“Kin san me ya sa na fada miki duk wannan?”
Ya yi maganar hade da dago kaina da ke kan kirjinshi
Kai na girgiza alamar a’a
“Ina son ki sani ko wane da kalar kalubalenshi a zaman aure, idan kika ji na wani, ba za ki iya dauka ba. Sannan da yawa ku 2nd wife din nan bonus kuke samu fa. Uwargida ta gama yi muku duk wani aiki, kila ita ce ta sha wahalar talaucinshi, ta biyu ta ci arzikinshi. Kila ita ta sha wahalar kuruciyarshi ta biyu ta samu dattakonshi”ya tsagaita hade da kallona.
Ganin komai ban ce ba ya sa ya ce “Ina sonki sosai Khadija, son da ba zan iya rabuwa da ke ba, kuma ba na son ganin bacin ran ki. Hakan kuma ba ya nufin ba na son Sakeena, bayan so akwai shakuwa irin ta ka dade da mutum din nan . Ki yi hak’uri ke ma za ki ta ka wannan matsayin but a hankali.”
Kai na jinjina alamar na fahimta
“Ina son ki zauna da ni fiye da yadda Sakeena ke zaune da ni.”
“Ahhh! Karya da ciwo mari da zafi ba zan iya ba, Sakeena bugun da ce, mu kuwa bugun zamani” A zuciyata na yi maganar a zahiri kuma sai na ce
“Zan iya yin hakan muddin ni ma za ka rika nuna ni matarka ce”
Ido ya zaro cike da mamaki “Yanzun don Allah bana nunawa, cikin jikinki na waye?”
“Naka ne, kuma ai anan din ne kawai na san ni matarka ce” na yi maganar hade da tura baki
“Za ki fara ko?”
“A’a.” Na ba shi amsa hade da mikewa a karo na biyu ina fadin “Mu je ka ci abinci.”
“Me kika dafa min?”
“abin da ka fi so”
“Tuwo?” ya yi tambayar a lokacin da yake sakkowa daga saman gadon, lokaci daya kuma mu ka jera zuwa falon
“Exactly” na ba shi amsa ina murmushi
“Kin san kuwa kin iya murmushi, kuma yana kayatar da fuskarki?”
Na dakata da zuba mishi miyar ina kallonshi cikin wani murmushi, da kuma wata sabuwar kaunarsa da na ji tana ratsa duk gabobina.
Don kuwa maganar ta yi min dadi.
“Don Allah jira a haka in yi miki hoto”
Maimakon cin abincin sai muka bige da yin hotuna kala-kala, sai wajen goma da rabi mu ka fara cin abincin.
Can dare kasa bacci na yi, mamakin labarin da ya ba ni nake yi, na godewa Allah lokacin da na zo ya shiryu don ni ba zan iya juriyar Sakeena ba gaskiya. Yanzu ma ina jin zafi, bare ace presently yake faruwa da ni.
Shi ya sa ya iya tafiyar da mace ashe ya ɗan taɓa bude idonshi. Duk irin zafin mace sai idan ba ta shigo hannu Basheer ba,, har mamaki abun ke ba ni, a shekarunsa amma ya iya salo-salo na janye hankalin mace.
Wanshekare ma Maman Khalil a gida ta bar Oga, amma kuma ban bari ta tafi da Ramla ba karbeta na yi.
Na fahimci tana jin dadi sosai idan na ja yaranta a jikina, abin da ba ta sani ba shi ne, Ita Ramla har cikin jinina nake jin sonta, ko wuni na yi ban ganta ba sai in ji duk na damu, bana gajiya da ita.
Bai fita gidan ba sai 12 saura na rana, a lokacin kuwa ina ta hidimar abincin rana Ramla na barci.
Dambun shinkafa na yi, ya ji zogale carrot da kayan miya, na soya man gyada hade da daka kuli-kuli da ya sha citta.
Na kammala komai a kan tebur sannan na shiga wanka.
Doguwar rigar atamfa mai ruwan hoda na sanya, wacce ta sha adon duwatsu tun daga sama har kasa.
