Skip to content
Part 6 of 34 in the Series Halin Rayuwa by Hikaya

Ke Lantana ke fa sharrinki yawa ne da shi yaushe ki ka bata ta ce miki cinya kawai take ci? Yanzu wannan fuka-fukin in kin bata sai ta ce bata ci? Tayi dariya ta ce a’a to in ma sharrine ubanta yayi mata ni kam yaushe nazo balle in fara nawa? Shi ne ya kawo kaza dankwaleliya gasasshiya.

Yasa hannu ya balle cinyoyin duka biyu ya mika mata ya bar ni da sauran jikin wai abin da take iya ci kenan a jikin kaza.

Kawar tata ta kyalkyale da dariya ta ce, Ai daga ni kasan Kura za ta ci Akuya ‘yar tashi aî ta kiwatu komai nata luwai-luwai da shi, ga ta kuma dama tubarkallah, ke dai irin wadannan mutanen sai anyi hakuri a ke iya zama da su.

Uhun ai kuwa ni nasan sai anyi hakuri kin ga Ramatu! Ramatu!! Ramatu!!! Tana ambaton sunan Innata tana kwatanta yadda sunan yake fitowa daga bakin Babana, yayin da kawar tata ta zuba mata ido tana kallonta

Abinda aka kwana’ ana gaya min ke nan, labarinta ake ta bani ana yi ana karawa ni kuwa ina ta uh, wannan anyi mutuniyar kirki, garin ba ni labarinta hawaye suka soma zubo mishi, yana kici-kicin share su ni kuwa nayi maza na rushe mishi da kuka. Kawar tata ta kwashe da dariya kafin ta ce “Kuka gaba daya? Ta ce to me kike so in ce mishi yana bani labarin matarshi yana share hawaye ba sai in taya shi kukan mutuwar tata ba? Taja wani mummunan tsaki ta juyar da kanta can gefe.

To ashe ba ku’ samu kun yi wancan abin ba kenan? Ni kuma da nazo ne in ji yadda aka kwashe. Ta dago ido ta kalle ni. “Ke tashi ki bani wuri, kin wani tsare mutane da ido suna magana kina kallonsu, na mike na nufi hanyar fita daga gidan, tayi maza ta ce “Ina za ki? Yau ga abinda ya ishe ni, yazo ya same ki a waje? To ba wajen na ce kije ba dakinki za ki shiga.”

Na shiga dakin nawa na zauna sai dai cikin rashin sa’a nan din sai ya zamo nafi jin zancen nasu.

Ni na rantse miki kar ki ce maganar wasa dingishin nan da kika ga ina yi ba na iyashege, ba ne, don ma nayi aiki da ruwan zafi sosai, gabadaya suka kwashe da dariya, ke kice min kawai mutumi garau din shi yake.

Aa kalau yake Lami,  sannan kin san ya kwana biyu rabonshi da abin,  kuma gaskiya hadin nata mai kyaune,  komawa zaki yi ki sake karbo min.

Wari-wari ya soma shigo min daki, na yi maza na waiwaya wurinsu don ganin abinda ke faruwa, karan Sigari na gani a hannunsu suna zuka, cikin mummunan faduwar gaba nayi magana cikin zuciyata don kar su ji ni na ce Sigari kuma?

Ke dai kar kiyi wasa da wannan auren naki, zawarcin shekaru bakwai fa kika yi wannan karon, kafin shi kuma kin yi na shekaru hudu har da watanni, kika yi aure muna murna auren yazo ya kare a watanni uku kacal, kin ga in an hada zawarcin shekara goma sha daya ke nan. To don me za a hada bayan ga auren wata uku a tsakani, wata uku wasa ne?

Suna hirarsu ni kam tuni zuciyata ta shagala tunanin ashe mata ma suna shan taba sigari, na dauka maza ne kawai…

Ban ankara ba sai naji hirar tasú ta koma bayanin ai yarinyar bata da tarbiya, goyon gwauro yayi mata, sannu a hankali na gane wai maganata da Babana suke yi.

