Skip to content
Part 9 of 59 in the Series Halin Rayuwa by Hafsat C. Sodangi

Muna shiga gida ta takarkare ta sakar min wani irin azababben dundu da yayi sanadin da na durkusa a kasa nan take kuma ta rufe ni da duka tana kuma yi min tambayoyi ni na kashe miki uwarki ne da za ki tasa ni a gaba da masifa? Kiyi min sata kar in yi magana? Ni nan da ki ke kallona ubanki ma ba tsoro yake bani ba balle wasu can banza a banza in na gama dukan naki kije yau ma ki nuna musu ina nan ina jiransu su zo Su same ni don ni nan da ki ke ganina uwarki ce daidai nake da mazaunan kowa.

Ki min sata ki ce kar in yi magana? Ina kika kai min sauran kudin? Sau nawa kina yi min sata ina kyale ki? Eye? Haka kawai ni da gidan mijina kin takuramin kin hana ni sakat kin ishe ni da fitina wai a kanki ke kadai a ka fara maraici ne? Iye? Ta sake rufe ni da wani irin duka har ina fitsari a jikina amma bata fasa ba.

Sai ga Babah Sumaye ta shigo kai haba wace irin musiba ce wannan? Wannan wane irin duka ne da bai karewa haka? Haba yarinyar nan kinsan tana nan fa ki ka aurar mata ubanta kin kuma zo mata gidansu kin tasata a gaba da masifa, bayan ke ga taki kin kawo kina rike da ita a ina ake haka ne dan gida ya wulakanta agola ya zauna lafiya in ban da wurin azzalumai irin ki? To ki rama mata mana tunda kin shigo da kanki shugabar munafukai.

“Ba zan rama mata ba zamani ne zai tantance komai shi ne zai yi dalilin da sakamako zai hau kanki don ba za ki dauwama a haka ba.”

Bakin cikina ne zai kashe ku munafukai, mijina kuma ba ku da yadda za ku yi dani a kan shi yana sona. Babah Sumaye ta ce, wane bakin ciki za a yi da ke Lantana? Matar da ta gama rayuwarta a gwagwarmayar rashin gaskiya, yau ana nan gobe ana can duk in da a ka je din kuma sai an yi cinta? Menene naki ba a sani ba? Har dakin da ki ka zauna ki ka haifi shegun ‘ya’yanki an nuna min, babu wani abinki da ban sani ba, wai ma Mallam Habun muna nan muna yi mishi addu’a Ubangiji ya fitar da shi daga halin da yake ciki, ya bayyanar mishi da ke ya gane asalinki, ki kawo shegiyar yarki gida ta sake amma ki hana yarinya sakat, to ana me ina dalili? Ta juya ta fita ta bar Babah Lantana tana fadin ai tunda ki ka kulla min irin wannan sharrin to hukuma ce kawai za ta raba ni da ke, za kí san kin iya sharri.

Tana kuka tana kurma ashar ganin da nayi Babah Sumaye ta fita ta bar ni da ita cikin wannan hali yasa nima nayi maza na fita na bar gidan saboda ban san abinda zata yi min ba in ta dawo hankalinta ta gane ni ce a zaune kusa da ita.

Gidan Yaya Dijah naje tana ganina ta soma kuka me ki ka yi mata tayi miki wannan azabar kai yau kan abin ya ishe ni haka da sauri ta aika a kira mata Yaya Ibrahim, yana shigowa ya ganni tun kafin tace mishi komai ya zuba min ido yana kallonä wai me kike yi wa matar nan ne?

Saboda Allah me zata yi mata? Tayi tambayar cikin yanayin kuka, a’a zata yi mata mana haka kawai zata yi tayi mata irin wadannan abubuwan ne wane irin mugun hali ne haka? Shi halin dan wani da uwar wani kuma ai sai a hankali sannan ba ka marawa naka baya ko da kuwa zaluntarshi ake yi musamman idan ka san shi ne karami shi yasa nake yawan gaya miki ita uwa ki ninka yi mata fada kina nuna mata muhimmancin ta rinka girmamata.

