Skip to content
Part 57 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Ganin bacin ranta da ambaton matarshi da tayi ya sa ni ce mata, to ai yafi sonta da ni kinga bare-baren da yake yi ne… Ban karasa ba ta katseni, ba dole yafi sonta dake ba ita sulhu take nema a tsakaninta da shi ke kuwa kina nemanshi da fitinaa, haba in banda namiji bai gajiya da abinda yake so wane dadi yaji ne a tare da ke kuma karya kike yi mishi wane bare-bare zai yi a kanta da ya wuce wanda ya rayu yanayi a kanki? Kuma sai me in ya yi ba matar shi ba ce, ba da ita kika sameshi ba, na kara tsaranta kukan da nakeyi saboda tsananin bacin ran da kalamananta suka kara min gaba daya yaya Dija ba zata fahimceni ba ban san yanda akayi ba sai naji bakina yana ce mata kwacemin shi akayi aka bata, kwace min shi akayi saboda ita tana da gata ai ba nata bane, ni ba mijinta na aura ba ita ta auran min.

To yanzu ya ya za ki yi Maryam? Tambayar da ta yi ta fito a lafazi na baiyanar da canjin da zuciyarta ta samu, ki yi hakuri ai kaddarace ta yi miki hakan ba wani ba ne, itama matarshi ce rabon ta kuma yafî naki zafi baki ga ke har yanzu baki da komai ba? Ita wata tara babu kwana biyar tayi ta haihu a gidan nan ina lissafi ban yi magana bane kawai kina nufin da ya aureki a wancan ba zai aureta ba’? Zai aure ta domin ‘ya’yan dake tare da itan nashi ne.

Don haka ki yi hakuri, ina share hawayena da bakin gyalena na ce, to shi kenan ni na hakura ya daina taba ni, bana so bana so na hakura da shi tunda rabon ta ma yafi nawa karfi to na bar mata shi ni ya kyaleni kawai, na ci gaba da wani kukan.

Mubarak ya sake shigowa bayan ta amsa sallamarshi, bari muje in saukeki sai in wuce don za ni Bauci, to ko zakaje kawai in na gama sai in tafi? Ya ce a’a muje kawai ai babu damuwa.

Ta tashi suka tafi amma dai ranta a bace watakila saboda ganin kamar zuwan nata bai samar da wata mafita ba.

Ina zaune a falon ni kadai ina tunanin haushina take ji saboda bata san kishi bà saboda tayi sa’a ita kadai ce a gun mijinta ba zata iya fahimta ta ba saboda bata taba jin irin zafi da ciwon da nake ji a cikin zuciyata ba.

Da kyar na iya tashi nayi wanka nayi sallah na hau gado na kwanta ko nemarwa kaina abin da zanci ban yi ba ina jin Rumasa’u tana ta kyakyacewa da dariya na kuma san dadi ne ya kamata Mubarak ya yi tafiya a ranar da zan karbi girki.

Nayi duk abinda na sabayi na al’adata na sa makulli na kulle kofata na hau gadona na kwanta nufina wai in yi bacci da wuri sai dai baccin bai daukeni ba wajen karfe tara da rabi na dare na ji ana kwankwasa kofar tawa, na ta so nazo na bude shi na gani a tsaye fuskarshi a daure alamar ranshi ya baci da kulle kofar da nayi, ban ma tsaya a falon ba balle in yi tunanin yi mishi wani abu ina jin shi ya yi kaikawon da zaiyi ya gama, maimakon ya shiga dakin da yake kwanciya ya kwanta sai naji shi ya shigo wurina nayi maza na gyara rufata.