Tunda aka yi auren Babah Lantana kullum da irin kawayen da ke zuwa wurinta wadanda Babana zai yi ta hidima da su, in ya fita kuma ka ji suna hira mai ban mamaki, gashi kuma wani abin da ya fi komai ba ni mamakin shi ne daga ita har kawayen nata ba ka raba su da wani mele a gefen fuskarsu tamfar dai sun taba konewa.

Rannan na nemi izini wurin Babana da itama Babah Lantanan don ya ce duk abinda zan yi ko nake so ita zan rinka tambaya, wurin Yaya Dijah naje, muna zaune ni da ita yayin da “ya’yanta ke cikin gida wurin Kakanninsu.

Ni ‘yasu wannan mata da Baba ya aura rufa ido a ka yi mishi ne ko? Ba fa yarinya ba ce gashi da ganinsu ita da kawayen nata kaga ‘yan duniya, an yi bilicin har an gaji an kode an yi mele. Lokacin ne na gane melen da nake gani a jikin nasu na tabon mai ne.

Kamar in ce mata ai ma na gansu suna shan sigari, sai nayi maza na kama bakina nayi shiru saboda wa’azin Malamin Makarantar Asubahi da na tuna, da ya yi magàna kan tona asirin mutum bayan halin nashi bai bayyana kowa ya gane ba.

Ni dai fatan da nake yi Ubangiji yasa maganar da wata makwabciyarmu nan baya tazo tayi min ya zama ba gaskiya ba ne, cikin natsuwa na tambayeta wacce irin magana ce?

Yaya Dijah ta kalle ni ta ce min cewa tayi wai sun santa sani mai kyau, aurenta shida na Babanmu ne na bakwai,kuma wai “ya’yanta guda biyun da take cewa na Alhaji Tukur ne mijinta da ya rasu karya ne, asalin ubansu ne wai ba a sani ba.

Kamar ya ya ke nan? Nayi mata tambayar da ta zamo tamfar tuni a gare ta, cewar wannan maganar ta wuce sanina, don haka tayi maza tai gyara ta hanyar fadin mu dai mu bar wannan maganar kawai muyi abinda yake gabanmu. Shi kuma Baba muyi mishi addu’a, na ce to. Muka ci gaba da harkokinmu da muka saba yi in naje.

Rannan ina tare da Babah Sumaye da Jumare da tazo mata kwana biyu hirarmu muke yi muna wasanmu ni da ita sai naji Babah Sumaye ta ce min, Ke Mero kina da wata matsala ne naga kin yi wannan zubewar haka? Da sauri na dago ido na kalleta.

Nan take kuma na maida kallon nawa ga jikina da take fadin ya zube, me kika gani Babah? Ta ce, Uh’uh gani nayi dai kamar kin ragu kan in ce komai sai Jumare ta ce mata, zama da wannan matar ta Baba ba wani dadi zai yi ba, da na shiga gidan fa ba ki ga irin kallon da take yi min ba, kuma na rantse miki sigari na sameta tana sha.

Babah Sumaye tayi murnmushi ta ce, shan sigari wurinmu ne muke ganin shi kamar da aibu, amma wurin mutanen Bauchi da Katsina ba komai ba ne yin hakan face kwalliya, ko gaye tunda za ki samu har ‘yanmata a wurin kawance suna sha, da haka ta kashe hirar tamu a kan Babah Lantana.

Wani abinda na kasa hakura dashi in daina yin shi shi ne shiga dakin Babah Lantana, bansan dalili ba daga in da duk na fito sai na shiga, sai dai in na shiga naga ledar dakinne nake tunawa musamman ma da yake sau biyu tana rankwashina a kan taka mata ledar da nayi da kafata bayan kuma ni take sawa in goğe mata ita.

Yau ma nazo zan shiga kacibis muka yi muka hadu a kofar dakin ni zan shiga ita zata fito, don haka nayi maza naja na tsaya nan take kuma na juya zan koma nawa dakin ita ma har ta nufi kicin sai kuma naji ta ce min ke ni zo nan mana in tambaye ki, nayi maza na dawo kusa da inda take din kafin naja na tsaya cikin natsuwa ina sauraronta.

