Tahteef kwance yake akan makeken gadonsa wanda akayi odar sa daga ƙasar dubai, gadon babbane kuma girma ba naa wasaba don atsakiyar ɗakin akai masa mazauni kuma mai runfane inda aka zagaye runfar da fararen labullai masu laushi,
Juyi yake a gadon ya kasa bacci karo na farko a rayuwar sa da wani abu yake ƙoƙarin hanasa bacci domin kuwa da ya rufe idanunsa bai ganin komai sai kyakkyawar fuskarta lokacin da take masa murmushi, ahankali yake tuno surarta da irin yadda take magana cikin muryarta mai sanyi da daɗin sauraro golding voice .
Ahankali wani irin murmushi ya subuce masa. . .