Muje ki biyamin karatunki in ji, doguwar kujera ya nufa ya zauna ya mike kafarshi guda daya a kanta ya zaunar da ni a kan cinyarshi ya sake dauko daya kafar tashi ya dora a jikina nayi matukar takura da hakan da ya yi min saboda kunya da rashin sabo bana zaton a tsawon dadewar da nayi da shi ya taba taba jikina da nufin shi in dai ba a kan wani dalili ma karfi ba shima a wancan lokacin ne nan baya ba a wannan karon ba, a yau din kuma da ya dorani a hakan rigar baccin da ke jikinshi mai igiyoyi ce ko tsayawa daureta bai yi ba sai dan gajeran wando kirjinshi gabadaya a bude yake har zuwa kan cibiyarshi hannu biyu na saka na rufe fuskata yayin da jikina ke ta faman bari. Wai ina kike kokarin zuwa ne? Da kike mutsu-mutsun kwacewa, ya sa hannayenshi duka biyu ya cire nawa da na rufe fuskata da su ban yarda na bude ido ba balle in ga yanayin da yake ciki sai kawai naji ya dora bakinshi a kan nawa, gabadaya ya kidimani ya sanyani na shiga wani hali da ban ma san yanda zanyi in kwatantashi ba sai dai kuma nasan babu mamaki ya samu kanshi a yanayin da ya wuce wannan don sau biyu zuwa uku yana cewa me za ki ci Maryam, ga abubuwanci na kawo miki kin san bai kamataki kwanta baki ci komai ba, sai dai ya kasa sakina balle in iya ganin abin da yake cewa ya zo da shi din bale har in iya samun zarafin da na iya kai wani abin bakina, yanda ya fito da ni falon a dauke haka ya mike ya sake maidani dakin a dauke ya dorani a kan shimfidar, a jiyar da na bari wurinki za ki bani, kyautar da kika dade da yi min nake so in karba a yau, a kankame nake a jikinshi yake wadannan kalaman ina jinshi ban tanka ba ban kuma motsa daga yanayin da nake ciki ba sai na ji shi ya soma cewa.
Yi min wani alheri guda daya mana Maryam so nake ki martaba min irin martabawar da kika yi min a waccar ranar da wancan lokacin tashi ki sa hannunki rage min wadannan kayan na jikinki da kanki karki barni ki ce sai dai ni inyi yi min wannan alfarmar don in kara jindadi in kara farinciki zuciyata ta kara gamsuwa kuzarina kuma ya karu saboda na san zan karbi ajiyar tawa ne in karbi kyautar tawa cikin yarda da gamsuwa da amincewarki ba tilastaki zanyi ba.
Yana gama fadin hakan na mike na zauna nasa hannu na soma cire kayan da ke jikina da kaina yana karbar su yana yin jifa da su ba tare da yana lura da inda suke tafiya ba, sannu a hankali har na cire duk wani abin da nake sanye da shi saura rigar nono na maida hannayena baya da nufin in balleta itama kowa ya huta, sai naji ya ce min uh’uh Maryam bar min wannan in karasata da kaina, ai ko a wancan ban barki kin cire ta ba, yana daga kwancen ya miko hannayenshi ya balleta itama ya yi wurgi da ita komai naki yana nan tsaf Maryam kamar yadda na fara ganinshi sai dai ma kyau da kwarjini da suka kara.
Zai yi wuya rannan in har akwai wani wuri a jikina rannan da Mubarak bai yi mishi irin abinda yake ganin shi ne ya kamaceshi ba saboda wani irin yanayi da ya samu kanshi a ciki na kidima tamkar dai ace bai taba sanin wata mace a tube a gabanshi ba tsawon rayuwar shi. Sai a wannan ranar gyara ki ji dan tsaya ki ji abinda zan gaya min taimakeni ki karantamin wannan addu’ar don mu karantata tare da ke ya soma karanto ta, ni kuma na yi maza na sake maida tafukan hannuna a kan fuskata na rufe saboda tsananin kunya da nauyin da ambatonta a bakina ya yi min, sai dai nayi dabara na karantata cikin zuciyata..
Waiyo Maryam, waiyo Maryamu, Wayyo Mairona, bani da nake wahala da hakuri da juriya a dalilin shi ce nake furta kalmomin ba shi da yake yin yadda yake so ne kuma yake furta kalmomin da yake so ban iya ce mishi komai ba.
Nace in sonki Maryam nace ina sonki kin ji abinda na fada ko ba ki ji ba? Ba dai ke burinki ince ina sonki ba? To sau nawa yau kike ji na ina furta miki wannan kalmar? Maganar yake yi cikin yanayi na jaruntaka saboda gajiyar da ke tare da shi da dai ace so shi ne samu da shiru ya yi ya yi baccinshi don jikinshi ya samu hutun da yake bukata, ni kuwa ina jinshi bance mishi yi shiru ka huta ba saboda gani nake nima tamkar bai yiwa nawa jikin irin adalcin da ya dace ya yi mishi ba.