Tashi muje wancan dakin, nayi maza na ce mishi a’a ni a nan zan kwana wani irin cafka ya yi min mara dadi kan kace meye wannan sai gani a inda yake nufin ganin nawa, yi hakuri ki sa hannu ki rage kayan jikin naki, na sake cewa uh’uh ba zan yi ba bana so kar kuma, nayi maza na canza maganar saboda ganin abinda ya soma yi to ai kai kace baka tilasta mace ko sanda kake da guda daya ma baka yi hakan ba balle yanzu ya ce eh ita kadai zan rinka yiwa wannan adalcin banda ke, tunda kin bari na gane ki na riga na gane ita daban ke daban, ni kuma zan iya zama da ku dukanku bisa tsarin da ko wacce take so banda haka kuma daga yau ba zan sake kai kararki ba tunda na gane baki da mutunci mara kunya kawai sokuwa sakarya wacce gata yia hanata fahimtar abinda take ciki, zagin da ya yi min din zagi ne na wulakaci bai kuma hanashi yin duk abinda ya shirya yi ba.

Ance miki tsoro ne ya sa ni kai kararki wurinta? Tana da girma ne a wurina da kika barta har ta fita baki bata hakuri kan bacin ran da ta gamu da shi ba a dalilinki, sannan duk maganar da kika yin naji wani abin da baku fahimta ba ke da Rumasıi’u shi ne ni din babu wacce za ta sa ni n yi abinda banyi niyya ba, sannan ba zan saki wata a cikinku wani kato yaje ya auran min mata ba, ba kuma zan yarda in karkata karkatar da zata cutar da ni ba, dukkanku ina kaunarku, ina kuma son dorewar zamana da ku don haka zan zauna da kowacce ne a bisa tsarin da ta nemi mu yi zaman ni da ita wacce ta nemi zaman lafiya mu yi wacce ta nemi sabanin haka ma ina shirye in wani zai yi min laifi in kyaleshi kuma ina tabbatar miki in kikayi min ba zan kyaleki ba, ba zan yarda ki bata min rai ki ga kamar kin ci bulus ba za ki rinka tuna wane da kikayi min kaza nima nayi miki kaza ba kalau kika kwashe ba, don haka admision din da na saman miki na karanta Is!amic law a jami’a na janye shi, na fasa ba za ki yi karatun ba. Na soma kuka ina bashi hakuri ya ce ai sai ki yi ai ba hauka nake yi ba saboda kishi sai ki hanani taba jikinki tsawon wata guda? Kina so ne ki rinka tirsasani da hakan? Ai itama ban barta ta ci nasara a kaina da hakan ba balle ke, zuciyata ta kara kuntata da zafin da ke cikinta ya kara karuwa kwoacce magana zai yi sai ya hadani da ita kowacce magana zai yi sai ya nuna min ta fini, za ki rinka tuna sanda kika hanani kanki na hanaki, karatu saboda na gane wanda kakayi a baya bai yi miki amfani ba don bakya aiki da shi nan gabe in kika koyi sanya iliminki a cikin kanki sai mu san abin da muke ciki.

Babana ya shirya zuwa Gaidan wurin danginshi karo na farko cikin shekaru talatin da biyu shi da anti Safara da jaririnta da su yaya Dija yaya Ibrahim nema zai kaisu a cikin sabuwar motar da tace min Mubarak din ya bashi, banje musu sallama ba banje musu sannu da zuwa ba saboda bai ga dama ba, na rame na zube haskena ya ragu saboda abubuwan da na samu kaina a ciki, a hakan kuma na soma girkin gidan gabadaya saboda yace in karba ko dama can kuwa tun dawowar da muka yi daga Jaji na soma yiwa baba abincinshi na safe da na dare saboda kasancewarshi mai lalurar suga.

Banje ko ina da fara yin girkin ba naji hirar Rumas’au da kawarta tana gaya mata cewar a’a abubuwan sunyi sauki sun kuma lafa daman ashe doki ne kawai ya firgitata har ya nemi sata ta gudu ta bar ladanta ai yanzu wayar gari take yi tana kwance tana hutawarta a dakinta nike tashi da sassafe in yiwa yara wanka in shiryasu in basu abinci su ci su tafi makaranta dole kuma in yi ko don in zauna da shi lafiya tunda shi a kan ya’yanshi babu abinda ba zai yi ba ko ita da ta haifesu lallabashi take yi in dai a kansu ne.

