La kama ma nai da gwanin iya soyayya to kiyi gaggawar cire kama don ni gwanine akan soyayyarki, bani da babban burin da ya huce inji kalmarso ta fito daga bakinki kina furtata gareni ”.
Haka sukai ta fara cikin raha da nishaɗi har suka iso bakin gate ɗin HALAL CHINDENT'S HOME, kansa tsaye ya danna kan motar cikin gidan ya faka inda aka tanaza don Ajiye motoci, suna tsayawa Muheebbah ta fara kiciniyar buɗe marfin motar amma ta kasa saboda motar a kulle take, take ta zuba masa kyawawan idanun ta tace “ mun iso fa me kuma yayi saura. . .