Daga sallar magriba zuwa isha’i haka nan na yi su, ba don ina cikin nutsuwa ta ba, tun da na zo gidan, ban taba yin abin da na yi danasani ba irin wannan. Wata zuciyar fada min take yi in gudu gida kawai.
Dama ban yi tunanin zai shigo yi min sai da safe ba, Sai ko ga shi bai shigo din ba. Abin da ya kara dama min lissafi, duk soyayyata da bacci, yau dakyar na samu ya dauke ni, shi ya sa na tashi duk ba na jin dadin jikina. Hatta bakina testless ya zama
Yanzu abokin shawara nake nema, amma na rasa da wa zan yi ta, Ummana ba na son daga mata hankali, bai kamata ace mu biyu da ta aurar kullum cikin kawo mata Matsaloli muke ba.
Ga shi ba ni da wata yar’uwa ko kawa a Abuja bare in fada mata damuwata, don kuwa wannan matsalar ba ta waya ba ce.
Saboda gabadaya duk wata basira tawa ta kare, a duk lokacin da na yi kokarin daidaita abu, sai ya kuma lalacewa.
Haka na wuni zur ina sake-sake, har zuwa dare, lokacin da nake tsammanin shigowar shi, Sai ko ga shi ya shigo din, amma yanayin da ke kan fuskarshi, bai ba ni damar yin magana ba , dole na janye jikina, kila zai fi bukatar hakan.
Haka mu ka yi wadannan kwanakin, gaisuwa ce kawai ke hada mu, ya duba abin da babu a kitchen ya kawo, a haka ya koma dakinta, yayin da ya bar ni da kuka mai cin zuciya.
Kwanana ya kuma zagayowa. Wannan karon kam, na daura aniyar sasantawa, ba zan yi kasa a gwiwa wajen ganin na yanke wannan fushin na shi ba.
Abincin da ya fi so na yi, wato tuwo da miyar kuka. A aljihuna na cire kudi aka sawo min kaza na kawata miyar da ita.
Bayan na gama, na fita cikin dogon farin wandona jeans na mata da bakar riga mai guntun hannu, gaban rigar a bude haka ta zauna jikina hade da fitar mini da surar jikina. Dama ga matashin ciki ko ina ya kara cika tubarakhallah
Turare mai sanyin kamshin na sanya, bayan na manna kananan yankunne a kunnena.
Sosai na yi kyau musamman dana tsaya gaban mirror, cikina dan wata hudu kamar ba shi a jikina saboda yadda cikin yake a shafe.
Takwas daidai kuwa ya shigo, abin da ya sanyani farin ciki, duk da babu wata walwala a kan fuskarshi
“Sannu da zuwa.” na fada a daidai lokacin da yake zama a kan kujera.
Bai amsa ba, dalilin da ya kara tabbatar min da har zuwa lokacin dai fushi yake yi sosai.
Dukawa na yi a gaban sa hade da dora kaina a kan cinyarsa, na ci gaba da rera masa kuka, saboda ban da komai yanzu sai kukan.
Tsawon lokaci yana ji na, bai yi magana ba, ni kuma ban daina kukan ba.
Kila gajiya ya yi, kaina ya dago tare da fadin “Shi kenan ya isa” fadin maganar ta shi daidai da mikewarsa ya shige bedroom.
Ban yi kasa a gwiwa ba, na bi bayansa ina share ragowar hawayena
“Idan kin san kuka za ki yi min, please get outside” ya yi saurin fada ganin na nufi inda yake kishingide
Dakatawa na yi, hade da yin kalar tausayi, ni ban karaso ba, kuma ban koma baya ba.
Kamar 2mns muna a haka.
Kafin ya daga hannunsa hade da yafito ni “Zo nan.”
Na kuma langabewa sosai na karasa gurinsa.
Jikinshi ya janyo ni, hade da kwantar da ni sosai, ina jin yadda kirjinshi ke bugawa da sauri
“Khadija ki dawo cikin hankalinki, don Allah kar ki ɓata mana zama. ” A sanyaye ya yi maganar bayan ya kwantar da ni akan kirjinsa yana shafa bayana.
Ban yi magana ba, illa dai na dago hade share hawayen tausayin kaina, daga bisani kuma na koma na kwanta.