Wai zaryar me kike yi min a daki ne? Ba ki ji kashedin da nayi miki ba ko? Ba fa za ki iya hana ni komai ba, ni kuma da ki ke ganina fa ko da Ramatu na samu a cikin gidan ba za ta Takura min da komai ba, don bata isa ba sai dai ma in bata yi sa’a ba in korata waje, don kuwa da shirina na shigo.

Jikina ya dauki rawa yayin da ita kuma ta daga murya wajen yi min magana, haba wacce  irin jarababbiyar yarinya ce wannan babu hali ki ganni da mijina a daki sai ki kama yi min zarya ki ce biro, ki ce pencil, ki ce kudin jarrabawa. Da ya ce ki rinka tambayata raina ni ki ka yi kina ganin ban isa ba ko?

To ai kuwa za ki gane ke ce ba ki isa ba sakarya kawai, shashasha da ta gaji iyayi da munafurci wurin uwarta, kai ke kam ta tafi ta barki da mummunan abu za kuma ki sha wahala.

Taja tsaki kafin ta wuce ta bar ni ina ta faman bari ban saba jin irin wadannan kalaman ba balle kuma a ce a kan Innata a ke yin su.

‘Yan kwanaki kadan da zuwan Babah Lantana gidanmu sai nayi matukar tsorata da ita, ko maganarta naji sai gabana ya fadi, gashi bana sanin lokacin da nake aikata laifin da take cewa nayin, balle in rinka kiyaye mata, ban saba da mu’amalla ta tsawa da yawan duka ba, sai kawai aka wayi gari na tsunduma a cikinshi.

Yar tsarabar’ da Babana ya saba kawo min ina ci na kwalama bayan abincin gida na daina samu saboda yanzu komai yazo dashi ita yake mikawa wai ita ce mai bani, ita kuma sai ta cinye ina kallo.

Hakan bai dame ta ba a farkon zuwanta gidanmu, ban cin komai jikn kaza in ba cinya ba ne amma bata cika kwanaki arba’ in da zuwa ba sai da na zama har kai da kafa ci nake yi, wanda mu da sanda Innarmu take raye ba a saka su cikin miya.

A kowane lokaci a cikin yi min kashedi take in kika ce abinda zamu yi da ke kenan to kuwa lalle zamu sa kafar wando daya ni da ke a gidan nan, ba kuma zata fito ta ce min ga abinda nake yin ba wanda zai yi dalilin da za a sa kafar wando dayan da ni ba.

Rannan ta cika sati shida da zuwa gidanmu, wato kwanaki arba’in da biyu kenan, daga Makarantar allo na taso don haka na biya ta wurin Babana don in dan zauna mu dan yi hira inji dadi, tunda shima mu’amullar tamu ta dan sauya.

Bai bar ni na zauna ba ya ce min maza je ki gida uwarki tana can tana jiran dawowarki tunda in ba kin koma gidan ba ba dora girki take yi ba, sai tayi ta jiran zuwanki.

Kamar in ce wa Babana a’a Baba bata jirana, ni bata sani ma wani aikin da ya danganci girki tuna ta ma hana ni shiga kicina dalilin wai naman miyarta yana bata, amma sai na kasa cewa Babana komai, na kamo hanya ka na dawo gida.

Naje na gaishe ta sannu da gida Babah, bata amsa ba sai da nayi sau biyu sannan ta daga ido ta kalle ni sai yanzu ki ka dawo? Ai ni da ke ne gidan nan na wuce sumsum na shiga dakina na zauna don yanzu na riga na saba da zaman cikinshi.

Ban dade da zaman cikin nashi ba naji wata murya tayi sallama, ban ji amsa ba iyaka dai naji an kurma ihun da ya sanya ni nayi maza na yiwo waje saboda firgitan da nayi, sai dai sabanin yadda nayi zato abin tsoro ta gani ashe wai murna ne haka don ganinsu nayi sun rungume juna ita da bakuwar tata.

