Daga haka ta hau tunani akan yadda zata raba kanta da wannan talaucin da suke ciki, bata da burin da ya huce ta yi irin rayuwar gidan su sholy, nan take ma ta fara hango kanta a duniyar Masu kuɗi da irin yadda zataci karenta babu babbaka don haka ko ana ha maza ana ha mata sai ta auri mai kuɗi ko ɗan mai kuɗin, haka dai tai bacci ranta da ruhinta cike da tarin burika masu yawa da wahalar cikawa.
Kamar a mafarki taji ana dukan cinyarta ana faɗin “ ke Namsiyya ki tashi lokacin sallar asuba yayi ”.
Raɗau taji. . .