ABUJA
Gidan marayu sai da Tahteef ya haɗe jikinsa da na Muheebbaht ya rungume kafin ya soma faɗin “ kina lafiya babu abinda ya same ki ko? ”
Eh ta faɗi a hankali tana kallon sa cike da tausayawa saboda tsabar sonta da take iya gani a cikin idanunsa, saboda ba ya ɓoyuwa ko ba ita ba mutane da yawa za su iya gane hakan ta hanyar kallon ƙwayar idon sa idon yana tare da Muheebbaht .
Mai da kallon sa yayi inda su yahuza suke kafin yace “ ita ɗin rayuwa tace kuke son tozartawa, don haka dole ku karɓi hukuncin dai dai. . .