Skip to content
Part 56 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Isiyaku ya yi ta shigo da tsaraba yana jibgewa a wani daki na daban wanda yawanci kayan amfani ne ya gama ya miko min jakunkunan guda biyu na dauki daya na mika mishi daya na ce a a mayar min da ita ta ce a’a haba jaka tayi ta zama a cikin mota a sa miki su a daki mana.

Mubarak ya ce ai ba dadewa ma zamu yi ba Inna Kaduna zamu wuce gidan abokina, ta ce a’a ai dai ku ku wuce amma ita wannan ai nan ta zo za ta zauna ta ga yan uwanka su ganta ta sansu su santa in ya so in kuka juyo sai ku biyo ku dauketa.

Shiru yayi ni kuwa naji dadin hakan da ta fada tunda ni kam asalin niyyata dama ai ta zuwa wurina ne ya ce sai mu karasa Kaduna na ce to.

Ashe kuma baki sun zo ta amsa a yanayi na kunya, saboda hada jam’in maganar da akayi sai naji ta ce ni fa amarya ta fito na ce wannan tafiya mai nisa da tayi gashi ba ta gama hutawa ba ta sake yin wata ko da yake dai wannan tai bada ce muka gaisa da matar da na wuto a tsakar gida tajuya ta tafi cikin natsuwa na ce mata, Inna ban san da mutane a gidan ba ni su Izzátu kadai na yiwa tsaraba na tura mata jakar da tsarabar ke ciki, wannan duka su Izzatu? Ai kuwa dai su suka kwashe kayan jakar taki, to Ubangiji ya yi mulu aibarka ya rufa muku asiri ya zaunar muku da wannar aure lafiya lau, ya kuma kareku daga sharrin mahassada.

Mubarak dake can gefe ya ce anin ni kawa nayi shiru.

Ta mike ta fita, ya kalleni, ni fa zan wuce na ce mishi a’a mu kwana tare, da sauri ya kalleni a ina? Na nuna mishi ga dakuna in ma ba zaka kwana anan ba ai ba za ka rasa dakin kwana a gidan ba duk yadda za su kai da jin dadin ganina ai bai kai su ganmu tare ba, ya daure fuska mai don kar in ga yana wasa nima nayi kamar ban ganshi ba na kau da kaina gefe ta sake shigowa zata wuce, cikin natsuwa ta ce min wai so nake in yi sauri don mijinki ya danci wani abu kafin ya tafi, ban kalleshi ba na ce mata ai kwana zai yi, da sauri ta ce au haba? Lalle yau da bako a gidan to a zo a gyara muku wancan daki mana, ta fita tana kiran Izzatu mai yawon nunawa kawaye tsarabar da aka kawo mata.

Amma ba kina shirin turani wancan dakn ne ke ki dawo nan ki kwana ba ko? Na yi maza nace mishi aa, share dakin tasa aka yi ta canza labule ta fitar da katifar dake ciki ta sa aka kai wata akayi shimfida yana dawowadaga sallar magariba na ce mishi ko zamuje can ne in kai mana abinci? Bai yi musu ba daki ne har da bayan gida a ciki ya fita sallar isha’i ya dan tsaya wajen mai gidan suka gaisa wanda shima ya ji dadin ganinshi don har nan ya biyoni wai mu gaisa Innan ce ta ce mishi ai nima zanzo in gaisheshi ya ce to ba yanzu ba a barni sai da safe saboda duhu.

Nayi hira yar kadan wurin Inna saboda sanin da nayi mijina yana can shi daya a dakin, sai da safe Inna, ta ce min to sai da safe ‘yar nan dauki wannan kwanon ki tafi muku da shi na ce mata to, a dakin kwanciyar namu Mubarak ya yi kwanciyarshi irinta shi bako ne, ni kuwa na mike na zauna kan shimfidar na soma zare kayan da ke jikina daidai da daidai ina yin wurgi da su ba tare da ina lura da inda suke faduwa.

