Skip to content
Part 59 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Inna ta ce mishi kai tafi can da wannen maganar taka kai dai fitinannen mutum ne yanzu yanda wurin nan ya kacame da iface-ifacen mata har kana iya sheda ga muryar wata a ciki? Duk matan ma yanzu ba kukan haihuwar suke yi ba? Kai kasanta ne? Da sauri ya ce ba dukansu bane Inna ai Rumasa’u bata yi shiru take haihuwarta sai dai a ganta da danta kawai, haushi da takaici shi suka taru suka lullubeshi in har akwai wani abinda na tsana bai wuce misalin da yakeyi min da haihuwar Rumasa’u ba.

Da sauri naji Innan tayi mishi tsawa, kai tafi can ka bani wuri wadannan ‘yan mitsi mitsin ‘yayan da take haifowa in tace za ta yi kukama ba sai a dake ta ba, dadi ya kamani shi kuma yayi murmushi, Inna ba ki son laifin Maryam to a dan bani yaron in kaiwa abokaina da suka zo min barka su ganshi.

Yana barin dakin nayi kwafa na ce bari tunda abin nashi ya zama hakan nasan abinda Zanyi ba sai na yarda na kara baihuwar ba ne ma zai sake yi min irin wannan wulakancin? Ai yafi kowa son ‘ya’ya tunda shi ne mai zirga-zirgar nunawa jama’a su to na daina ba zan kara ba.

Ta harareni da gefen ido kafin tayi tsaki ta ce min kinji shirmenki kuma ni ina cewa wani abin za ki yi don ki kwato ‘yancniki a wurinshi ya kame bakinshi ya daina wannan iya shegen? To in kin bar haihuwa wa kika yiwa? Danki ai arzikinki ne, yanzu ni baki ganni ba? Haihuwarshi fa akayi aka kwace min shi na hakura na tafi da ya girma bai nemoni ba? Da sauri na ce mata ya nemeki Inna, to da wanda ya kai ni morarshi ne a yanzu? Da sauri nace babu. Ta gyada kai, to nemo wata mafitar amma ba wannan ba na ce to.

Kwanakin jego sun kare har inna da baba Sumaye sun koma gidajensu daga ni sai iyalina ne a gida ‘yayana uku Muhammad, Khadija sai mai sunan babana Abubakar Siddik sai kuma ‘yan mata na Inna da Izzatu da masu aikin gidan a yanzu ban cika lura ko neman sanin me Rumasa’u ke ciki ba balle ta dameni, musamman da na gane irin maganganun da yake yi min, suke yi min ciwo na ita daban ce ba halinku daya ba ita ai tana jin maganata, ashe itama yanayi mata dace nayi naji shari’ar da akayi musu inda take ta kuka tana fadin kusan kullum sai ya kirata da sunan Maryam, banda haka kuma sai ya gaya mata ni din daban ce ni ina girmamashi, ina jin maganrshi ina gudun bacin ranshi tun daga nan na tattara maganganun nashi na ajiye a gefe saboda na gane dabi’ar shi ne in za a yi fada da shi ya fadi mai zafi in kuma ana zaman lafiya kaga tamkar bai iya komai ba sai alheri.

A yanzu kokarina yafi tafiya ne wajen ganin ban bashi damar da ya sake shigo min da wata ba amma, Rumasa’u wata a tsakaninmu ya fada ya kara nanatawa wacce bata shigo ba za a iya hana shi kawota ya hakura amma wacce take ciki to babu mai rabashi da ita don shi din wani irin kishi ne da shi da ba zai iya lamuntar ganin wani kato ya aurar mishi matarshi ba don haka sai ya gwammace in tayi mishi yayi mata in anji jiki a gyara amma ba saki ba.

Ita kuwa Rumasa’u a yanzu babi abinda take so irin ganin ya kara aure ya dai kawo wata wai nima in ji irin abinda taji sanda aka kawoni.

Mubarak ya shigo dakina bina yakeyi da kallo ban fa gane irin yangar da kike yi min ba na lura wani yanga kike yi min kin a wani shan kanshi kina jammin rai ko sanda zan karbi ajiyata a wurinki ai ba irin wannan jan ajin kika yi min ba, wuce shi naje zanyi yayi maza ya cafko kuguna ya rike zo ki gaya min me ya faru? Wata uku da haihuwarki amma har yanzu ba ki yi min ban gajiya ba.

Na daure fuska sosai don kar yaga alamar wasa na ce ai ni na daina irin wadannan abubuwan, wadanne? Nayi shiru ban amsa ba ia magana dai kenan ya jani zuwa inda yake nufin kainin ya shimfideni shima ya kwanta a gefena nayi maza na tashi na zauna, me kike yi ne haka? Na ce mishi a’a ai ba zanyi bane ba kuma zan yarda in sake ba da inje ina yin abinda zai zama sanadin da zan rinka ja maka abin kunya a cikin mutane suna kallonka ai gara ba a fara ba.

To a ina kika ga ana yin hakan Maryam kice kin daina samun ladan mijinki kin daina faranta mishi rai, kin daina menene menene? Wai ma me yakawo wannan maganar ne kinji wani ya ce miki wani abu ne? Na bata rai na ce, ina ruwana da wani? Me wani zai yi nin ya dameni? Wulakancin ka ne kawai ya isheni na gorin da kake yi min a kan kukan hai…

Ban karasa ba ya yi maza ya ce, ni Maryam ai babu sharri a tsakanina da ke to ni yaushe nake iya sheda wata murya a wurin nan abinda Inna ma ta ce gaba daya duk matan zamanin yanzu kukan haihuwar sukeyi, ai in dai don ta wannan ne sha kuruminki gasa wannan bakin nawa’ zanyi ba za ki sake jin wata kalma ta fito daga cikinshi in dai a kan ihun nan ne sai san barka da godiya, don haka sa hannayenki biyu kawai ki rage min kayan nan dake jikiniki don ki sa ni in ji dadi in samu farin ciki da natsuwa a zuciyata saboda sanin duk abinda nake yi, yinshi nake bisa yarda da amincewarki, kina so ne nima ina so ba tilastawa ko fin karfi na nuna miki  ba.

Sannu a hankali cikin yanayi na natsuwa da jan rai irin na mace don dai in kara sashi ya kara matsuwa da abinda ya riga ya matsu, nasa hanu na soma zare kayan dake jikin nawa ina jifa da su daidai da daidai ba tare da na damu ko na lura da inda kayan suke faduwa ba.

Wassalam

Taku

HAFSAT C. SODANGI

Fatan alheri gareku dukanku, na gode Ubangiji ya saka muku da alheri bisa kulawar da kuke yi ma rubutuna na gode.

18/2/2015

<< Halin Rayuwa 58

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×