Ɗari biyu Abbas ya ciro acikin aljihunsa tsohuwa duk ta cukurkuɗe ya bama ɗan acaɓar, sai da mai acaɓar ya kallesa sama da ƙasa kafin yace “ malam ɗari ukku ne kuɗin ka”.
“Don Allah mai gida kai haƙuri wallahi matsalace ta taso shiyasa na ruɗe ban tsaya jin kuɗinba kuma ita kaɗai ke gareni kai haƙuri kayafeman sauran da inada shi ko nawa ne zan biya wallahi nasan ban kyauta ba amma kayi haƙuri Allah ya haɗaka da mai baka fiye da abinda ka buƙata Allah ya tsare asauka lafiya. ”
Amsar ɗari biyun mai mashin ɗin yai yana cewa “ amma. . .