Skip to content
Part 58 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Tun daga ranar muka koma zama mai dadi tsakanina da shi sai dan abinda ba za a rasa ba ban sake yarda wani abu ya faru tsakanina da shi da ya zama dalilin da nayi mishi rowar kaina ba, hakan kuma sai ya zama sanadin raguwar bacin rai a tsakaninmu.

Ana cikin hakan cikina ya kai watanni bakwai yaya Dija ta soma yi min aiken magugunan zaki da saukin nakuda sai dai bana sha don basa yi min dadi rannan ta zo dubani muna hira sai ta ce min bakya shan magungunan saboda bakinki ya saba da zaki bari zan kara tambayar baba Lami inji rake ne yake maganin zaki ko zuma ne? Wadannan kam ai za ki sha ko? Nayi maza na ce garama dai ace raken ne, to ki dai bari in kara bincike tukunna nace to.

Tun daga washegarin ranar na soma shan rake a matsayin maganin zaki da kuma saukin nakuda, sai i wuni ina sha ina gyatsarshi ina karawa in naga ya kusa ya kare mi ince Isiyaku a kawo min rake ya ce to ya kawoshi cikin wheelbarrow, ke Maryam kin tabbatar raken nan da kike sha haka maganin zakin ne ko? Ince mishi eh baba Lamin gidan su yaya Dija ce fa ta fada ita kuwa ka san babba ce haihuwarta goma sha hudu sai Mubarak ya ce min to babu laifi.

Rannan na wayi gari bani da lafiya nayi maza na yiwa baba abincinshi na safe da na dare na aike mishi da shi saboda tun daga jin cabkar farko da nakudar nan ta fara yi min na gane uh lalle da magana ba karamin artabu za a yi da ita ba. Kafin hantsi har na fara gundura da ita na fara gurnani ina mita tafdijan yanzu duk uban raken nan da nayi ta sha dama haka zamuyi da nakudar nan?

Mubarak ya kalleni ya kawar da kai, to rake da kika yi ta sha ba dadi kika sha ba? Na soma kuka, yayi maza ya dakatar da ni, ke Maryam tsaya in gaya milki mata fa basa kuka in zasu haihu har ki yarda ki yi abinda Rumasa’u za ta zo tana yi miki gori don ita ba ta kukan haihuwa.

Hankalina a tashe na ce to kar tayi din mana ni ina ruwana? Ya mike ya kama hanyar fita tare da fadin, bari in kira su Umma su zo su kaiki asibiti da wuri tun baki jawa kanki wani abin magana ba a gidan.

Suka zo suka dudduba ina aa, ta ce uh uh uhh tafi can lalle yau za a yi ta, ba za a yi komai ba, lafiya yau za ki haihu ai duk wanda kika gani da danshi abinda ya ji kenan kafin dan ya kai ga zuwa hannu.

Waiyo waiyo kwankwasona ai yau kam ina jin gabadaya zai ratattake ya zube a kasa da dai ace na san haka ne da ban bata lokaci ba ma wajen shan raken nan.

Rumasa’u ta kyalkyale da dariya har tana neman wurin zama, a dalilin dariyar ta tsananta lalle yau mata zasu haihu tafdijan.

Takaici ya kama Mubarak ya rasa yanda zaiyi dani to wai ke babu dama ki rufe bakinki ki yi shiru ne? Umma ta ce a’a to wai kai ina ruwanka da ita ne? Nace uhun kyaleshi kawai bai san yanda abin yake ba ne waiyo waiyo kwankwasona.

Sannu Maryam, Umma ce mai yi min sannun sai in ce mata yauwa Umma na gode.

A haka mukaje asibiti muka samu yaya Dija don an gaya mata za a kaini asibiti, ita kam saboda takaici ji ta rinka yi tamkar tayi amai don bakin ciki, to wai ke ba dama ki yi shiru ne? Sai ince uh uh yaya Dija ba ki fa san abinda nake ji ba kin san ke naki masu saukin kikeyi da rakin da magana, ganin da kukan da ihun kiran likitan gaba daya basu sa haihuwar tazo ba sai da lokacinta yayi wajen karfe goma da rabi na dare gabjejen yaro kato ga girma ga nauyi tubarkalla gashi mai kyau sai raba idanuwa yake yi tamkar dai ace kallon mutane yake yi.