“Kina kokwanto ne a kan son da nake yi miki?”
Girgiza kai na yi alamar a’a
“To me ya sa kullum kike tuhumata a kan na fifita wata a kanki?”
“Ka yi hakuri don Allah, sha Allah ba zan kara ba.”
“Hmmmm!” kawai ya ce kafin shiru ya ratsa tsakaninmu.
“Ya kamata in sanar da ke wacece Sakeena a wajena, kuma ki san wacece ita.”
Ya yi maganar hade da janyeni daga jikinsa, wanda hakan ya nuna mun yana bukatar natsuwata.
Ni kaina ma ina son sanin wacece ita, kuma tun farko ma abun da ya kamata kenan in sani ta yadda zan san ya zan zauna da ita.
Dalilin da ya sa kenan na tattara hankalina ni ma kaf a kansa ina sauraronsa.
“Duk wani namijin da ya samu Sakeena a matsayin mata, to sai dai ya kara aure a matsayin sunnah, ba wai don gazawarta ba.”
Ya yi maganar idonsa a cikin nawa.
“Ni ce zan ba wani labarin hakan, don kuwa ni ma da nake mace kuma Sakeena take matsayin kishiyata, sosai take burgeni da halayyarta, har ina jin ina ma ni ce ita. To bare kuma namiji” a cikin zuciyata nake maganar a zahiri kuma shiru na yi
“Wani irin zama ne muke yi da Sakeena mai cike da kauna, sadaukarwa, kyautatawa, kawaici, taimakeninya da kuma fahimtar juna.” Ya dan tsagaita hade da kallona, ni din ma shi nake kallo bayan da na rungume hannayena a kan kirjina.
“Ko wanne fanni Sakeena kwararra ce, girki, iya mu’amala, tsafta, kwalliya kula da, gida, babu wanda Sakeena ba ta kware ba.”
“Dangina basu da matsala da ita, ta iya zama dasu da tafiyar dasu yadda ya kamata duk kuwa da yawansu.”
Jijjiga kai na shiga yi, don ni ma na san gaskiya ya fada. Babu inda ya yi kari.
“A yadda muke zaune da Sakeena babu wanda ya taba tsammanin zan yi mata kishiya, saboda ta ba ni komai. Akwai hidimomi masu yawa na gida da ni sam na manta dasu ma ita ce ke yi.”
Na kuma Jijjiga kai alamar gamsuwa.
“Ke hatta matsalolin dangina wani lokaci ita ke magancesu, sai dai in ji an ce an yi ka za, da na ji na san ita ce ta yi.”
“Eh Sakeena ta same ni da abun hannuna amma ni ma da nata na sameta, na dan ciccibata ne kadan. Babu wani raini ko gori a tsakaninmu, tana da hakuri sosai, zan yi mata laifuka masu yawa, amma ba za ta yi magana ba, ni da kaina wani lokaci nake zaunawa in ba ta hakuri hade da yi mata ihsani da zai sa ta manta da wuri. Babu wanda za ki ji a yan’uwanta ko yan’uwana ya ce ta kai mishi korafina “
Hannuna a kan haba nake sauraronsa.
“Ban ce miki ba ma fada ba fa, muna yi sosai ma, don tana da zuciya idan aka kureta, ba ta ki a mutu ba. Kin san an ce mai hakuri bai iya fushi ba. “
“Wannan haka ne” a karon farko da na yi magana.
“Mun sha yin fada, fada sosai, wani lokaci mara dadi da kyan gani ma. Na sha amfani da wannan hannun na mareta, kin san ni ma ina da zuciya da saurin fushi” ya yi maganar hade da daga hannun nasa yana wani irin murmushi.
Ido na zaro ina ma sa kallon mamaki
“Yes!” ya fada alamar tabbatarwa
Shiru na yi komai ban ce ba. Shi ne ya dora da
“Da can ni namiji ne mai hange-hange, na yi yan’mata kala-kala masu addini da marasa shi. A lokacin Khalil kawai Sakeena take goyo, ba sai na fada miki halin da mace kan shiga idan ya kasance mijinta yana neman mata ba. To irin wannan halin Sakeena ta shiga, ta rame, ta lalace ta fige yayin da ni kuma hankalina yake a kwance.
