A yanzu haka malam Giɗaɗo ya koma ƙauyen Jikamshi babu daɗewa shida iyalinsa, inda ya tashi daga unguwar kashe nera, anan unguwar yaransa su kai karatun firamare ɗinsu har suka gama ayanzu haka basu daɗe da fara zuwa makarantar sakandarba dake nan cikin charanchi a sabon layi, kullum yake kawosu da kansa kuma idon antashi yazo ya ɗauke su akan mashin ɗinsa jen can ƙarfe wanda ya tsufa har ya kwararraɓe, Azima itace babba shekarunta sha shidda tana aji biyu a babbar sakandare wato (ss2) ita kuma Muheebaht shekarunta sha huɗu tana aji ukku a ƙaramar sakansare wato (Jss3).
JIKAMSHI. . .