Kalaman Yaya Ibrahim ne suka yi matukar rage karfin fushin Yaya Dijah amma duk da haka sai ta nemi izininshi don muje gidan tare.

To babu laifi amma ban yarda in kin je kiyi fada da ita ba, kiyi magana da ita cikin natsuwa don kiji abinda ke faruwa cikin natsuwa da nuna girmamawa gare shi ta ce to.

Duk da mummunan karbar da Babah Lantana tayi wa Yaya Dijah tabi umarnin mijinta nata tabi al’amarin a hankali.

Ina wuni? Ta kalleta a lalace au gaisuwa za ki tsaya yi ai na dauka za ki rufe ni da duka ne kawai, ban zo dukanki ba amma nazo ne in ji laifin da take yi miki kike yi mata irin wannan azabar, a’a aha aji kawai abin zai tsaya ai na dauka za ku yi fushin zuciya ne dawo da uwar taku kawai, haba yara kun tasa ni a gaba sai ka ce ni na kashe muku ita a yi min sata a hana ni yin magana.

Yaya Dijah ta kalleta a lalace ta ce me ki ke dashi da uwa zata satan miki? Ke da kika tare a gidanmu ko gadon kwanciya ba ki da shi a kan  gadon uwarmu fa ki ke kwanciya duk wani abin da yake gidan kuma nata ne har yanzu ban ga naki ba. Gorin da ki ke yi mana kuma na mu tono ta to ba zamu tonota ba, don bamu taba ganin in da aka yi hakan ba, sai dai kema za ki je in da taje din, da ana tonowa kuma to da mijinta ya riga kowa tono ta don da bai kwaso ki kin zo kin addabe shi kin addabi iyalinshi da makwabtanshi ba.

Ta tashi zata fita daga gidan yayin da Babah Lantana ke ta faman zagnta tana hadawa har da Innarmu da Babah Sumaye tare kuma da jaddada ita ubanmu ma ba tsoro yake bata ba balle wani can banza a banza.

Yaya Dijah ta ce tunda mijinki ma ba komai ba ne a wurinki ai kowama lada ne, sai dai kanki ki ka yi wa tunda miji ai aure ne aurenki ki ka wulakanta mai auren kuma ya tanadi maganin irin ku, mara mutunci wacce bata san a ,girmamata ko mu din kuma ba tsoronki muke yi ba kina cin darajar ubanmu ne kawai.”

Nabi bayanta ta shiga gidan Babah Sumaye ni kuma na zauna a kan dakali ina jiran fitowar tata tun da yanzu bana shiga gidan.

Babana yana dawowa ta kwashe bayani na karya da gaskiya duka ta gaya mishi gaba daya maganganun da Babah Sumaye ta gaya mata da na Yaya Dijah ta hada duka ta ce Yaya Dijan ce tayi mata su.

Babana yayi fushi mai tsanani wai ta raina shi ne yasa ta iya buda baki ta zagar mishi matarshi, in ba haka ba ai matarshi uwarta ce da sai ta kai mishi karar abinda ya farun taga abinda zai yi, kan wannan maganar sau biyu Yaya Ibrahim ya rako Yaya Dijah suka baiwa Babana hakuri, sai ya ce wai shi ya wuce a wurinshi amma sai an ba Babah Lantana hakuri tukuna, ita kuwa Babah Lantana da aka bata nata hakurin sai ta ce to ya wuce amma daga yanzu babu sauran mu’amallah a tsakani.

A wannan lokacin saboda tsabar samun wuri ba Asabe kadai ba ‘ce a gidanmu har da wanta Sallau wanda gansamemen saurayi ne sosai, sai kawai a ka bude mishi daya dakin aka Sanya mishi sabuwar katifa, shi kuma Babana ya zama bai da wani wurin da zai dan shiga ya zauna sai dakin Babah Lantana kawai, da wannan gırma nashi kuma bai hana shi ma ya dora hannu a jikina ba da sunan dukan wai shi ma ina yi mishi laifi.