Ba kunya wani lokaci nake kwana a waje da safe kuma in dawo ina mazurai, wani lokaci ta yi magana wani lokaci ta yi shiru. Sakonnin yan’mata, hotuna, babu wanda Sakeena ba ta kama a tare da ni ba.”
Ya dan tsagaita hade da kallona, yayin da ni ma shi nake kallo cike da mamaki
Sosai na tsorata da abin da yake fada min, don kuwa bai yi kama da wanda zai iya aikata haka ba.
Ganin ba ni da niyyar magana ne ya sa ya ci gaba.
“Sam! Ba ni da lokacinsu ita da Khalil lokacina daga aiki sai rayuwar dana sanya a gaba, aikin da take ya taimaka mata matuka, saboda ba ta tambayata komai sai idan ni na yi niyya na ba ta. Sai in fi karfin wata ban hada shimfida da ita ba.”
Ya kuma dago kai ya kalleni, ni ma shi nake kallo cike da mutuwar jiki, yayin da tausayin Sakeena ya kama ni, ni ma nan da Allah ya halatta mishi Sakeenar haushi da kishi nake in gansu a tare ina kuma ace yana tarayya da mata a waje. Kila zan yi ta suma ne kullum. Amma ita baiwar Allah ta jure ta kuma shanye. A hakan ma bai kyale ta ba, Sai da ya hada ta da kishiya wato ni.
“Mun sha rikici ba kadan ba, ta matsa lallai sai na sake ta, ni kuma na ki yin hakan, watarana sai ga ta da condom wai gudunmuwa ta kawo min, tun da na ki sakinta, in kare lafiyarta” ya karasa maganar cikin wani kalar murmushi da na kasa fassarawa.
Ko motsi ban yi ba, hakan ya sa ya ci gaba
“Karon farko a rayuwata da na fara bude baki na zageta,, na ce ta mayar da ni mazinaci, na rika shiga ina fita cikin masifar nade tabarmar kunya da hauka, saboda ai ta sha kama condom din a cikin kayana, sai in ce a office namu ne ake rabawa. Wani lokaci ta ce “Saboda an san halinku, a rasa abun arzikin da za a raba maku sai condom” wani lokaci kuma shiru take yi”
Ya sauke ajiyar zuciyar da ke nuna tsantsar nadama a kan fuskarsa
“Har na gama bala’ina ba ta ce komai ba, tana zaune a gefen gado hannunta rike da condom, da ta fahimci na yi masifar mai isata, sai ta mike ta aje condom din a aljihun jakar da nake zuwa office ta yi ficewarta. Abin da zai ba ki mamaki shi ne daga karshe dai na yi amfani da condom din da ta ba ni.”
“Kuma ta gane ka yi amfanin da shi? ” Na Jefo mishi tambayar cikin zakuwar jin amsarta.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya ce” Ranar na shigo gida misalin 12 saura na dare , ina toilet na ji alamar ta shigo dakina, lokacin da zan fito sai na sameta hannunta rike da jakata”
“Lafiya na tambayeta?”
Ba ta yi magana ba illa ta koma gefen gado ta zauna hade da bude gurin da ta sanya condom, sosai gabana ya fadi a lokacin.
Ba jimawa kuwa ta zaro ragowar condom din guda uku da ya rage ta ce
“Balan-balan ka yi da sauran ko ruwa ka dura kana wasa?”
Ta yi tambayar hade da tsare ni da ido.
Na fara kame-kamen na ba abokina ne kyauta, sai kawai ta fice daga dakin.
Hannuna a kan haba nake kallonsa, yayin da bangare daya nake tausayawa Sakeena, gaskiya ta yi hadiya kamar maciji. Wato kai dai ga mata da miji, su suka san yadda suke zaman auransu, ni dai ina ji a jikina ba zan iya wannan ba.
“Irin wannan kalar labarin ba zai kare ba. Ita din jaruma ce. Duk wani abu da zai faru a nan gaba, ba kamar na baya ba ne. Ita a yanzu take jin dadin zama, shi ya sa za ki ga kamar babu wani abu na bacin rai da ake yi mata. To ai ta hadu da abun yafi, abin da yake faruwa yanzu”
Ni bakina tuni ya kulle sai ido.
