Sadda layin ya iso inda suke tuni Namsiyya ta ƙosa har ta fara mitar su tafi gida amma Sholy ta taita bata baki da sanar da ita irin nasar da zasu samu anan gaba, suna shiga ɗakin zuciyar Namsiyya tai wani irin bugawa saboda ba haka tai tsammanin ganin ɗakin ba ga wani wari da ke tashi wai a haka turarene, kaya ne shirgi guda da komatsai inda mutum biyu zasu zauna ne kawai sararin ɗakin sai inda mutumin yake zaune ƙatone babba irin mutanan nan masu tsayi da kwari ya sha babbar rigarsa har da rawani, haƙoransa duk sun. . .