Raina ya baci na samu kaina cikin wani al’amari nayi kamar in daure in ci gaba kawai da abinda nakeyi sai kuma naga ba zan yi ba, in dai hidimar yaran zai iya zama sanadin zamana to ina ganin gara kawai ya zama ko na samu in huta da bacin ran da nake gamuwa da shi gashi ko bacci bana iyawa matukar yana dakinta to ni kuma bana iya bacci da daddare gashi tsakanina da shi abin ya ki dadi.

Na karbi girki ina cikin dakina a kwance da safe ban fito ba balle in yi abincin karyawa balle in yiwa yaran wanka, Ummulkairi ta shigo falon ina jinta tana gaya mishi baba wai inji maman mu wai zamuyi lattin makaranta, to menene? Wai Anti tazo tayi mana wanka ta shiryamu.

Ina jira in ji ko kiraná zaiyi ko me zai yi sai naji ya ce mata ke tafi bani wuri ba a dade ba naji isowar uwartata, na ce Ummu tazo ta gaya maka za su yi lattin makaranta, ya ce to menene? Ta danvi shiru kafin ta ce, nace, wai wankan ba zata fito ba ne? Wacece mai wankan? Ke kuturwa ce da ba za ki yiwa ‘ya’yanki wanka ki shiryasu ba, sai wata tayi musu?

Ta ce ahh hakama zaka ce? To su bar zuwa makarnatar mana ya’ ya na ne? Ai dama na sani tunda ka samu kwana biyu ya yi maza ya katseta, in kika gayamin magana a gaban yara, bata tsaya ba ta juya ta fita, ban san yanda akayi ba sai naji an tafi kaisu makarantar bai kuma dai fita ba balle ince ko shi ya yi musu girki biyu a jere ban yi ba. Rannan ya zaunar da ni yana tambayata, kina da mas’ala da shirya yara da safe ne Maryam? Na ce mishi ch, menene mas’alar? Na ce a canzamin wani aikin kawai ba wannan ba, bai ja ba ya ce, to ki rinka yi musu lesson, na ce to, za ki yi? Na ce eh zan yi, ya ce to shi kenan na tashi nayi tafiyata ba tare dan a tsaya gaya mishi wani dalili ba balle aje ana kace nace, da na samu zarafin gaya mata magana kuma sai na gaya mata cewar ni din zama kaina nake yi a wurin mijina ba zaman wani ba duk wata kunatawa da zan yiw wani to zan yi ne don in kara gyara auren nawa amma ba don ina tsoron kar ya zamo mishi wani sanadi ba.

Rannan ya dawo daga tafiya ya shigo dakina ya sameni Inna da Izzatu suna gaisheki da sauri na tambayeshi kaje ne? Ya ce min eh, na ce amma baka gaya min zaka ba’? Ya ce e ban yi niyyar cewa najen ba, sakon da ta bani in baki ne ya sa na gaya miki, tana ta tambayata wani har yanzu haka kike babu komai? Nace mata eh shi ne ta bani wani ita ce tace ni kawo miki wannan amma na gaya mata cewar ke din maganin hana haihuwa kike sha, ban yi mamakin jin maganar a don naji irinta ko makamanciyarta a bakin Umma, bance mishi komai ba na sa hannu biyu kawai na karbi Itacen na ce mishi na gode na kai daki na adana.

To a haka abin yake jifa-jifa zan danji wasu kalamai suna fitowa daga bakinshi wanda nasan ba ganin abin yayi ba gaya mishi aka yi kamar in tambayeshi ta inda maganganun suke zuwa mishi sai na fasa na ja bakina kawai na yi shiru.