Suna Mubarak ya yi irin wanda Rumasa’u da yan uwanta sukace wai bai taba yi ba ya kuma sanyawa yaron suna Muhammad ya kara yiwa babanshi takwara bayan da ya yi mishi da danshi na biyu wanda yake namiji ‘yan uwan Mubarak na Jaji sunzo sunan ba kadan ba sun kuma zo min da alheri mai yawa, Inna ma ta cika alkawarin da ta yi na turo min Izzatu ita da Inna ne da kuma tsohuwar da aka daukar mun suke tayani hidimar jegon.

Duk kokarin Mubarak na ya boye ya barwa zuciyarshi al’amuranshi don ya samu tsaida adalci tsakanin iyalinshi ya kasa kawar da kai a kan al’amarinshi yana ganinshi yake sakin lallausan murmshi na kuma san da wuya in har ya san sanda yake yin hakan.

Wani irin lafiyayyan jego nayi ni da yaron muka zama tubarkalla in banda ina aka saka damu babu abinda Mubarak yake yi da mu.

Rannan ya shiga dakina ya fito a lokacin nan kuwa satina uku ne da haihuwa na tsala wata irin kwalliya da in ka ganni sai kayi zaton ranar ne zan karbi hidimar mai gidan, bishiyoyi nayi tsakar gida ina rungume da yaron a kafadata, karbeshi mana to ba ka ce wurin baba zaka ba?

Kaje mishi da shi mana, maganata nakeyi ba tare da nad amu da zaman Rumasa’u a tsakar gidan ba.

Mubarak ya juyo ya karbeshi yana kara lillibeshi tare da fadin, ki fa rinkayin hankali da shi girman jiki ne kawai… Bai karasa ba sai kawai muka jiwo Rumasa’u ta kwallara ihu da sauri muka juya don ganin abin da ya sameta, kwankwaso naga ta rike da iyakacin karfinta, gabana ya yi mummunan faduwa don tsoron abin da take shirin yi don kuwa damkar da naga ta yiwa kwankwason nata irin wanda na rinka yiwa nawa kwankwason ne a ranar da nayi gwagwarmaya da nakuda waiyo-waiyo kwankwasona, Umma ina jin dai yau din nan za a yi abinda ba a taba yi ba don gani nake tamkar kwankwason nan nawa zai tarwatse ne ya ratattake ya zube a kas,a me rake kai yara ku kira min mai rake.

Mubarak dai tunda ya yi mata kallo guda daya bai sake ba balle ya nuna ya ji ko ya ga abinda take yi, hannu biyu kwai ya saka ya dauke danshi ya wuce ya yi tafiyarshi da shi ya barni nan wurin a tsaye ina kallon busasshen wulakancin da Rumasa’u take yi min, ni ba abin in sureta in fyadeta da kasa ba damben tsiya za mu yi kafin in kaita kasa don itama karfi ne da ita to balle a halin da nake ciki yanzu na jego danye.

Humhum hum waiyo waiyoo bayana in dai haka raken yakema to ba zan sake shanshi ba, ta kwashe da dariya ai kuwa dai an bar dadi.

Na shigeta nayi tafiyata na shiga daki na zauna ina jirani zuwan Mubarak don ya san da ni takeyi amma ya ja bakinshi yayi shiru.

Yana shigowa na soma magana yanzu nan haka matar nan za ta yi tayi min irin wannan wulakancin a gidan nan ba za ka tsawatar mata ba? A fusace kwarai ya ce min an ki a tsawatar din sanda kikeyi ban yi miki kashedi ba? Bance miki za ki yi abin da za ta zo tana yi miki iya shege da shi ba don ita bata kukan haihuwa, kikace tayi din, sai kuma yanzu da kika jawa kanki abin magana inje ina tare miki? Ba zanyi ba in taji kin yi shiru ba ki tanka mata ba za ta gaji ta bari ai babu abin da ya tabbata kar ki kulata kin ji? A kan dole na ce mishi to don na gane ba zai yi komai a kai ba.

Ta tasoni a gaba abin har ba a magana, kyakkyawar dariya in taji nayi sai ta shiga kwalawa mai rake kira.

