BISMILLAHIR- RAHMANIR-RAHIM
GARGADI
Wannan labari mai suna a sama kagaggen labari ne, da ba shafi wata ko wani ba. An yi shi ne kawai da ilmantarwa, fadakarwa da kuma nishaɗantarwa. Idan kin /ka ji wata halayya da ta yi daidai da ta ki/ka arashi ne kawai.
TSOKACI
Labarin HASASHENA Labari ne na wata jarumar da take hasashen duk namijin da ya kara aure, to matarshi ta gida ta gaza ne, ko kuma ta wajen ta fi ta gidan komai. Shi ya sa lokacin Bashir ya zo neman auranta, a matsayin mata ta biyu, ta rika jin za ta ci karenta babu babbaka, za ta more rayuwar aurenta, za ta ja zarenta yadda take so. Ta rika jin ba sai an fada ba, ta yagawa matarshi ta gida ta ko wane bigire. Sai dai bayan auran ta riski abubuwa da yawa. Da har ta gwammace kida da karatu.
*****
Daga inda nake kwance na ji karar rufe kofa, wannan ya sa na yi saurin duba agogon wayata, takwas saura na safe ya nuna.
Zumbur! Na mike hade da ficewa zuwa falona, lokaci daya kuma na yaye labulen tagata da zai hasko min tsakar gidan.
Tsaye take cikin riga da siket na lace mai launin ja da digon bakin fulawa, hade da kwalliyar zare mai ruwan gold.
Dinkin ya zauna a jikinta daram, daurin dankwalinta das ya zauna a kan goshinta, gilashin da ta manna ba ƙaramin kawata mata fuskarta mara wadatacciyar kwalliya ya yi ba.
Karamar purser ce baka a hannunta, wacce ta yi daidai da bakin dogon takalmin da ke kafarta.
Sabe take da Ramla yarinya yar kimanin watanni takwas a kafadarta, yayin da daya kafadar ta sagala bakin gyalenta.
Wannan ita ce kishiyata Sakeena wacce kowa ya fi sani da Maman Khalil.
Na kai dubana akan yaranta biyu, da suka fito fes cikin uniform din makaranta, Khalil shi ne babba, wanda yanzu zai kai shakaru 7, sai Affan mai shekaru 5.
Na kuma kai kallona a kan maigidan namu, a lokacin da yake saka mata keys din kofa a cikin posern da ke hannunta.
Sanye yake cikin manyan kaya farare tas, wadanda aka yi wa kwalliya da bakin zare, takalman kafarshi da hula, su ma sun kasance launin baki da fari.
Sosai kyawunsa ya fita a cikin kayan, yayin da kuma suka boye shekarunshi.
Fuskarsu kawai za ka kalla ka fahimci suna cikin walwala da farin ciki.
Na sake labulen a lokacin da na ga ya nufo bangarena, lokaci daya kuma na fada kitchen hade da goge farantan da ni kaina ma ban san dalilina na goge su ba.
Don zuciyata cike take fam da kishi hade da danasanin auran mijin wata.
Na tuna yadda wasu kawayena da ƴan’uwa suka rika jimami, lokacin da aka ce zan auri mai mata. Amma ni a lokacin ban ga wani abun jimami ba,tun da ni ce amarya. An cewa kuwa sabo ya fi tsoho, koda sabon kashi ne.
Shigowarshi ne ya sanya ni juyawa hannuna rike da plate da ƙaramin towel.
“Kin tashi lafiya?”
Ya tambaya lokacin da yake kallon kwayar idona.
Bakina ya yi nauyi, ba zan iya furta komai ba, dalilin da ya sa kenan na daga kaina alamar “Eh”
Matsowa ya yi daf da ni, hade da amshe plate din da ke hannuna da towel din ya aje a kan carbinate.
Ya janyoni zuwa jikinshi wanda ya gauraye da kamshin turarenshi, na matarshi da kuma yaranshi.
Jikina ya gama mutuwa, dalilin da ya sa kenan na kasa aikata komai fa ce jin yadda yake shafa bayana alamun lallashi.
Tsawon mintuna biyu ya dago ni hade da saka kwayar idonshi cikin nawa.
” Idan akwai wata matsala don Allah fada min?”
Girgiza kai na kuma yi, don kuwa idan na ce zan bude baki, kukana ne zai fita a maimakon magana.
“Ina sonki Khadija.” ya fada hade da kama kafaduna duk biyun.