Da sauri ya dago kai ya kalleni a hankali cikin murya kasa-kasa da ke kare baiyanar da bakuntarshi a wurin ya ce min, “Ke Maryam a gidan mutane kike irin wannan tubewar?”

Ban kula shi ba, ya yi maza ya jawo gefen babbar rigarshi ya rufe fuska, wai ma ba zai bari ya ga abin da nake yi ba, ban daina ba bar na kai ga babu abinda ya saura min sai brazier da ke jikina na mika hannu daya da nufin in karasata itama sai na ji caraf ya rike hannun nawa.

“Tun da dai abin da kike so kenan to barni kawai zan karasa wannan din.”

Ban sani ba ko bakuntar da yake ji a zuciyarshi ne ya hanashi makara duk da abubuwa masu dadi da suka kasance a daren wadanda suka hanashi samun baccinshi, kiran sallar farko naji ya tashi ya kammala abubuwan da zai ya yi nufin fita masallaci ina jinshi yana tashina ban ayrda na tashin ba.

Mubarak da dole dole ce ta sanyashi kwana a gidan nan sai gashi shi da kanshi ya cewa Inna zai bar tafiyar sai gobe saboda ganin yanda yan uwa ke ta isowa suna fadin sun zo ganin babban yaya da amaryarshi, ita kuwa Inna duk wanda ya shigo mace ko namiji dan uwa ne ko abokan zama abokan mutunci sai ta dauko wani abu cikin tsarabar da mukazo mata da ita ta mika mishi a yi ta godiya ana sa albarka, shi ma Mubarak rannan ya yi kyauta har na rinka tsorn kar dai kudin nashi su kare sai dai kuma anyi sa’a basu karen ba, bai yiwuwa in tsaya cewa Inna tayi farin ciki sai dai kawai in ja bakina in yi shiru.

Washegari da hantsi ina zauze a gabanta yayin da Mubarak yake waje wajen mai gidan don yin sallama dashi saboda tafiya za mu yi sai ta kalleni ta ce min “Ubangiji ya yi miki albarka ya rufa miki asiri ya baki zuriya mai albarka, ya jikan mahaifiyarki da rahamarsa, in kunje gida kuma ki sa hannu ki kar6i girkin gidan mijinki da yace min baki soma ba ki rinka girki kina baiwa uban mijinki yana cin abincinki, itama matar gidan uwar taku kar ki yarda ki samu mas’ala da ita don tana da tasiri mai karfi a kan al’amarin mijinki sannan ya’yanshi ki sa hannu biyu ki rikeiSu babu ruwanki da uwarsu kin ji ko baki ji ba ko?

Na ce “Naji Inna na gode Ubangiji ya kara girma.

Izzatu ta shigo dakin kuka takeyi wai zata bini na ce “To Inna inje da ita mana ai itama ‘yar yata da na goya haka take kamarta.

Ta yi maza ta ce “A’a ba yanzu ba in kin haihu dai za ta zo ta tayaki jego.” Shiru nayi ban amsa ba.

Inna ta ban tsaraba kashi biyu tace daya namu daya kuwa na yaya Dija, muna barin Jaji Kaduna muka karasa gidan Abdulhamid muka sauka shima mata biyu ne da shi sai dai shi amaryarshi har ta haihu nan din ma fafata kishi mai zafi akeyi a tsakaninsu.

Mun dawo da kwana uku anti Safara ta haifi da namiji zuwa ginin yaron da nayi shi ne shigata gidanmu na farko tun taifiyata Gaidan shi ma barka kawai naje bai yarda naje sunan ba wai ban kai zuwa suna ba don haka Rumas’au ya tura taje a madadina duk da ba wani shiri muke yi ba.

A wannan lokacin ne akayi gagarunin zama tsakanin Rumasau da Mubarak da kuma iyayensu gaba daye ashe duk wani iya shege da take yi da nunannin ita da miji kut da kut suke a manne da juna ita kishi ne kawai ya sa take yin hakan tsakanin nasu ba mai dadi bane.

Wurin yan tsegumi masu kai kawo tsakanin jama’a na samu labari don a bakin Mubarak dai ba zan ji ba, saboda baya yin maganar wata a wurin wata musamman ace ba ta nan.