Rannan na fito waje ina zaune kan dakalin kofar gidanmu, kuka nake yi saboda al’amuran sun ishe shi wahala tayi min yawa duk wani taimako da da a ke yi min an daina gaba daya, makwabta sun fita harkata saboda kowa haushin Babana da dabi’arshi ta fada a kan mata a ke ji a kan kuma rashin gaskiya.

Na shagala babu abinda nake yin sai kukan ta hanyar sharbe yayinda na sunkuyar da kaina kasa ina kallon ‘yan yatsun hannuna ban ji wani motsi ba balle in san wani yazo in da nake sai da naji ya buda baki yana tambayata ke Maryam me ya same ki kika zama haka?

Nayi maza na dago kai na kalle shi duk da na dade bana ganinshi, kallo daya nayi mishi na shaida shi, Mubarak ne ya girma yayi kyau, gayenshi yayi matukar karuwa sai kamshi yake yi.

Nayi maza nayi shiru saboda ganin irin Kallon da yake yi min me ya hana ki tafiya Makaranta yau Talata? Ban iya ce mishi komai ba saboda ban san me zan e mishi ba, tashi ki shiga gida kije kiyi wanka ki wanke kayan jikinki kar kuma in sake ganinki a gida a ranar karatu kin ji ko?” Ban ce mishi komai ba ya wuce ya tafi bayan ya ga tashina zuwa cikin gida.

Tun daga ranar ban sake fitowa waje na zauna ina kuka ba sai dai in yi zamana a zauren gidanmu ranan ma ina wani kukanne a cikin zauren a dalilin Babah Lantana ta ce wai tana shirin duba ni saboda ta gane na fara bin maza shi yasa babu halin ta aike ni sai naje na dade.

Ban san yadda aka yi yasan ina cikin zauren ba sai ganinshi kawai nayi yana tsaye a kaina, yau ma kuka ki ke yi? Yayi tambayar cikin natsuwa yayin da fuskarshi take daure sosai wai me ke faruwa ne a gidan nan naku? Ban ce mishi komai ba ban kuma daina kukan da nake yi ba. Yau ma ranar Makaranta ce ba ki je ba jiya, na je makarantar taku ban same ki ba, Malamarku ta gaya min ba kasafai ki ke zuwa ba, nayi magana da Ummana ta bani wasu labarai marasa dadi a kan matar Babanku kar ki yarda ta hana ki karatu, ungo wannan ki share hawayenki ki fyace majinar da ki ke mayarwa ciki kina shanyewa.

Nabi umarnin da ya bani nasa hannu na karba na kai hancina, kamshi mai dadi irin kamshin da ke tare da shi ne, ina gama fyace majinar yasa hannu ya karbi hankicin ba tare da ya ji kyamar majinar tawa ba ya miko min ledar da ke hannunshi karbi wannan kici yanzu ina kallo, nasa hannu na karba ba tare da nayi musu ba, saboda sanin alakarshi da Innata shi da Mansur. Iyaka dai na dade sosai ban ganshi ba na kuma san yana canne wajen hidimar karatunshi.

A sanina sanda Mama take raye kina cikin wadanda ake yi wa kyautar tsabta a makaranta to don me kika yarda ta maida ke haka? Ga ki da kokarin karatu duk kin daina, ai ba ayin haka ita rayuwa ai bata tabbata a wuri daya komai canzawa yake yi, wani mutumin da ya yi wa rayuwa irin fahimtar da yayi mata ma sai ya ce “It is the law of nature and condition of all thing for all things are craselessly changing. Komai da ki ke gani zai wuce wata rana kuma sai labari.

Kalamai masu dadi har ban san sanda na cinye meat pie din da ya kawo min tare da lemon gwangwanin ba, gashi kuma dama ya same ni cikin bukatar abin saboda ko karyawa dama ban yi ba.