Hawayen da nake ta boyewa tun dazu suka gangaro zuwa kan fuskata.
Hannu ya kai yana share min hawayen.
“Bana son kuka, zan tafi office kar in makara, idan na dawo za mu yi magana.”
Kai na kuma dagawa, a lokacin da nake share hawayen.
Ina kallonshi ya fice, ko rakiya kofar falo ma bai samu ba.
Sai da na ji fitar shi sannan na fito zuwa falo.
Dankwalina na tuge, lokaci daya kuma na tura yatsuna cikin gashin kaina ina sosawa ba don yana min kaikayi ba.
“Anya kuwa wannan ba shi ne kuskure ma fi girma da na yi a rayuwata ba na auran mijin wata?” A zuciyata na yi maganar, a zahiri kuma kwantawa na yi kan doguwar kujera ta, hade da kallon P. O. P da ya kawata rufin falon nawa
Kawata Samira ce ta fado min a rai, hakan ya sa na yi saurin tashi, na nufi bedroom da zummar dakko wayata in kirata.
Sakon dana taras ne ya dakatar da ni daga kiran Samiran
“Kin gama kukan” abin da na gani kenan, na dan murmusa a hankali, na mayar mishi da amsa.
“Na kusa dai”
“Hhhh! Shagwababbiyata”
“Smile” abun da na tura mishi kenan
“Ina yi miki wani abu mara dadi ne Khadija?”
duk da ba na ganin fuskarshi a lokacin na san ba alamun wasa a tare da shi
“Me yake so in ce to?” na tambayi kaina.
“kana nunawa matarka so da kulawa sosai, sannan matarka ta cika duk wasu sharudda da mace ta gari ya kamata ta cika. Sannan ka yaudareni da aka aureni bayan ka san kana samun duk wani farin ciki a wurin matarka. Haka yake so in fada mishi?” na kuma tambayar kaina.
” Ba ka yi min komai ba, bana jin dadi ne idan duk kuka fita, kuka bar ni kadai.” Na tura mishi.
” Sorry Deejahna, kamar yadda na yi miki alkawari kina cika shekara daya zan nemar miki aiki sha Allah.”
“Ina godiya Alhajina.”
“Bukatata ku zauna lafiya cikin aminci ke da abokiyar zamanki. Maman Khalil mutuniyar kirki ce.”
“Ka san da haka me ya sa ka aure ni, kullum kana cikin yabon matarka” A badini na yi maganar a zahiri kuma tura masa sako na yi kamar haka.
“In sha Allah za ka yi alfahari damu.”
“Me za ki yi min da rana?” ya canja salon hirar.
“Me kake so?”
“Tuwon shinkafa miyar kuka” ya kuma turowa da sako.
Na zazzaro ido cike da mamakin sakon na shi, ina maimaita ” Miyar kuka kuma!”
“an gama ya Hajj” na tura mishi
“Na gode”
“Uhhhh! Na ce ba, yau fa ba ni ce da kai ba, ba matsala ko?”
” Ba komai, ki yi kamar yadda na ce”
“Ok” na kuma yi mishi reply
Tsawon mintuna biyu bai turo wani sakon ba. Hakan ya sa na kira Samira.
“Kawata!” ta fada da alamun muryar bacci, ajiyar zuciya na sauke kafin na ce “Yar gata, bacci ma kike yi?”
“To me zan yi, yau ba ni ce da duniyar ba.” ta ba ni amsa.
“Samira! (na kira sunanta a sanyaye kafin na ce) ina ma ni ce ke”
“Me ya faru?” ta yi saurin tambaya
“Aka raba mana gida da abokiyar zamana, kin ga duk kazantar da ban gani ba, tsabta ce.” ta amsa ta
“Hmmm! Ke babu fa wani sauki wlh, ya fi ma ana ganin idon na ki, wani abun ba za a yi shi ba. Saboda Hausawa sun ce ganin ido na hana cin kai. Amma ba a ganin idonki sai abin da kika gani.”
“Duk da haka Samira” na tare ta
“Ba za ki gane ba Khadija, amma ni kam da za a hade mu da ita gaskiya da na so, ko ba komai zan rika ganin motsinta. Kin ga kishi da jahilar mace, sam bai yi ba, ba karamar artabu nake sha ba, baƙin asiri a wurinta ba a magana. Kuma ke ma dai kin sani, kina ganin har gida na dawo jinya. “
Kai na jinjina a hankali ba tare da na ce komai ba, saboda tun kafin in yi aure na san irin yadda Samira ke shan fama da kishiyarta, har auran aka so rabawa amma Allah bai nufa ba. Sau uku Samirar na samun ciki yana zubewa, kuma an ce wai duk siddabarun kishiyarta ne. Duk dai an ce wai mai kishiya ba ya ciwon Allah. Amma tabbas kishiyar Samira tana da baƙin asiri.