Rannan kawai nayi sa’a tana cikin tsala tsiyarta a tsakar gida tana murde-murde da iface-ifacen a rike mata kwankwaso zai ratattake ya zube a kasa sai kawai na ji muryar baba yana kwalawa Ummana kira,  ina Ummulkhairi ta ke? Da sauri Umman ta fito tana rike da dankwalinta a hannunta, gani Alhaji lafiya dai ko? Bai amsa mata ba ya soma jero mata tambayoyi, yanzun nan kina nan a gidan nan ake yin wannan iya shegen baki hana ba? Ko kina jira ne sai abin ya zama tashin hankali a tsakaninsu? A kidime Umma ta ce mishi, nayi magana Alhaji.. Da sauri ya sake tambayarta ba ta ji ba kenan, saboda kema ta rainaki? To ai kuma shi kenan na riga na gano kan al’amari na gane dalilin da ya sa fitina taki karewaa tsakaninsu shi ne na kina da bangaren da kike marawa da kinja kin tsaya a matsayiniki na uwar danki kawai wanda ya yi ba daidai ba ki tsawatar mishi da abin nasu bai yi tsanani haka ba don haka zanyi maganin abin in kuma na sake jin sunyi fada to na san mai laifin tunda na gane ita din fitinanniyar yarinya ce.

Tun daga nan jikin Rumasa’u ya yi sanyi ta shiga tsoron kar wani abu ya hadani da ita baba ya ce itace mai laifin, ni kuwa sai nayi anfani da wannan damar nima muna hada ido da ita sai in mata gwalo, rannan ina falona a kan kujera shirya Muhammad nakeyi sai ga Mubarak ya shigo zuwa ya yi ya zauna kusa da ni ko ince manne da ni tamkar dai a ce maida mu cikinshi zai yi daga ni har yaron, rike yake da kafarshi yayin da shi kuma yake ta faman modar nono.

Ban taba ganin mai son da ba irinki gyara dai gyara dai kowane lokaci ba kya gajiya da gyarashi ke duk kokarinki wai ki nunamin kin fini sonshi ne ko? Da sauri na ce mishi wace ni yallabai? Baba ne ya ce akai mishi shi shi ne nake kara kintsashi. Ya kara baiyanar da ji dadinshi ya ce min, kin san abinda yasa baba yake son yaron nan, nayi maza nace mishi uh’uh, to tunawa yake yi da irin wahaloli da kai kawon bacin ran da nayi ta gamuwa da su a kanki Maryam domin shi din shi ne takuici na duk wani abinda kika sani a tsakanina da ke na bada yaron aka fita da shi ya kankameni a jikinshi na tsawon lokacin da yaga hakan ya isheshi sai da ya sake ni don kanshi sai kuma ya kalleni ya ce min, na ganki kina yiwa Rumasa’u gwalo dazu kar ki sake don ba zai zamo min komai ba inje in sameshi in gaya mishi cewar ba ita kadai ce fitinanniyar ba ku dukanku biyun mutane ne da baku da kirki don baku damu da son zaman lafiya ba, to kawai nace mishi na ja bakina nayi shiru ban dai sake ba.

Rannan sai ga Asabe ta zo wurina a wan1 irin yanayi da ba zai kwatantu ba na rashin kyan gani ga kazanta na tuna tsabta da kwalliya irin ta Asabe wai ta zama kazamar da karnintama kawai ya isa ga ‘ya ya uku su ne biye da ita daya kuma a bayanta hudu gaba dayansu. Kallo daya zaka yi musu ka kawar da kai, aka ce min kin haihu shi ae nace bari inzo in ga yaron daga nan in yi miki barka, na ce ai na gode bari in kawo miki shi ki ganshi, ne shiga daki don dauko mata shi.

Mubarak dake wurin ya kalleni, ke kada ki rinka yi min rashin hankali kin ji ko? Na ce mishi to na dawo na sameta muka dan soma hira har ta kaima na tambayeta ina baba Lantana’? Ta tabe baki ta ce tana can Enugu tana jin dadinta mu tayi banza da mu a nan ta barmu tamkar ba itace tayi mana sanadin wannan wahalar ba, ai ko rannan da naje wajen yaya Salau da sauri na ce a’a Sallau yana ina ne Asabe, ta ce yana can wani gari nan baya yana ta sana’arshi ta gwari, na ce kai madalla kowa Ubangiji ya bashi yanda zai yi, maimakon tace amin sai ta ce uhun kai kam ai uwa ta riga ta lalata maka komai sai dai sakaiyar Ubangiji kawai don ta cuceka, zuba mata ido nayi ina kallonta cikin zuciyata na ce, me wannan haihuwar ta amfanar? Iyayen da akace mu yi musu addu’a ita sakaiya take nema a kanta uwar uba kuwa dama ba a maganarshi na sake yin wani tunanin na tuna rayuwar dá baba Lantana ta so inyi kenan a gidan Nalami sai kuma reshe ya juye da mujiya da hannunta ta kai yarta.