Nayi maza na koma dakin nawa na zauna a zuciyata ina mamakin yadda babba zai iya kwallara ihu irin wannan da sunan oyoyo ko murna.

“Na rantse ko jiya sai da nayi maganarki cikin zuciyata, ashe kina hanya Delu. Delu ta  ce “Ke Lantana juna biyu ki ka samu ne naga kin habake kin zama wata danya?

“Juna biyu wane iri? Kalau dina nake shimna dai maigidan na ji shi yana maganar waiko juna biyun ne, ni kuwa bai sani ba yaushe rabona da al’ada, na fa shekare, sai dai zan koma wurin mutumin nan ko zai ba ni maganin da al’adan tawa zata dawo.

Ta kyalkyale da dariya “Tana tafiya ne dama ta dawo? Ai in ta tafi ta tafi ke nan in dai ba ciwo ne yayi dalilin daukewar nata ba.”

To ai nima ciwon ne. Delu ta sake wata ‘yar dariyar kafin ta ce “Ke dai kin samu gida na kuma yi miki murna don da gani ba sai an tambaya ba kin yi shar da ke har kuruciya ta dawo miki, kai ni’ima da dadi take, sai dai kawai in bawa bai samu ba ya hakura Ubangiji ya samu a danshinku.”

“Kai Delu kenan, abin dariyarki yawa ne da shi. Tayi maza ta mike ta shiga cikin daki ta fito mata da abubuwanci da na sha da Babana yake kawowa tana hana ni tana ci tana boye saura don masu zuwa mata.

Haba, gaskiya ni’ima da ta bayyana a jikinki ke ki ce gara kawai yake shirya miki, ke in ban da ita haihuwa lokaci ne da ita da sai in ce gidanta kika zo ki neme ta.” Babah Lantana tayi dariya, ai iya shegenki yawa ne da shi kina nufin lokacin nata ya wuce ne a wurina? To bari mu gani.

“Ke ki ce aure sosai ki ka yi, ai tunda ki ke aure ma ina ganin in banda aurenki na biyun nan ba ki taba dacen aure irin wannan ba, sai aka yi rashin dacewa aka tare mishi da dan zani, ai daga rikicin cikin nan ne abin duk ya shiririce, zama ya ki dadi sai da aka rabu daga baya ma yazo ya rasu.

“Delu ke nan to wa ya tambaye ki wannan dogon bayani ko kuma duk a santin naman da na kawo miki ne ki ke kokarin yi min wannan tonon asirin?”

Delu tayi dariya ta ce, “To gida mu biyu tonon asirin me zan yi miki Lantana? Auren naki ne ya bani sha’awa, gashi kin yi fes da ke da alamar shi mutumin bai da wata damuwa. Ta ce, Eh to kamar dai hakan nake zato tunda zuwa yanzu ban ga wata damuwa a wurinshi ba, shi ba a musu da shi in kuma takamanki son kudi ne ma to shi ke zai baiwa ajiyar ribar cinikin nashi ya dauki jarin da gobe zai koma dashi kasuwa, duk abin da ki ka ce kin yi da kudin kuma ba magana zai yi ba.

In har ina da wani abinda ya tsaya min a rai game dashi to yar shi ne sai ko matarshi da ta rasu, kinga ita ‘yar duk inda tayi yana bin ta da kallo sau goma kuma in zai yi miki wata magana to shida a kanta ne hudin akan uwarta da bata duniya.

Yanzu haka akwai wani hoto na uwarta da ya kakaba min a cikin dakin maganar hoton kawai nayi kan ko za a cire shi ne a adana tunda dai mai shi ta riga ta mutu kar kiga irin fushin da yayi, to ga maganar wadannan yaran da nake so in dawo da su gidan nan a matsayin ‘ya’yan Yata da ta rasu ta bar min su.

<< Halin Rayuwa 5Halin Rayuwa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×