Wayar na yanke, hade da
mikewa na nufi kitchen ina ta bitar miyar kuka
“Ya zan fara miyar kuka ta yi dadi ne? Duk cikin koyon girkin da na yi don zan zo gidan kishiya, ban ko yi miyar kuka ba, don gani nake kamar yanzu ba a yayinta.
Lokacina na bata shi ne kaf wajen koyon girkin zamani”
A zuciyata nake maganar a lokacin da nake tsaye cikin kitchen kamar na kayar da suruka.
Komawa na yi bedroom din inda na yasar da wayata.
Kawata Badiyya zan kira, na san yadda ta kware gurin cin tuwo miyar kuka dole ta san yadda ake yin mai dadi.
Wayar na fara ringing ta daga
“Ke ni ki bude baki, ki yi min magana sosai” Na yi maganar cikin muryar fada.
“Ki fadi me kike so ki fada ina jin ki?” ita ma ta ban amsa.
“Turo min yadda ake miyar kuka, da kayan hadinta yadda za ta yi dadi fa.”
Ina jin yadda ta yi yar dariya mai sauti, ganin ba ta da niyyar tsayawa na ce “Idan kin gama dariyar ina jiranki, sauri nake yi.” katse wayar na yi hade da debo shinkafar tuwo na fara wankewa.
Kamar mintuna uku, wayata ta yi haske alamar sako ya shigo, da sauri na bude sakon ina karanta yadda Badiyya ta rubuto min yadda ake miyar kuka.
Ban gama karanta sakon ba kiranta ya shigo
“Sakon ya shigo?”
“Eh” na ba ta amsa
“Shi ne ba za ki gode ba?”
“Kar fa ki dame ni don kawai kin koya min miyar kuka”
Dariya ta kuma yi kadan, kafin ta ce
“Wai ina littafin koyon girkinki?”
Tabe baki na yi kamar tana kallona, kafin in ce
“Ai wallahi in fada miki tun na zo gidan nan tsawon wata biyu, ban taba yin girkin da ke cikin littafin can ba ko sau daya.”
“To me ya faru?” ta tambaya.
“To duk ba haka tsarin gidan da abincin gidan yake ba. Shi ya sa ma ban gwada zan yi ba. Gara ma ranar can dana gidan ba kowa na gwada yin wani abu, na manta ma sunanshi ban iya ci ba wallahi, na faki ido na zuba a bola. Ko ban iya ba ne, ko kuwa dai haka yake ba dadi oho?”
Wata dariyar ta kuma saki, hade da fadin “Amma ke ba sai ki zo da na ki sabon salon ba”
“Ina jin tsoro Badiyya, in yi bai yi dadi ba, kin ga ai na fado kenan.”
“Wlh kam. Ga shi ba ke kadai ba, zama da kishiya akwai kalubale Khadija. Gara ma ke, abincinki kike yi ke kadai. Amma mu masu gabadaya muke tantancewa. Yau yara su ce kin yi basu koshi ba, jibi su ce babu dadi. Citta su ce ba ki gama da wuri ba. Kullum da sabuwar tsirfa.”
Haba na rike kamar tana kallo na, kafin na ce” Wato tukunyar dai tare ta tafasa? “
” Wlh kam. Don yanzu haka raina bace yake, kiranki ne ma ya dan warware ni. Yaron can Abbah sarkin gadara, shi ne yake yi min abin da ba na jin dadi, kai tsaye ki ji shi a kitchen dina yana min bincike, kuma ba damar in yi magana, Sai ace wai yaro ne in yi hak’uri zai bari”
Cikin sigar lallashi na ce “ki yi hak’urin to, komai zai wuce sha Allah.”
“Allahu Ya sha” ta amsa, kafin mu ka yi sallama. Duk jikina a mace, ashe haka aure yake, ko wanne da irin kalubalenshi, ba masu kishiyar ba, ba wadanda suke su kadai ba. Kanwata Yusrah da take ita kadai ma a gidan miji, ita ma da tata matsalar.
Haka na ci gaba da tattauna kalubalen da zuciyata, lokaci daya kuma Ina aikin tuwona.