Ashe wai tun sanda babana ya zo ya yiwa Alhaji Muhammadu maganar nan cewar in har Mubarak yana da muradin aurena bai fasa ba to su zo su karbi auren ya basu, ya ce eh basu fasa ba, da ta ji maganar ta rokeshi va yi mata alfarnmar neman wata ya aura in yaso ma kar ya auri guda daya ta yarda za kuma ta zauna da su lafiya in har ni zai hakura da ni ya ce mata a’a wannan bai shafe ta ba in tana da wani abin dai ta fada, ta ce ita kadai ce ya ce to a’a ba huruminta bane don ba itace zata zabar mishi matar da zai aura ba, tun daga nan in yazo gareta da bukatarshi bata sauraronshi ba ta yarda da shi, haka suka yi ta zama har akayi bikina watanni uku don haka da na zo gidan shi kuma sai bai sake komawa ta kanta ba shiga dakin yake yi ya yi baccnishi in gari ya waye ya tashi ya fita, ba ki ga yadde ta kare ba, na cewaa mai bani labarin ai bana kallonta, ta ci gaba da bayani, ai yanzu ba ta fi rabin da ba don irin wannan wulakancin ciwo ne da shi to yanzu shi ne ta gayawa kakar tata irin zaman da sukeyi shi ne akayi zaman to yanzu wai an sasantasu shi anyi mishi fada an gaya mishi laifinshi ya ce a yi hakuri zai gyara itama anyi mata na ta fadan ta rokeshi gafara ya ce ya yafe.

Hausawa suka ce wai kishi kumallon mata gashi dai dama can ban san irin zaman da sukeyi a tsakaninsu ba, amma da akayi min wannan bayanin sai na dan ji nauyi a zuciyata nan take kuma sai ta fara tunano min to wato abinda ya faru kenan shi yasa jiya na ganshi ya makara a dakinta bai kuma iya fitowa mun karya da safe ba har na gaji na karya a wurina ni da Inna wai yana bacci kan kace meye wannan sai zuciyata ta soma nunawa idanuwana irin bare-bare. da zumudin da Mubarak din yake yi a kan daidaitawar tasu nan da nan sai naji na kullace shi a cikin raina.

Kusan sati biyu ya kasa gane al’amarina tun yana kallon abin a wani irin yanayi har dai ya gaji ya tambayem Kina da damuwa ne? Na ce babu, to me ke faruwa ne? Na ce ba komai, a’a yaya za ki ce min babu komai, na mike na tafi na barshi wuri bai sake ce min komai ba muka ci gaba a haka. Rannan mun kai sati hudu a wannan lokacin ko yarda mu hau gado daya da shi bana yi cikin dare ya taso ya zo ya sameni a kan katifar da nake kwance na yi zumbur na tashi na zauna, wani irin lalataccen kallo ya yi min, ke kar ki maidani sakarai mana kina ganin kamar wai zan tilastaki ne? To a kan me? Ai ba haka nake ba ko sanda nake da mace daya bana wannan shirmen balle yanzu.

Maganar tashi ta soki zuciyata naji zafin ta ba kadan a raina na ce ai kuwa dai sai dai mu yi ta zama a haka in don ka ga ana kai kararka ne, ya katsemin tunanin nawa a dalilin maganar da ya yi, so nake in tambaye ki wane laifi nayi miki? Na tabe baki tare da girgiza kai don in nuna mishi bai yi min komai ba, ya zubamin ido yana kallona haka kawai kike nishadin ki ka ga bari ki yi min wulakanci? A zuciyata nayi nufin ce mishi eh sai dai ina dagowa da nufin yin maganar idanuwanmu suka hadu sai naji ba zan iya ba nayi maza na sunkuyar da kaina kasa, ba kya ganin kamar in na gaji da hakurin da nakeyi zan iya ramawa don kema ki ji inda dadi? Cikin natsuwa na ce mishi ai gara ka raman, ya ce to shi kenan ya mike ya koma in dai ya fito ya yi kwanciyarshi.