Ni da Rumasa’u kuma a wannan lokacin wani irin zama mukeyi na kai da gindi iyaka dai naki yarda mu yi zaman gaba zaman da babu wata mu’amala a tsakaninmu ko bata kulani ba gaisheta nakeyi sai dai hakan ba yana nufin zata yi min in kyaleta ba ne ina kuma mu’amala da yara in musu lesson in yi musu alheri gwargwadon iyawata in kuma sukayi min ba daidai ba in hukuntasu tun ina yi musu hukuncin a ce su jira babansu in ya zo su gaya mishi har abin ya zama rikici tsakanina da ita ban daina ba shima kumaban taba ji ya yi min magana ba.

Rannan Mubarak yana dakin ban san yanda akayi ba dasawa mukeyi tun safe dai nasan yake tattalina yake tarairayata watakila saboda yana bukatar daren ya zamo mai cike da kwanciyar hankali, to dansa hannu ki rage kayan jikin nan naki mana Maryam yaushe rabon da ki yi min irin wannan mutuntawar? Ba fa najin dadin irin wadannan abubuwan, na tashi zaune na soma cire kayan jikin nawa saboda nima ba jin dadin karfin da yake gwada min nake yi ba, dadi ya kamashi, yanzu in duniya tana da gaskiya Maryam ni ace tsakanina da ke zaki iya hanani jikinki? Wannan jikin dai to na wane ne? Ban kalleshi ba nace naka ne, to me nayi miki ya sa kike gayawa mutane ba za ki yi a zama da ni ba? Wa ya gaya maka? Ya ce uh’uh kar ki tambayen wanda ya gaya min kin fada ko baki fada ba? Cikin natsuwa na ce mishi, na taba gayawa yaya Dija banda ita ban taba gayawa wani ba itama kuma nasan ba zata fada ba, ya yi maza ya ce haka ne me nayi miki? Bance mishi komai ba sai naji ya ce min, kishi ne ya yi miki yawa Maryam ni kuma bakya barina inji tausayinki sai kice zaki tirsasani, ba zan iya ba, ba zan iya yarda da hakan ba saboda ina gani na cancanci abubuwa guda uku daga wurinki saboda dalili guda daya, na cancanci kulawa tausayawa da kuma rangwame, ki kula da ni ki kyautatamin saboda kasancewata a tsakaninku a tsakanin naku kuma ina cikin zargi, dole kuma in yi adalci saboda shari’a bata barni in yi abinda naga dama ba ta kewayeni da dokoki in nayi miki kuskure kuma ki yi min rangwame saboda kin san kuskure nayi kin sani sarai ba zan 6ata miki da gangan ba ai ina gudun bacin ran naki bakya ganewa na wadannan abubuwan kuma don kin yi min su ba komai bane saboda ina sonki ba dabi’ata bace fadin hakan amman kin sani na koya karfi da yaji a hakan kuma ban tsira ba. A hankali na ce mishi, to ka yi hakuri, ya ji dadi sosai, a hankali ya sake ce min, to yi min wani alkawari bayan hakurin da kika bani don in kara samun natsuwa a raina, ba zan sake hanaka jikina ba, ya sa hannu juyar da ni ta yanda muka fuskanci juna, ba za ki sake ganin bacin raina ba kenan ai ko laifi kikayi nasiha kawai zan rinka yi miki ba fada ba, ai da wata ce tayi min yanda kika yin sai in bata wata shida to amma ke da yake kin san ba zan… Na katseshi ta hanyar tambayarshi, wa ya ce maka ina hana kaina haihuwa? Ya ce uh’uh ai nace kar ki tambayen amma ba ga magani nan Inna ta ce ta kawo miki ba ki sha ba me yasa? Yaya Dija ce ta ce in ajiyeshi tukunna, ya danyi shiru kadan kafin jimawa ya sake tambayata, da ma ita ma tasan da wani abu ne? Nayi shiru to shi nę ni ba za ki gaya min in sani ba, In ma in gaya mata hankalinta ya kwanta, kinga yadda ta kosa taji kina da wani abu kuwa sai kace bata taba ganin jika ba.

<< Halin Rayuwa 56Halin Rayuwa 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×