Sai da na gabatar da sallahr azhar sannan na zauna gaban madubi ina murza mai.
Karar bude kofa ya sanyani saurin juyawa, shi ne ya shigo dauke da Ramla
“Ta tashi?”
“Ina bude kofa ta tashi.”
“Ka ce dai kawai kai ne ka tayar min da yarinya”
Cikin murmushi nake maganar, lokacin daya kuma na katse shafa man da nake ina niyyar daukarta
“Wani fresh kike yi fa, Abuja ta karbeki.”
“Abun kuma har da tsokana” na yi maganar a daidai lokacin da nake shiga toilet don watsawa Ramla ruwa, don ana zafi kadan
“Yunwa fa nake ji, ku mata idan kuka yi yara shi kenan duk kulawarku sai ku mayar da ita a kan yaran” cikin zumbura baki ya yi maganar wai shi shagwaba
Sosai nake dariya a lokacin da nake yi wa Ramla wanka
“To wai kishi kuke?”
“Kishin ma ai sai mu yi, tun da na shigo fa hankalinki a kan yarinyar nan yake, kalli kuma kin bar ni tsaye wai kina mata wanka, ki gama ki ce shirya ta za ki yi, to ni a tsaye zan kare kenan?”
Na kuma tuntsirewa da dariya “To ba ga shi har an gama wankan ba” Na yi maganar ina dora Ramla a bayana.
“To mu je falon ranka ya dade Alhajina” komai bai ce ba ya juya zuwa falon
Bayan na zuba mishi Dambun da yake ta santi tun kafin ya ci, kan kujera na koma ina shirya Ramla, rising powder kawai na sanya mata a wuya, na dakko guntun wando na jeans wanda iyakarsa rabin cinya na sanya mata hade da farar singileti. Saboda kayanta rabi duk suna dakina.
Sosai ta yi kyau, don haka na dakko waya ina mata hoto, Babanta na kallonmu cike da kauna.
Daga bisani shi ma wayar ya dakko yana mana.
Sallamar da aka yi ce ta dakatar damu, lokaci daya kuma mu ka mayar da hankalinmu wurin kofar shigowa.
Su Khalil ne da Affan suka shigo ko kayan makarantar su ma basu cire ba
“Yarana kun dawo?” na tambayesu, ina kallon yadda suke ta ɗokin ganin Ramla kamar sun shekara basu ganta ba
“Ehhhh!” suka amsa ba ki daya lokaci daya kuma suna ba Ramlan tsarabar sweet, da biscuit.
“To ku mu je kuma ku yi wanka sai mu ci abinci.” na dakatar da wasan da suke niyyar farawa
“To! Ni bari in je in nemi wurin bacci don ba za ku bar ni in yi bacci ba.” Abbansu Khalil ya yi maganar hade da mikewa tsaye daga kan dining din
“Dady ina wuni?” yaran suka fada yanzu hankalinsu a kansa.
“Sai yanzu kuka ganni?”
“Da gaske kana da kishi” cikin dariya na yi maganar, lokaci daya kuma ina tasa keyar yaran zuwa toilet
“Ka yi hakuri muna gama wanka zamu fita sai ka y baccinka” na kuma fada wanda ya yi daidai da shigewarmu cikin toilet.
Wankesu na yi fes, na murza masu mai mara maiko, su ma na basu guntun wando da vest suka sanya, don su ma akwai kayansu kadan a wajena.
Dambun na zuba a babbar kula hade da daukar robar yaji na ce su mu tafi bangaren Momynsu.
A kitchen muka sameta tana ta kiciniya, saboda yar aikinta ta je ganin gida, kodayake ko tana nan ma, nata wanke-wanke ne sai mopping da shara, mopping din ma watarana Maman Khalil din sai ta sake.
Kullum cikin fada suke da yar aikin, wai ba ta yi mata aikin yadda take so.
Ta fadada fara’arta tana kallon yaran cike da kulawa, “Auntyn Ramla ce ta maku gayu?”
