafi a bata atamfofi ne wadanda akayi don bakin, hoton ango da anmarya ne a jiki da hakan ya kashe bakin mitar da suka soma yi mishi nan da nan aka shiga rabo, bayar kowacce ta karba sai ta wuce ta tafi tana murna da godiya da fatan karin budi haka a dawo suna ana fadin amin amin, kafin karfe shidan yamma sai ya zama babu kowa daga ni sai Hasiya Jibrin sai ko ita anti Asiyan saboda suna kokarin ganin komai yayi tsaf, a haka kuwa Mubarak ya shigo ina jin gaisuwar da ya tsaya yi da su nayi maza na jawo gyalena na lullube kaina, yana shigowa bai tsaya yin komai ba ya durkusa a gabana ya sa hannu biyu ya yaye lullubin gyalen nawa ya sake sa hannunshi na dama ya ture dankwalin dake kaina kafin ya sake sa hannun nashi ya damki gashin da ke gaban goshina ya rike amma ba damka mai karfi ba, addu’o’i yayi ta karartawa sai da ya gama ya tofa min a fuskata sannan ya mike ya fita, yana fita anti Asiya ta shigo tayi min sallama ta tafi sai muka zama daga ni sai Hasiya Jibrin mai jiran mijinta ya zo daukarta ita ce ta kara gyara min komai ko ina ya zama sai kamshi yake yi kasancewar itama ta samu wata a gida su ma kuma suna fafatawa, tana ta ba ni shawarwarin da take ganin tamkar za su yi min a matsayina na Amarya, na ce kai ai dai Hasiya nafi son zaman lafiya a kan rikicin nan ni yanzu ba na son bacin rai, na gaji da shi, ta ce to ai bashi da dadi ni su din ne gadara ne da su sai su rinka fadin mai mazansu aka aura, nayi daríya kawai bance mata komai ba. To kafin a yi sallar magariba shigowar ango biyu shi ne ma ya bada mtoar da ta maida Hasiyan gida tare kuma da yi mata alheri.

Yana idar da salar magariba ya sake shigowa, kin yi salla ne? Yana daga tsaye ya yi min tambayar na ce mishi eh, ya ce to bari in koma wajen wa’azin nan kar su Abdulhamid su sani a gaba don ba wani kirki ne da su ba ga sa ido, na yi murmushi na ce mishi to, amma ai kin san in anyi sallar ish’ai zamu shigo tare da su ko, zasu rakoni sayen bakin amarya, ban ce mishi komai ba ya sake juyawa ya fita, ni da kaina tunani nake yi cikin zuciyata ina tambayar kaina ko ta ina yake biyowa yake wannan zirga-zirgar oho?

Ko da yake Mubarak bai bar kawaen da na zo da su daga Gaidan suna zaune ba sai ya ce aje da su in gari ya waye zaije ya yi sallama da bakin gaba daya zai hada har da su ni kadai din sai nayi shiri na tunda a shekaru baya can na taba yin kawancen su Jumare su Hasiya Jibrin, na kara gyara kaina ko da dai dama akwai kwalliya mai kyau nake wacce kuma ban dade da yinta ba ga kuma kanshi mai dadi a tare da ni.

Ina jin sanda suka shigo falon saboda sallamar da suka yi sai dai ban yi musu amsawar da zasu ji ba daga falon suka zauna a kan kujerun dake wurin, to ina amaryar take? Kai Alhaji Ahmad to ka kori ‘yan matan amarya yaya za a yi a sayi bakin amaryar? Maimakon ka barsu in mun zo mu maida su? Ai sai ka fito mana da ita. Mubarak ya leko dakin da nake a takure cikin lullubi zo ki basu ko ruwa ne Maryam in kuma da wani abu ki hado musu, ban yi musu ba na tashi na shiga kicin na shirya musu ‘ya’yan itace a plate daya sai da na cikasu da nau’o’insu kala daban-daban sannan na cika wani plate din da kayan tsarabar amarya na zuba soyayyan naman rago da yaya Dija ta sa a kawo min a wani plate din na hadasu kan wani madaidaicin tirem ai kyau na kawo musu, maimakon in yi shiru kawai in ajiye musu sai na manta na kara gaishesu, Mubarak ya ce, shi kenan ta hutar da ku sayen baki, Abdulhamid ya ce, a’a a’a kai kayi mata wayo ka korar mata kawaye ka kuma sanyata aikin da yayi dalilin da ta yi magana don haka ga kayan sayen balkinta nan turarurruka ne akwati guda muka kawo mata ta yi ta fesawa tana yin kanshi.

Sunkuyar da kaina kasa nayi nayi shiru tare da kasa rufe fuskata da gyalen dake hannuna saboda kunya, Ubangiji ya zaunar da wannan aure naku lafiya Maryam ya kuma sanya albarka mai yawa a rayuwarku, gabadayan maganar Amiru kenan yayin da Abdulhamid ke fadin, amin amin.

Kawo ledoji in akwai ki juye musu kayan su je da shi can, ban yi magana ba na tashi naje na kawo ya juye musu suka yi min addu’a suka tafi, shima ya bi bayansu don rakiya da kuma zama wurin wa’azin da akeyi, ina jin duk karatun da akeyi har aka kai ga gamawa malamai suka yi addu’o’i ga kasa, jama’ar kasar, al’ummar musulmi da kuma ango da amarya, ina jin hakan na tabbatar ya kusa shigowa don haka nayi maza na jawo gyalena na kudundune a kasa na rufu da shi na daddanne ko ina ina jinshi ya shigo yanakiran sunana Maryam, Maryam, to wai-ke ya ce miki amarya tana yin bacci ne tun kafin angonta ya shigo, ban motsa ba shima bai tsananta ba sai ya juya ya fita, motsin ruwan da naji ya saa na gane wanka yake yi, ya sake shigowa dakin Maryam, sau daya kawai ya kira sunan nawa sai kawai ya sunkuya ya sa hannu biyu ya sureni ya nufi falo da ni, ke ance miki amarya irin ki tana da wani lokaci ne na yin bacci a darenta na farko?

<< Halin Rayuwa 52Halin Rayuwa 54 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×