Kinga baya bamu sabulun wanka bare na wanki balle man shafawa balle zani abincima na dare kawai yake bayarwa in nayi magana ya ce wai shi yana ganin kokarin kanshi in nace zan yi sana’a matarshi ta hana in wasu sukayi tausayina suka bani abu tace satar mata nayi, shi kuma yana kallo bai cewa komai don tsoronta yake ji tafi karfinshi.

Mama ga kudin cizo a jikinki tayi maza ta kai wa yarinyar duka wannam ne kudin cizo? Kyankyaso ne, na mike na shiga daki na debo turare guda biyu na kawowa Asabe tare da kudi masu dan auki don na Mubarak ne na gani a ajiye tayi ta godiya ta tafi ta bani ina tunanin rayuwa tare da tambayar kaina ko me baba Lantana taje yi a Enugu?

A wannan shekarar ne dai babana ya tafi aikin haji, Alhaji Muhammadu mahaifin Mubarak ne ya biya mishi amma sai ya ce wai Muhammad dan jariri ne ya biya mishi.

Shekaru biyar bayan wannan lokacin na sake jin wani jegon jegona na uku sai dai a wannan lokacin ina yin jegon ne a wani sabon katafaren gida da Mubarak ya gina mana in da ni da Rumasa’u muka zama sai wacce taga dama ne take shiga wurin ‘yar uwarta don bama ma jin motsin juna iyaka dai katanga ta hadamu a wannan lokacin kuma ina jegon nawa ne bayan na kammala karatuna na digiri a jami’ar garinmu banda wannan kuma wani karin jin dadin shi ne ina yin jegon ne a karkashin kulawar uwar miji wacce bata taba zuwa gidan dan nata ba sai a dalilin haihuwar tawa ga kuma baba Sumaye da na riketa matsayin uwa saboda sanin da nayi taso uwartawa sanda take raye taso ta kuma bayan bata nan ta kuma rike amanar dake tsakaninsu yana kuma daga daga kuntatawar da da zai yiwa iyaye a bayansu ya mutunta wanda suke mutuntawa.

Inna da Izzatu suka shigo su biyun a yanzu manyan ya mata ne in ka barni ma sai in ce shirin aurensu Mubarak yake yi ko da dai bai gaya min ba don su din a hannuna suke.

Shirin mikewa nake yi inje wurinshi saboda dawowarshi da naji sai gashi ya shigo da murmushina na tareshi ina fadin, yallabai kaji wai ashe musakai da mabaratan nan da gwamnatin kudu ta tattara ta dawo arewa da su ashe wai har da baba Lantana a cikinsu ashe can Enugun da taje bara takeyi sannan wai bata barar hakan kawai sai ta lallankwaye ta maida kanta tamkar wacce aljanu suka taba yanzu kuma da aka dawo da su anyi juyin duniyá ta koma yanda take abu ya gagara komai ya makale tana can sai zuwa kalon ta akeyi tana ta kuka.

Juyawa yayi zai fita ba tare da ya ce min kala ba, Inna tayi maza ta ce mishi haba kai kuwa wane irin miskilanci ne wannan? Yarinya tana ina taka saka da kai sai faman gwaleta kana shassharewa kakeyi me tayi maka ne?

Ranshi a hade ya ce, haba Inna gajiya nayi da abin kunyar da yarinyar nan take jawa mutane, yanzu ace ita ba zata daure tayi hakuri da bainda sauran mata sukeha kuri da shi ba? Kullum in zata haihu ta rinka ihu kenan tana yi mana bankada a wuri ana kallona? Kuma wai har a gabanki ba zata fasa ba?

<< Halin Rayuwa 57Halin Rayuwa 59 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×