Natsuwa tazo cikin zuciyata har ña fara baiwa Mubarak amsar tambayoyin da yake yi min, ni kina aji nawa ne? na ce biyu, to ki shirya gobe zan tsaya a kofar gidanmu don in ga wucewarki da safe kin ji ko?

Na ce mishi to, yanzu shiga gida kiyi wanka ki wanke wannan kayan jikin naki ki daina zama cikin kazanta ba ki ga yadda ki ka zama ba ne? Ban ce mishi komai ba na mike na shige cikin gidan, sai dai wanka da wankin da ya ce in yin ba su samu ba, a dalilin wai ba za ta bani sabulu ba.

Rannan tun dare nayi wanke-wankena saboda in samu damar tafiya makarantar da wuri, amma da garin ya waye a kaga ina shiri sai a ka sake taro min wasu kwanukan da ban ma san ta inda suka fito ba, na gama shara da wanke bayan gida nazo na same ta cikin ladabi na ce a bani abin karyawa in na dawo daga Makaranta zan yi sauran aikin.

Da sauri ta juyo tana kallona da wani bawanki ne a gidan zan da zai yi miki aikin? Na tsaya ina kuka saboda ganin Babana a wurin ko zai tausaya yasa baki cikin maganar, sai kawai naga ya tashi ya shiru takalmanshi ya suri kwandonshi ya fita aimar wai wajen tumatirinshi zai tafi.

Ganin haka yasa na bar kukan da na fara na  sunkuya nasa hannu da nufin daukar fatattakakkiyar jakata in tafi saboda in bi umarnin da Mubarak ya bani sai naji ta ce ai kin bar kukan ne munafuka? To ai babu inda za ki sai kin je kin yi min wanke-wanke nan.

Na ajiye jakar a tsakar gidana kama yanke-wanke, sai kawai naji muryar Mubarak dagacikin zauren gidanmu yana kwala min kira.

Da sauri Babah Lantana ta fito tana tambayar waye a nan? Waye ne mai keta min haddin cikin gida? Suna hada ido da shi taja ta tsaya tana kallonshi tare da sharbebiyar bulalar da ke rike a hannunshi yana gaisheta yana kallona.

Tayi maka laifi ko? Ya ce eh, Makaranta nace taje bata je ba, a to ai ga ta nan, ta wuce ta tafi dakinta. Daga inda yake din ya kira ni, na taso na tafi bayan na wanke hannuwana da kafafuwa,mbata kula ba saboda watakila tayi zaton dukan zai yi min tunda ta ganshi da sharbebiyar dorina a hannunshi.

A zauren gidanmu ya tsare ni babu alamar wasa a tare da shi na duba naga bulalar Babah Lantana bata gama karasa girman tashi ba, amma irin jin jikin da nake yi in tayi min duka da ita to balle kuma wannan.

“Me yasa nace kije Makaranta ba ki je ba?” Ban boye mishi komai ba, nayi mishi bayanin komai don tsoron kar ya ce na raina shi yayi min duka.

“To wuce muje na.” Na wuce muka je din, shagon unguwarmu ya kai ni ya saya min sandal da littattafai da biro ya kuma kawo sule biyu ya bani “Ki ci abinci a Makarantar, ki kuma yi sauri kar ki tsaya a hanya.” Na ce mishi “To.”

Sanda na dawo daga Makarantar hana ni abincin da Babah Lantana tayi bai wani daga min hankali ba, saboda a koshe sosai na dawo gida. Tun daga wannan lokacin karfe bakwai da rabi nayi in Mubarak bai ga wucewata ba zai tako ya zo zauren gidanmu ya tasa ni a gaba ya ce in wuce in tafi Makaranta, komai kuma na Makarantar yi min yake yi, kan ka ce me ye wannan? Sai ya zama shi ne babban abokin gabar Babah Lantana

<< Halin Rayuwa 8Halin Rayuwa 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.