Ɗagowa Namsiyya tai ta kalli Mama saboda yadda ta kira sunan muryarta a dake.
“Wannan kalamai basu kamata aji su daga bakinki ba a matsayinki na ƴar talaka kuma Allah Ya wanke miji kamar Areeyan ya baki sai ki gode masa ki karɓi komai a yadda yazomaki, domin kuwa duk duniya kowa da iyakar wahalar da zai sha kada ki cika baki ko kiyi fariya da bugun gaba da abinda ba nakiba bari na baki wani misali zakiga wajan da ake sai da litattafai na addini ga sunan a yashe duk sunyi ƙura sai mutum ya saya ya kai gidansa. . .