(Haka yaran ke kirana Auntyn Ramla)
Dukkansu suka amsa da “Ehhh”
Mika hannu ta yi hade da karbar kular hannuna
“Wowww!” ta fada bayan ta bude
“Yau kam kin yi babban masoyina aiko zagina za ka yi kuma ki ba ni dambu zan amsa wallahi” Ta kai karshen maganar tata hade da fitowa daga kitchen, tare muka shiga falo da ita
A kasa na zauna, hade da kwantar da Ramla a kan cinyata ina warware mata kitson da ke kanta.
“Wai wani kitson za ku sake kuma?” ta yi tambayar a daidai lokacin da suka zagaye plate din dambu ita da yaranta suna ci
“Eh”
“Kuma dai gashin ba fitowa zai yi ba,, irin yadda kuke so din”
Dariya na yi kafin in ce “Amma ai ba a cewa Ramla ba ta da gashi kuma, sannan zamu baku mamaki”
“Ni ce zan ba ku mamaki, yayeta zan yi”
Na yi saurin kallonta hade da dakatawa daga tsifar kan da nake yi ba tare da na ce komai ba
“Da gaske gobe zan Yayeta, ta sha da yawa ai” Cikin murmushi take maganar.
“Haba don Allah, duka watanta nawa?”
” Sha shidda fa”
“Har ta yi sha shidda?”
“To ki lissafa,, lokacin da kika zo watanta goma ke kuma yanzu watanki shidda”
“To ki bar ta ta kai sha takwas mana” na yi maganar cikin maraicecewa
Dariya ta yi kafin ta ce “Allah ya isheni haka nan”
“Eyyahhh Momy ki bar ta ta kai sha takwas mana” Cewar Khalil da ya cika baki da dambu
Muka tuntsire da dariya kafin ta ce “ji shi kamar ya san abin da ake magana a kai”
A bangarenta na yi sallahr la’asar, mu ka yi homework da su Khalil sannan na baro bangaren, inda na sanyawa raina ni ce zan yaye Ramla.
Kashegari kuwa da ya kama Juma’a sai ga ta da kayan yaye irin su Bobo, kwai, kayan tea, happy hour na yara, pampers ƙaramin flask, biscuit da cheese.
“Wannan duk kayan yayen ne?”
Na tambaya a lokacin da nake tattabasu
Dariya ta yi, amma ba ta ce komai ba
“Allah sarki mutanen kauye, wallahi yaransu na ganin rayuwa idan za a yayesu, yaro ya tashi cikin dare yana kuka a mika mishi tuwo ko koko me sanyi, amma ji wai nan duk kayan yaye ne kamar za a bude shago.” na yi maganar a zuciyata, a fili kuma sai na ce
“Ina za ki kai Ramlan yaye?”
“Ba ko ina, dama kawata Rahma ke yayesu to yanzu kuma ba ta nan, suna waje ita da mijinta”
“To ni zan yayeta.”
Waro ido ta yi hade da zuba su a kaina, ba tare da ta ce komai ba.
“Da gaske nake fa”
“Don Allah ki ji da kanki, yaushe za ki iya da rigimar yaye?”
“Ba za ta yi min rigima ba” cikin dariya na yi maganar.
Ita ma dariyar take lokacin da take fadin “Don Allah rufa min asiri”
“Kin san Allah ni zan yayeta a cire maganar wasa.”
Kallo na take yi cikin ido cike da mamaki.
“Gaske nake fa”
“To ai shi kenan, idan ta dameki ai kya maido ta”
Murmushi na yi ina tuna shawarar Samira da Badiyya lokacin da na fada masu matsalata, masalaha ta farko da suka ba ni, shi ne in ja yaranta a jikina, in rika kyautata masu, mai ɗa mahaukaci ne, muddin ina hakan, zan saye zuciyar mijina, ta kishiyata da kuma yaran, sannan zai wahala ya rika ganin laifina, dalilin da ya sa kenan nake son fara yi masu bauta, tun da na fahimci muddin ka auri mai mata da yara sai ka zama kamar bawa. Ko ba komai za ka samu karɓuwa wurin miji.