Da misalin ƙarfe bakwai na safe Muheebbah na tsaye abakin wani waje da aka tanadar don yin alwallah ga yara, tana wankema wani yaro baki da brosh sai ga Anty Ainah shugabar masu kula da wajan ta shigo a rikice tana kiran Atika kafin kace tak tuni ma'aikatan wajen da yaran sun taru waje guda don sun san ba lafiya ba, Anty Ainah ta fashe da kuka kafin ta sheda masu ƴan fashine suka shiga gidan Hajiya Babba suka kwashe komai kuma sukai mata dukan mutuwa yanzu hakka tana kwance a gadon Asibiti.
A take kowa ya sami kansa. . .