Washegari da safe ni kan farkawa nayi a makare saboda bude ido nayi na kalli agogo hannunshi dana gani kusa da ni na ga karfe shida ne har da mintoci guda biyar na mike na shiga bandaki nayi wanka sosai na yiwa jikina duk wani abinda nake ganin zai taimake shi nayialwa la na fito ina cikin yin salla ne na ganshi ya shigo dakin ya koma gefen gado ya zauna sai da na idar na shafa addu’ar da nayi sannan ya mika hannu ya sake kamoni ya dorani a kan cinyarshi kamar yanda yayi min jiya, saukin abin kawai babu irin mas’alolin jiyaa tare da shi banda haka kuma a yanzu yana sanye da sabuwar jallabiya ne da ta saukar mishi har idon sawunshi. Kin yi min addu’a kuwa? Na gyada kai a hankali nuna alamar eh, don kuwa ban tashi a wurin ba sai da na yi mishi, ya ji dadin amsar da na bashin, cikin natsuwa ya ce min addu’o’i masu yawa nayi miki Maryam na kuma yiwa Inna. Muka dan yi shiru kafin ya kawar da shirun da tambayata me kike so ki ci yanzu nasan kina jin yunwa musamman ma da yake kin kwanta ba ki ci komai ba, ban yarda mun hada ido ba na ce mishi nafi so in yi bacci. Ya yi maza ya mike na kwanta ya tayani gyara kwanciyar sai da na ce mishi ya yi sannan ya fita ya ja kofar dakin wai don in kara samun nutsuwa.
Na farka ne ina tunanin lalle nayi bacci saboda yanda naji yanayin jikina ya canza ban dade da farkawa ba na soma jiwo muryar Mubarak a falo yana magana da wata da nake zaton Umminshi ce.
To ko Maryam ce kadai a gidan yau kam ai a ba za ta yi girki ba, in ta ga dama tayi in bata gani ba ta bari duk abinda take ganin kamar in tayi ita ta yiwa ta bari ba ita na yiwa aurena ba.
Ban ji maganar Umman ba saboda muryarta ba mai karfi ba ce kamar tashi sai na ji shi yana cewa, eh Umma dukansu nawa ne na kuma yi alkawarin yin adalci a tsakaninsu, to amma yana daga cikin adalcin ne ace don na kwana a dakina marya jiya ace yau ta fito ta yiwa mutanen gida girki? Banji abinda tace ba na sake jinshi ya ce, a’a Umma ku yi hakuri kar ku roketa na gaji da rokon da ake yi mata in dai alfarmar yiwa Maryam girki ne kar ta yi bana so.
Assalanmu alaikum, wata sassanyar murya ce na ji tayi sallama na kuma ji dadi saboda na gane mai ita, a’a Ramatu ce Umman ce ta fadi hakan ta amsa eh ta soma gaisheta kafin naji tana cewa Mubarak sannu kawu, ya amsa tare da amsa gaisuwar da take yi mishi, yaya su babanki da antin, tace sunce a gaisheku.
Ban san me ya gani ba naji yana ce mata, ai tana bacci ne, cikin ladabi ta ce msihi ba dakin zan shiga ba zan shiga kicin ne in ajiye kayan da nazo da shi ya ce mata to.
Tana shiga kicin din naji motsin ruwa ya fara zuba a fanfo na tabbatar zata gyara wurin ne tayi wanke wanke, Inna yarinya ce da yaya Dija ta yiwa tarbiya iyawar iyawarta aka kuma yi dace ita din mai daukar tarbiyya ce.
Tashi nayi na shiga bandaki na sake watsa ruwa a jikina an fito na zauna nayi shafa nayi kwalliya da wani lallausan leshi na sanya ‘yan kunne da sarka na zinarinda a ke yayi loakcin me ludayi nayi matukar yin kyau ga kashi na fito na tsaya a bakin kicin din ta juyo ta kalleni saboda motsin da taji cikin natsuwa ta soma gaisheni mama ina kwana? Na ce mata lafiya Inna yaya su Abbati? Ai da wai zasu biyoni Mamanmu ce ta hanasu zuwa to a kan me? Na yi tambayar daidai na shiga kicin din na dauko kwalbar zaitun da cokali na dora kan dan karamin tire saboda hangen Mubarak da nayi a falo a mike kan doguwar kujera a hankali na matsa kusa da shi na durkusa cikin nutsuwa na tambayeshi, kana bacci ne?
Ya yi maza ya bude ido ya kallen, uh’uh ina jiran farkawarki ne, sai dai kuma idanuwan nashi sun canza launi watakila bacci gami da gajiyar hidimar da akayi watakila damuwa ko bacin rai.