Washegari da muka tashi ko gaisheshi ban yi ba na ci gaba da harkokina na kuma zuba ido cikin sauraronta ina ramakon nashi zai faro.

Ina cikin dakina a kwance sai kawai naji sallamar yaya Dija da sauri na taso ina rike da dankwalina a hannuna kai yaya Dija ba kya ko jin tausayina, sai ki ki zuwa in yi ta jin marmarinki har in gaji in hakura,  bata amsa ba ta nemi wuri ta zauna na wuce naje na kawo mata abubuwanci citrus wrapes,  perrz da grapers ciko farantin nayi nazo na ajiye mata na sake komawa naje na kawo mata soyaiyan naman rago na sake komawa na kawo niata kindirmo na sake juyawa na dauko wani kwanon tayi maza ta dago ido ta kalleni, ke bana son rashin hankali ina zan kai wadannan abubuwan da kike taramin?  Zo ki kwashe su duka ‘ya’yan itace kawai nake bukata yanzu nace mata to.

Wani abu ya faru ne? Tayi min tambayar bayan mun gama gaisawa a hankali na tambayeta me kika gani? Idonta yana kaina ta soma yi min magana cikin natsuwa, Alhaji Amadu ne ya aika a gayawa babansu wai in babu damuwa yana son ganina yanzu, na taba baki tare da girgiza kai, fuskarta tayi saurin canzawa alamar ba ta ji dadin yanayin amsar da na bata ba kan tace min komai sai gashi ya shigo adonshi yayi kyau gashi sai kanshi yake yi.

Ki yi hakuri na tasoki, ta ce a’a babu mas’ala ina fata dai babu damuwa, ya ce eh babu a hankali ya soma magana, ba ina nufin kawo kararta ba ne don gaskiya ba dabi’ ata ba ce ma yin hakan amma ina so in rokeki a yi mata magana saboda bana son fitina a tsakanina da ita, na tambayeta in wani abu akayi mata ta fada ko ba ni ba in wani ya yi mata tana da yancin gaya min domin zamana take yi taki ta yi magana nace zan rama abinda take yin don itama tai in da dadi ta ce wai gara inr ama, kinga kenan tana sane da abinda take yi tana yi ne kuma da wata manufa shi yasa na neme ki me akayi mata? To in an yi mata sai ta neme ka da fitina wane irin al’amari ne wannan? Me aka yi miki? Nayi shiru kenan gobe ko ya ganki kina yina abinda kika ga dama kar ya nemeni don ban isa ki gaya min damuwarki ba? Ya mike ya fita ya barmu ni da ita, tana ganin yaf itant a soma yi min fada mai tsanani ni kuma na soma yi mata kuka don tayi shiru, taki yarda ta yi shirun.

Ke ba za ki gane abubuwan ba ne, a halin da ake ciki fa ni babu mai sona a gidan nan nice bare, su kansu a hade yake in banda kwarata babu abinda ake son gani.

Me suke yi miki na kwarar? Nayi shiru na rasa ta inda zan bullo mata, to a soka a gidama ai halinka ke ja maka kuma yaushe kika zo gidan har kika soma wadannan maganganun? Kenan har kin fara samun mas’ala da mijinki Maryam in banda mummunan tarbiya da kika samu? To kin girma gaban mai cewa miji ya kunshe baki kamar masai ai ni dama gabana yana faduwa ina tunanin wane irin zaman aure za ki yi? Kuka sosai ta soma yi har tana fyace majina da zaninta, wace irin magana kike so kija mana? Yanzu a irin yanda akayi auren nan naku da irin dawainiyar da mutumin nan yayi babu abinda ba a fada ba babu wahalar da baiyi ba ga bacin rai a kan auren ne fa matarsa tayi ta tsalle tana cewa gara a mata kishiyoyi hudu da ke ke kadai bata sani ba ma ashe sakarya za a kawo mata, kai ba a kyautar zuciya Maryam da na samo wacce tafi dacewa dake na baki.

<< Halin Rayuwa 55Halin Rayuwa 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×