Yayin da shi kuma yanayin ya kara canjawa sosai alamar rashin jin dadi, kafin ya ce
“Watarana ina tare da sabuwar budurwarta kiran Sakeena ya shigo wayata,, kamar in daga sai kuma na fasa, don sai mu fi wata ba ta kirani ba, idan har zan ga kiranta to na san matsala ce, ni kuwa bana son abin da zai yanke min jin dadina a lokacin.
“Ta ci gaba da kira, ni kuma ban daga ba, can sai ga sakon ta kamar haka.”
Khalil ba lafiya don Allah ka zo ka kai mu asibiti”
“Na karanta sakon nata hade da aje wayar, na san halinta akwai rudewa a kan ciwon yaro kila ciwon bai yi zafi ba amma duk ta rude. Ban kashe wayar ba haka ban tafi ba.”
“Da misalin karfe biyar na yamma na fita da Ruky don yi mata shopping kawai na hadu da Maman Khalil da kawarta Rahma na rungume da Khalil yayin da Sakeena ke rike da ledar magunguna…”
“Subhanallah!” na yi saurin katse shi, kafin ya yi magana na kuma cewa “To ya ka yi?”
“Yadda ba ta min magana ba, haka ni ma ban yi mata ba, suka tare napep, ni kuma na shige mota da Ruky, sosai Rahma ke ta kallona, don har tuntube ta yi saboda kallona.”
“Dole kam” na yi maganar a sanyaye
“Daurewa kawai na yi na shiga gida misalin goma na dare, dole dakinta na wuce. Zaune take kan sallaya hannunta rike da alqur’ani tana karantawa. Ji na yi jikina duk ya mutu don rabon da in dauki Qur’ani da sunan karatu har na manta lokacin. Ni kaina wani lokaci na san ba a kan daidai nake ba.
Khalil na nufa da niyyar taba jikinsa, amma kamar fitar kibiya haka na ji Sakeena ta hankade ni gefe, lokaci daya kuma ta zuba min idanunta da ya canja zuwa kalar bacin rai tsantsa, tsana da kiyayyata da kuma kyamata kawai nake hangowa cikin idanun nata.”
Ya dan numfasa kadan, kafin ya dora da
“Kar ka sake ka taba min yaro Bashir! Sai yanzu ne ka ga sakonmu? Yanzu ne ka tuna kana da yaro? Yanzu ka ji ya kamata ka waiwayi lafiyarshi? Tur da kasancewarka mahaifin Khalil, na tsani zama da kai Basheer na tsaneka, ka fitar min daga daki.” Haka ta rika fada min cikin hargowa mai tattare da bacin rai
“Na yi kamar ban ji gargadin nata ba, na nufi yaron a karo na biyu.”
” Fittt! Na ga ta fitar da sabuwar wuka daga kan mirror, sannan ta tsaya inda yaron yake tana fadin
Wallahi idan ka kuskura ka matso nan sai na farke cikinka
“Sosai abun ya ban mamaki, saboda na fahimci za ta iya aikata hakan a kwayar idonta
Rikici mu ka yi sosai a wannan dare, wanda har ya yi sanadiyyar da na wanketa da mari bayan na yi amfani da karfi wajen karbe wukar hannunta. Karon farko da ta hada kayanta da niyyar yaji”
Haka nan na ji idanuna sun cika da kwalla, saboda ina jin daci da zafin abun a zuciyata. Ji nake kamar ni ce aka yi wa haka. Ga mari ga tsinke jaka kenan.
“Ai tun farko ya kamata ta yi hakan” na yi maganar cikin kunar rai hade da dauke hawayena.
Jikinshi ya janyo ni hade da bubbuga bayana alamar lallashi kafin ya ce
“To ai dalilin da ya sa kenan ki ga ina mutuntata ba na son bacin ranta, don kuwa duk cikin Yan’uwana ko nata ba na jin wani ya san halin da muke ciki, amma kawarta Rahma ta sani, na san Maman Khalil ta yi kokari sosai wajen shiryuwata, ta hanyar hana idonta bacci don yi min addu’ar shiryuwa, yanzu kuma ga shi na shiryu, rayuwar ba ya ba ta burgeni, har na kuma cin karo da wata abincin ruhin nawa.”
Ya kai karshen maganar tare da dago kaina, yana yi min wani irin kallo.