Ba ki karya ba, kai kaci wani abu ne? Uh’uh na fara mikam ishi robar ruwan swan, ya ce a’a na sha ruwa na ce to ungo zaitun magani ne bai yi musu ba ya karba ya ci kwaya uku, wai me za ki ci ne? Na danyi murmushi kafin nace mishi, me yasa ka damu da yawa, a dakina fa nake maganar tayi mishi dadi ko kina dakinki ai ke din bakuwa ce Maryam ban amsa ba na mike na shiga kicin don nasan ina da wasu abubuwan a ciki sai kawai na ci karo da kayan da Inna ke cewa zata ajiye sinasir ne da miyar taushe da ya ji kayan ciki a ciki da kashi na bude oven na sa kwanon farfesun kajin da tun jiya ta aikomin da shi ban samu naci ba ga kuma gasassun kajin da shi Mubarak din ya shigo da su bai barni na tabasu ba, nan da nan na kewayeshi da abubuwa iri-iri kasancewar kuma dama na riga na saba da cin abinci a gabanshi sai kawai na zauna muna ci tare, ga dukkan alamu kuma dadi ne ya kamashi watakila ya ga alamar in ma so ake a takurashi kan abinda zanci to zai iya samun sauki ta wurina tunda zan iya kula da kaina, kina nufin duk da bakuntar dake tare da ke zaki iya hidimominki? Cikin natsuwa na ce mishi me zai hana? To yi min wanial kawari man Maryam, a hankali cikin natsuwa na tambayeshi kamar wanne fa? Tsareni yayi da idanuwanshi kafin ya ce min, zaki barni in zauna lafiya za ki barni in samu natsuwa a tare da ke, na zaki barni in yi hukunci da duk wani abinda kika san nawa ne, za ki taimakeni in fita daga mas’aloli in har ina cikin su.
Ban kalleshi ba na ce mishi in har kayi min bayanin yadda zanyi in yi maka hakan ina ganin kamar zanyi, amma yadda kayi min maganar a haka ai ba zan gane abinda zanyi ya zama ya yi maka wadannan abubuwan ba.
Yana kallona ya ce min, ki taimakeni ki yarda in na saki ki yi, in na hana ki cikin sauki na ce mishi zanyi saboda ba tare da na tsaya yin wani tunani ba saboda yaya Dija da sauran mutanen da suke ganin sun isa su gaya min inji sunyi ta gayamin cewar in ya hanaki ki bari, in ya sa ki i yi shi aure da kike gani ba komai bane face ladabi da biyayya sai ko mututnawa na ce musu to don haka hankalina a kwance na ce mishi to kamar yadda Suma na gaya musu.
Wanka yayi ya tsalo wata irin kwalliya da zan iya cewa ban taba ganin yayi kyau irin na rannan ba ya wuce can cikin daki, zo mana, na tashi na bishi ina tunanin ya yi kiran ne don ina tare da Inna.
Wannan hular da wannan wacce ya fi kamata in saka? Na raba kallo tsakanin hulunan duka biyu kafin ince mishi wannan, bai sake dubava ba ya sanya wacce nace din.
Me da me kike so a kawo miki? Na gane abinda yake nufi na ce ni na fi so in yi girki da kaina, kina amarci kina girki? Ba a yin haka abubuwa sai su yi miki yawa, ki kwanta ki yi bacci ki huta, nace uh amma ai Inna tana nan za ta yi min aiki bai sake magana ba kudi ya cire ya ajiye a gefen madubi, zan turo Isiyaku ki yi mishi lissafin abinda kike so a kawo miki, nace mishi to a dawo lafiya, ya ce Ubangiji yasa ya fita.
Kudin da ya ajiye din masu yawa ne sosai har zuciyata tana tunanin me zan saya da su haka? Ina zaune ina jiran zuwan Isiyaku cikin tunanin ko dai bai ganshi bane ko kuma ya manta ya yi tafiyarshi? Sai ga Isiyakun ya shigo da manya manyan ledoji a hannunshi kicin ya wuce ya ajiyesu na ce mishi, kai Isiyaku ba nice mai girkin gidan ba kai musu can, ya ce a’a nan ya ce in kawo wadannan ga nasu can a waje na ajiye musu, Inna nasa ta duba kaji ne da koda, sai kayan ciki da kuma sauran abubuwan da zan nema ba tare da na tambaya a gidan ba na dawo na zauna ina tunanin a yadda zanyi da aiki irin wannan, da na sani da bance mishi zanyi ba saboda dai karfin hali kawai na ke yi nake daure amma gaba daya jikina ciwo yakeyi sai ga anti Kubra ta yi sallama ta shigo bayan na ji ta tana gaisawa da Rumasa’u a tsakar gida ina ganinta naji dadi ya kamani sannu a zuws anti, sannu ‘yar albarka ke dai ai daga gidan Hadiza nake ina can sai ga mijinki yaje kunyar ambatonshi a matsayin mijina ya kamani saboda yanayin da take magana a ciki, nashi yaje ya kai mata fan hamsin ya ce ta sallami duk wasu baki da suke nan daga wurinta har zuwa gidan baba ya kuma sake bada jakar guda ya ce a sai miki abinda aka san zai yi miki amfani don ya tambayeki kin ce ba kya son komai.
Kunyar anti Kubra ta sake kamani na sunkuyar da kaina kasa har na kasa dagowa, ato ina masu cewa ita tana aiki ne kawai ke kina waje yanzu ai tun a wajen ana tare ne kawai ba komai ake yi ba? Shiru nayi ban iya ce mata komai ba.